Showing 120001 words to 123000 words out of 221978 words

Chapter 41 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

wannan gantalin nata na tayar min da hankali musamman a kwanakin nan data san Yazeed baya Abujan. Narasa mi yarinyar nan take yi a garin nan?”.
Murmushi kawai Maanal tayi amma taƙi gayama Shahidah gaskiyar abinda ta sani akan Huznah ɗin. Badan bata son ta sani ba sai dan bata son sako al'amarin mutumin (AA🤣) da Huznahr ke bibiya sam a al'amuranta. Sai ma kawai ta basar da zancen ta hanyar faɗin, “Didi nima ina son zuwa Kaduna a weekend ɗin nan”.
“Amma Auta kinfa san satin ne bikin Yazeed”.
“To minene a ciki Didi. Dan ana bikin yaya Yazeed kuma sai naƙi zuwa Kaduna?.”
“Baƙya gudun abinda zai iya zuwa ya dawo”.
“In sha ALLAHU babu komai Didi. Kawai ina kewar Ammie ne sosai wlhy. Sannan ina son Rafeeq yaje su gana da Daddy dan na bashi damar hakan”.
Da sauri Shahidah ta dubeta. Harshenta har harɗewa yake wajen furta, “Maanal akan mi kike son Rafeeq ya gana da Daddy?”.
Ɗan jimm Maanal ɗin tayi tana kokawar saita kanta da danne duk wani yinƙurin raunin da zuciyata ke son bayyanawa akan fuskarta, sai kuma ta saki murmushin karfin hali. Kanta tsaye ta ce, “Na bashi damar neman aurena”.
“What!! Neman aurenki fa kika ce Manaal? Rafeeq ɗin? Shifa ɗin ɗaya daga cikin zuri'ar su Ajwaad ne??”.
“Tabbas hakane Didi. Shiyyasa ma na bashi wannan damar. Sannan kin manta ne, alaƙar dake tsakanin Oum da Rafeeq tafi ƙarfi fiye da wadda ke tsakani da su. Dan haka na yarda na amince zan auri Rafeeq in sha ALLAHU”. Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin ko waiwayen Shahidah data saki baki da hanci da ido tana kallonta batai ba.........✍️




_🥱🥱Nifa a wata gaɓar rasa abincewa nake 😆._












✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖5️⃣2️⃣




______________




.........Wani irin kalar zubewa Shahidah tayi a saman gadonta kamar wadda aka kwashema dukkan ƙarfi da zuciya a lokaci ɗaya. Kalaman Maanal na mata wani irin kai-kawo dai-dai da bugawar zuciyarta. Sai kuma kamar wadda aka zabura ta lalubo wayarta. Kira ta sake dannama Amaal. Aiko bugu ɗaya ta ɗaga dan dama tun ɗazun nemanta take itama amma ta gagara samunta....
“What! Rafeeq fa? Maanal kuwa nada hankali? Kota manta alaƙar dake tsakanin Rafeeq da Ajwaad ne?”.
“Nima na faɗa mata hakan wlhy Amaal. Amma ta nuna min ai alƙar dake tsakanin Oum da Rafeeq tafi ƙarfi akan wadda ke tsakanin Rafeeq da su Ajwaad. Ni wlhy nama rasa wane tunani zanyi. Dan tabbas akwai ƙura babba. Anzo gaɓar fa da dole Ammie tasan halin da ake ciki kin san dai Auta da taurin kai da kafiyar tsiya”.
“Amma kin san zamusha faɗa akan ɓoye matan da mukai. Sannan na faɗa miki jiya naje gidan na samu Daddy na shirin zuwa Kebbi domin ganawa da waɗan can mutanen na Giro. Na tabbatar kuma yau ɗin nan sun tafi ma shiyyasa nake ta nemanki tun safe. Yanzu haka can gidan zanje dan Hameed ya kirani ya sanar min Ammie na ciwon kai yau gaba ɗaya a kwance ta yini kuma yaga Daddy ya fita daga wajenta da safe kamar a fusace. Kinga ko ya tabbata akan zuwa Giro ɗin ne maybe ta nuna bata so ko”.
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Amaal komai zai iya faruwa kam. Wannan wace irin gaɓa ce mai rikitarwa da tada hankali. Aiko muma bamuga ta zama ba dole na ɗauka hutu Kona kwana huɗu ne muzo Kadunan gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga nan kawai har biki”.
“To gaskiya hakan ne ya kamata kawai ku taho. Bara naje naga halin da Ammien ke ciki”.
Jiki a sanyaye Shahidah ta amsa ta da to kawai suka yanke kiran.


Bata leƙa Maanal ba sai bayan sallar magriba, ta sameta tana karatun Alkur'ani. Zama tai dan haka Maanal tana kaiwa inda ya kamata ta tsaya ta dakata. Duban Shahidah tayi da da faɗin, “Didi kina son wani abu ne?”.
“A'a Auta, ina Huznah take?”.
Sai da Maanal ta ɗan taɓe baki sannan tace, “Naga Yaseerah ta kiranta yanzun nan ta saka hijjab ɗina ta fita a rikice. Ban san mita gaya mata ba amma da alama Yaseerahn na wajen gidan nan ma dan naji tana cemata gata nan zuwa ba sai ta shigo ba”.
Kai kawai Shahidahn ta girgiza da faɗin, “To ALLAH ya ƙyauta. Dama zance miki ne inaga gobe in sha ALLAHU zamu wuce kadunan gaba ɗaya”.
“Didi aikinki fa? Wani abu ya faru ne?”.
“Babu damuwa zanma Abban Barrah magana ya nema min hutu na kwana huɗu tunda oga na abokinsa ne. Kinga idan biki ya tashi sai mu taho gaba ɗaya kawai”.
Magana Maanal taso yi, sai kuma ta ce, “Okay ALLAH ya kaimu to”......


_____________★

A ɓangaren AA kam shima bayan wucewar su Maanal ya matsa aka sallamesa. RK yaso ƙin yin hakan amma ina. Ganin yana neman birkice musu Oum tace yasa a sallame san kawai. Sun iso gida Mamy da Abah na shirin zuwa asibitin dubashi. Dan shi Abah yau yaje gidan gwamnati tunda safe sakamakon kiran daya samu daga mataimakin shugaban ƙasa. Ita kuma Mamy ta fita dan ko kai AA ɗin asibiti bata san anyi ba sai da ta dawo ko sashenta bata shiga ba taci karo da Abah ya fito zaije asibitin. Shine yace ta juya suje dan yasan halinta zata iya ƙin zuwa saboda kawaici. Bata ce masa komai ba suka nufi motarta data ajiye yanzu, dai-dai nan kuma sai ga ƴan asibitin ma. Sai kawai suka runguɗa zuwa sashen Oum dan AA yace shi can zaije baya son sashensa. Can ɗin kuwa aka nufa da shi har ɗakin Oum. Anan suka zagaye sa cike da kulawa da tsantsar soyayyar da kowa ke masa a gidan....


★★★


Abdul-hakeem mijin Yaseerah yazo gidan kawoma Mamy saƙo data manto a wajen mamansa shi kuma yaje gidan ta bashi ya biyo Mamyn dashi ya samu batun ciwon AA ɗin bai sauka ba da har yau ya kaisa ga zuwa asibiti. Shine ya kira matarsa Yaseerah yace tazo itama ta duba shi sai su koma gidan tare. Ita kuma ta kira Huznah ta kuma biya ta ɗakkota a gidan Shahidah kamar yanda mijin nata ya bata umarni. Koda suka shigo kai tsaye sashen Oum suka nufa dan har lokacin itama Mamy na acan dama duka ƴan gidan har su Saheeba da Nibras da Nuratu. Mai aikin Oum Mamy ta saka shigowa da su Abdul ɗin har falon sama na Oum.
Duk suna a falo, idan ka cire AA dake can bedroom ɗin Oum da yay barci. Sai Babban Yaya da bai dawo gidan ba tun baro asibiti da yay ɗazun. Nibras da Nuratu na'a falon ƙasa suna girki. Nuratu ce ta fara cewa zata girka ma AA abinci kamar yanda uwarsu da suka kira suna gaya mata abinda ya faru a asibiti ta basu shawarar yi. Sai ita kuma Nibras ta ce itama zatayi dan wani irin tsanar Nuratu take ji tuni batun yanzu ba. Abinda ma ke ɗan sassauta mata ƙinta ganin yanda shi AA ɗin baya wani shiga sabgarta. Itama dai taci kuka bayan dawowar tasu daga koro sun da akayi daga asibiti. A hakan ma ba wani tarihin Maanal ta sani cikakke ba game da alaƙarta da AA, amma ta ɗauki aniyar bugar cikin Fawzan ta sani yau dan tasan irin matakin da zata ɗauka akan Maanal ɗin da dukan ahalinta ma. Dan itafa a yanda take jin AA a ranta ALLAH ko mahaifansa da su Fawzan zata iya kawarwa ta mallakesa ita kaɗai.
Su Huznah sun hawo Nibras da Nuratu dake a kitchen basu sani ba. Sai da har su Abdull sun gama gaishe da Abah da Mamy da Oum Abah na tsokanar Abdull sannan suke haurowa da kayan abincin da suka shirya harda mai aikin Oum. Sannu Oum da Mamy ke musu, duk suka amsa tare da tambayar Mamy ina za'a kai masa abincin. D/table Mamy tace su ajiye. Dan haka duk suka ajiye a can ɗin. Juyowar nan da Nuratu zatai tana magana da Abdull sai idanunta ƙuru-ƙuru a cikin na Huznah da tun shigowar Nuratu falon mamaki da ruɗani suka baibayeta. Cikin kuwa ɗan waro ido na nuna mamaki Nuratu ta ce, “Kai wai wa nake gani kamar Huznah?”.
Murmushin ƙarfin hali Huznah ɗin tayi, sai kuma ta sinne kai ƙasa wai ita kunyar surukai na wajen ta ce, “Nice Nurry”.
Idanu Yaseerah da Abdul-hakeem suka haɗa. Yayinda Mamy ta saki wani murmushin jin daɗin ganin Nuratu da Huznah ma kenan sun san juna. Dan haka sai kawai ta miƙe tana faɗin, “Kunga muje can kafin Maman ɗan nan tace zamu hana mata shi barci”.
Dariya Oum tayi dan sanin da ita Mamy take. “Oh abun ma harda ƴar sharri. To shike nan kuje ɗin dai dan kuwa ban san a tada shin”.
Mamy ma dariyar ta sake yi. “Ai nasan gaskiya na faɗa”.
Shima Abah dariya yaketa musu. Haka Mamy ta fice tare da su Huznah. Nuratu ma tai wuff ta bi bayansu. Suna gama fitowa daga apartment ɗin Oum ɗin caraf Nuratu ta riƙo hannun Huznah dake kusan ƙarshe. Cak Huznah ta tsaya, sai kuma ta juyo tana kallon Nuratu. Murmushi ta sakar mata da faɗin, “Oh oh friend ashe kece? ALLAH duk kin saka mamaki yama rufe ni da ganinki gidan nan kodai gidanku ne?”.
Nuratu da zuciyarta keta watsal-watsal a ƙirji ta ce, “Eh gidanmu ne. Amma ba inda aka haifan ba. Gidan da zanyi aure kenan, kuma wanda zan aura ɗin ma kuka zo dubawa. A ina kika san Abdul-hakeem?”.
Tsabar yanda zuciyar Huznah tai wata girgiza har taurari ta dinga gani na mata yawo a cikin ido. Cikin rawar baki ta ce, “Waye zaki aura ɗin?”.
Cike da gadara da alfahari Nuratu ta bata amsa da, “Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, wato AA Darma”.
Ai zabura gefe Huznah tayi tana mai fisge hannunta daga cikin na Nuratu, sai ko gata jikin bango kamar mage ta gamu da kare a kwanar da babu hanyar ɓillewa. Yanda tai ɗin ya saka Nuratu kafeta da ido itama zuciyarta na wantsalawa a karo na biyu. Sai kuma ta matsa gaban Huznah tana faɗin, “K jira-jira wai badai dama Yaya AA kike bibiya ba?. Babbar bala'i wai dama shine kika bamu labari?”. Bata jira amsar Huznah ba tai saurin fara danna wayarta ta latso hoton AA dake cikin wani lallausan farin yadi da yay masa shegen ƙyau ta nuna mata. “Shine wannan?”.
Jinjina mata kai Huznah tayi a mutuƙar harmutse.
“Kambu are you mad? Wai dama mijin aurena kike bibiya. Ehhhh ahhh lallai kin taro match yarinyar nan. Yau naga baƙar shegiya ubanwa ya aiko ki?”. Tai maganar da nufar Huznah gadan-gadan tana neman kai mata hannu ta shaƙota. Hannun nata Huznahr ta riƙe caraf, a dai-dai nan Fawzan ya iso wajen.
“Kai kai kai lafiya?!!”.
Ya faɗa cikin daka tsawa. Dan shima abinda Nuratun tayi a asibiti har yanzu haushin bai bar ransa ba. Dakatawa Nuratu tai daga shirin shaƙe Huznah. Sai dai cikin wani irin ihu da hargowa ta ce, “Yaya Fawzan wai har wannan tsinanniyar ce zatace tana son Yaya AA. Son shi take amma tazo ta raɓu da jikina inata bata shawarar yanda zata sameshi. Ni wannan ƴar iskar zata maida bahuwa. Na rantse da ALLAH yau saina haɗa miki jini da majina ta yanda bazaki taɓa sake sha'awar yima kowa ƙwacen saurayi ba dan ........” ta ƙarasa da ashariya mai girman gaske tana sake zaburowa kan Huznah.
Cikin ƙanƙanin lokaci rikici ya harƙume a tsakaninsu da hayaniyar ta saka su Mamy fitowa. Hakama Oum sai gata da Abah harda masu aiki duk sun yo waje. Itama Nibras da Saheeba haka. Wani irin jan faratunnan ƙarin da Nuratu tayi a hannunta tai a saman fuskar Huznah,tun daga wajen kunnenta har zuwa bakinta. Ƙara Huznah ta saki na azaba tana mai dafe fuskarta da duka hannuwan biyu jikinta na rawa. Aiko cikin tashin hankali Mamy da Oum sukai kan Huznah ɗin, ita kuma Saheeba ta riƙe Nuratu. Mugun ciwo Nuratu taima Huznah , dan yanda kasan tsagar yarbawa irin na farkon ƙarnin nan haka suka kasance har sanda huɗu na yatsunta. Jini tuni ya jiƙe wajen abinka da farar fata jiki kuma babu wahala.
Ai Fawzan baima san ya kwashe fuskar Nuratu da mari ba. Yana ƙoƙarin sake kai mata wani Abah ya riƙe hannunsa yana mai girgiza masa kai. Kuka Huznah take sosai na azaba, hakama Nuratu kukan marin da Fawzan ya mata take yi. Sai dai bakinta bai mutu ba sai sake jadadadama Huznah take idan bata fita a sabgar AA ba ALLAH sai dai ta kasheta. AA nata ne ita kaɗai. Yanda taketa surutai yasa kowa ya fahimci akan AA suke faɗan, dan in ka cire Mamy da su Abdul-hakeem sai ita Saheeba babu wanda yasan alaƙar Huznah da zuwa gidan ma.
Dole Abdull da Yaseerah da jikinta duk ke faman rawa suka kama Huznah zuwa mota domin kaita asibiti. Ita kuma Saheeba taja Nuratu sashenta. Nibras da bayanin Nuratu ya sata jin wani irin ƙaiƙayin baƙin ciki a zuciya fuuuu ta wuce nasu sashen itama. Sai Mamy da Oum da Abah da Fawzan kawai aka bari. Cikin ɓacin rai Fawzan ya ce, “Wannan yarinyar sam bata dace da Ajwaad ba wlhy Abah. A haka kuke son aura masa ita tana abu kamar ƴar daba. Daga zuwan yarinya taji mata wannan mugun ciwon a fuska. Haka dama ɗazun a asibiti tayi akan Lilly, tana wani tambayar wai ba itace tasan labarinta ba, uwar mi ta sani to? Mi aka gaya matan akan su Shahidahn”.
Cike da mamaki Abah ya ce, “Wace Lilly da Shahidah?”.
“Lilly dai daka sani Manaal da Shahidah na Kano”.
Wani irin girgiza zuciyar Mamy tayi, haka Oum ma sai da ta ɗan rumtse ido. Yayinda Abah ya furta, “Fawzan kasan mi kake faɗa kuwa? Da gaske kake yi?”.
“Wlhy Abah da gaske nake yi. Itama an kwantar da ita a asibitin ne shine suka shigo duba Auta”.
Wani irin lumshe idanu Abah yayi zuciyarsa na masa nauyi a cikin ƙirji........✍️


















✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖5️⃣3️⃣




______________


........A ɓangaren Maanal kuwa bayan fitar Shahidah text ta turama RK dan tana son su ƙarasa maganar da suka fara. Ko minti biyu ba'a cikaba kuwa da tura saƙon sai ga kiransa ya shigo. Kamar bazata ɗauka ba ta dai daure ta ɗaga ɗin tare da saka hans free kawai. Sallama tai masa da sassanyar muryarta da a yau rauninta ya sake fita fili. Shima sai ya amsa mata da tashi sassanyar muryar. Tare da faɗin, “Gani a compound ɗin ku”.
Sosai mamaki ya kama Maanal, harta kasa ɓoyewa sai da ta furta, “Wasa kake amma?”.
Murmushi yayi mai sautin da har taji, “Da gaske nake my queen, dama ina gidan kusan minti goma kenan bana son takura miki ne kawai, harma ina shirin juyawa sai kuma ga saƙonki”.
Ajiyar zuciya Maanal ta sauke, zuciyarta na sake ƙarfafata akan RK ɗin. Tabbas bata buƙatar yin rayuwar aure da kowa. Hasalima bata da burin yin auren kwata-kwata. Amma tasan iyayenta da ƴan uwanta bazasu bari ba. Sai kuma Ajwaad, dole ne ta tabbatar masa da abinda yake ganin bazata iya ba. Zatai auren a cikin zuri'arsa kodan tabbatar masa da wannan Maanal ɗin ta yanzu tafa banbanta da wadda ya sani a baya. Miƙewa kawai tayi ta ɗan gyara hijjab ɗinta na salla da har yanzu bata cire ba, sai ɗan turare data ƙarama jikinta ta fita. Babu kowa a falon dan su Barrah na tare da Abbansu basu dawo gidan ba. Kitchen ta shiga ta ɗauka ruwa a tray da glass cup. A karo na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login