Showing 75001 words to 78000 words out of 221978 words

Chapter 26 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

har anyi la'asar RK bai kirata ba bai kuma zo gidan ba ta fara tunanin ko lafiya? Gashi ta riga ta ɗauri niyyar zuwa dubiyar nan yau dai ta huta. Kuma jiya da dare ta sanar masa da anyi la'asar yazo ya kaita dan Didi tace bata yarda sai bayan magrib ɗin nan ba. Jitai kamar ta sharesa, sai kuma dai ta danne zuciyarta ta tura masa gajeren saƙo, daga haka ta koma falo ta zauna dan ta shirya tsaf hakama Barrah da Haneeff da zasu mata rakkiya tsaf suke.
Sai kusan huɗu da rabi RK ya iso gidan, yana sanye da shadda shima yanzu ruwan zuma harda hula. A ranta ta ɗan taɓe baki da faɗin (idan anga kuna wankan shaddoji sai juma'a kawai) a fili kam tayi kicin-kicin da fuska daga gaisuwa bata sake kulashi ba, dan shima dai fuskar tashi yau babu walwala. Da alama tun fushin safen ne bai gama sakinsa ba........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣4️⃣




........A motar ma gaba ɗaya sai ya maida hankalinsa akan tuƙi da surutun su Barrah ya shareta, itama dai hankalin nata naga duba wasu novels da Aneesa ta tura mata sunayen su. Tafiyar tasu ba wata mai nisa bace suka iso. Gidane daya amsa suna gida, dan ko'a cikin garin Abujar kasan mai shi yaci ya ƙoshi. Sai da security ɗin ƙofar yazo har inda suke yaga waye sannan ya danna remote ɗin hannunsa gate ɗin fari tas ya zuge kansa. Godiya RK ya masa tare da shigewa cikin katafaren gidan daya yalwatu da shuke-shuke masu matuƙar ƙayatarwa da bama zuciya nutsuwa. Kafin yau Maanal na jinjina girma da tsaruwar gidan Daddy, hakama gidan Didinta Shahidah gidane mai ƙyau da ƙawa. Sai dai gidan nan ya matuƙar disashe mata waɗan can da take tunanin babu kamarsu. Hatta da parking space a tsare yake anan.
Tunda suka fito su kansu yaran ke bin ko'ina da kallo baki a buɗe, Haneeff dai daya kasa haƙuri matsowa yay kusa da Maanal cikin raɗa ya ce, “Mie-mie! Uncle R house ya haɗu kamar ba'a Nigeria ba”.
Kasa cema yaron komai tayi, sai hannunsa daya riƙo nata ta ɗan matsa kaɗan. Dai-dai nan RK dake tattaro kayan tsarabar da bai san ko minene ba ya juyo garesu. Ƙaramin murmushi ya mata ganin yanda take binsa da kallo, batare da yace komai ba ya nuna mata hanya alamar suje, tare da kama hannun Barrah. Ɗauke kanta tayi kamar bata fahimta ba, sai ya sake sakin murmushi yay gaba, dan wannan yana ɗaya daga cikin halayenta dake matuƙar birgesa. A gidan sassa ne har kusan shida. Kuma kowanne da tsarinsa, sannan tsakaninsa da ɗan uwansa akwai ƴar tazara ta yanda baka isa sanin mi nacan keyi ba, ko shi yasan mi kakeyi a naka part ɗin.
Part na tsakkiya a hannun dama suka nufa, RK ya danna bell tare da ɗan juyowa ya kalla Maanal. “Ni dai kar aje ana fushi dani a gaban Aunty na”. Yay maganar yana kashe mata ido ɗaya. Harararsa ta ɗan yi kawai, tare da ɗauke kanta. Shi kuma sai ya sake sakin murmushi. Zaiyi magana aka buɗe ƙofar. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce sa'ar Maanal ba, cike da girmamawa ta ɗan rissina tanama RK ɗin sannu da zuwa. Duk da jikinta fes yake cikin tsafta a kallo ɗaya zaka fahimci mai aiki ce, sai dai masu aikin ma irin wanda ke samun kular nan dan babu wani nakasu a tare da ita. Kayan hannun RK ɗin ta amsa, yayinda shi kuma cikin dakewa kamar bashi ba yake tambayarta “Aunty fa!?”.
“Tana upstairs....”
Kansa kawai ya jinjina mata, batare da yace komai ba suka ƙarasa shiga cikin falon da yasha black & golden color na kujeru da labulale, sai wani irin ƙamshin turaren wuta ke tashi mai ratsa zuciya. Ga sanyin ac mai kashe jiki. Gaba ɗaya jikin Maanal sai ya ƙara sanyi. Bata sake tsinkewa da al'amarin ba sai da ya danna wani maɓalli ƙofar glass ɗin dake kamar bango guda ta zuge kanta suka shigo wani falon, nan kam komai golden yellow & white ne, shima dai babu kowa sai ƙamshi dake tashi, wayar da yake dannawa ya kai kunnesa, ba'a wani jima ba aka ɗaga.
“Aunt mun iso”. Ya faɗa cike da girmamawa. Maanal dai data zama kamar wata gunkiya bata san amsar da aka bashi ba taga ya juyo ya kalleta da murmushi, sai kuma ya furta, “Okay gamu nan”. Yana yanke wayar.
“Sorry muje tana sama”.
Ya sake faɗa idanunsa akan Maanal ɗin. Kanta kawai ta jinjina masa batare da tace komai ba. Sai dai tana mamakin ta ina kuma zasu bi zuwa saman dan bataga hanya ba sam anan. Amma a mamakinta sai ya nufi wata ƙofa da su, anan ne taga ƙafar benen da shima aka ƙawata matuƙa, dan hatta a ƙasansa ma wasu kujeru ne guda biyu aka tsara da gani wajen zaiyi daɗin hutawa. Haka dai suka haura upstairs ɗin Maanal na sake jinjina jin daɗin da masu hannu da shuni keyi a ƙasar nan. Dole su manta da talaka, dole talaka yasha wahala dan bataga ta yanda za'a iya tunawa da rayuwarsa ba anan. A sama ma wani tsararren falon suka samu, wanda aka ƙawata da ash color na kujeru dama labulalen, nan ɗin ma dai ƙamshin turaren ne yay musu sallama da sanyin ac kaɗan, sai kuma nutsatstsiyar muryar dattijuwar dake musu lale marhabun cike da ƙasaita. Kasancewar RK ya rufe Maanal yasa bata ganin dattijuwar itama bata ganinta, sai dai muryar ta wani irin dakar mata ƙirji.
“Rafeeq ƙaniyarka, dalla gyara ka wani rufe min ƙanwar tawa bana ganinta”.
Dariya RK yayi tare da matsawa gefe yana faɗin, “Oh Aunt ni yau baki son ganina kenan?”.
Baki ta buɗe zata bashi amsa amma sai ta gagara hakan, sakamakon saukar idanunta akan Maanal da ita nata idanun ke kallon ƙasa, dan RK ɗin na matsawa daga rufetan da yay ta rissinar da idanunta saboda yanda bugun zuciyarta ke ƙara ƙarfi. Ga wani irin yanayi mai wahalar fassara dake ratsata. Hakama zuciyarta ta mata nauyi matuƙa a cikin ƙirjinta.....
Gaisuwar Barrah da Haneeff ce ta katse dattijuwar daga kallon Maanal, ta saki ajiyar zuciya da sakin murmushi tana miƙama yaran hannu da faɗin, “Ƙanwata kinga ƙaraso mana, Bismillah zo gareni”.
Sake motsawa zuciyar Maanal tayi a karo na babu adadi, dan Muryar nan tana mata wani irin amsa kuwwa ne da maimaita kanta a matsayin wata murya da amonta ya faru ya kuma shuɗe a duniyarta ta baya. Amma sai ta dake, cikin yanayinta na nutsuwa ta cigaba da taka lallausan carpet ɗin dake tsakkiyar kujerun zuwa inda dattijuwar take zaune, dan tana zaune ne daga ƙasa abinta duk da tima-timan kujerun dake falon. Cak Maanal ta tsaya yayinda take gab da kaiwa inda dattijuwar take, bakomai ya sakata tsayawar ba sai murya ta biyu data daki tsakiyar kunnenta tayi amsa kuwwa a cikin kanta. Sam batai zaton akwai wani bayan dattijuwar a cikin falon ba duk da taji wani ƙamshi bayan na turaren da aka saka a gidan da wanda ta tabbatar dattijuwar keyi. Sai da RK ke faɗin, “Wai dama da gaske kake daga massallaci gida zakayo ashe?”.
“Kaje nemana ne?”.
AA dake kishingiɗe a saman lallausan carpet ɗin kusa gab da dattijuwar dan filo ne kawai ya raba tsakaninsu gabansa wasu document ne barbaje, sai dai a hannunsa shi novel ne yake karantawa, a maimakon shaddar ɗazun yanzu kam ƙananun kaya ne baƙaƙe a jikinsa. Amsar da RK ya bashi yana nuna Maanal da faɗin, “No naje ɗaukar Maanal ne kawai dai” ya sashi wani kallar ɗago idanunsa ya sauke a kan Maanal ɗin data kasa gaba ta kasa baya. Dai-dai nan itama Dattijuwar da hankalin ta ke akan su Barrah ta ɗago tana maimaita sunan.
“MAANAL!” Sai kuma ta miƙe zaram. “Rafeeq da gaske Maanal ɗina ce kamar yanda zuciyata ta ayyana min yanzu-yanzu ko suna ne yazo ɗaya, to amma akwai kamanni mafa” ta kai ƙarshen maganar tana ƙarasowa inda Maanal take. Lallausan hannunta mai ɗauke da zabba masu ƙyau da ɗaukar idanu, tare da bangles takai kan haɓar Maanal data lumshe idanunta da suka cika da ƙwalla ta ɗago. Sosai take raba idanunta akan fuskar Maanal ɗin, sai kuma ta juyo ta kalla RK da shima ya miƙe cike da mamaki, janyewa tai ta maida ga AA da ya maida idanunsa ga book ɗin hannunsa sai dai tuni abinda yake karantawar ya suɓuce masa.
“Auta gane min nan, wlhy Maanal ce ko? Ko Auta Manaal ɗina ne dai ba wata ba. Ajwaad taso, taso dan ALLAH ka tayani gani ko idanun nawane dai ba Baby ba bace....”
Da wani irin ƙarfi AA ya rumtse idanunsa batare daya ɗago ɗin ba, ko motsima baiyi ba daga yanda yake. Sai RK ne ya ƙaraso wajen cikin sassarfa yana faɗin, “Aunt da gaske kin san Maanal ɗina? Maanal Please! Da gaske kema kin san Aunty na?”. Duk ya ruɗe da farin ciki shi kam.
Cikin rawar muryar kuka Maanal da tausayin yanda dattijuwar ta rikice ya sake mamayeta, a hankali ta shige jikinta tana faɗin, “Oum nice, Maanal ɗinki ce Oum. Dama baki manta dani ba, dama zan sake ganinki? Ashe muna da rabon sake haɗuwa kafin na koma ga ALLAH”. Wani irin kuka mai ban tausayi ya suɓuce mata, sai dai hakan bai hana muryarta fita cikin nutsuwa da sanyi ba. Sanyin dake bayyana tasirinsa a jikin AA, duk yanda yake sake kamewa da dakewa abin na neman fito da kansa. Dan Barrah da kukan Auntyn tasu ya sakasu yin narai-narai da idanu suma zasuyi kukan ta matsa gab da shi tana faɗin, “Uncle kaga Mie-mie na kuka ita da Grandma”. Amma ina baiji yarinyar ba, sai da ta ɗan girgiza shi sannan firgigit ya buɗe idanunsa da suka kaɗa matuƙa tare da ɗagosu ya sauke akan yarinyar. Dai-dai kuma Barrah ta miƙe ta nufi inda Maanal take ta rungume mata ƙafafu tana kiran sunanta.
Ɗago Maanal Oum tai daga jikinta itama tana share nata hawayen ga murmushi yaƙi barin fuskarta. Hannayenta duka biyu tasa tana sharema Manaal hawayenta da suka gagara tsayawa, dan gaba ɗaya ma ta kasa cewa komai saboda ita kaɗai tasan irin kalar farin cikin da take ciki. Juyawa tai ga RK da ke kallonsu cikin ruɗani, murmushi ta sakar masa shima. “Rafeeq ALLAH yay maka albarka kaji, yau kam kayi mun babbar ƙyauta daka kawo min ɗiyata har gida.....”
“Aunty duk kin ruɗar dani wlhy, wai kin santa ne daman?”.
“Sosai kuwa Rafeeq, zan iya cemaka kusan nice na raini Maanal ma”.
“What!? Raino fa?”.
“Ƙwarai ma kuwa. Haihuwar Maanal ne kawai ba'ayi a gabana ba. Kunga bismillah kumuje mu zauna”.
RK dai da ƙyar ya kai zaune, sai dai idanunsa akan Oum da Maanal kamar mai tsoron su ɓace masa. Waya Oum ta ɗauka tare da bada umarnin a kawo ruwa. Babu jimawa kuwa sai ga yarinyar nan data buɗe musu ƙofa ɗauke da tray wata da bazata wuce sha huɗu ba biye da ita. Cike da ladabi da girmamawa suka ajiye kayan a saman Centre table, sai kuma suka shiga gaishe da su RK. A dai-dai nan Oum dake riƙe da hannun Maanal kamar mai gudun a ƙwace mata ke tambayarta,
“Ina ƴar uwata Maanal? Ina su Shahidah da Abban ku?”.
“Oum Ammie na nan lafiya Lau, hakama su Didi, wannan ma yaran Didi Shahidah ne”.
“Masha ALLAH! Masha ALLAH! Yanzu yaran Shahidah ne wannan? Kai jama'a ALLAH mai alkairi. Kuzo nan kuyi haƙuri ganin ƴata ya ɗauke min hankali”. Tai maganar tana kamo su Haneeff da sukai ƙwale-kwale saboda kukan Maanal ɗin. Cikin ɗari-ɗari bakamar ɗazu da farko ba suka ƙaraso wajen Oum ɗin, sai da Maanal ta kallesu da sakar musu ɗan murmushi ta ce, “Itama Grandma ce ku gaisheta ku faɗa mata sunayenku”.
Karo na farko yaran suka saki ajiyar zuciya, sai kuma suka shiga gaishe da Oum ɗin. Barrah ta faɗa mata sunanta, da sauri Oum ta kalla Maanal. Murmushi Maanal ɗin tai mata da jinjina kanta. “Eh Oum sunanki aka saka mata, Ammie ce taso sakawa tun akan su Waleed, sai kuma suka kasance maza. Shine Didi na haihuwa aka saka”.
Wani irin rungume Barrah Ammie tayi a jikinta, ƙauna matuƙar ƙaunar Ammie na ratsa ƙashinta da ɓargo. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “ALLAH sarki ƴar uwata. Ashe Asiya bata manta da ni ba”.
Murmushi mai ciwo da ƙuna Maanal ta saki batare data iya cewa komai ba. Sai wasa take da yatsunta kawai. Oum ta juya ga AA tana faɗin, “Auta kaji fa ashe Asiya bata manta dani ba. Sunana aka sakama ɗiyar Shahidah”.
Karo na farko ya saki wani irin murmushi mai ban mamaki, irin mai maƙalewa a gefen bakin nan da sai kana kallon mutum kake sanin yayi, sai kuma ya yunƙura a hankali ya riƙo hannun Barrah, matsota yay jikinsa kawai ya rungumeta. A mamakin kowa dake falon sai ji sukai ya furta, “I love you so much tunda kikaci sunan Oum na, ALLAH ya albarkaci rayuwarki”.
“Uncle ni banda ni?”.
Haneeff ya faɗa babu zato. Dariya Oum da RK da masu aikin nan sukayi, yayinda Maanal tai ɗan murmushi da girgiza kanta. Shi kam AA idanunsa ya buɗe sosai a kan yaron, sai kuma shima ya sakar masa murmushin da miƙa masa hannu ya riƙosa, cikin maganar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Kaima ALLAH yay maka albarka”.
Cike da farin ciki Haneeff ya amsa masa. Shima RK da Oum duk suka amsa............✍️


🤔Nayi tambaya ko nayi shiru wai???.. kai Bara dai na haɗiye kayana🥱. Idan kuma akwai mai irin tunani na mu haɗu a comment 🏃🏃🏃🏃🏃






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣5️⃣




........Sosai zuciyar RK ke yin kaikawo a ƙirjinsa matuƙa akan wannan al'amari. Ba komai ya kawo hakan ba mamakin Maanal da AA da koda wasa basu taɓa nuna masa sun san juna ba. Sannan miyyasa AA ɗin bai sanar da Oum fara aikin Maanal a companyn sa ba kusan sati uku kenan. Ko shima dai bai san Maanal ɗin bane? Alaƙar iya Oum ɗin ce kawai da su Maanal ɗin?. Zuciyarsa na ƙoƙarin gamsuwa da hakan sai ga sallamar yayan AA ɗin, da'alama ma yanzu ya shigo gidan daga wajen aiki.
Zama yay a kujera yana sauke numfashi. Oum dake kallonsa cike da tausayawa na jera masa sannu. Amsawa yay fuskarsa da murmushi sai kuma ya ɗora da gaisheta. Sai kuma ya juya ga RK yana faɗin, “Barka da juma'a Uncle”.
Amsa masa RK yay shima yana murmushin. “Wai sai yanzu kake dawowa gida? Ƙarfe biyar fa?”.
“To ya muka iya Uncle. Bakaga shi Autan Oum da yake ɗan shagwaɓa ne ya gudo wajenta da wuri ba”. Dariya RK yayi ganin yanda AA ya dallo musu harara su duka ya maida idonsa ga novel ɗinsa batare da yace komai ba. Sai da suka tsagaita Maanal da kanta ke ƙasa ta shiga gaisheshi ita da su Barrah. Kallonta ya ɗan yi, sai kuma ya ɗauke idonsa ya maida gasu Barrah yana amsa musu da murmushi. Kasancewarsa mutum mai barkwanci idonsa akan RK yake faɗin, “Uncle R kodai Momyn tamu ce ne wai? Dan ɗazun Oum ke sanar min zaka kawota yau”.
Kallon Maanal RK yayi yana mai jinjina kansa fuska ɗauke da murmushi. “Gatanan ai na kawo muku”.
“Kai kai Masha ALLAH, Momyn mu ai ban san ke bace dana durƙusa har ƙasa. Matar Uncle Rafeeq fa. Bara kiga na taso ki saka min albarka ga ɗanki yazo gaisheki”.
Dariya Oum da RK sukayi, yayinda Maanal ta ɗan ɗago ta kallesa a karo na farko. Dai-dai yana ƙoƙarin sake yin magana amma sai maganar tasa ta maƙale a saman harshe saboda saukar idanunsa akan Maanal. Ɗan wara idanunsa yayi na rikicewa, sai kuma ya maida kallonsa ga Oum dake sakin murmushi itama idonta a kansa. Ai da wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login