Showing 45001 words to 48000 words out of 221978 words

Chapter 16 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

dole mukai gaggawar barin ƙasar da ita. Tashin hankali yasani manta wayar da number ɗinki ke ciki. Jiyan nan muke dawowa”.
A hankali Maanal ta sauke numfashi da faɗin, “ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. A wace anguwa take?”.
“Amin ya rabbi nagode sosai. Zakije dubata ne kike tambayar anguwarsu?”.
“Ina ruwanka to. Kai dai ka faɗa min mana”.
Murmushi yayi daga can har tana iya jin fitar sautinsa. Sai kuma ya ce, “Okay ba damuwa zan tura miki address ɗin. Sai dai kuma yanzu ma na kiraki ne akan batun aikin can. Sun buƙaci ganinki, sai ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu kamar around eleven thirty haka zanzo na ɗaukeki”.
Wani irin sanyi ne ya tsargama Maanal. Amma sai ta danne cikin dakewarta ta ce, “Miyyasa bazaka bani address ɗin ba kawai naje da kaina”.
“Kina tsoron na saida ki ne?”.
“Ai nasan nafi ƙarfin siyarwa”.
“Hhhh haka dai kikace. Bari na barki ki kwanta lokacin barcinki na wucewa. Sai nazo”.
Daga haka ya yanke kiran kafin tace komai. Murmushi ta saki itama, ta jima da fahimtar bayan naci RK ɗan rigima ne na bugawa a jarida. Sam daga ganinsa baya jin magana. Bazatace tana sonshi ba. Amma wasu abubuwa nashi sun ɗan fara birgeta kaɗan. Fasa kwanciyar tayi, ta tashi ta ɗauro alwala ta hau nafilfilin neman nasara da zaɓin alkairi akan wannan aiki. Duk da dai dama tunda aka tsira zancen taketa gayama ALLAH. Tayi raka'a biyun farko ta sallame ta ɗauki wayarta ta turama Ammie text. Tasanta bata wasa da ƙiyamullaili, kusan za'ace ma ita suka gado dan tun suna yara tai musu wannan horon na ibada. Kuma Alhamdullah su dukansu sun horu da wannan tarbiyyar tata. Dama itace mai ɗan raunin cikinsu lokacin tana a ganiyar rashin ji. Amma yanzu Alhamdullah kam komai ya sauya kamar yanda jiyanta ta zama tarihi mai ciwo da raɗaɗin tunawa agareta.....




*_WASHE GARI_*


Da safe ta sanarma Shahidah da mijinta komai. Sun tayata murna da fatan alkairi suma. Ta kumayi waya da Ammie da Daddy dan itace da shi jiya da yau. Hakama Amal. Bayan wucewar su Shahidah nasu ayyukan itama tai nata shirin. Kasancewar ta mai jinkirin shiri yasa ten nayi ta fara shirin nata. Sai ya zam kafin eleven ma tayi ta gama komai duk dama bawani shiri bane na'azo a gani. Amma tayi ƙyau sosai cikin Abaya ƙirar saudia baƙa. Daga ciki ta saka wandon jeans blue mai duhu da farar riga datai mata ƙyau. Ɗan kwalin abayar kawai tai rolling a kanta ta saka turare mara ƙarfi bayan na wuta da kayanta keyi dama jikinta gaba ɗaya da yuni gyara yasa ƙamshi ya kama. Sai ƴan tarkacenta data haɗa a hand bag ɗinta sannan ta fito. Kitchen ta shiga ta saka ruwa a ƙyaƙyƙyawar bottle water ɗinta ƴar zamani sai ta ɗan saka Linda ta daka mata snacks da basa rabo da shi a gidan kaɗan wai ko taji yunwa. Dan ta tsani sayen abincin waje a rayuwarta. Shiyyasa da wahala kaga Maanal ta fita anguwar data san zata yini babu wani abin ci a tare da ita. Tun Ammie na faɗa har ta saka mata ido ma. Falo ta dawo ta zauna kasancewar akwai sauran mintuna ashirin, sai kawai ta buɗe novel ɗinta ta cigaba da dubawa. Tanayi tana ɗan cin shawarma ɗinta guda ɗaya data ɗakko da drink a kofi. Batafi mintuna goma a wajen ba kira ya shigo wayarta. Ƙaramin tsaki taja a ranta tana addu'ar ALLAH yada ba Yazeed bane ba. Numfashi ta ɗan sauke ganin RK ne. Sai da ta kalla agogo sannan ta ɗaga. Yau dai bai roƙaba ta gaishesa. Sai shi kuma batare daya amsa ba yace ta fito gashi a waje. Sake kallon agogo tayi da mamaki ta ce, “Akwai fa sauran ten minutes”.
“Oh kona koma sai ya cika na dawo?”.
“Humm”. Ta faɗa kawai tana yanke wayar. Linda ta ƙwalama kira. Da sauri sai gata tana faɗin, “Yes Aunty kina bukatar wani abu ne?”.
“No Linda zan wuce ne dai. Dan ALLAH ki kula sosai da gidan duk da dai nasan kina ƙoƙari dama. Ai baki manta ba dai Didi tace kima Uncle tuwon shinkafa ko?”.
“Eh aunty ban manta ba har ma na ɗora”.
“Yauwa to yayi, sai su Barrah kuma kisaka musu white rise kin san bazasu ci tuwon nan ba. Tunda akwai stew a fright kema kin huta kenan. Nima na wuce sai na dawo”.
“To aunty, ALLAH yasa ayi nasara. Amma ke baza'a miki komai ba?”.
“No Linda na huttashsheki kinji, bamma san ni sanda zan dawoba. Komai na dawo na samu a gidan zanci bye”.
“Okay bye bye”.


Tunda ta fito ya wani zuba mata idanu ko ƙyaftawa bayayi kamar yanda ya saba. Bashi kaɗai ba kowa na faɗa a zuciya ko'a fili Maanal ƴar gayu ce gata kuma ƙyaƙyƙyawa. Ko bada kwalliya ta saka kaya ba zakaga sun mata ƙyau. Balle kuma ace tayi kwalliyar ai abin sai wanda ya gani. Gata dai ba fara ba, amma da wahala namiji ya kalleta bai sake mata kallo na biyu ba duk ustazancinsa da kamewa. Badan tafi sauran mata ƙyawu ko wani abu ba, a'a itama kamar kowacce mace take, kuma komai nata irin na kowacce mace ne. Sai dai yanayinta na kamewa da ɗaure fuska kan taka musu birki wajen yimata magana ko fuskantarta kai tsaye. Sam bata da sakewa da mutane, sannan bata da yawan fara'a ko magana sai a inda taso yi ko ga wanda taso yimawa....
Sai da ta tsaya a gabansa ta ɗan yamutse fuskarta da babu walwala sam. Dan bata son kallo sam, ko yaya ake kallonta takan tsargu taji a jikinta, shi kuma taka kallo ɗabi'arsa ce. Yanda take faman yamutse fuskar da sake ɗaureta ya sakashi sakin murmushi da warware hannunsa daya harɗe a ƙirjinsa. Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai nauyi a bakinsa yana sake zuba mata idanun. “Wannan ɗaure fuskar fa? Ko duk laifin rashin cikar lokacin ne?”.
Maimakon amsa masa zancen nasa sai kawai ta basar tace masa, “Ina kwana?”.
“To lafiya ba ƙalau ba”.
Kamar zata sharesa sai kuma ta ɗan kallesa. Fuska ya marairaice mata kamar wani ɗan yaro. Janye idanun nata tai kawai. Shima sai ya saki murmushi. Ƙofar motar ta buɗe mata yana faɗin, “Bismillah”. Komai batace da shi ba ta shiga. Shima ya zagaya nasa ɓangare ya shiga. Motar yayma key suka fice a gidan. Sai da sukai ɗan nisa a tafiya ya kalleta kaɗan ya maida hankalinsa ga titi. “Nace miki ina lafiya amma ba Lau ba, baki tambayeni mike damuna ba?”.
Hankalinta na'akan novel ɗinta ta amsa masa da, “Ai banga alamar ciwo a tare da kai ba. Nasan neman maganarka ne”.
“Oh oh, ni Rafeeq bin Kasheem. Ni har wani neman maganane da ni kuma?”.
“Humm”.
Kawai tace a taƙaice. Shima sai ya murmusa yana mai jinjina miskilancin yarinyar nan. Bai sake cemata komai ba sai zuwa can a bazata yaji tana ce da shi “Yaya jikin Aunty?”.
Har cikin rai yaji daɗi, dan haka ya amsa mata fuskarsa ƙawace da murmushi. “Jikin Aunty babba Alhamdullah. Duk da dai yau ban leƙata ba sai zuwa anjima. Da ƙyar ma na kuɓuto kaina a asibiti dan na zo na kaikin nan.”
“Ai sai da nace ka barni naje kawai”.
“Bazan iya hakan ba ai. Shi abu mai daraja killacesa ake. Kaffa-kaffa da shi kuma akeyi. Fatana ma na samu na ɓarar da waccan gwamnatin data tare min ko'ina. Sai kuma nayi sakaci wasu ƴan bani na'iya su shigo neman hanyar min kutse?. Ko baki yarda ba”.
“Kaima kasan mi kake nufi”.
“Ki rantse kema baki sani ba?”.
Shiru ta masa. Dan tama gaji da surutun. Yasa ko fahimtar labarin batayi ma. Sun iso katafaren comyanin *_MAWAAD_* daya tsaru da gini na zamani. Gashi babba sosai ta yanda hasashenta bai taɓa hasaso mata ba. Yanda aka tsara ƙaton harabar wajen da furanni koraye da jajaye harma da wasu kalolin abin ƙayatarwa, ga kwalta lafiyayya shimfiɗe. Hatta ababen hawa na ma'aikata an fakasu ne cikin tsari da birgewa. Bawani hauma-hauma ko hayaniya. Sai securitys dake kula da tsarin shiga da fitar kowa a wajen hatta cikin harabar. Dole ne wajen ya birgeka, dan duk iyayin mutum idan yazo *_MAWAAD COMPANY_* sai tsarinsa ya birgeka..........✍️










✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖2️⃣2️⃣




.........“Ya kikaga companyn?”. RK ya katse mata tunaninta. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tare da juyowa ta ɗan kallesa. Ganin shima ita ɗin yake kallo sai ta ɗauke kanta kawai. Cikin ɗan yamutse fuska ta ce, “Balaifi komansu da tsari gaskiya. Sai dai ina fatan ba ƙawar gini bace kawai”.
Dariya ya ɗan yi a taƙaice. Ya ce, “Maanal bari na baki a buɗe, Mawaad Company ko kamfanin Rolex bazasu nuna masa yatsa ba a ɓangaren agogo. Basa ɗaukar ma'aikaci sai wanda yasan abinda yake yi. Sannan babu zancen sai ɗan wane ko sanayya, akwai turawa ma'aikata anan tun daga Chinese harma da Europe da sauran ƙasashen baƙaƙen fata. Komansu da ƙa'ida da doka yake tafiya. Kayansu ba kayan yara bane, manyan sarakuna da attajirai ke iya sayen kayansu a kowacce kusurwa ta duniya, tunda kikaga turawan nan da larabawa na tururuwar amfani da agogunan Mawaad ai ba sai na cigaba da cewa komai ba. Barama dai na daina cewa komai, ke da kanki zakizo kina bani labari watarana in sha ALLAHU. Abinda nake so dake dai ki nutsu wajen interview nan. Dan harda boss ɗin companyn da kansa za ai miki ita, ina nufin CEO na companyn. Duk da dai nasan banda matsala dake in sha ALLAHU. ALLAH ya bada sa'a da nasara idan alkairi ne. Muje na rakaki har ciki. Zan jiraki har ki kammala sai muje ki duba Aunty babba ko?”.
“A'a ka koma wajen aikinka kawai ba damuwa. Idan na gama zan koma da kaina. Tunda bamu san yanda abin zai kasance ba. Duba Aunty kuma basai ka kaini ba zanje da kaina ne”.
“Hummm” ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi. Daga haka suka fito a tare. Idan ka gansu dolene su birgeka matuƙa. Dan sun dace da juna. A jere suke tafiya cikin tsari da nutsuwa. Dan shima RK dai-daita tafiyar tasa yay data Maanal duk da kasancewarta mai sanyin tafiya da tsantsar nutsuwar iya taku. Sam bata da hauma-hauma ko garaje a tafiya ita. Sun tsaya a haɗaɗɗiyar ƙofar wajen data kasance ta zallar gilashi, koda yake bama ƙofarba shi kansa ginin akwai gilashi sosai a cikinsa shiyyasa ya zauna da ƙyau kaikace ba'a Nigeria kake ba a wata Chaina ce can dan sune mayu. Sai dai kuma a cikin Abuja wannan ba komai bane kasancewar akwai gine-gine na ƙawa da ƙasaita da sukafi Mawaad Company komai ma. Duk da sanin da securitys ɗin ƙofar sukaima RK sai da ya saka I'd card ɗin aikinsa akan wani computer sannan ƙofar ta buɗe masa da kanta. Ya gaisa da securitys ɗin idanunsa akan Maanal datai kicin-kicin da fuska. Juyawa yay ya musu ɗan taƙaitaccen bayani a kanta. Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai...
(Eh lallai ashe kallo na daga ciki) cewar Maanal a zuciya. Dan kuwa tabbas Companyn nan ya ginu da iya nasa tsarin da ƙawa. Sun fara iske reseption, anan suka tsaya suka saka sunansu sukai signing kamar yanda tsarin Companyn yake ga baƙo ga ma'aikaci, kafin ma'aikatan dake a floor na farko, zamu iya cewa wani department ne anan na sashen Companyn, duk sun duƙufa aiki, yayinda wasu ke faman kai kawo da uzirin gabansu daya shafi aiki. Tunda suka shigo wasu ke kallonsu, wasu na zungurar wanda basu gani ba, yayinda wasu ke ƙuskus, wanda ke ɗan kusa da su kuma na gaishesu. RK kaɗai ke amsawa, Maanal kan ɗan jinjina kanta kawai itadai tana mai kallon komai. Daga haka suka isa ga elevator, shi ya danna ta buɗe, ya mata nunin ta fara shiga sannan shima ya shiga. Shine ya sake daddana number floor ɗin da zasuje sannan ya matso kusa da ita yana magana a hankali. “Kin fara ganin yanda tsarin yake ba?”.
Maimakon amsa masa da baki sai ta ce masa, “Uhmm”. Kawai, dai-dai nan suka iso inda suke son zuwa. Sai da ta gama buɗewa suka fito. Sun samu matashiyar budurwa ɗauke da files a hannu zata shiga elevator ɗin. Tana ganin RK ta saki ɗan murmushi da faɗin, “A'a ashe shiyyasa yau garin kamar da hadari, ashe babban baƙo ne damu a Mawaad”.
Murmushi yay mata da amsa mata da, “Kedai masheranciya ce Labibah. Ykk ya aikin?”.
“Babu wani sharri sai gaskiya. Aiki gashi nan muna ciki. Nikuma ina lafiya”.
“To Masha ALLAH. Iji dai boss na nan?”.
“Humm zaune kuwa. Kasan baya wasa ai sai da dalili ko zai leƙa office ɗin gwamnati. Yanzu naga ya dawo dan ya shigo da safe sai kuma ya fita.”
“Okay, to bari mu ƙarasa”.
“Babu damuwa. Sis.. barka tunda shi ya kasa gabatar min dake”.
Karan farko Maanal data ɗauke kai daga garesu ta ɗan juyo ta kalleta. Hannu ta bata kawai alamar suyi musabaha batare da tace komai ba. Sai shine ya ce, “Labibah bazaki taɓa canjawa ba. Da kinyi haƙuri ai zanzo da ita har office ɗinki ne idan na gama da boss”.
“Ato shike nan babu damuwa kuje. Nima zanje office ɗin CMO ne”.
“Okay tom ba damuwa sai mun fito”.
Daga haka ta saki hannun Maanal ta shige elevator ɗin su kuma suka wuce. Office ɗin Assistant ɗinsa shine farko kafin na boss dake ciki. Ya tarbesu da girmamawa alamar akwai sanayya tsakaninsa da RK ɗin sosai. Dan RK ɗin yata tsokanarsa kafin yace masa bari ya sanarma boss ɗin zuwansu. Ita dai Maanal hankalinta ma nakan ɗan bin Office ɗin da kallo. Komai tsaf kuma ƙal babu wani tarkace ko hayaniya. Baifi mintuna huɗu ba ya fito yana sanarma RK oga yace ya shiga shi kaɗai. Murmushi kawai RK yay da ɗan girgiza kansa. Kafin ya matsa inda Maanal take zaune dan shi dama yana daga tsaye ne.
“Kinga ina zuwa. Minti biyar kawai”.
Kanta ta jinjina masa batare da nuna damuwar da yay tsoro ko ɓacin rai daga fuskarta ba. Daga haka ya wuce ita kuma ta ciro novel ɗinta daga bag ta cigaba da karatunta. Shima Assistant ɗin barin Office ɗin yay da alama akwai inda zaije. Kusan mintina huɗu sai gashi ya dawo. Mazauninsa ya koma ya zauna bayan ya ajiyema Maanal ruwa da lemo. Baice mata komai ba itama batama kulashi ba balle kallon abinda ta ajiye. Tana nan a zaune fin mintuna goma sannan RK ya fito. Zama yay a kusa da ita yana bata haƙurin daɗewarsa. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Ba komai”. Ta maita hankalinta ga book ɗinta. Shima dai wayarsa aka kira, dan haka ya miƙe ya fita aka sake barinta ita da Assistant. Suna nan a haka wani ɗan abu dake desk ɗinsa yay ƙara, miƙewa taga yayi ya nufi hanyar officer ɗin ogan kamar yanda suka faɗa. Bai wani jima ba ya dawo, cikin mutuntawa yace mata ta taso suje. Littafinta ta saka a bag ta miƙe batare da tace dashi komai ba. Ta wani elevator ba wanda suka shigo ita da RK ba suka shiga da Assistant ɗin, cikin sakanni ya saukesu inda suka nufa, koda suka fito nan ma sai taga offices ne a wajen. Sun shiga wani waje da alama ta nuna conference room ne, sai dai bai ƙarasa da ita can ciki ba ya nuna mata wajen zaman daga nan ta inda aka shirya kamar masauƙin baƙi. Tana zama wata ta kawo kofin coffee ta ajiye mata da drink. Atare suka bar wajen ita da Assistant ɗin sai ita kaɗai kenan. Babu abinda ta taɓa ta sake ciro novel ɗinta ta cigaba da karatu......


Fin tsahon mintuna talatin tana a wajen babu wanda ya sake zuwa, har ranta ya ɗan fara sosuwa sai ga wasu mutane uku sunzo sun gittata sun shiga conference room ɗin, tsakanin inda suka bin da inda take akwai ƴar tazara, shiyyasa bata wani shaida kowa ba. Bayan shigewarsu fin mintuna biyar wasu biyu suka sake wucewa, kasancewar bata ɗago ba a yanzu sai da suka gama shigewa taji motsin rufe ƙofa. Ƴan mintuna kaɗan Assistant ya zo wajenta yace ta shiga. Kanta kawai ta jinjina masa tare da maida book ɗinta a bag ta miƙe. A ranta tana mamakin wannan abu kamar wulaƙanci, ana tattalin ɗaukar ma'aikaci da alama su nan yanga sukeyi. Da wannan tunanin ta tura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login