Showing 87001 words to 90000 words out of 221978 words

Chapter 30 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

a office”.
“Ban yarda ba kuwa. Zauna in ba hakaba nasa Fawzan ya riƙe min kai na maka ɗura”.
Dariya sosai Fawzan yake yi, ya ce, “Tsaf kuwa zan danne miki shi Oum dan wannan girman jikin nasa da ƙarfuna suka bubbuɗe ba tsoro zai bani ba.”
Harararsa AA yayi, dan dole yakai hannu yaja kofin gaban Maanal da tunda ya shigo tai masa kallo ɗaya ta maida kanta bata sake ba, daga tsayen da yake ya kai shayin bakinsa, dai-dai Maanal ɗin tana ɗagowa ta kallesa da mamaki, hakama Fawzan da Oum duk kallonsa sukayi. Amma ya wani basar kamar bai gani ba. Sai Oum ce tai masa nuni da kujera. “Maza zauna tunda kadai san babu ƙyau shan abu daga tsaye”.
Baice komai ba ya zauna ɗin, sai faman kallon agogonsa yake yi alamar dai a ƙagare yake. Barrah da Haneeff ne suka fito daga kitchen tare da mai aiki. Dan sunce su noodles zasu ci shine taje dafa musu suka bita. Ganin AA ya sasu nufosa, cikin haɗa baki da ɗokin ganinsa sukace, “Uncle good morning”.
A mamakin kowa sai ya saki murmushin nan nasa na rowa tare da shafa kawunansu ya na amsawa. “Good morning Handsome & Oum na. Fatan kun tashi lafiya?”.
“Uncle Alhamdullah”.
Suka faɗa cikin haɗa baki. Murmushi ya sake sakar musu da cewa, “Masha ALLAH”. Daga haka ya miƙe yana ajiye kofin da sauran shayi a inda ya ɗauka. Sai Maanal ta samu kanta da tsurama kofin ido kawai har yay sallama dasu Oum ya fita kafin ta farga. Yaya Fawzan ne ya katseta. Kayan shayin ya tura gabanta yana faɗin, “Haɗa wani shayin tunda ya shanye miki kinji Lilly”.
Ɗan murmushin yaƙe Maanal tayi, cikin muryar nan tata mai sanyi ta ce, “Yaya akwai a ciki ya isheni”.
“Kin tabbatar?”.
Kanta ta jinjina masa. Oum dai Murmushin ta take irin na manya batace komai ba. Sun kammala breakfast ɗin babu jimawa sai ga RK. Da gudu su Haneeff suka maƙalƙalesa suna murna. Hakan yasa Oum sake fahimtar akwai shaƙuwa sosai tsakaninsa da yaran. Fawzan ma har yanzu yana a sashen Oum ɗin suna hira, sai kawai RK ɗin ya baje aka dora da shi bayan mai aiki ta haɗo masa breakfast dan yace bai karya ba. Anan falon ya karya suna hirar, idonsa akan Maanal dake kwance kanta a cinyar Oum tana karatun novel ɗin nata na fama. Sai ƙara jinjina shaƙuwar Oum ɗin yake da Maanal ɗin, dan kuwa yanda Maanal ɗin ta saki jiki ya ishesa shaida. Musamman idan yay dubi da miskilancin tsiya irin na Maanal ɗin....


____________


Da mamaki Shahidah ke sauraren Linda dake mata bayanin fitar Huznah tun 8. Ranta ne ya fara ɓaci da iskancin Huznah ɗin. Yaya tana a gidanta amma bata da mutuncin da zata dinga gaya mata zata fita. Kai ko gaisuwa tunda Huznah tazo gidan nan bata jin ta mata. Shi kansa Abbansu Barrah duk kawaicinsa yau da safe sai da yay magana. Shine ma dalilin da yasa yanzu da zasuyi zaman breakfast taima Linda magana akan ta tado Huznah ɗin su karya. Amma sai take sanar mata wai ta fita tun 8. Da alama kuma anguwa ta tafi dan taci gayu.
Komai batace da Linda ɗin ba ta juya tabar dining ɗin. Bedroom ɗin ta ta shiga ta ɗau waya tayi kiran Ammie. A lokacin Ammie na tare da Daddy dan yau itace da shi. Bata ɗaga kiran ba har ya tsinke. Cikin hikima tacema Daddy tana zuwa dan wayar tata dama a silent take. Sashenta ta koma sannan tai kiran Shahidah ɗin. Bayan ta amsa gaisuwar da Shahidahn ke mata ta ce, “Mike faruwa da safen nan kira Shahidah?”.
Cikin matuƙar ɗacin murya Shahidah ta ce, “Ammie akan yarinyar nan ne Huznah. Nifa gaskiya ina jin tsoro. Tunda tazo fa ba zama take ba, da mun fita aiki take shiryawa itama ta fice gidan nan wani lokacin ma sai mu rigata dawowa. Yau kuma da take weekend ma kinji tun 8 tabar gidan nan. Ammie ina jin tsoron kar wani abu ya faru ace a zamanta nan ne ban saka ido a kanta ba fa”.
Numfashi mai nauyi Ammie ta sauke. Cike da nazarin maganganun Shahidah ɗin ta ce, “Kenan akwai dai abinda tazo yi Abujan, saboda uban ya barta suka jinginata da zuwa gidanki ta zauna. Ki kwantar da hankalinki in sha ALLAHU babu abinda zai faru. Zuwa anjima zan kira Yazeed nai masa bayani ya sanya ido a kanta tunda yana Abujar.”
Ajiyar zuciya Shahidah ta sauke cike da gamsuwa tace, “Yauwa Ammie hakan dai yafi kam gaskiya. Dan shi kaɗai ne maganinta nikam bajin maganata zatai ba tana ganin shekarunmu ɗaya. Yasu Hameed da Aunty Sakina”.
“Lafiyarsu ƙalau gaba ɗaya. Ya batun dubiyar da su Auta sukaje jiyan?”.
Gaban Shahidah ne ya faɗi, amma sai cikin wayancewa ta ce, “Lafiya lau Ammie babu wata damuwa. Dan yanzu haka ma barci takeyi”.
“To Alhamdullah, dan inata tunanin kar taje gidan mutane ta nuna bata son yaronsu. Ni kuma harga ALLAH yaron ya shiga raina saboda nutsuwarsa da sanin darajar mutane. Tunda al'amarin Yazeed ya koma wani iri gara ta haƙura da Rafeeq ɗin ayi a wuce wajen zaman nan nata damuna yake yi”.
“Ammie adai cigaba da addu'a, in sha ALLAHU komai zai dai-daita, nawa ma Maanal ɗin take, rigimarta ce ta sata gama karatu da da wuri amma da yanzu ne fa ma ya kamata ta shiga jami'a. Rafeeq kam baida matsala mutumin kirki ne. Ya cancanta ai masa komai, kuma sun dace da Maanal ɗin. Sai dai nasan akwai rikici Ammie.....”
“Rikicin mi kuma? Wani abu ya faru ne?”.
“A'a babu abinda ya faru Ammie. Kawai nasan janyewar Yazeed akan Maanal bazai kasance mai sauƙi ba. Dan yana matuƙar sonta, auren nan dan baida yanda zai yi ne kawai uwarsa tafi ƙarfinsa ne. Yanzu haka kullum cikin roƙon Maanal yake akan ta bari a haɗa bikin ayi gaba ɗaya zaifi samun kwanciyar hankali. Ni wlhy duk sai ma tausayinsa ya fara damuna”.
“Nima ina jin tausayin nasa Shahidah. Sai dai su haƙura da junan sai yafi alkairi fiye da yin, dan nasan wacece Hajiya Sadiyya. Komai zata iya yi kamar yanda ta faɗa. ALLAH dai ya kawo mafita cikin sauƙi. Bari anjima mayi wayar na bar babanku shi kaɗai ina wajensa kika kira”.
“To Ammie ba damuwa sai anjima”...........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣9️⃣




______________




.........A ɓangaren Huznah tana can gidan Yaseerah. Dan dama sunyi da ita yau da wuri zataje gidan kasancewar tunda tazo sai dai tayi zuwan fisha. Ta samu ko barci basu tashi ba. Saboda weekend ne mijinta na gida. Sai kawai ta shige ɗayan bedroom ɗin Yaseerah ta kwanta itama ta ɗora barcin da bata samu yi ba a daren jiya isashe.
Sai wajen sha ɗaya Yaseerah da mijinta suka fito. Suna a d/table zasu fara breakfast mai aikinta ke sanar mata zuwan Huznah ɗin. Mijin nata ta kalla tana ɗan murmushi. “Baby Uncle ɗinka fa ya rikita min ƙawata. Munata binsa kuma yaƙi bamu muhimmanci. Yakamata ka shiga lamarin nan haka nan”.
Murmushi yay shima dakai kofin tea bakinsa. “Ai dama na faɗa mata tun farko, shi bana wasan yara bane. Dama Uncle Fawzan ne da sauƙi, amma Uncle AA tab ɗin, ina tausaya mata ALLAH. Da zata ji shawarata da ta jima da manta ta taɓama saninsa kawai.”
“Bazan iya haka ba Abdul-hakeem. Dan a yanzu bani da wani burin daya wuce mallakar Uncle ɗinka.”
Muryar Huznah da basu san da zuwanta wajen ba ta ratsa kunnunwansu. Gaba ɗayansu juyawa sukai suna kallonta, ganin yanda hawaye ke sauka mata da gudu a saman ƙyaƙyƙyawar fuskar ta ya sasu miƙewa. Hannunta Yaseerah ta kamo ta zaunar a kujerar kusa da ita, itama takai zaune tana riƙe hannunta alamar lallashi. Shima zama yay mijin Yaseerah ɗin, wani irin tausayin Huznah na ratsa shi. Tabbas yasan ta ɗaukarma kanta abinda yafi ƙarfinta, amma ko ya cigaba da gaya mata gaskiya yasan ba lallai ta fahimcesa ba. Gyaran murya yay a hankali, hakan ya sasu ɗagowa su duka suka kallesa..
“In sha ALLAHU zan taimakeki. Sai dai ki sani wlhy Uncle AA nada wahalar sha'ani. Amma akwai mafita ɗaya da nake miki hasashen idan kin gwada maybe ki dace....”
Jikin Huznah har rawa yake ta ce, “Wace irin mafita ce. Komai wahalarta ALLAH zan gwada, komai ƙalubalenta kuma zan jure”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya sauke numfashi. “Batun yanzu ba nasan Grandma suna fama da Uncle AA yay aure. Kuma a yanzu haka ma suna gab da masa auren ne amma bani da tabbacin sun sama masa matar ko basu sama masa ba, duk da dai akwai wata sister ɗin mu dake sonsa matuƙa kuma naga duk dangi nason a gaɗasu aure, shine dai bai maida hankali ba. To ina ganin mafita ɗaya ce na baki number ɗin grandma, ko kuma ki shirya na kaiku ke da Yaseerah kamar zaku gaisheta sai muce ai ke budurwar Uncle AA ɗin ce. Idan ALLAH ya taimaka aka dace sai kiga ya amsheki dole bisa umarninsu. Hakan yayi miki?”.
Cike da zumuɗi ta amsa masa, tana share hawayenta ga dariya. Shima murmushi yayi hakama Yaseerah. Ya ce, “Sai ki zama cikin shiri dan sai nan da kwana uku”.
“Miyasa ba yau ba?”.
Ta faɗa cikin damuwa.
“Bata nan ne shiyyasa, amma ina saran dawowarta gobe ko jibi in sha ALLAHU”.
Ajiyar zuciya Huznah ta sauke. Badan taso hakan ba tace ALLAH ya kaimu. Dai-dai nan kira ya shigo wayarta. Koda ta duba sai taci karo da Yaya Yazeed. Mamaki ta kamata, dan hakan kan jima bai faru ba ganin kiran yayan nasu. Haka dai ta daure ta ɗaga dan tasan in har wayar ta tsinke bata ɗaya ba sai taci ubanta a hannunsa. Ko amsa sallamarta baiyi ba cikin kaushin murya ya ce, “Kina ina nazo gidan Shahidah baƙya nan?”.
Rawa jikinta ya fara, cikin karkarwar harshe tace, “Yaya wlhy bawani wajefa naje ba ina gidan Yaseerah ne nazo gaisheta”.
“Na baki mintuna ashirin kawai ki dawo gida. Idan ba haka ba hummmm!”. Ya yanke kiran. Kanta tai wani irin dafewa dan takaici, batama san ta fara antayama Yazeed ɗin zagi ba Yaseerah na tayata. Babu dai yanda zatai dole ta kimtsa mijin Yaseerah ɗin ya ɗauketa domin maidata da kansa. Dan hakan kawai zatai ta kuɓuta daga bala'in Yaya Yazeed. Dabarar tata kuwa ta taimaketa, dan ganin Abdul-hakeem ɗin ya sassauta tanadin da Yazeed ɗin yay mata. Sai dai duk da haka taci zagi da faɗa akan fitar sassafe babu kuma sanarwa. Ya kuma ja mata dogon gargaɗi akan in har ta kara fita a gidan wlhy sai ya mata dukan mutuwa.
Yana tafiya ta koma ɗaki tai kiran uwarta ta gaya mata tana kuka. Zage-zage itama Hajiya Basariyyar ta dinga yi da tsinar Yazeed ɗin. Sai da sukai san ransu ta koma lallashin Huznah da kwantar mata da hankali akan zatama Yazeed ɗin magana da kanta. Daga haka sukai sallama. Bata ko ƙara fita a ɗakin ba duk ɓuruntun da su Shahidahn keyi akan shirin tarbar baƙi su Oum. Sai ma nacin son samun AA take a waya amma hakan ya gagara. Da alama ma yayi blocking ɗin ta ne ita bata gane ba. Ai ko saita zauna tanata kuka. Sai da tayi mai isarta barci yay awon gaba da ita.....


___________★


Ƙarfe huɗu da kusan rabi danƙareriyar motar Fawzan ta iso gidan. Yana gama parking Barrah da Haneeff suka fice zuwa cikin gida aguje suna ƙwala kiran mamansu. Dariya Fawzan ya dingayi, dan shi ALLAH ya ɗaura masa son yara matuƙa. Kodan har yanzu ALLAH bai bashi bane. Dan matarsa bata taɓa ko ɓatan wata ba shekara shida kenan. Oum ma dariya take ma yaran. Maanal dai komai batace ba, sai ma jagorantar su Oum tayi zuwa cikin gidan. Sun sami Shahidah na ƙoƙarin fitowa tarbar su Oum, dan haka sukaci karo a ƙofa. Cike da wani irin farin ciki Shahidah da Oum suka rungume juna. Sai kawai Shahidahn ta saki kuka. Harga ALLAH tana matuƙar son Oum, dan mace ce ƴar halak da bazasu taɓa mantawaba a tarihinsu. Ta matuƙar taka rawar gani a garesu da Ammien su ta yanda baki yayi kaɗan ya bada labari. Itama Oum ɗin hawaye take da murmushi duk a lokaci ɗaya, ta ɗago Shahidah tana mai share mata hawaye. “Uhm-uhm kefa yanzu kin girma Sheedan Oum, ke uwa ce babbar yaya kuma”.
Dariya Shahidah ta shigayi, hakama Fawzan dan tuno wani abu daya shuɗe. Maanal ma dai murmushi ne mai faɗi akan fuskarta. Abinda a yanzu yake da matuƙar tsada da wahala a gareta. Sai da Shahidah ta saki Oum sannan ta lura da Fawzan, cike da mamaki ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni ALLAH wanake gani haka ya zama dattijo?”.
“A'a tsoho na zama ba dattijo ba”. Fawzan ya bata amsa yana hararta. Dariya duk suka sanya masa. Shahidah ta ce, “ALLAH kuwa ka yarda ka zama dattijo yanzu Yaya Fawzan”.
“Kema kin zama dattijuwar ai”.
Ya faɗa dai-dai suna kaiwa zaune a ƙayataccen falon nata. Dai-dai nan mijinta ya fito. Cike da mamaki idonsa akan Fawzan ya ce, “Kai kai wanake gani haka kamar Darma a gidana”.
“Ya arrahaman Busam!”.
Shima Fawzan ya ambaci sunansa yana miƙewa. A tare suka cafke alamar lallai sun san junan kuwa sani bana wasaba. Ai sai su Oum suka koma ƴan kallo. Sai da ƙyar Shahidah ta iya faɗin, “Nifa ban gane ba, wai dama kun san juna ne?”.
“Farin sani ma kuwa. Darma tare mukai degree master namu ai a Germany, sannan a yanzu haka akwai alaƙar aiki a tskaninmu. Kawai dai baya son zumuncine shiyyasa baki taɓa ganinsa a gidan nan ba.....”
“Wulaƙanci ai kai zumuncin kake so?”.
“Nadai fika tunda ni naje gidanka har sau biyu”. Cewar Abban su Barrah. Dariya Fawzan yay da faɗin, “Gori kenan. To yanzu ai gashi ALLAH ya kawoni, ashema ni ƙanwata kake aure kai wannan abin kunya da yawa yake”.
“Ato kaima dai ka faɗa”.
Cike da girmamawa Abban Barrah ya gaida Oum. Itama ta amsa masa da kulawa cike da farin ciki. Nan fa aka ɓalle taɗi tsakanin Oum da Shahidah, Fawzan da Abban Barrah. Yayinda Linda tuni ta cika musu gabansu da kayan ciye-ciye Maanal na tayata. Duk wannan bidiri da ake Huznah na ɗaki tana shaƙar barci abinta. Sai da Maanal ta taje ɗakin ajiye kaya ta ganta baje a gado. Komai bataceba ta ajiye ta dawo wajen su Oum. Sai ga RK da dama yay musu alkawarin samunsu a gidan. Nan fa hirar ta ƙara armashi dan tuni Abban Barrah ya janyesu sun koma falon baƙi dan Oum ta sake itama suyi tasu hirar. Hakan yama Oum ɗin daɗi sosai, dan ta samu tattauna abubuwa da yawa da Shahidah wanda Maanal ta kasa sanar mata komai saboda zurfin ciki da miskilanci. Sai da akai magriba sun dawo Huznah ta fito. A ɗan yatsine ta gaishe su, sai dai saukar idanunta akan Fawzan yaso birkita mata lissafi. Sai da ta nutsu ta fahimci ashe ba AA ɗinta bane kammanni ne kawai. Dan suna kama sosai da AA ɗin, sai dai wasu abubuwa da suka ɗan babbanta su. Hakama kuma suna kamanni da Oum matuƙa. Hankalin Huznah ne ya tashi, dan haka kawai take ji a ranta wannan mutumin na kama da AA ɗin ta hakama matar, sai dai yanda ta gaishesu yasa daga amsa gaisuwar kowa ya watsar da ita musamman RK da kamar basu ƙaunar juna ita da shi.
Su Oum na gidan nan har tara, dan har sai da Autan ta ya kirata yana damunta shi dai ta dawo ya koma gida tun ɗazun duk basa nan gida babu daɗi kuma yana jin yunwa. Dariya Oum take masa da tsokanarsa akan wannan hali nasa na ɗafa, ya girma amma bai san ya girma ba koda yaushe yana laƙafe da ita. Idan tai masa aure yaya kenan. Shi dai roƙonta ya cigaba da yi akan su taho kawai. Tace shi bazai zo ya samesu anan ba yace ya gaji. Ƙyalesa tai tace gasu nan tahowa. Amma wayar Maanal fa ba'a gyara bane?. Sai cemata yay eh wai mai gyaran yace sai Monday ma.
“ALLAH ya kaimu” ta bashi amsa tare da sanar masa gasu nan dawowa. Sosai Shahidah ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login