Showing 216001 words to 219000 words out of 221978 words

Chapter 73 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

muryarsa da yay sallama ya sakasu juyowa gaba ɗayansu lokaci guda suna kallonsa. Yayinda shi kuma nashi idon ke akan Oum datai wata zabura har tana ture hannun Babban Yaya dake bata abinci, abincin daya ɗibo a spoon ya zube musu a jiki ita da shi. Hawaye ne suka ciko idannunta dake kallonsa, ta nunashi a hankali lips ɗinta na rawa. “Ajwaad! Da gaske kai ne ka dawo? Ko mafarkin dana saba yi ne Fadeel?”.
Kafin wani ya samu bata amsa AA da nasa idanun suka kaɗe ya shiga takowa a hankali, gefenta ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaɗarta, cikin wata irin murya mai rauni sosai ya furta, “Oum ki gafarceni. I miss you, really really miss you”. Sai kawai ya kife kan nasa a kafaɗar tata, tana mai jin damshin hawayensa na sauka mata. Itama sai hawayenta suka shiga sakkowa a guje, tasan a duk duniya abinda zai saka Ajwaad ɗinta hawaye ba ƙaramin abu bane ba. Gefe Mamy ta kauda kanta, zuciyarta na mata wani irin ƙuna, jitai sam bazata iya daurema zaman ɗakin ba, sai kawai ta nufi hanyar fita. Da sauri Nibras da Saheeba da suka biyo bayan AA suka bata hanya ta fice.
Abah kam ajiyar zuciya kawai yake faman saukewa da godema ALLAH. Dan shi kansa kwana biyun dannewa kawai yake yi, amma yana cikin matsananciyar damuwa akan batun AA ɗin da halin da Oum ke ciki. Yana dannewa ne kawai baya nunawa a zahiri. Su kansu su babban Yaya tausayin Autan nasu ne ya sake shigarsu, duk da suna jin haushin abinda ya aikata ɗin. Bayan AA ya ɗago ya share hawayen Oum ya juya yana bama Abah da su Babban Yaya haƙuri suma. Babu wanda ya nuna masa komai dan a ganinsu babu amfanin hakan, tunda har ALLAH ya dawo musu da hankalinshi gidan batare da ankai wani mataki ba ai Alhamdullah. Dan danan sai ga Oum ta ware kamar ba ita ba, taci abincin sosai tasha magani. Shima kuma ta tsareshi yaci abinci dan duk ya faɗa nata a ido.
Sai da komai ya nitsa yaje sashensa har yay wanka sannan Abah ya zauna da su, AA ya sake bada haƙuri tare da neman gafarar su, musamman Mamy data nuna fushin ta a fili, harda tabbatar da cewar wai tana fushin ne saboda halin daya jefa Oum a ciki. Al'amarin Mamy na bama AA mamaki da tayar masa da hankali, shin wace irin zuciya ce da ita? Miyasa ta zaɓi irin wannan rayuwa ga waɗan da suka aminta da ita. Miyyasa shi ta yarda ta nuna masa ainahinta sauran ƴan uwansa kuma taƙe musu lulluɓin biri da mahaifinsu da Oum? Amma ba komai, yayi alƙawarin cigaba da rufa mata asiri, da mata addu'a da nasiha ko hakan zai sa ta gane, dan har abada baya fatan ace Oum da Abah sun gane wacece Mamy, ya tabbatar zuciyar Oum zata iya bugawa.
Nasiha sosai Abah yay musu daga ƙarshe ya ɗakko batun zuwansu Kano da batun kai kuɗin auren Rafeeq gidan su Maanal. A mamakin kowa sai sukaga AA yayi murmushi mai sanyi, babu alamar damuwa a tare da shi ya ce, “ALLAH ya sanya alkairi”.
A firgice Oum data kasa daurewa ta ce, “Ajwaad! Maanal fa akace an kaima kuɗin aure, kuma Rafeeq?”.
Kansa ya jinjina batare da ya yarda ya kalla kowa ba ya ce, “Eh Oum naji, Rafeeq mutumin kirki ne ai, na tabbatar zai riƙe min ƙanwata da mutuntawa, dan haka ina musu fatan alkairi”.
Babu wanda baiyi mutuwar zaune ba a falon. Baki sake Abah da Oum suka kalla juna, hakama Fawzan da Babban yaya kallon AA ɗin kawai suke. Mamy tai ƙasa da kanta tana sakin wani ɓoyayyan murmushin cin nasara, koda suka haɗa ido da AA sai ta lumshe masa ido. Kansa kawai ya maida ya ɗuƙar...........✍️




09032345899


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖9️⃣4️⃣




______________






..........“Nifa wannan yanayin na Ajwaad ya fara bani tsoro babban Yaya. Anya babu abinda ke damun yaron nan? Ko wanda bai san alaƙar baya data shuɗe tsakaninsa da Maanal ba ya kalli idanunsa yasan akwai soyayyar ta a ciki, amma batun aure yaƙi ya amsa. Wannan abu na birkita min tunani”.
Nannauyan huci Babban yaya ya furzar, idanunsa akan Fawzan ya ce, “Bakai kaɗai ba, ni kaina a wannan gaɓar zuciyata ta fara shiga nazari. Fawzan mu dukanmu mun san soyayyar Maanal ce ta hana Ajwaad aure, ka duba kaga jiyyar da yayi, yasha wahala matuƙa, amma ace yanzu haka na faruwa? Wlhy nayi zaton duk randa Ajwaad ya haɗu da Maanal sai yasa an ɗaura musu aure a washe gari koda tsiya-tsiya”.
“Kowama irin wannan hasashen yake yi Babban Yaya. Amma kaga yanda abubuwa ke tafiya.”
“Yanzu yana ina?”.
“Ai sashensa ya nufa”.
“Inaga muje mu sameshi”.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Abah dake bayansu batare da sun sani ba ya sauke. Yayinda zuciyarsa ke faman kai-kawo. Tabbas shima a yau irin tunaninsu yake yi, dan al'amarin Ajwaad ɗin ya fara bashi tsoro, yaro kamar mai aljanu. Yayi zaton a wannan zaman da sukayi yanzu zai amsa abinda suke buƙata ne koda jin abinda ke shirin faruwa. Shin mike faruwa ne? Mike damun yaronsa?. Da wannan tunanin ya juya ya koma sashen Oum.
A hankali Saheeba ta fito daga maɓoyarta itama. Ta riƙe ƙugunta da duka hannayenta biyu tana hararar sashen Oum, sai kuma kamar wadda aka tsikara zaram ta zabura hanyar sashen AA. Dan ya kamata tasan mi su baban Yaya zasu tattauna da shi anan ɗin ma....


______★


A bazata sallamar su Babban Yaya ta shiga kunnen AA dake bedroom ɗinsa. Sai da ya ɗan rumtse idanu kafin ya miƙe cike da ƙarfin hali daga kwancen da yake a cikin sofa dake a bedroom ɗin. Tissue ɗin daya zubar a saman lallausan carpet ɗin gaban kujerar fari tas yasa hannu ya tattare. Toilet ya nufa da su ya zuba a dusbin ɗin can, dan baya buƙatar kowa ya gani daga abinda ke jikinsu. Bayan ya wanke hannunsa da fuskarsa ya fito daga bayin, ruwa ya ɗauka yasha sannan ya daidaita yanayinsa ya fita. A bakin ƙofa suke tsaye har yanzu, sai kawai ya basu hanya suka shiga. Saman sofa ɗin ya koma ya zauna, su kuma suka zauna a bakin gadonsa duk idanunsu a kansa.
Fuska ya ɗan yamutsa, tare da shagwaɓe ta cike da son danne komai ya ce, “Wai lafiya kuke kallona?”.
Babu wasa sam a fuskar Fawzan ya ce, “Ajwaad mike damunka ne?”.
“Kamar ya? Yaya Fawzan”.
Harararsa Fawzan ɗin yayi, kafin Babban Yaya ya amshe da faɗin, “Ajwaad ka tsaya da pretending ɗin nan naka haka nan. Munzo nan ne domin tambayarka. Kuma gaskiya muke buƙatar ji. Shin akwai wani ne dake maka barazana akan lamarinka da Maanal shiyyasa ka kasa amsar aurenta duk da soyayyar da kake mata”.
Wani irin girgiza zuciyar AA tayi, amma da yake namijin duniya ne sai ya danne. Idanunsa a cikin na Babban Yaya ya ce, “Barazana kuma Babban yaya? Ni kuma wani zaima barazana kamar ƙaramin yaro. Kawai dai ku kun kasa fahimtata ne tun farko. Yarinyar nan ina mata kallo ne tamkar ɗaya daga cikinmu. Ina mata soyayya ne irin ta ƴar uwa ƙanwa ciki ɗaya, shin miyasa ku kuke fassara hakan da wani abu daban.....”
“Ƙarya kake Ajwaad, wlhy son Maanal kake soyayya irin ta aure, soyayya irin wadda baka taɓa yima wata ba a duniyar nan idan aka cire iyayenmu. Soyayya kake mata irin wadda zaka iya rasa rayuwarka ma idan babu ita a ciki. Kalleka Ajwaad, kalla yanda ka zabge a kwanakin nan. Sannan a kwankin baya na bayyanar Maanal sosai hankalinka ya kwanta, farin cikinka ya dawo. Idan kuma ba haka bane ka rantse baka sonta, mu kuma mun maka alƙawarin barin ka, ko kuma ka fidda matar aure mana!!”.
Cikin matuƙar pretending AA ya miƙe yanama Fawzan da yay maganar fusataccen kallo. “Anƙi a rantse ɗin, shin Yaya Fawzan kai ubana ne da dole saika titsiyeni na amshi abinda kake so, kai kaje ka aurenta mana ko an hanaka ne. Nifa bana son takura!!”.
A fusace shima Fawzan ɗin ya miƙe, yaje gaban AA ya tsaya yana kallonsa cikin ido. A matuƙar kausashe ya ce, “Hummm Ajwaad kenan, ka godema ALLAH zuciyata a matsayin ƙanwa kuma masoyayyar ƙanina take kallon Maanal, amma wlhy da sai na baka mamaki a wannan gaɓar, da sai naje na auri yarinyar nan naga yanda zakai. Kuma ko a yanzu, da ace wani abu bai taɓa shiga tsakanin kai da ita ba na ƙaddara wlhy da sai na aureta ɗin, sakarai kawai mai mugun hali”.
Ya hankaɗesa ya wuce fuuu. Wani irin masifar rawa jikin AA yake yi, gaba ɗaya fuskarsa ta gama birkicewa. Cikin ɓacin rai ya kalla Babban Yaya da kamar al'ajabi ya sashi suma shi kam. Fawzan mutum ne mai matuƙar haƙuri, nuna fushinsa akan Ajwaad yau ɗin nan ya girgiza babban Yaya. Sannan abubuwan Ajwaad ɗin sun sake birkita masa tunani. Kamar AA ɗin zaiyi magana sai kuma ya fasa. Fuuu ya zagaye Babban yaya ya wuce bathroom ɗinsa. Yanda ya wani bugo ƙofar da masifar ƙarfi ya dawo da babban Yaya hayyacinsa. Ya jima yana kallon ƙofar bayin kafin ya fita jiki a sanyaye, dan shifa zuwa yanzu ya fara wani kuma tunani daban....


AA kam yana bugo ƙofar a jikinta ya manne, ya wani kalar runtse idanunsa da suka gama juyewa. A saman lips ya furta, “Kayi haƙuri Yaya Fawzan kayi haƙuri kaji”. Zuuu wani damshi ya gangaro daga hancinsa, yasan minene, dan haka bai damu da buɗe ido ya kalla ba, haka abin ya cigaba da zirara masa akan gashin gemunsa har zuwa ƙirjinsa sai da yaji jiri na neman kada shi a wajen kafin yaja ƙafa da ƙyar zuwa ƙarƙashin shower ya sakar ma kansa ruwa. Ya jima a haka kafin ya fito da ƙyar, a haka jikinsa na zubar ruwa da sumar kansa ya faɗa saman gado yaja bargo ya ƙudundune. Dan wani irin sanyi yake ji da zazzaɓi da ciwon kai.


★Tuni Saheeba ta kaima Mamy rahotan abinda ke faruwa tsakanin Fawzan da AA. Dan haka hankalinta ya ɗan so tashi, Fawzan nada haƙuri sosai a cikin yaran, amma idan yay fushi koya ƙwafama abu sai fa yasan asalinsa da tushensa. Bata buƙatar kowa ya fahimci wacece ita a tsakanin shi da Fadeel a yanzu sai anyi auren Ajwaad, dan agaɓar take son fara shirinta na dawowarsu hannunta. Dan haka ta miƙe, bedroom ta nufa ta ɗauka waya tai kiran layin AA, sai da tana gab da tsinkewa ya ɗaga, duk da yanda taji muryarsa ya motsa zuciyarta amma sai ta dake. Maganganu masu zafin gaske da dogon gargaɗi taja masa akan ƴan uwan nasa guda biyu, batare da jiran cewarsa ba ta yanke wayar.
A karo na farko al'amarin Mamy ya saka AA sakin murmushi mai ciwo. Kowa da tashi jarabawar a rayuwa, su kuma mahaifiyarsu ce tasu jarabawar. ALLAH ya basu ikon cinyewa. Musamman ma shi da ya daɗe da sanin wacece ita a duniyarsu. Bawan ALLAH haka yasha fama cikin zazzaɓi har dare, koda Oum ta kira shi a waya sai yace mata barci yake. Data bukaci yazo yaci abinci yace a kawo masa kawai sashensa zai ɗan yi wani aiki ne. Bata kawo komai a ranta ba duk da itama dai halin da take ciki na tunani da neman mafita akan al'amarinsa da Maanal yasa bata so yazo ya ganta a yanda take. Gefe ga gargaɗin Abah na tada mata hankali. Amma babu yanda zatayi...


*_JUMA'A_*


Ranar juma'a jirgin ƙarfe goma suka bi zuwa Kano. Kowa ka gani a cikinsu sam babu walwala a tare da shi. Sai ma AA ɗin ne ke ɗan nuna dakiya. Sai dai a kallo guda zaka fahimci yanda yay wata irin zabgewa ta rama a tsaye. Sai manyan idanunsa da suka sake fitowa fatarsa ta sake haske ga gashin fuskarsa ya fara taruwa fiye da yanda yake barinsa dan yaƙi yay gyaran fuska. Shi kaɗai yasan irin dogon gargaɗin da yasha akan Mamy a safiyar yau da daren jiya. Shi yanzu al'amarin mahaifiyar tasu yama daina bashi mamaki ko tsoro. Abinda kawai bata sani ba ko bata cigaba da takurashi da gargaɗin ba a shirye yake ya mata biyayya koda kuwa hakan ne zai zama ƙarshen rayuwarsa. Dan shi ya sani a wannan gaɓar babu kuma abinda ya rage masa a wannan rayuwar sai jiran mutuwar.
A gefe kuma Oum sai dama-dama take da shi. Tun daga jiya zuwa yau sai faman lallashinsa da lallaɓashi take akan batunsa da Maanal ya sanar mata ko akwai wani abu da basu san da shi ba ne. Baya son tada mata da hankali, dan haka murmushi kawai yake mata yace ta kwantar da hankalinta ALLAH na tare da kowa. Duk da bata fahimci abinda yake nufi ba ita dai lallaɓashi take yi akan in sunzo koda an tambayesa ya faɗi yana da wadda yake so. Dan ita bata ɗauki wani batun kai kuɗin Rafeeq gidan su Maanal ɗin da muhimmancin da zai hana komai ba. Kawai gargaɗin Abah ne ma ya hanata kiran Rafeeq ɗin ta masa tas, dan yaja mata dogon gargaɗi akan hakan. Shi kuma Rafeeq ɗin kamar yasan abinda ta shirya masa yaƙi komawa Abujan. Ko waya yaƙi kiranta ma.
Mahmud da Hassan ne sukaje ɗaukarsu a airport. Koda suka iso gidan Baba Sardauna sun samesa cike da dukkan ahalinsu. Dan kamar ma su kaɗaine basu kai ga isowar ba sai Gwaggo Khadi data taho daga Yola. Dan sai da sukai kamar awa ɗaya ma sannan itama ta iso da tata tawagar. Itama dai bayan Mahmud data mallakama Baba Sardauna a wancan lokacin tana da yara biyar a yanzu. Uku maza, biyu mata. Mazan biyu sunyi aure. Hamza da Lamiɗo. Sai Nuwaira da Raihana. Sune ƴammata da take damuwa da rashin yin aurensu. Sai autanta Abdullahi, shi kam da sauransa. Koda yake koshi ɗin yanzu akama auren zama zai yi da matar sumul.
Tuni an kacame da hirar zuminci a ƙaton falon gidan Baba Sardauna da dama an tanadesa domin irin wannan haɗuwar. Ƴaƴa da iyaye anata zabga hira cike da farin ciki. Akwai irin AA marasa yawan magana a cikinsu, amma idan akai irin wannan haɗuwar kakanji bakin kowa ya buɗe. Hatta shi AA ɗin yakan ɗan saki jiki kaɗan. Sai dai yau tunda aka gama gaisawa yama zame jikinsa yabar falon. Sai da Oum ta farga baya nan ta fara jajensa. Sai Modibbo ke sanar mata ai yana waje yana waya, jin haka yasa ta cigaba da hirarta, duk da rabin hankalinta na kansa, wani kuma tsagi nakan rashin ganin Rafeeq. Wasa-wasa AA bai dawo falon ba sai da za'a fara meeting. A lokacin ne kuma Rafeeq shima ya iso tare da Abbu, dama shima bai kai ga isowaba. Alhaji ƙarami da Mah-mah ne kawai sai Rufaidah. Bayan addu'a ga wanda suka rasa da kuma su da suke raye aka fara abinda ya tara kowa. Nasiha ce mai ratsa jiki Baba Sardauna ya fara sannan ya tafi kai tsaye kan abinda yasa su tara wanan taro na gaggawa. Ba komai bane face auren da suke son ƙullawa. Maganar Rafeeq itace farko, Baba yay bayanin sun riga sun kai kuɗi kuma an amsa nan da sati uku biki, dan haka zasu haɗe da sauran suma ayi a huta kawai. Amma an bama AA da Najeeb da su Nuwaira dama idan suna da wanda suke so su faɗa. Da Najeeb aka fara kasancewar uba a wajen su AA ɗin. Kansa a ƙasa yace shi baida wacce yake so, amma su ƙara bashi lokaci zai kawo. Baba Sardauna yace Sam bashi yiwuwa, babu wata dama da zasu ƙara basu, ya zaɓa a cikin ƴaƴan dangi gasu nan. Rasa abin cewa Najeeb da ransa ya gama ɓaci yayi, sai kawai yace shike nan ya basu dama kowacce suka zaɓa masa. Albarka aka shiga saka masa. Kafin aka koma kan AA. Sarai yana kallon irin kallon da Oum ke masa, hakama Mamy, hakama Yaya Fawzan da Babban Yaya. Abah ne kawai baya hangowa da ƙyau. Amma duk sai ya ture komai cike da dakiya yace shima ya basu dama duk wadda sukaga ta dace su bashi. Da ƙarfi Oum ta runtse idannunta, yayinda Fawzan kema AA wani irin kallon takaici da jin haushi. Mamy kuwa murmushi ta saki tare da sauke ajiyar zuciya a cikinta. Dan tasan dai zaɓinta data ba su Baba Sardauna zasu bashi. An koma kan su Nuwaira sukace suma sun bada zaɓi.
Sai dai me, bayan an sakama AA albarka shima buɗar bakin Baba Sardauna sai cewa yay, “To Alhamdullahi, munyi farin ciki da wannan biyya taku. Dan haka bama sai anje da nisa ba. Mun yanke shawarar haɗa auren ku ku huɗun lokaci guda, zakuma muyi amfani da ranar Rafeeq da aka tsaida dan ayi a wuce wajen.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login