Showing 126001 words to 129000 words out of 221978 words
Chapter 43 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
faɗa miki shi na sani, itama kuma Huznahr na tabbatar shi kaɗai ɗin ta sani”.
Ajiyar zuciya Maman Yaseerah ta saki, sai kuma ta jinjina kanta da faɗin, “Aminiya wannan maganar tafi ƙarfin waya kizo kawai”.
“Okay in sha ALLAHU cikin satin nan kafin a fara bikin nan zanzo. Ai dole ma na shigo dan na fahimci al'amarin nan shiri yake so na haƙiƙa. Babu ruwana da wata alaƙar yaron da Majdiya, koma ya suke sai Huznah ta mallakesa tunda tana sonshi kuma yana da kuɗi”.
Dariya Maman Yaseerah tayi daga can, sai kuma ta ce, “Ina bayanki wlhy. Ni kin ma tuna min miya faru ne wai naga jiya Alhaji ya dawo da dare, yau kuma da safe naji suna waya da Alhaji Usman akan zai zo kadunar”.
“Wlhy bamu san abinda ke faruwa ba muma. Tashi mukai kawai muka ganshi a gidan. Ina shirin naje na bincika da safe sai kuma ga baƙi anyi ban san daga ina ba, naga dai ya shiga dasu sashen Asiya, yanzu kuma sai ga ƴaƴanta da Huznah”.
“To aiko kiyi azamar bincikawa. Dan al'amarin kamar ba ƙarami bane, ina kuma ƙyautata zaton wannan baƙin sun fito ne daga zuri'ar ita Asiya da yaran nata ne”.
“Iye! Ya akai kika sani?”.
“Ba tabbatarwa nayi ba nima. Amma ga Alhaji nan na shirin tahowa Kaduna ɗin ma, amma lallai akwai abinda ake ɓoye muku”.
“Tab ɗin cakwakiya kenan, a lallai dole ne na bincika, ko dama shiyyasa naga tun jiya Uwar ɗan ke cika da batsewa, ban san miya faɗa mata ba mai gidan, haka itama Asiyan duk tayi sukuku”.
“Humm munafukai, wannan gida naku ai sai ku, na tabbatar akan auren ƴayan nasu ne”.
“Wlhy fa sai mu. Kinga bara naje kozan samesa a sashen nasa zan kiraki daga baya. Amma ki farama Malam bayani akan al'amarin dai kafin na shigo, dan ƙilama zuwa gobe zan shigo kawai in sha ALLAHU”.
“To shike nan hakan ma yayi, sai na jiki”.
Daga haka sukai sallama kowa ya ajiye wayar. Shiru Hajiya Basariyya tayi zuciyarta cike da tambayoyi fal. Sai dai rashin makamar riƙewa yasa ta tattara komai ta ajiye gefe. Fitowa tai ta shiga ɗakin Huznah. Sai ta sameta ta fito wanka tana shafa mai. Zama tai har sai da ta kammala ta shirya ta taimaka mata taci abincin tasha magani ta kwanta sannan ta tashi ta fito. Sashen Daddy ta nufa, amma sai ta samu yana tare da baƙi. Haka dole ta fito bayan ta gaidasu dan ya haɗe fuska ta yanda bataga wajen wargi ba balle samun damar yin halin nata na munafunci..
Shima Daddyn ɗan girgiza kansa kawai yay yana mai kai ɗauke idanunsa daga kallonta. Dan yaji a ransa wani tsegumin ne kawai ya kawota......
____________★
*_TUNA BAYA.._*
Sautin kukanta a maimakon sallama daya karaɗe gidan ne ya saka mahaifiyarta da ƴan uwanta fitowa kusan a lokaci guda. Sai dai babu wanda yay magana sai ido da suka zubama ɗan saurayin yaron dake goye da ita a bayansa da ita kanta mai kukan.
Kallo ɗaya yay musu batare da yayi magana ba ya ƙarasa ga tabarmar dake a jingine jikin bango ya ɗauka ya shimfiɗa. Kafin ya sauketa a hankali tamkar mai tsoron yaddata ƙasa. Ita kam kamar wadda ta ɗosana a kan wuta. Yana direta a saman tabarmar ta wani sake ƙwallarewa da ihun kukan nata. Cikin ɗan nuna rikicewa da sake bayyana damuwarsa akan fuska ƙarara ya juyo gareta. Ƙafar da take ɗangalewa ya riƙe. “Banace kiyi shiru zan rama miki ba. Na rantse miki daga nan gida kawai zan shiga na ɗauka kekena har gidansu sai naje na rama miki. Sannan na masa dukan tsiya”.
“To ni ka tashi kaje”. Ta faɗa cikin taɓara da ƙara ƙarfin ihun kukanta. Bama ta gama rufe bakin ba ya miƙe. Fisha ya kalla matar dake tabbatar da mahaifiyar yarinyar ce saboda kamanninsu. “Ammie dan ALLAH ki saka min ruwan zafi a ruwa yanzu zanje na dawo zan gasa mata ƙafar”.
Cikin sauri Ammie tai ƙoƙarin dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Sai dai ina har ya fice da mugun hanzari da sassarfa. Kanta ta ɗan dafe tare da maida dubanta ga ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha ɗaya. “Amaal! Kinga maza bisa gida kicema Oum-Fadeel karta barsa ya fita”.
“To Ammie!”. Yarinyar ta faɗa cikin hanzari itama tana fisgar hijjab. Dai-dai nan Ammie ta dawo da kallonta kan yarinyar data sake wani ƙwallara uban ƙara tana tittirza ƙafafu da faɗin, “Ni dai kar a hanashi. Sai ya ramomini....”
Tsawa Ammie ta daka mata. Tare da nunata da yatsa. “Idan baki min shiru ba na rantse da ALLAH zan tsantsama miki jiki da magribar nan. Ai dama tunda naga kun jima baku dawo ba nasan kina can ɗaukar maganar da kika saba. Shima Ajwaad ɗin sakarai dake biye miki, kin tashi kin cire uniform ɗin ko sai na ci ƙaniyarki....”
Kuka ta sake fashewa da shi amma bamai sauti ba yanzu dan tana tsoron Ammie. Sai kuma ta nuna ƙafar tana faɗin, “Ammie nafa karye ne a ƙafar...”
“Karyewa?”.
Ɗayar yarinyar da zata kaiwa sa'an saurayin yaron, idan ma ta girmesa kaɗan ne dake tsaye tana kallonta ta faɗa kafin ma mahaifiyar tasu ta amsa.
“Eh wlhy Didi. Ba Najib ɗin gidan Maman Ayna bane ya bugeni da keke mun fito islamiyya. Kuma shine yaƙi tsayawa harda cema Besty wai in ya isa yazo ya rama min”.
Shigowar Amaal da wata ƙyaƙyƙyawar mata mai kama da yaron sosai yasa babu wanda ya tanka mata. Matar ta nufeta tana faɗin, “Subahanallahi Baby na miya faru?”.
Fuska ta taɓe tana satar kallon Ammie, sai kuma ta ɓarke da kuka tana nuna ƙafarta da shigewa jikin matar da takai kusa da ita zaune. “Oum ba Najib bane ya karyani a ƙafata. Kuma na kasa tafiya sai da Besty ya goyoni ma”.
Sosai Oum ta shiga faɗa tana dudduba ƙafar da faɗin in fa har taji ciwon da gaske bazasu yarda ba. Ammie da taga abin nasu bana ƙare bane ta katseta da faɗin, “Aunty ALLAH ki daina biyema iskancin Manaal. Ni yanzu ma sonake nasan baki dai bar Ajwaad ya fita ba ko?”.
Kafin Oum ta bata amsa Amaal ta ce, “Wlhy Ammie ya tafi, inata kiransa ko kallona baiyiba ma ya kwashi keke da gudu”.
“Innalillahi banga ta zama ba”. Ammie ta faɗa tana shiga ɗaki. Babu jimawa sai gata ta fito da hijjabi a hannu. Sai lokacin Oum ta dubeta tana dariya. “Wai ina zaki je?”.
“A binsa zan mana. Sai na bari a cutar min da yaro tunda ke naga kinama ɗaukar abun bada muhimmanci ba, in dai kika biye ta wannan yarinyar wataran sai ta saka har ke an kai station ɗin ƴan sanda” Bata jira amsar Oum ba ta fice abinta.
Fitowar Ammie a gidan dai-dai da isowar Ajwaad a kekensa rigarsa ta islamiyya a yage. Fuskar nan ciɗin-ciɗin ga goshinsa ya ɗan kumburo kaɗan, sai gefen lips ɗin da jini kaɗan shima. Da sauri ta nufesa tana riƙe keken da faɗin, “Innalillahi Ajwaad, yanzu faɗan kaje kayo saboda ALLAH. Anya wataran Manaal bazata saka a maka dukan da zaka kasa tashi ba a anguwar nan?”.
Cikin ɓacin ran da muryarsa dake fita can ƙasa-ƙasa ta kasa ɓoyewa ya ce, “Ammie ciwo fa yaji mata a ƙafa, sai na ƙyalesa yaci bulus? Ko yanzu ban ƙyalesa ba sai na jera sati ina masa duka”.
Ƙasa magana ma Ammie tayi ta zuba masa ido kawai. Har ya shige shi da keken gidan bata iya ta motsa ba. Wannan abota na bata mamaki tsakanin Manaal da Ajwaad. Wata irin abotace mai ban mamaki da tsayawa a zuciya. Basu kasance sa'anni ba dan ya girmeta sosai kusan shekara bakwai ne tsakaninsu ma, sannan basu kasance jinsi ɗaya ba. Amma akwai wata irin shaƙuwa a tsakaninsu da sam babu ita a tsakaninsu da ƴan uwansu na jini ma. Ita abun har tsoratata yake yi.........✍️
_Tofa wasa farin girki, 🥱🥱yanzu zamu koma tushe fa._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣5️⃣
______________
.......Su ɗin ƴan asalin jihar Kebbi ne, a garin Giro dake ƙarƙashin Suru LG. Aiki ne ya kawo mijinta nan cikin Kano kasancewarsa jami'in ɗan sanda. Ba Kanon suka fara zama ba. Sun zauna jihohi kusan uku a tsahon shekarun aikinsa. Sai dai shekara biyu data wuce aka maidosu nan cikin Kano suke zaune a anguwar sharaɗa. Yaransu uku ne duk mata. Shahidah itace ta farko, sai Amaal. Sai Manaal. Lokacin da sukazo Kano shekarar Manaal huɗu kacal, amma sai baƙar fitina a cikinta da shegen surutu. Manaal irin yaran nan ne masu shegen wayon tsiya da ɗan karan surutu kamar an musu ƙauri da kan akku. Ga ɓarnar masifa da jan faɗan tsiya. Sam bata ragama ƴaƴan jama'a dan ko anfi ƙarfinta saita ƙwaci kanta da cizo da bula ƙasa ko jifa. Gata suke mata matuƙa kasancewar itace kamar auta a gidan yanzu. Kowa ya kwaso abunsa zai ce Maanal. Musamman ma mahaifinsu da suke kira Baabu.
Dawowarsu cikin Kano sun samu abubuwan cigaba da dama, ciki harda ƙarin girma da Baabu ya samu, ita kuma ta fara kasuwancin turarruka da gyaran jiki irin na mata. Inda suke sabon wajene da aketa gine-gine, dan ko gidan dake a jikin nasu ma ana kan gina shi ne ba'a kammala ba. Sai dai an kusa kammala aikin. Hakan yasa kusan kullum zakaga mai gidan yazo da yaransa maza uku musamman ma weekend. Jefi-jefi sukan ɗan gaisa da Baabu idan anyi sa'a yana gida ko ya dawo wajen aiki. A haka ranar wata asabar yana gida suka tashi da shirin yin alala da yace yana buƙatar ci. Ammie ta kammala gyara wake ita da Shahidah da zata kai markaɗe. Sai kawai Maanal ta sanya rigima itama zataje. Cikin haushi Shahidah ta ce, “Dama kin bar damun kanki dan babu inda zanje dake. Haka kawai muje kita jibgar yaran mutane a gidan markaɗen kamar ranar da kika fasama ƴar mai markaɗen kai”.
Ihu Maanal ta sake ƙwallarawa tare da zubewa ƙasa tana burgima akan ita wlhy sai taje fa. Dai-dai nan Ammie ta fito da bulala da nufin tsula mata amma sai Baabu ya hana ta hanyar amshe bulalar ya ɗaga Maanal daga ƙasan. Daga haka ya fita da ita a gidan yana lallashinta. A dai-dai lokacin motar makwafcin nan nasa ta iso anguwar. Baabu bai wani maida hankalinsa ba dan baima san shi bane kasancewar bawai ya wani riƙe motar tasa bane. Sai da yay parking a gaban gidan nasa ya fito tare da matasan samarin ƴaƴansa uku sannan Baabu ya maida hankalinsa kansa. Sun gaisa cikin mutunta juna, yayinda suma yaran suka gaida Baabu da girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana mai shafa kansu, yayinda shima babansu yakema Maanal wasa.
“Ƴan samari yaya sunanku?”.
Cewar Baabu yana shafa kan ƙaramin su. Babban ne ya bashi amsa da. “Ni Fadeel. Wannan Fawzan. Sai Auta Ajwaad.”
“Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarku manyan gobe.”.
A tare suka amsa da Amin. Yayinda mahaifinsu keta faman murmushi saboda surutun da Maanal ke zuba masa. Sai kuma can ta kalla Ajwaad dake ta faman cin chocolate ɗinsa, cikin ɗan tura baki ta ce, “Kai yaron nan bazaka tsammin alawanka bane. Inata haɗiyan yawu amma sai sha kakeyi rowa haramun dai”.
Ba ƙaramin dariya ta basu ba. Banda Ajwaad ɗan kimanin shekaru goma sha ɗaya daya wani yamutsa fuska ya harareta ya ɗauke kansa. Sai Baabu da ya ɗan harareta shima. Amma ita ko'a jikinta ta maida kallonta ga Babansu ta na sake faɗin, “Abbansu kace masa ya tsammin raina ya biya”.
“Kinga manta da shi Babyna. Muje na baki ina da ita da yawa. Daga yau kuma kema ni Abbanki ne ba nasu su kaɗai ba.”
Cike da murna tace, “Eh”.
Gaba yay da ita zuwa motarsa. Ya fiddo chocolate uku ya bata biyu a hannu, tare da ɓare ɗaya ya sake miƙa mata. Cike da jin daɗi ta amsa. Tare da juyawa ta murguɗama Ajwaad baki da faɗin, “Mai rowa ɗan wuta. Nima kuma ga nawa”.
Harararta nan ma yayi. Yayinda su Fawzan sukayi dariya. Shiko Baabu duk kunya ta ishesa. Ƙarfin halin Maanal da banne a rayuwa. Shegen surutunta da wayonta da suka girmi shekarunta na tada masa da hankali. Duk inda ake neman fitinannen mutum aka samu Maanal an rufe littafi kawai. Sai dai yana mata fatan idan ta ƙara girma ta canja daga hakan.. ƙiri-ƙiri da zai shiga gida yace tazo suje taƙi. Dole babu yanda ya iya ya barta wajen Alhaji kamar yanda ya roƙa.
Yini guda Maanal na tare da Alhaji Aliyu Darma, Tare da yaransa uku da tuni ta saki jiki da su. Musamman Ajwaad da tunda ya fito da kayan wasansa ta naniƙe masa. Lokacin da rana tayi sai ga Shahidah da kula cike da alala an kawo musu. Sosai Alhaji Aliyu ya nuna jin daɗinsa tamkar ya ari baki dan godiya. Anan ma Shahidah tayi-tayi Maanal ta bita suje gida amma taƙi. Dole ta barta itama ta tafi. Sai da akai la'asar sazu tafi sanan su Fawzan suka rakata har gida da ledan kayan ciye-ciye da kulan da aka kawo musu alala sukai godiya. Yayinda ita kuma ta shiga kuka saita bisu, sai da Baabu ya mata tsawa sannan ta nutsu. Dan a duniya Maanal na tsoron hargagi musamman na Baabu..
Wannan rana itace sanadin tarayyar waɗan nan ahali guda biyu. Dan kuwa washe gari sai ga itama mahaifiyar su yaran ta biyosu domin yin godiya. Anan ne kuma ta tarar da Ammie nama wata amarya gyaran jiki, itama tace ai sai ai mata kuwa.. tunda tazo Maanal na manne da ita. Kasancewar yaranta ita duk maza ne tana masifar son ƴar budurwar yarinya, shiyyasa tana ganin Maanal da jiya tasha labarinta a wajen ƴaƴanta yarinyar ta shiga ranta. Ga wayonta da surutunta na sakata nishaɗi. Yau ɗin ma dai da ƙyar aka raba Maanal da su, musamman Ajwaad da wasansu na yau yafi na jiya armashi. Dan yau ya saki jikinsa ba kamar jiyan ba. Haka yake bashi da saurin sabo sam, akanyi baƙi a gidansu kwana da kwanaki babu ruwansa da su, dan shi yarone mai irin shegen tsantsenin nan, ga zuciyar tsiya da ƙulafucin iyaye. Ammafa idan ya soka to yaso ka kenan. Idan kuwa baka masa ba to babu abinda zakai masa ka birgesa ko kaja ra'ayinsa da shi. Shiyyasa a yau ɗin ma mamakinsa ya kasa barin Oum ganin yanda ya saki jiki a gidan tamkar a gidansu. Dan duk inda kaga Ajwaad yaje yaci maka abinci kansa tsaye to lallai yanayi da masu gidan....
★★★
Kafin Alhaji Aliyu ya kwaso iyalansa su tare a sabon gidan nasu daya haɗu matuƙa gaya shaƙuwa da zuminci mai ƙarfi ya shiga tsakaninsa da iyalan Baabu ta yanda har suna kallon kansu tamar wasu ƴan uwa na jini. Oum ba itace kawai matarsa ba, ashe tana da amarya ma, sai da suka tare su Ammie suka sani. Bayan tarewar tasu kuma sai al'amarin ya ƙara ƙarfi fiye da tunanin mai hasashe. Ba shaƙuwar ahalin biyu ne kawai abin mamaki ba. Wadda ke a tsakanin Ajwaad da Maanal tafi zama abin kallo ga kowa. Dan takai a yanzu ako ina ɗaya yake ɗaya na wajen, shiyyasa idan baka sani ba baka taɓa gane ainahin gidan kowannensu. Dan takai yanzu ma Maanal taƙi zama a makarantar da take yi da yan uwanta. Da safe anta dagama kenan tace ita Ajwaad zata bi tasu makarantar. Anyi lallashin, an daka, anyi kurarin duk a banza. Hakan yasa Alhaji Aliyu roƙar Baabu damar maida Maanal makarantar su Ajwaad ɗin, kasancewar itama tana tare da Nursery, primary harda da secondary ne a tare. Daƙyar Baabu ya yarda dan bashi da yanda ya iya, haka aka maida Maanal makarantar su Ajwaad amma a ɓangaren Nursery. Shiko yana a primary 3 ne. To ashe rigima bata ƙare ba, dan kuwa Maanal sam bata zama ajinsu saina su Ajwaad. Anyi-anyi amma taƙi, da malaman sukaga tanada ƙwalwar karatu matuƙa, dan duk abinda akayi kafin kace me ta ɗaukesa a kanta harma tafi wasu ƴan ajin sai kawai aka ƙyaleta.