Showing 123001 words to 126000 words out of 221978 words
Chapter 42 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
farko ta nufi falon baƙi sannan ta fita compound inda RK yake. Iso tai masa zuwa falon baƙin, hakan sai ya sake bashi mamaki sai dai baice komai ba ya bita.
Koda suka shiga ita ta zuba masa ruwa da kanta sannan ta zauna. A karan farko da yaji ya kasa daurewa ya furta, “Gaba ɗaya sai mamaki kike bani. Gani nake kamar bake ba”.
Guntun murmushi kawai Maanal tai masa. Sai kuma ta kallesa. “Idan kiɗa ya canja itama rawar canjawa take yi ai. Ina son ka san yanzu muna akan gaɓar serious ne”.
“Hakane. Nima hakan nafi so mu kasance ɗin Maanal. Na kuma ji daɗi da godema ALLAH daya kawo mu wannan gaɓar ɗin.”
A hankali ta haɗiye ƴan kwallar data ciko idanunta. “Ɗazun mun fara magana sai dai bamu ƙarasa ba, shiyya nace kazo yanzu dan in sha ALLAHU kamar yanda na sanar maka gobe zan wuce Kaduna.” batare da jiran amsarsa ba ta miƙa masa diary ɗin data shigo da shi a cikin wata kyakkyawar bag. Amsa yay yana ciro sa daga jakan, sai kuma ya ɗan jujjuya shi a cikin hannunsa sannan ya ɗago ya kalleta. Itama shi take kallo, dan haka ta janye nata idanun.
“Na yarda da kai fiye da yanda kake zato. Badan komai ba sai dan wasu dalilai. Sannan kai ɗin koba komai jinin Oum ne. Wadda nake kallo uwa nagartacciya bayan mahaifiyata. Kaje da wannan zaka samu dukkan tarihin rayuwata data shuɗe a ciki, dan in har akwai abinda na rage ban rubuta ba to zai kasance ƙalilan ne, ko kuma baida muhimmanci. Bayan ka gama karantawa zaka iya sake tun-tuɓar Oum dan sake samun gamsuwa. Daga nan sai ka yanke dukkan hukuncin daya dace koyaya ne zan amshe shi. Dan ALLAH in har baka gama karanta shi har ƙarshe ba kada ka kirani a waya, kada kazo kaduna.” daga haka ta miƙe tsaye, shi dai kallonta kawai yace yama rasa abin cewa.
“Dare ya farayi sai da safe”
A karo na farko ya ɗan ja numfashi ya fesar, sai kuma ya jinjina mata nasa kan yana miƙewar shima. Haka suka fito a tare kamar wasu kurame. Dai-dai nan motar Abdull ke shigowa gidan. Duk tsayawa sukai suna kallon motar har wanda ke ciki suka gama fitowa. Da mamaki RK ya furta, “Abdul-hakeem”. Sai kuma ya juya yana kallon Maanal. Itama shi ɗin ta kalla, tare da faɗin, “Ka sanshi ne?”.
Kafin ya bata amsa Yaseerah ta fito da Huznah, fuska duk facin bandage musamman ɓarinta na dama. Nufarsu RK yayi, dan haka badan taso ba itama tabi bayansa. Duk da Abdull yayi mamakin ganin RK a gidan sai ya danne, sai da suka gaisa RK yake tambayar abinda ke faruwa idonsa akan Huznah. Bayani Abdull yay masa a taƙaice. Kamar RK ɗin zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yana kallon Maanal.
“Inaga ni bara naje, ki musu iso ciki ko?”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa, sai kuma tai masa ALLAH ya kiyaye hanya tai gaba abinta batare da tace ma su Yaseerah komai ba.. Suma komai basu ce ɗin ba suka bita kawai, yayinda Abdull yake ta satan kallon Maanal ɗin. A ransa yana raya aji da nutsuwar yarinyar, gata ƙyaƙyƙyawa da wani skin nata mai ɗaukar hankali da yay ƙaranci ga matan wannan zamanin da suka maida kansu fararen dole da bleaching.....
Gaba ɗaya Shahidah kasa cewa komai tai da bayanin Abdull ɗin. Dan Yaseerah taso su ɓoye amma Abdull ya kware zance ga mijin Shahidah abinsa, dan shi dai namiji ne babu ruwansa. Godiya sukai musu, suma suka miƙe suna musu sallama dan dare ya fara. Dama ita Maanal bama ta tsaya a falon ba ganin kallon ƙurullar da Abdull ɗin ke mata a kaikaice duk da kuwa hijjab ne a jikinta har ƙasa. Ko bayan wucewarsu da Huznah ta shigo ɗakin Maanal bata kulata ba, tanata ma haɗa ƴan abubuwan da zata wuce da su Kaduna ne kawai. Itama Huznah ɗin bata kulata ba tai kiran mamanta a waya. Basu wani jimaba sukai sallama dan ta sanar mata ne kawai zata dawo Kaduna gobe....
_______________★
A Kaduna kam kamar yanda Daddy ya faɗa sunje Kebbi garin Giro asalin tushen su Maanal. Sai dai an samu saɓani tsakaninsu da manyan da ya kamata su gana da su. Dan kuwa an tabbatar musu kakarta da babanta da baffanta sunje Kaduna, wani kuma babban Senator ne ya aiko aka ɗaukesu a mota wai zasuje wajen Asiya daya tabbatar musu yasan a inda take.
Rasama abin faɗa Daddy yay, Dan ya rasa yanda zai fassara zancen musamman akan batun senator da suka ce. Haka dole suka baro garin gwiwa a sage. Basu iso gida ba sai dare, zuwa lokacin kuma kowa yay barci, sai dai hakan bai hanashi zuwa ya sami Ammie a sashensa ba tana jiransa. A kallo ɗaya da yay mata ya fahimci hankalinta a matuƙar tashe yake kuma.......
___________★
Washe gari Shahidah, Maanal, Huznah da yara suka tashi da shirin wucewa Kaduna. Dan yaran ma babansu yaje school ɗinsu ya daidaita komai. Jirgin ƙasa zasu bi, dan haka Uncle Sadeeq ɗin da kansa ya kaisu train station bayan sallar zuhur. Basuyi ko mintuna goma ba suka wuce. Koda suka iso Kaduna Amaal ce tazo ɗaukarsu. Dan ita kaɗai tasan da zuwan nasu sai Hajiya Basariyya. Itama saboda Huzna ne ta sani ɗin.
A dai-dai sashen Ammie Amaal tayi parking motarta. Bata ko gama kashewa ba Huznah tai ficewarta daga motar. Da kallo duk suka bita, sai kuma Amaal ta taɓe baki da faɗin, “Wawuya kawai”. Babu dai wanda yace komai tsakanin Maanal da Shahidah. Sai ma ficewa da sukai daga motar suma. Itama Maanal bata jira su ba tai sashen Ammie da sauri, dan kewarta take sosai, burinta kawai ta ganta a jikin Ammien. Da sallama ta buɗe ƙofar, sai kuma ta ɗan tsaya turus tana kallon yarinyar dake ƙoƙarin buɗe ƙofar itama alamar zata fito. Yarinyar Maanal ta zubama ido. Dan sam bata santa ba. Itama dai yarinyar kallonta take yi. Sai kuma ta nuna ƙofar dake da takalma kusan ƙafa goma tana faɗin, “Ki shigo mutanen gidan suna ciki. Muma baƙi ne yau muka zo”.
Kamar Maanal zatai magana sai kuma ta jinjina kai kawai tayi gaba, a ranta tana maimaita zancen yarinyar da daga gani zatai ɗan karen surutu. Sallama ta sake yi bayan yarinyar ta matsa ta bata hanya, batare da jiran amsa ba kawai ta shiga ɗauke da handbag nata tana faɗin, “Ammie, Hameed, Waleed wai duk kuna in......”.
Turus ta haɗiye sauran maganar sakamakon saukar idanunta akan Ammie dake zaune kanta a sunkuye kamar ma tana kuka. Da sauri ta saki bag ɗin hannunta ta nufeta, a gabanta ta durƙusa tare da riƙo hannunta tana mai leƙa fuskarta. “Ammie miya sameki kamar kina kuk....?”.
Nan ma ta kasa ƙarasawa ganin fa da gaske kukan Amma keyi. Amma sai Ammie ɗin ta sakar mata murmushi da sake jimƙe hannunta cikin nata tana ƙoƙarin sharce hawayen da ɗayan hannun. Ina tuni Manaal da zuciyarta ta tsarga tai wata irin juyawa tana kallon wanda ke cikin falon. Nene ta fara kalla. Sai Daddy, sai wani dattijo daya sata ɗan sakin baki, tana kai dubanta ga wanda ke a gefensa ta miƙe zambar, jikinta har wani tsuma yake ta nuna tsohuwar dake a gefen mutumin da ta zuba mata idanu. Sai dai kuma ta kasa ma magana lips ɗinta ne kawai ke ɗan karkarwa. A hankali Ammie ta riƙo hannun nata cikin tsawatarwa ta ce, “Manaal minene haka kike yi. Ki zauna ki gaishe su”.
“Ammie never!!”.
Ta faɗa wani irin kuka dake zuwa maka batare daka shirya ba na kufce mata. Hannunta dake cikin na Ammie ta warce ganin mutumin ya yunƙura ya miƙe da alama wajenta zai nufo. Tuni tai ƙofar dake cikin falon da gudu abinta tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi da taɓa zuciya. Duk kallo suka bita da shi. Yayinda mutumin ya furzar da zazzafar iskar bakinsa maƙoshinsa na wani irin kaikawo a wuyansa da sauri-sauri alamar shiga tsananin damuwa. Tsohuwar nan ya kalla, itama kallonsa take cike da damuwa. Kanta ta ɗan girgiza masa. Sai ya sake furzar da huci mai kauri yana komawa ya zauna a inda ya tashi saboda maganar da tsohon nan yay masa.
Nene ce ta katse shirun nasu da faɗin, “Kuyi haƙuri mu bata lokaci zata huce. Kunga ana saka ran sai ma gobe in ALLAH ya kaimu zata iya tazo gata ma tazo yau babu zat.......” Sauran maganar ta maƙale sakamakon shigowar Shahidah da Amaal dake dariya Barrah da Haneeff biye da su... Sororo Amaal da Shahidah sukai suma cikin wani yanayi, sai Shahidah ce tai ƙarfin halin juyawa ta ɗan kalla Ammie. Ganin kan Ammie a gefe ita bama kallon ta inda suke take ba ya sakata maida kallonta ga Amal da itama ta ɗago. Sai kuma duk suka maida kan suka duƙar ƙasa fuskokinsu na sake bayyanar da fushinsu. Nene ce tai ƙarfin halin musu sannu da zuwa. Sai kuma ta nuna musu wajen zama na kujerun dake kusa da su.
Wani irin tsuma jikin Babu dake tsaye kamar ma wanda ya daskare yake, gashi ya zubama Amal da Shahidah idanu kawai...
“Shahidah bakuga baƙi bane?”.
Nene ta faɗa cikin son katse musu yanayin. Kallonta duk sukayi, da ido tai musu nuni da mahaifin nasu. Wani irin taunar lips Amal tayi, sai kuma tai yunƙurin barin wajen tana hawaye. Ganin haka yasa itama Shahidah yunƙurawa zata bar wajen da sassarfa, amma sai carab Babu ya riƙo hannunta. Cak ta tsaya hawayen da take riƙewa na rige-rigen zubowa.
“Shahidah”.
Ya kirata cikin tsananin taushin murya da sanyi. Hawayenta ta share tare da juyowa cikin dakiya ta kallesa. Hannun nata ya saki, dan duk da ba kallon raini ta masa ba ko wulaƙanci har tsakkiyar ransa yaji nauyi da tasirin kallon. Batace masa komai ba itama tabar wajen tabi ƴar uwarta data shige ɗakin Ammie. Duk abinda ke faruwa a idon kowa ne harda Daddy dake a falon, hatta Ammie datai uwar watsi da su tana kallonsu ne ta gefe ido......
Tsohon nan ne yayi murmushi, da faɗin, “Masha ALLAHU girman ɗan mutum ba wuya. Shekara bakwai da wasu watanni kawai da bamu gansu ba sai duk suka canja mana kamar ba su ba”.
Murmushi Nene ta sake yi mai faɗi, “A sosai su Maanal duk sun canja musamman ma Maanal ɗin. Dan wannan gaba ɗaya ba waccan Maanal ɗin da kowa ya sani bace ba. Sai dai muyi fatan kuma yanzu ALLAH ya kawo miji na gari”.
A tare suka amsa da Amin. A hankali Ammie ta miƙe tana faɗin tana zuwa. Babu wanda ya dakatar da ita ta nufi ɗakin da Maanal ɗin ta shiga, dan tafi tsoron yanayinta fiye da na Amaal da Shahidah. Gashi taga su ɗakinta suka shiga, ita kuma Maanal nasu ta shiga.....
Fitowar ta daga bayi dai-dai da shigowar Ammie ɗakin. Juyawa tai da sauri zata koma cikin bayin Ammie ta dakatar da ita.
“Maanal!”.
Cak ta tsaya sai dai bata juyo ba. Sai ma hawaye dake rige-rigen zubowa daga idanunta wanda dama su takeyi tunda ta shiga wankan. Cikin ɗacin murya da fitar sautin kuka ta ce, “Ammie waya kawosu garemu? Mi sukazo yi mana? Mi suke buƙata kuma yanzu a garemu. Ko anan ɗin ma sun zo su koremu ne? Sun zo su sake tozartamu a idanun mutanen arziƙinmu na nan ne suma? Ko sunzo su sake shegantamu su aibanta ki.....” kuka yaci ƙarfinta ta kasa cigaba da maganar. Hannu Ammie takai ta share hawayen da suka wanke mata fuska itama. Tare da matsowa kusa da ita, hannunta ta riƙo tare da juyo da ita suna fuskantar juna...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣4️⃣
______________
......... “Maanal!”.
Ammie ta kira sunanta cikin rawar murya tana mai share mata hawaye da sakin murmushi mai ciwo. Da ƙyar ta sake ƙoƙarin yin magana amma ta kasa saboda muryarta dake neman sarƙewa. Sai kawai ta jawo Maanal ɗin jikinta ta rungumeta tsam-tsam. A tare suka saki kuka mai ƙarfi.
“Ammie kice su tafi, bana son ganinsu wlhy. Sam bana ƙaunar sake ganinsu a rayuwata. Ko tunasu nayi ƙara jin tsanarsu nakey.....” yanda take magana cikin kuka itama Ammien cikin kukan ta ce,
“Shiiiiii bana son irin wannan maganar sam Maanal. Shi ɗin mahaifinku ne. Ita ɗin kakarku ce. Sunada muhimmanci mai girma da hakki a kanku. Koma mi kike tunani ki bari kinji, wannan tsakanin ni da su ne. Kuma ai komai ya wuce ko”.
“Bai wuceba Ammie, bakuma zai wuce ba, har abada kuma bazai wuce ba. Ni dai kawai su tafi. Idan ba hakama zan bar musu gidan. Gara na wuce na koma Abujan. Idan sun wuce sai na dawo”.
“Babu inda zaki je Autana. Kin san yanda nayi kewarki kuwa. Wata nawa ban ganki ba sai video call da bai gamsar dani. cikin lallashi Ammie take maganar, tare da kama Maanal suka koma bakin gado. Sosai take matuƙar ƙaunar Autar ta, dan ita ta fuskanci jarabawa guda uku ne a lokaci ɗaya. Shiyyasa ta fisu jigata da galabaita. Ga babbar jarabawar ciwo mai haɗari da take tare da shi. ALLAH ma dai ya ƙaddara tana da sauran kwana da tuni ta zama tarihi a cikinsu. Shigowar Nene ya katse Ammie daga lallashin Maanal ɗin. Kofin hannunta ta miƙama Maanal ɗin da faɗin, “Ga masoyiyar taki tunda kun mamemu, muda ke muku shirin zuwa wani satin biki sai kawai ku diro mana yau babu notis ja'irai kawai”.
Hannu takai ta share hawayen da suka gagara tsaya mata. Fuskarta a ƙwaɓe ta ce, “Ni garin ya isheni Nene kuma ina kewarku sosai.”
Cike da dabara irin ta manya Nene ta sanya dariya da dungure kan Maanal. “Ja'ira baki son garin amma gaki nan kinyi ƙyau ai. Nifa har wani ɗan ƙiba naga kinyi ma, ji kumatu dan ALLAH ko Asiya?”. Ta ƙare maganar da kallon Ammie tana jan kumatun Maanal. Murmushi Ammie tayi cike da ƙara jin ƙaunar Nene dake tamkar mahaifiyarta a yanzu, ta matuƙar taka rawar gani akan lamarin Manaal musamman a sanda take a halin mutuwa da rayuwa. Ta jinjina kanta da share sauran hawayenta tana faɗin, “Sosai kuwa Nene. Autah tayi ƙiba ba kamar sanda ta dawo sarvese ɗin nan ba. Ga fatanta yay wani kwanciya luff abinta halan ma bata tunawa damu ne a can”.
Da sauri Maanal ta waro idanu akan Ammie, sai kuma ta shagwaɓe fuska da faɗin, “Kai Ammie kema kina biyema Nene ko?”.
Dariya Nene da Ammie sukayi a tare. Nan fa suka cigaba da tsokanar Maanal har sai da sukaga ta ɗan sake tasha kunun gyaɗar da Nene ta kawo matan. Ammie da kanta ta ɗakko mata kaya ta tashi ta shirya. Tana ƙoƙarin maida towel ɗin datai wankan cikin toilet Daddy yay sallama....
___________★
A bala'in hargitse Hajiya Basariyya ke kallon Huznah. Hakama sauran ƴan uwanta. Sai kuma duk suka zaburo kanta suka baibayeta suna tambayarta accident tayi?. Babu wanda ta iya amsawa a cikinsu, hakan yasa Hajiya Basariyya ta kama hannunta kawai suka shiga bedroom. Kamar jira take suna shiga ta rungume mahaifiyar tasu tana mai fashewa da kuka. Ƙanƙameta itama Hajiya Basariyyar tayi hankalinta na ƙara tashi. Sai dai bata iya cewa komai ba har sai da Huznah tai kuka sosai sannan. Ruwa ta bata tasha kafin ta tambayeta abinda ke faruwa.
Huznah bata ɓoyemata komai ba daya faru tun daga zuwanta Abuja har yau da suke tahowa. Shiru tayi tana nazarin komai daki-daki. Ta jima shiru kafin ta miƙe tana cema Huznah, “Tashi kije kiyi wanka zan saka Afrah ta kawo miki abinci da magani, sai kisha ki kwanta ki huta zamuyi magana anjima”.
Kai kawai Huznahr ta jinjina mata itama....
Ɗaki Hajiya Basariyya ta shiga tare da ɗaukar waya tayi kiran aminiyarta. Bugu biyu kuwa ta ɗaga, ko gaisawa basuyi ba ta ce, “Aminiya akwai matsala fa?”.
“Matsala kuma Aminiya! Tami?”.
Tsaf ta zayyane mata komai da Huznah ta sanar mata. Cikin jinjina al'amarin Maman Yaseerah ta ce, “Eh lallai akwai matsala. Dan kuwa Darma family da su Majdiya jini ɗaya ne, auren zuminci ne tsakanin Aliyu Darma da babbar yayarsu Fateema. Amma Aminiya miyyasa tun farko baku sanar min cikakken sunan yaron ba?”.
“Wlhy nima iyakar abinda na