Showing 135001 words to 138000 words out of 221978 words

Chapter 46 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Oum da maganar tace ita dai babu ruwanta ya sanarma Aba. Bai Musa ba ya samu Aban da batun. Amma sai ya kwaɓesa akan maganar. Kai tsaye ya sanar masa bazai iyu ba. Suma zasuyi tasu tafiyar zuwa Adamawa suga gida...
Tafiya ta tabbata, amma ansha fama da badaƙala kafin Maanal ta yarda. Sun tafi tana kuka kashirɓan kamar zata shiɗe. Shima uban gayyar da taurin kansa yasa baiyi kukan ba da farko yana ganin sun wuce ya shige ɗaki ya kwanta a gadonsa sai ga hawaye. Daga ƙarshe da zazzaɓi ya yini ranar. Har washe gari sai da aka sanya masa ƙarin ruwa.
A ɓangaren Maanal ma kuka taci sosai har sai da Babu ya mata buyagi, itama ƙarshe zazzaɓi ya rufeta. Taita kwara musu amai a mota. Haka suka isa Kebbi tayi ligiff a wahale. Anan suka ɗan tsaya aka dubata. Washe gari suka ɗauki hanyar Suru da shima keda ɗan nisa daga nan cikin birnin Kebbi ɗin. Dan a ranar ɗin ma basu isa ba sai da zuhur..
Gari ne tsaka tsaki a komai. ba ƙato bane can sosai. Ba kuma ƙarami bane ba. Suna da wutar lantarki sannan akwai titi har a cikin garin. Kusan zaka iya samun duk abinda kake so naci ana saidawa musamman wanda ake mu'amala da shi ako ina kamar su kayan sanyi, kayan marmari, nama, da ire-iren hakan. Mutanen garin na neman ilimi gwargwadon iko, dan suna da manyan mutane sosai a ƙasar da ake damawa da su a gwamnatin jahar dana tarayya. Daga Suru hanyar Giro suka ɗauka, nan kam basu isa ba sai yamma sosai. Giro dai ƙaramin garine, amma ƙauyene mai ƙyau da ƙayatarwa. Tun kafin motar Babu ta isa labari ya iso gidansu. Lokacin da motarsa ta tsaya tuni yara sun zagayeta cike da zumuɗi musamman ganin harda baƙin fuska da basu sani ba. Dan duk sanda aka haifesu wasu kuma sukai wayo Ammi bata garin.
Tun daga waje zaka san gidan ƙaton gaske ne. Dan ƙofa ce wangamemiya ƙwarai da gaske. Sai ƙatuwar bishiyar ceɗiya da kufan wutar makarantar allo irin ta tsangaya an zagayeta da dutsuna. Gefenta kaɗan massalaci ne da ɗakuna a jere kusan guda goma ko muce shaguna da jikin bangonsu duk alluna ne. Jiki a sanyaye Ammie ta fito fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarfin hali. Yayinda su Shahidah keta kalle-kalle suna son tuno abinda suka manta musamman ma ita da aka tafi da ita da ɗan wayonta. Tuni yaran sun fara kwasar kayayyakin suna shiga dasu, yayinda su kuma suka bisu a baya Babu biye da su. Ɗakuna ne guda biyu masu kallon juna a farkon shiga. Ana hannun dama ke buɗe wani dattijo mai farin gashi fatt zaune kan buzu yanata rubutu a wani ƙatoton allo. A hanli Ammi ta cire takalman ƙafarta zuciyarta na mata ɗan sanyi, ganin haka yasa suma su Shahidah cirewa, yayinda Maanal ta dogara tana kallonsu...
“Barka da hutawa Baffah”.
Ammie ta faɗa a hankali kanta a duƙe dai-dai tana shiga cikin ɗakin. Sai lokacin tsohon ya ɗago ya ɗan kallesu fuskarsa da murmushi. Cikin kamala da tausa harshe ya furta, “Lale da mutanen garin dabo”.
Murmushi Ammie ta sake yi hakama Babu da ya shigo riƙe da hannun Maanal data dogare a ƙofa. Sai da suka kai zaune tsohon ya sake faɗin, “Ashe zaka cika alƙawari Habibu ka kawo min iyalanka na sake gani kafin na koma ga ALLAH?”.
Sosai Babu ya sake sunkiyar da kansa cike da girmamawa ya furta, “Ai min afuwa Baba, ai min afuwa”.
Murmushi tsohon yay mai faɗin gaske. Sai kuma ya miƙama Maanal dake ta faman kallonsa cikin zare ido hannu alamar tazo gareshi. Da sauri ta matsa jikin babanta tana maƙe kafaɗa alamar bazata je ba. Turata Babu yay yana mai daka mata tsawa. Cikin harshen turanci ya ce, “Wuce kije mana ban son raini”.
Duk da tsohon bajin abinda Babu ya faɗa yay ba sai yay murmushi. Dan ya fahimta ganin yanda Maanal ta zabura jiki na karkarwa ta matso inda yake sai dai duk a ɗarare. Bai ƙiba ya kama hannunta ya zaunar a gabansa. Cikin tausasa harshe ya furta, “Wannan shi ake gudu dama ai Habibu. Shiyyasa muke kwaɗayin ku ringa matso da iyalan naku gab damu koda lokaci-lokaci ne”.
“ALLAH ya huci zuciyarku Baba”.
Babu ya sake faɗa da sauri. Cikin sanyin murya itama Ammie ta nema afuwa. Kafin ta ɗora da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta bayan rabuwa. Hakama su Shahidah duk suka shiga gaishesa. Hannu duka ya miƙa musu alamar suzo garesa. Babu musu duk suka matsa. Sai da duk ya taɓa kawunansu sannan ya tambaye su sun ganesa?. Kai tsaye Shahidah tace ta ganesa. Amma Amaal na ɗan inda-inda. Ta dai san ta sanshi sama-sama. Sai dai a wancan lokacin bai kai haka tsufa ba. Gashinsa kuma bai furace kamar yanzu ba. Murmushi yay da akazo kan Maanal da yana tambayarta kawai ta fashe da kuka. Itafa harga ALLAH tsoronsa take ji. Musamman wannan farin gashin nashi dogo sosai daya zagaye ƴar ramammiyar fuskarsa. Ga farin rawani ya naɗa akan nashi. Lallashinta ya shigayi tare da bata farar alewa dake cike da wata ƙwarya a gefensa. Badai ta sha ba amma ta daina kukan.....
Sun jima a wajensa dan har duhu na neman rufawa kafin su shiga cikin gidan. Lallai ƙaton gaske ne da sassa daban-daban. Tarin manyan turamen daka dake a ƙarƙashin bishiyar dalbejiya a farkon shigowa gidan zai tabbatar maka da hakan. Sai runbuna da ake ajiye abinci da aƙalla sun kai kusan ashirin. Yara ne sosai a haka ma dan mangariba ta rufa ne wasu basa gida. Sai mata da akalla sun kai goma sha biyar dake tsaitsaye wasu ma daga su sai karin ƙirji. A hakan kuma ƙalilanne a matan gidan, waɗan nan wanda bazasu iya haƙuri bane saboda zumuɗin son ganin Ammie da yaranta.
Itama Ammien ganinsu yasa tuni ta manta da fargabarta. Fuskarta da murmushi ta nufesu. To suma dai bakunan nasu a washen suke. Duk da dai wasu fara'ar tasu bata kai ciki ba. Su dai su Maanal na raɓe jikin Babu da matan nan keta faman yima sannu da zuwa. Garama Shahidah da Amaal na ƙoƙarin gaishesu da kalmar “Ina yini”. Lallai shekara shida ba kwana shida bace. Suma sai kallon yaran suke da mamakin canjawarsu. Sun yi girma kuma sosai musamman ma Maanal da aka tafi da ita daga garin tana ƴar shekara biyu. Yanzu ko gashi tana ƴar budurwa shekara takwas ai ba wasaba su a wajensu. Dan yara sun ma fara kula samari. Kamar Shahidah kuwa masu sha biyar ai sun haihu ta biyu kota farko dana biyu a ciki. Kamar Amaal mai sha uku sune amaren wannan shekarar..
Har sashen gwaggo akai musu rakkiya. Inda anan ne ɗakin da Ammie tai rayuwa a ciki yake. Wajene aka dan katange da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Gwaggo mahaifiyar Babu ɗaya nata. Sai ɗayan na kishiyarta da bata wuce wata biyar a gidan ba ta fita. Fitar tata ce kuma ya ƙara mata baƙin jini a gidan da ma wajen surukar tata da bata samu sassauci ba sai da suka bar garin da zama. Gwaggon na saman wani ɗan dutse daga ƙofarta tana alwala. Sau ɗaya ta ɗago ta kallesu ta maida kanta. Amma haka Babu ya nufeta fuskarsa da fara'a yana faɗin, “Barkanki da wannan lokaci Gwaggona”.
Ganin haka itama Ammi da sauri ta matsa ta tsugunna tana faɗin, “Sannu Gwaggo! Mun sameku lafiya?”.
Maimakon ta amsa su su duka a daƙile ta jefama Ammie wani kallo ta maida idanunta akan su Shahidah dake tsaye suna kallonsu sannan ta maida ga Babu ta sakar masa murmushi. “Babana kasha hanya”.
Murmushin ƙarfin hali yayi dan abinda taima Ammin ya ɗan sokesa. Sai dai bai nuna ba ya danne abinsa ya maida mata da murmushin yana faɗin, “Aiko dai Gwaggo. Bara na je salla gashi har za'a shiga damma ina da alwala”.
Kanta kawai ta jinjina masa. Ya miƙe yana kallon su Shahidah dake rakuɓe suna kallon Ammie dake duƙe kanta a ƙasa har yanzu. “Ku kuma kukai tsaye anan. Ku shigo mana”.
Jikinsu a sanyaye suka ɗaga kawuna. Shi kuma ya fice batare daya waiwayesu ba zuciyarsa duk babu daɗi. Yasan dole sai haƙuri, dan hutun nan sam bazai zame musu na farin ciki ba sai abinda suka gani. Tsakaninsa da mahaifiyarsa babu wata damuwa. Amma yanda takema matarsa da yaransa abun na damunsa matuƙa. A ganinsa matarsa bata cancanci hakanba kodan hallacin iyayenta a garesa ya kamata Gwaggo ta rangwanta mata. Amma ina, ya rasa wace irin ƙiyayyace wannan mai zafi........✍️

















✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖5️⃣9️⃣




______________


Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR GOLDEN COLLECTIONS TA TANADAR MUKU KAYAN ADO N FITA KUNYA KAMAR SU ATAMFA,LACES ABAYA SHOES AND BAGS DA KAYAN DECORATIONS D FURNITURES A FARASHI ME SAUKI


__________


.........*_SU WAYE SU AMMIE?:-_* Alhaji Umar da mutane sukafi sani da Alhaji Umar Giro ɗan asalin jihar Kebbi ne a garin Giro dake ƙarƙashin Suru LG. An haifesa a babban gida da yay suna matuƙa a cikin garin Giro saboda kasancewarsu manyan mutane masu ƙarfin ilimin addini. Su kusan ashirin da bakwai mahaifinsu ya haifa, maza sunfi yawa, dan mata huɗu ne kawai a cikinsu, sauran su ashirin da uku duk maza ne. Malam Ibrahim shine mahaifinsu, sai iyayensu mata su uku. Ta tsakkiyar itace mahaifiyar Alhaji Umar, shi kaɗai kuma ta haifa a duniya, sauran ƴaƴa ashirin da shida duk na matan biyu ne. Dan matarsa ta farko haihuwarta goma sha ɗaya amma ƴaƴa goma sha shida duk nata ne. Sai amarya nada goma cif duk da itama dai wasu sun rasu a ciki.
Kishi sosai ake zubawa a gidan Malam Ibrahim, hakan yasa ƴaƴansa suka tashi da zafin ƴan ubanci. Kowa ɗan ɗakinsu kawai yake so. Wannan aƙidar tafi wahalar da Umar, dan shi kaɗai shi mahaifiyarsa ta haifa shiyyasa sam baya wani jin daɗin zaman. Yasha wahala ƙwarai da gaske a hannun ƴan uwansa, har takai karatun ma baya fuskanta dan anan cikin gidansu suke ɗaukar karatu wajen mahaifinsu, ƴan uwansa manya kuma sune gardawa a yanzu.
Ganin yanda Umar ɗin ke cikin tsangwama da ƙyara yasa mahaifinsu ɗaukarsa ya bama wani amininsa shima malami ne amma a can cikin birni, yanada tarin almajirai kuma Alhamdullah ana karatu. Mahaifiyarsa tasha kuka, amma hakan yafi mata kwanciyar hankali akan zamansa a gidan. Umar ya koma cikin birnin kebbi, kuma Alhamdullah yana samun ilimi, ya kuma kwantar da hankalinsa sosai dan Malam Khamisu ya saka shi cikin ƴaƴansa babu banbanci. Ƴaƴan malam Khamisu su suna karatun boko, hakan yasa shima Umar aka saka shi a boko.
Zamu iya cewa Umar ya fara karatunsa cikin nasara, kasancewarsa yaro mai basira cikin ƙanƙanin lokaci yay zarra. Ga kuma ilimin addini shima alhmdllh. Umar na zuwa Giro akai-akai saboda mahaifiyarsa, dan haka canjin da rayuwarsa ta samu a bayyane yake ga kowa. Cigabansa na saka ƴan uwansa sake jin tsanarsa da hassadarsa su da iyayensu, sai dai babu yanda zasuyi. A haka ya gama secondary school ya fara jami'a, yana level 2 ALLAH yay ma mahaifiyarsa rasuwa. Ya shiga tashin hankali matuƙa daga shi har mahaifinsu, sai dai babu yanda aka iya da hukuncin UBANGIJI. Bayan rasuwar mahaifiyarsa ya sama ransa dangana ya maida hankalinsa ga karatunsa, har ALLAH yasa ya kammala jami'a. A kuma wannan lokacin ALLAH yay ma uban riƙonsa Malam Khamisu rasuwa shima. Umar ya sake shiga ruɗani, dan komai ya fice masa a rai. Dan haka ya tafi yin sarvese ɗinsa nesa da Kebbi. A jihar Niger cikin garin Minna Umar ya fara Sarvese, inda anan kuma ALLAH ya haɗashi da matar aure. Lubabatu yarinya ƙyaƙyƙyawa mai ilimin addini da nutsuwa. Gata da haƙuri da tarbiyya. Cikin ƙanƙanin lokaci soyayya ta ƙullu tsakaninta da Umar da hidimar ƙasa ta kawosa garin Minna. Lubabatu su biyu ne a wajen mahaifinsu, daga ita dai ƙanwarta Shamsiyya. Suma ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa matar uba ke riƙonsu, suna matuƙar shan wahala a hannunta. Hakan yasa Umar na nuna yana son Lubabatu mahaifinta ya bashi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai, dan kafin ya gama sarvese har ranar aure an saka musu. Yana kammalawa akasha biki. Nan Giro aka kawo amarya family house ɗinsu, dan ba auren nasu kaɗai akai ba harda wasu a cikin ƴan uwansa da suma akayi duk a ranar. Sai da aka gama shan biki, bikin da aka nuna matuƙar banbanci dan sam Umar baida wani gata a cikinsu, gashi itama Lubabatun duk sai a hankali tunda basu da wani gata suma sakamakon rashin uwa. Haka dai akayi biki aka gama, amare suka tare da mazajensu. Umar baya son zama a Giro, amma saboda kunyar mahaifinsa ya kasa magana. Ga aiki ya samu a Kebbi, sai ya zam dole ya koma Kebbin sai weekend yake zuwa. Sam Lubabatu bata jin daɗin zama a cikin waɗan nan ahali, dan kishi da ƴan ubancin da ƴan uwansa ke nuna masa duk sai ya tattaru ya koma kanta a yanzu. Ga matan ƴan uwansa suma sun sakata a gaba, facalanci mai muni ake zubawa a tsakaninsu. Musamman ma da Matar yayansu na biyar wanda Umar ke bimawa a wajen mahaifinsu mai suna Talle. Talle irin matan nan ne masu mugun hali da hassada da ƙyashi, duk wani cigaba tafi son ace itace da shi. Yaranta biyu a gidan, Habibu da mace, sai ƙaramin ciki da take laulayi. Tayi matuƙar tsanar Lubabatu a gidan, dan tafisu wayewa da cigaba. Ita tayi karatun boko har zuwa secondary kuma gana addini dan tayi sauka. Suko mafi yawansu musamman ma Talle kota allon bata nutsu tayi ba sai talla. Sosai matsi yayma Lubabatu yawa, dan matan ƴan uwan mijin nata sun haɗe mata kai bisa jagorancin Talle. Koda yaushe tana a ɗaki babu sakewa, idan kaga farin cikinta sai idan Umar na gidan. Ba kuma wai zaman nasa na hana ai mata abu bane, a'a farin cikin da yake bata a gidan ne kawai ke sauƙaƙa mata baƙin cikinsu. Ana haka ta samu ciki, haka taita rainonsa har lokacin haihuwa, sai dai ALLAH baiyi mai rayuwa bane wajen haihuwa ya rasu. Itama tasha wahala, wahalar data saka Umar roƙon mahaifinsu ɗaukarta su koma cikin Kebbi, dan kuwa tana naƙuda matan gidan babu wanda ya kulata wai ai bata gaya musu ba. Wannan yaja tasha wahala har ɗan ma ya rasu. Sai da Malam ya shigo gidan ne yake ji a wajen yara ransa ya ɓaci yasa aka kira wata unguwar zoma dake anan kusa da su. Ɗari bisa ɗari Malam Ibrahim ya basa goyon baya. Aiko ya tattara matarsa suka wucewarsu. Wannan abu ya baƙantama mutanen gidan rai sosai musamman irin su Gambo, sai dai basu da yanda zasuyi sai haƙuri.
Komawa Kebbi tama Lubabatu daɗi matuƙa, dan hayar gida madaidaici Umar ya kama musu. Ya kuma nema mata admission ta koma makaranta. Alhamdullah komai Lubabatu na samu yanzu, bata da wata damuwa. Ga Umar abubuwa nata zama masa. Dan ya shiga harkar kasuwanci tako ina kuɗi ke shigo masa. Sosai yake ƙoƙarin taimakama mahaifinsa dama ƴan uwansa duk da basu taɓa nuna jin daɗin abinda yake musu ba, sai dai Haruna mijin Talle shi da yake dama tun can yana son Umar, kasancewar sun tashi ne a tare. Matarsa ce da mahaifiyarsu da ƴan uwansa kan canja masa tunani wasu lokutan. Amma a yanzu sai yake ƙin biye musu suka ƙulle da Umar ɗin har ya fara jan ra'ayinsa ya fara kasuwanci shima anan dai Giro ɗin. Abinda Haruna ɗin yayi ya ƙona ran matarsa da ƴan uwansa, amma ya nuna musu shifa babu abinda Umar yay masa dan haka babu ruwansa da ɗaukar ma kansa hakkin ƙuntata masa. Wannan abu da Harunan yayi yasaka mahaifinsu farin ciki, ya dinga saka masa albarka kuwa.
Shaƙuwar Haruna da Umar tasa Umar ɗin cewa Haruna ya bashi Habibu ya saka shi a makaranta, babu musu kuwa Haruna ya bashi yana faman godiya. Sai dai rigima ta ɓarke dan Talle tace bata yarda ɗanta ya koma hannun maƙiyinta ba. Shi ko yace bata isa ba dan ya bashi kuma babu yanda zatai. Rigima tai rigima har Haruna yama Talle saki ɗaya, ya kuma ɗauki Habibu ya bama Umar. Sai da akaita roƙonsa Talle ta ma kusa gama idda sannan ya maidota.
Rayuwar Habibu ta inganta, dan Lubabatu da zuciya ɗaya ta riƙe Habibu kamar ba uwarsa ce ba ta gallaza mata. Habibu ya fara boko da islamiyya, kuma Alhmdllh yana fahimtar komai Dan yaro ne mai ƙwazo. Yana son Lubabatu da Umar, dan yanda suke tattalin rayuwarsa har ji yake sunfi masa iyayensa, saboda Talle masifaffiyace har su ƴaƴan nata ba daɗi suke ji ba. Sai da Habibu ya kammala primary sannan ya fara zuwa Giro, dan malam ne ya saka wannan dokar saboda sanin halin uwarsa. Duk da cigaban da Habibu ya samo bai hana Talle nuna tashin hankali da son ganin ɗanta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login