Showing 153001 words to 156000 words out of 221978 words
Chapter 52 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
you”. Daga haka babu wanda ya sake shiga sabgar ɗan uwansa suka maida hankalinsu ga malamin. Tun daga wannan ranar sai ya zam duk wanda ya riga wani zuwa a cikinsu sai ya tanadarma ɗan uwansa waje a kusa da shi. Tun abin na musu kamar wasa har shaƙuwa ta fara tasiri a tsakaninsu. Sai dai babu wanda yasan komai daga rayuwar ɗan uwansa, karatun kawai suke yi har tsawon watanni. A hutun farko da suka farayi har aka dawo akaci kusan sati biyu babu Kamila, hankalin Fateema ya fara tashi ta fara bincike a wajen ƴan ajinsu, sai dai kowa kance shi bai san inda Kamila take ba ba tare ake ganinsu ba. Kamar wasa Kamila ta shafe watanni har biyu bata dawo school ba. Har Aliyu ya fahimci matsalar Fateema ya tambaye ta. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar masa, shiko dama yasan labarin Kamila a wajenta tun farko. Haka domin farin cikinta yazo har makarantar ya tayata bincike har ALLAH yasa suka samu wanda yasan gidan su Kamila ɗin. Shine yay musu rakkiya.
Sosai Kamila ta shiga matuƙar mamaki tare da jin ƙaunar Fateema a ranta. Suka rungume juna suna kuka. Aliyu ne ya shiga basu baki, inda sai a lokacin Kamila ta ganshi. Mutuwar tsaye tayi dan lallai bawan ALLAHn ya haɗu, ya kuma daki zuciyarta da nashi tsarin, amma sai ta danne. Da farko tayi zaton yayan Fateema ne kawai saboda tsananin kamanni da sukayi, dan haka ta gaisheshi da girmamawa da kiransa da sunan Yaya. Shima ya amsa mata kadaran kadahan dan babu wata mace dake birge Aliyu sai Fateemansa. Hatta sauran yara matan family ɗinsu sam baya sakar musu fuska. Anan soro aka masa shimfiɗa, su kuma suka shiga daga ciki.
Su Kamila talakawane sosai, sannan tana rayuwane a hannun kakarta Iyale. Ashe ciwone ya kwantar da Iyalen ita kuma Kamilar ke jiyyarta shiyyasa bata koma makaranta ba. Ta wani gefen kuma babu kuɗin da zataje tai buƙatun makarantar ma. Dan mahaifinsu kaɗai Iyale ta haifa, su uku kuma suka haifa duk mata. Mahaifiyarsu ta rabu da babansu tuni saboda tsananin rayuwar talauci da suke a ciki. Yayi yunƙurin ƙwacesu a hannunta amma sai ALLAH ya bata nasarar guduwa da yayarta da ƙanwarta. Ita kuma a lokacin tana hannun Iyale dan tun yaye dama take anan. To a yanzu hakan dai ance Maman nasu na Saudia tana tukari, suma ƴan uwanta biyu na'a tare da ita. Babansu na son karatu shiyyasa ya tsaya mata cewar zatayi, dan baya son nan gaba ƴan uwanta dake a wajen mahaifiyarta su fita cigaban rayuwa. To da ƙyar da ya ALLAHU aka haɗa kuɗin makarantar ta fara saboda takardunta sunyi ƙyau, sai kuma gashi tunkan aje ko'ina karatun na neman fara tangal-tangal, dama Sakandire ɗin ma dayaya aka gama, mahaifiyarta ce ke turo kuɗi. Ɗan tsakanin nan kuma ta ɗauke musu wuta saboda roƙon da Iyale ke mata akan ta dawo garesu kodan ƴaƴan dake tsakani.
Zuwan Fateema da Aliyu gidan shine ya zamewa Kamila rahama da tarin alkairi, dan kaɗan daga tarihinta da Fateema taji ya ɗaga mata hankali, suna dawowa gida ta sanarma Aliyu komai tare da roƙonsa ya taimakawa Kamila ta koma makaranta. Baiyi musu ba kuwa ya taimaka da iya nasa ƙarfi Baba Sardauna ya ƙarasa sauran shi kuma. Hakan ya zama sanadin komawar Kamila makaranta, aka kai Iyale asibiti, aka kuma bama mahaifinta jari ya fara sana'a tare da tsaya masa ya ƙara aure. Wannan hidima mai ban mamaki daga ahalin Fateema shine ya sake dunƙule Fateema da Kamila waje ɗaya, wadda zuwa yanzu ta fahimci Aliyu mijin Fateema ne Kuma yan uwane na jini. Tayi kuka sosai dan harga ALLAH Aliyu ya shiga ranta sosai, amma ta dannema zuciyarta tare da ƙoƙarin ciresa a ranta duk da tasan abu ne mai matuƙar wahala.
Haka wannan abota ta cigaba da tafiya, shaƙuwa da zumunta mai ƙarfi na ƙara tasiri a tsakanin Kamila da Fateema. Har takai Kamila kanzo gidan Sardauna tai kwanaki a wajen Fateema. Babu wanda ya taɓa ƙyamatarta ko ƙyararta balle kallon banza. Ƙyautata mata suke da iya iyawarsu har ma da iyayenta. Suna da shekara biyu sun shiga farkon ta uku a jami'a hankalin Fateema ya fara tashi da ganin bata sake samun ciki ba. Ta fara takurama Aliyu suje asibiti amma sai yay biris da ita. Ta cigaba da masa naci daga ƙarshe yace babu inda zaije. Haihuwa ta ALLAH ce kuma lokaci ce. Idan sukai hakuri lokaci yayi zai basu. Shi ba haihuwar yake so ba ita yake so. Sam kalamansa basu gamsar da ita ba, dan haka ta samu Kamila da ƙorafin. Amma itama Kamilar kasancewar bata san komai ba sai ta lallasheta da bata shawarar ta bisa a hankali ta kuma cigaba da yin addu'a. Hakan kuwa akayi, Fateema ta sake yin haƙuri, sai dai kuma ta kasa daurewa dan sosai take son haihuwa. Musamman daya kasance ta ɗanɗana haihuwar da daɗin ɗa a hannu taji. A wata ranar juma'a ta zagaye taje asibiti batare da sanin Aliyu ba. Acan ne fa ta jiyo abinda ya sakata yanke jiki ta faɗi dan tashin hankali, dan sai nemo ahalinta akai suka sameta a nan.
Hankalin Aliyu da Baba Sardauna da Umma ya tashi jin abinda Fateema tazo ta binciko, dan haka suka rufeta da faɗa musamman ma Aliyu, yayinda ita kuma take kuka mai ban tashin hankali da tsuma zuciya. Dole suka koma lallashinta kuma. Kwananta biyar a asibitin aka sallameta, ta koma gida da sabuwar jiyyar zuciya. Sai dai mijinta da iyayenta na tsaye a kanta da lallashi daban baki da nasiha. Dan har malami sukutum Aliyu ya ɗakko mata yay mata doguwar nasihar yarda da ƙaddara ga bawa. Alhamdullah hakan yayi tasiri zamuce, dan ta rage damuwa sosai. Gefe kuma ga Kamila itama tana sake tausar zuciyarta. Yin haka babu jimawa mutanen Saudia sukazo hutu gida, a lokacin kuma aiki ya maida Dr Kasheem Kura Paris dan haka sukazo hutu gida daga nan kuma can zasu wuce. A wannan ɗan zama ne Maryam (Mahaifiyar Fateema kenan ta asali) ta nutsu wajen yima ƴarta Fateema nasiha da nusar da ita karta sake saboda ƙaddaratta ta tauye ɗan uwanta kuma mijinta daga samun ƴaƴa daga wata matar, ta barshi ya ƙara aure duk wadda ta zo ta haifa kamar nasu ne su duka. Tun wannan nasiha na tada hankalin Fateema saboda dunbin soyayyar da takema mijinta harta fara tasiri saboda tausayi da ƙaunar da take masa ta haƙiƙa ce. Bayan tasha fama da yaƙi da kanta da tsananta addu'a bayan wucewar iyayenta da ƙannenta biyu ta tunkari Aliyu da batun ƙara aure. Wayyo ai ranar Fateema taga ainahin abinda ake kira tujara. Dan rufe ido Aliyu yay ƴamata tas, ya kuma tabbatar mata idan ta sake tunkararsa da wani batun ƙara aure sai ya ɓata mata rai fiye da haka. Shi yace mata yanada sha'awar zama da mace fiye da ɗaya ne. Koya sanar mata rashin haihuwarta matsala ce ga rayuwarsa. Ita yake so ai, zai kuma cigaba da rayuwa da ita a haka har ƙarshen rayuwa........✍️
_🥲Tofa rikitata_
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣7️⃣
______________
.........Bayan yin hakan kamar Fateema ta haƙura tabar Aliyu, zuwa wani lokaci kuma saita dawo da zancen. A wannan gaɓar ma sunyi rikici sosai da har ya kaisa ga kai ƙararta ga Baba Sardauna da Ummu. Dole sukai zama dasu domin sasanta rikicin. Sai dai a wannan sasanci ma bawai Fateema tabar wannan rikici bane, dan ko'a gaban su Baba Sardauna tace tana akan bakanta. Shima yace yana akan bakansa. Fateema ta cigaba da naci da takurama Aliyu akan batun aure da yaƙin son fahimtar da su Baba Sardauna dalilinta. Tun kowa bai fahimceta ba har aka fara goya mata baya. Musamman da taga su Baba Sardauna kamar basa so sai ta shirya tai tafiyarta gidan Kakanninta wato Alhaji Lawan mahaifin Kasheem Kura. Sai da ta bari hankalin Aliyu yay masifar tashi sannan ta bayyana kanta bisa tasota gaba da Baba Lawan ɗin yay suka zo gidan Baba Sardauna. A wannan zamane suka tattauna sosai Baba Lawan ya nuna musu Fateema ta fisu gaskiya, ya kuma kawo hujjoji da dole suka amsa kodan kasancewarsa Uba ga harsu su Baba Sardauna ɗin.
Duk da haka har a lokacin shifa Aliyu bai gamsu ba. Amma baice komai ba. Sanin halinsa yasa anan Fateema tace ayita ta ƙare dan karma yace ya fasa. Ya zaɓa a ƴaƴan dangi duk wadda tai masa in ma a gefe ne ma duk taji ta gani. Ai ko a fusace Aliyu ya balbaleta da cewar shi bai son kowa. Ita da tace taji ta gani sai ta kawo matar tunda ita zai aurowa dan ita ta damu. Dariya kawai su Baba Sardauna sukayi, dan sun tabbatar fa Aliyu bai ƙaunar batun ƙara auren nan sam. Aiko Fateema bata gusa ba tace to ga ƙawarta aminiyarta Kamila, tasan halinta tasan tushenta ta kuma yarda da tarbiyyarta. Wani mugun kallo Aliyu ya watsa mata kuwa. Itama ta murguɗa masa baki ta ɗauke kanta dan zuciyata ta gama rufewa ita dai kawai Aliyu yay aure su samu yara ace nasu ne.
Anan ma Aliyu yaso tirjewa. Amma sai su Baba Sardauna sukaita lallashinsa da ƙarfafashi. Badan yaso ba ya amsa kawai. Ammafa suna komawa sashensu ya balbale Fateema da faɗa itako ta masa banza. Ita dai tunda burinta ya cika yaje yayta yi. Anyi haka da sati ɗaya Fateema ta shirya taje har gida ta tunkari Kamila da zancen. Ruɗewa Kamilar tayi.
“Haba Fateema wace irin maganace wannan. Shin kina zargin ina son MIJINKI ne komi?.....”
Hannu Fateema tai saurin ɗaga mata. “Kinga Kamila kada ki sauya min magana. Ni ban taɓa zarginki da koda kwatankwacin hakan ba. Hakama mijina nasan wanene shi, dalilin ƙara auren ne kawai ya taso masa. Kamila da'aje a auro wadda ban san halinta ba tazo ta rabani da shi ba gwara wadda na sani nasan halinta tasan nawa ba. Ina sonshi Kamila so mai tsanani, bazan so wadda zata zo ta cutar damu ba, domin maganar aure fa ake ba hutu ko zaman wucin gadi ba. A gaba ɗaya na hanga na hango kece kawai halayenki sukai min dai-dai da rayuwar mijina. Na kuma tabbatar miki zai soki kamar yanda yake sona in sha ALLAHU in har kin cigaba da zama akan ƙyawawan halayenki. Ba tallarki nai masa ba, haka kema ba tallarsa nake miki ba. Cancantar kasancewar mu a inuwa guda mu uku kawai na hango. Ki taimaken Kamila kada kice a'a, dan cewar a'a ɗinki na nufin wata da ban sani ba zata shigo min gida. Bai zama lallai ta kasance mai ƙyawun zuciya irinki ba. Maybe ta rabani da shi, maybe ta maidani gefe maimakon farina ya koma ganin baƙina da kasawata. Amma ke fa. A tsahon shekaru uku da muke tare ina jinki tamkar jinina, tamkar wata twin sister ɗina da muka tashi tare muka girma tare. Dan ALLAH ki tausaya min, ki auresa kizo ki haifa mana yara mu haɗu mu rungumesu tare. Mu rainesu tare, mu basu tarbiyya tare, su tashi a tskaninmu tare. Ba'a auro wadda kota haifi ƴaƴan zasufi ƙarfina ba, su ringa min kallon matar uba ba uwa ba. Please na roƙeki”. Kuka ya sarƙe Fateema. Itama Kamila kukan takeyi, sun jima a haka kafin Fateema ta miƙe ta tafi, tare da bata damar yanke hukunci....
To bayan dai kai ruwa rana da faɗi tashi, da kace nace da ƙyar dai Kamila ta amince bisa tsayawar ƴan uwanta biyu da suka dawo Nigeria a lokacin tare da mahaifiyarsu. Sosai farin ciki Fateema ta nuna da amincewar Kamila, taje har gida tai godiya. Anan ne suka fara sanin juna da sauran ƴan uwan Kamila da kuma mahaifiyarta da a yanzu itama take ƴakin neman komawarta ga mahaifin su Kamila ɗin.
An fara shigi da fici akan auren Aliyu da Kamila, sai dai shi ango ya tare gabas ya tare yamma akan shi babu ruwansa. Da ƙyar ma ya amince yaje yaga Kamila a gidansu sau biyu. Dai-dai da lefe da sadaki duk Fateema ta biya. Dan kaf Family ɗin Baffa Ishaq Darma nada kuɗaɗensu a asusun bankuna tun daga manya har yara. Kamar yanda Fateema ta buƙata babu wanda ya saka mata hannu a hidimar wannan aure itace tai komai da kuɗaɗen asusun bankinta. Sai abincin taron biki ne da abubuwan da suka biyo baya Baba Sardauna ya sauke mata akan dole ba dan taso ba. Haka dai aka ɗaura Auren Aliyu da Kamila. A kuma lokacin ne Baba Sardauna ya bama Aliyu gidan zama, dan yace yakamata shima ya koma nashi da iyalinsa yabar gidan gandu. Hakan baima Aliyu ba, amma baya iya musu dole ya amsa. A sabon gida aka kai amarya Kamila, ita kuma Fateema tace sai bayan kamar wata guda zata tare. Da kanta taima ango rakkiya gidan amarya. Sai kuma bayan ta koma gida taci kuka harta godema ALLAH. Daga baya kuma ta maida komai ga ALLAH taita sallolinta harta samu natsuwa zuciyata tai fayau kamar ba ita ba. Sai ma walwalarta ta ninku a safiyar ranar. Har Aliyu da yazo gidan ya nuna jin haishin yanda ya ganta cikin farin cikinta. Wai ai bata kishinsa ta masa auren dole. Bayan dariya kawai bata kulashi ba ita dai. Tunda dai taci nasara sai fatan kuma ALLAH ya azurtasu da abinda ake nema...
To da farko dai zaman Aliyu da Kamila babu wani armashi. Dan bai taɓa kulata a shimfiɗa ba. Baya sakar mata fuska. Baya zama suyi hira. Takurar Fateema ma ke sakashi zaman gidan amaryar da cin abincinta dan yasan idan yaje can wajenta ba bashi zatai ba. Gashi ta saka masa takunkumin bayan sati ɗaya ta ƙara masa sati uku wata guda zai yi a wajen amarya. Su Umma kuma sun goya mata baya. Hakan kuwa dole ya cika wata gudan nan a wajen Kamila sannan Fateema ta tare a gidan, har lokacin kuma bai taɓa kusantar Kamila ba. Itako Kamila hankalinta a tashe yake, dan bata tabbatar tana son Aliyu so mai tsananin gaske ba sai a yanzu da suka zama ma'aurata. Yanda yake mata, ko duk motsinsa Fateema dai yasa ta fara jin kishin Fateema mai tsananin gaske a zuciyarta. A ganinta ba'ai mata adalci ba. Idan ance Fateema tasa aka aurota to ai dama bawa baya wuce ƙaddarasa. Tun ran gini tun dan zane. Koda sawar Fateema koda rashin sawa dama ALLAH ya ƙaddara sai Aliyu ya ta zama mijinta. Wannan zafin kishi daya fara taso mata yasa ta tunkari mahaifiyarta da ƴan uwanta da batun, maimakon su tausheta su lallasheta su kuma sai suka fara ɗorata a hanya mara ɓillewa. Aiko ta mitsithtsike ido ta nunama Aliyu bafa zata yarda ba. Dan yanzu matsayinta ɗaya da Fateemar da yake damun mutane da batunta. Tofa wannan abu ya tayar ma Aliyu da hankali, yo tunkan aje ko'ina kenan ma. Tab ɗin jan inji mata, ai dole yayma tufƙar hanci. Nan fa ya zauna ya warware Kamila tsaf da rashin mutunci, yo har a gayama bafillace zuciya da baƙar magana. Uwar watsi sukai yace taje gida za taga aike. Hankalinta ya tashi sai kuma duk ta gigice. Ita ina taga ƙafar tafiya gida tabar wannan daular da kowa ke mata barka da arziƙin shigowa. Sannan ma auren sati uku kawai ai wannan abun kunya ne da ko'a mafarki bata fatansa. Dole fa ta zubar da makaman yaƙi ta shiga neman afuwa da rusar kuka da ban haƙuri tana tabbatar da sharrin shaiɗan ne. Hakan ma bai saurareta ba, yace saifa ta tafi. Haka kuwa dole ta tafi gida batare da kowa ya sani a dangin Aliyu ba. Amma sai dai me, a ranar iyayenta suka maidota, suka kuma duƙufa bama Aliyu haƙuri suma da tabbatar masa ƙuriciyace ke damun Kamilar kawai. Amma yay mata afuwa ko Fateema kada ya bari tasan wannan al'amarin dan ALLAH. Suka kuma masa alƙawarin canjawar Kamilar fiye da yanda yake buƙata.
Badan dai Aliyu yaso ba wannan wuta ta mutu a haka. Sai dai kuma ya sharɗanta ma Kamila sharuɗai masu tsauri game da Fateema in har tana son cigaba da rayuwa a cikinsu. dole kuwa ta amsa da hannu bibbiyu tayi biyya. Sai dai kuma acan ƙasa ta ɗauke karatun uwarta da ƴan uwanta tsaf. A haka Fateema ta tare gidan itama. Da gaske Kamila ta kwantar da kai fiye da zaton Aliyu. Tana bin shariɗɗansa sau da ƙafa. Bawai shariɗɗansa kawai ba, da gaske Fateema mugun kwarjini take mata, dan matar nada wata irin baiwa da nagarta mai ban mamaki. Ga ƙyaƙyƙyawar zuciyar zama da kowa da gaskiya. Sai dai bata son raini, bata son munafunci da wulaƙanci. Wannan abinda Kamila ta sani ne tuni, dan haka ta shirya yaƙar Fateema da su har ma da Aliyu. Sannu a hankali kuwa suka fara tasiri, dan duk wata hanya ta gwaji Aliyu yabi akan Kamila game da zamansu bai kamata da kowane laifi ba. Sai ma yanda take bin Fateeman ya fara saka masa jin nutsuwar zama da ita. A gefe kuma ga Fateema kullum damuwarta da fatanta taga Kamila da ciki.
To tsakanin mace da namiji kwance