Showing 198001 words to 201000 words out of 221978 words

Chapter 67 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

ayyukansa. Tsuru kawai tai tana kallonsa na tsawon lokaci. Shiko ya cigaba da aikinsa kamar ma ya manta da ita, dan kalamanta wani mugun saka zuciyarsa tafasa suke ainun. Itama kasa cewa komai tayi, sai kawai ta miƙe tana mai ajiye masa key ɗin motar ta wuce abinta da shopping bag ɗin da laptop ɗin kawai. Dan wadda ya bata ranar ce ta kuma fahimci wayace. Tana buƙatar wayar ne a yanzu dan har sim cards ɗin suna a hannunsa dama, bata sani ba kuma ko ya haɗa mata da su. Sai da ta fice ta maida ƙofar ta rufe sannan ya ɗago a hankali ya sauke idanunsa akan key ɗin. Janyewa yay ya maida kan ƙofar kamar yana hangota har yanzu a wajen. Sai kuma ya furzar da iska yana mai ajiye document ɗin hannunsa da ɗan ƙarfi ya tura duk hannunsa biyu cikin sumar kansa ya shiga yamutsata, tare da kwantar da bayansa jikin kujerar yay sama da kan nasa yana furzar da zazzafan huci. Tsohon lokaci ya ɗauka a haka da shima bai san adadi ba, kafin ya sake sauke numfashi mai nauyi ya cigaba da aikinsa...........✍️






_😂Jaraba, idan aka haɗu kamar abin arziƙi, amma daga ƙarshe da wahala a rabu lafiya sai da bala'i🤣, wai mike damun gayun nan ne😆😆? Maga dai yanda za'a ƙare da batun zuwa chaina😌🥱. 🏃🏃_




09032345899








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖8️⃣6️⃣




______________




.........A Kaduna kam shirin biki ake sosai, dan a yau laraba akai gagarumin kamun amarya daya zaga ko'ina na media. Waje suka kama yasha ado da kwalliya kamar yanda itama amarya tasha ado. Dj ya warware sauti ƙawayen amarya da amarya da ƙawayen uwar amarya da ƙannen ango har ma da gayyar soɗi suka cashe gwargwadon iko. Amarya tasha turare har yana hawar mata kai. Ango dai baima ƙaraso ba sai bayan sallar isha'i. Shima a media ya tsinta shagalin kamun. Tsaki kawai yay ya dinga wuce videos ɗin dan shi a nasa tsarin baya buƙatar duk waɗan nan bidi'oin. Amma yasan bai isa cewa baza ai ba Mammah ta hargitsa masa hazo. Yau ɗin ma itace ta kafa masa dogon gargaɗi akan ya dawo Kaduna domin halartar events ɗin da za'ayi. Duk da dama dai yayi niyyar hakan shima bisa umarnin Daddy. Yaso fara tsayawa Abuja wajen Maanal amma sai aka samu akasi, dole ya haƙura ya wuce akan zuwa gobe zai koma Abujan, dan baya tunanin Maanal zata zo wajen bikin nan. Shima a karan kansa baya son ma tazo ɗin...
Ammie da Nene da surukan Nene da Sakina sunje wajen kamun, duk da da dai Ammie batayi niyyar zuwan ba Hajiya Majdiya tace suje. Dan zuwa yanzu kam sun ƙulle da Ammie sosai bisa umarnin Oum da tuni ta zayyanema ƙanwar tata komai dake tsakaninsu da su Maanal. Su Ammie sun sha habaici, dan har Hajiya Yaya ma taje wajen kamun. Amma kamar yanda Ammien ta saba sai ta nuna bama tasan suna yi ba. Su Hajiya Basariyya dai anata safa da marwa su amarori. Ta shige taro tayi damal-damal dan ta san sirrin komai da takun komai, gefe kuma ta gogama Ammie kashin kaji da bata haushi. Sai dai kuma hakan bai samu ba, dan ta firgita da ganin su Ammie a taron kamun batare da tayi tunanin zatazo ɗin ba. Duk sai jikinta yay sanyi.
Itako Ammie bama ta nuna ta san da zamanta a wajen ba. Sai da tsabar munafuncin Hajiya Basariyyan ya sata zuwa ta wani ranƙwafo tanama Ammie magana a cikin kunne. Ba wata magana bace mai ma'ana, amma mutane sai su ɗauka wani sirrin ne akeyi irin na iyayen biki. Nan ko tambayarta tai kawai wai mi za'a kawo ma baƙinta. Murmushi Ammie tayi tana sake jinjina makirci irin na Hajiya Basariyya, itama sai kawai ta amsa mata da komai ma a basu zasu ci. Daga haka ta maida hankalinta ga wata ƴar uwar Daddy da yaranta da suka ƙaraso wajen, dan suna ɗasawa sosai da Ammien....


______★


A media su Manaal sukai kallon kamun, sai kuma ga Amal ta kira Shahidah. Nan suka ɓige da zancen suna dariya. Dan sun fahimci duk anayi ne wai a basu haushi. Ita Maanal ma tunda suka fara wannan zancen sai kawai tai shiru ta maida hankalinta ga saita wayarta. Dan tunda ta dawo ta cireta a kwali ta sanyata a caji. Ganin ta cika ta ciro ta dan ta saka sim card ɗinta, ɗayan kuma ta ajiye akan gobe in sha ALLAHU zata sayo wata wayar dan riƙe waya biyu ya kamata kenan. Shiyyasa bata taɓa damuwa da wannan iPhones ɗin banzar ba ita kam. Bayan sun gama wayar ma tashi tai ta nufi ɗaki domin kwanciya....


_____________★


Kamar yanda RK ya faɗa a safiyar yau yay shirin zuwa Kano, dan haka misalin goma na safe daga asibiti daya leƙa Mawaad Company ya wuce. Maanal na tsaka da aiki Yaqub na mata bayani aka sanar da ita tana da visitor a waje. Ta ɗan yi mamaki, amma sai zuciyarta ta hasaso mata RK ne. Dan shi kaɗai ne ke zuwa companyn wajenta. Amma to miya hanashi shigowa har office ɗin nasu?. Rashin mai bata amsa ya sata miƙewa tana cema Yaqub tana zuwa. Kai kawai ya jinjina mata, dan haka kawai yaji kishi a ransa da koma waye wannan visitor ɗin. Canjawar yanayin nasa ya saka su Zaharadeen.. kwashewa da dariya. Bai kulasu ba, dan ya fahimci sa'idonsu ya fi na mata....

RK dake tsaye jikin motarsa ya zubama Maanal dake nufosa idanu. Sosai tai masa ƙyau cikin atamfar jikinta data kasance skert da riga. Daka ganta kaga cikakkiyar bahaushiya ƴar asali. Zazzaƙar muryarta data rangaɗa sallama ta ratsa kunnuwansa. Amsa mata yay fuskarsa da murmushi, sai kuma cike da tsokana ya furta “Anya bazan saceki ba daga nan a biyomu da kayanmu kawai”.
Batare da niyya ba ta saki guntun murmushi, tare da ɗan jan gyalenta ta rufe fuskarta. Sai hakan ya sashi sakin dariya cike da shauƙi. A haka ta gaishe shi, tare da ɗorawa da faɗin, “Amma miyya hanaka shiga ciki?”.
“Boss ɗinki mana, yace in dai da soyayya nazo na dinga tsayawa a waje nayi, in ba hakaba kuma zai hukunta mu ni da ke”..
Sosai mamaki ya kashe Manaal a tsaye, a ranta tana sake jinjina halayyar Ajwaad. Yanzu ashe sai da ya iya yima RK maganar nan? ALLAH ta ɗauka wasa yake yi iya kanta gargaɗin nasa kawai zai tsaya. A fili kam sai cewa tai, “Yanzu kai kuma kaji maganarsa ka daina shiga kenan?”.
“Kai haba shi ɗin mi, kawai dai dan ina a hanya ne shiyyasa. Jirgina nanda minti arba'in zai ne”.
“Kanon dai?”.
“Eh mana, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe my queen. So nake next week in sha ALLAHU a gama komai na mallaki ƴar baiwar nan kafin na zube ƙasa”.
“Humm daɗin baki”.
“Oh haka kike tunani kenan? Ai tsakani na da ke har abada babu daɗin baki. Duk abinda kika ji baki ya furta shine har a ƙarƙashin zuciyata”.
“To ALLAH ya tabbatar da hakan”.
“In sha ALLAHU ya tabbatar. Na ganki a online jiya da dare, ya dawo miki da wayar ne?”.
“Oh kaga ma na manta shaf, ya dawo da ita, gashi na manta da taka a gida”.
Murmushi yay mai sanyi da faɗin, “No taki ce, ki cigaba da amfani da ita kawai. Dan ma nasan bazaki yarda muje a sai wata ba shiyyasa nayi shiru”.
“Amma Yaya Rafeeq.....”
“Shiiii!!! Don't say anything madam. Yimin addu'a kawai na wuce kar naje airport a makare”.
Murmushi ta masa, tare da jera masa addu'ar daya buƙata. Cikin nuna jin daɗi yake amsa mata da amin. Kafin suyi sallama ya shiga mota. Tana daga tsaye a wajen har sai da ya fice yana ɗaga mata hannu sannan ta juya ta koma ciki fuskarta cike da murmushi. Koba komai zuciyarta na girmama RK, yana da wani kaso mai girma kuma a wajenta, dan yana sakata a farin ciki da sauƙin kan nan nasa. Jinin Oum ai ba abin da zata taɓa wulaƙantawa bane a rayuwarta har abada....


Cikin wani irin takaici da raɗaɗin zuciya AA dake kallonsu ta jikin gilashin office ɗinsa ya kai hannu ya shafa ƙasumbarsa. Babu abinda ya tsaya masa a ƙahon zuciya ya ƙi ya wuce sai sassanyan murmushin da yaga sunama juna da wanda ta shige tana yi. Wato ya fahimci Rafeeq bazai gane karatun kurma ba, sai ya fito masa a ainhinsa sunyi uwar watsi tukunna.
Ji yay gaba ɗaya ma aikin ya fita masa a rai. Sai kawai ya fito a office ɗin. Ko kallon AS baiyi ba ya wuce. Gaba ɗaya yabar companyn, sai ma ya nufi villa dan dama yana da meeting da ministar yau.....
Yanda basu haɗi ba yau kwata-kwata baya buƙatar su haɗun, dan yana son ya bata lokaci shima ya nema mafita....


A ɓangaren Maanal ma dai tayi mamakin yau bai tsakura mata ba. To sam bama su haɗu ba har lokacin tashi, sai tayi tunanin ko dai baizo office ba yau, kokuma yaji gargaɗin data masa. Koda yake tasan mutumin nan tasan halinsa. Gargaɗinta bazai sa ya fasa abinda yay niyya ba, akwai dai abinda yake shiryawa. Hakan na nufin dole ta saka ido, dan tayi alwashi a ranta saifa ta tabbatarmasa a yanzu WUTSIYAR RAƘUMI TAYI NESA DA ƘASA. Rafeeq da kowa yake ganin bazata iya aura ba shine zaɓinta....


_🏃Yauwa ƙawalliya, ina bayanki sai Uncle Rafeeq ko Abuja ba kowa🤪. Dangin AA ku kama Nuratu da Huznahn ku yafi muku🥱🏃_.


____________★


“Yanzu ke wane mataki kika shirya ɗauka ne Kamila?”.
Numfashi Mamy ta sauke mai nauyi, sai kima ta dubi Maman Saheeba datai maganar. “Inaga zanje Kano a weekend ɗin nan”.
“Kano kuma? Yin me? Wajen wa kuma?”.
Sai da Mamy taja fasali, ta sake furzar da numfashin takaici sannan ta ce, “Abbu”.
“Mahaifin Fateema fa kenan?”.
“Yes shi, harma da Baban Yola da Baba Sardauna. Ita kanta Gwaggo Khadi ɗin da Mah-mah ɗin duk zanyi magana da su”.
Sosai yanzu kan Maman Saheeba ke murmushi. Ta ce, “Wato dai tarihi ne zai maimaita kansa?”.
“Wannan itace kawai mafita ai. Idan ba haka ba narasa ta inda zan ɓulloma al'amarin. Ke dai kawai mu fara shiri ma Nuratu. Amma fa kamar yanda na sanar miki ina son a haɗa masa da yarinyar nan da su Abdull suka kawo, dan so nake na birkita Fateema matuƙa fiye da akan su Fawzan”.
Gimtse fuska Maman Saheeba tayi. Mamy ta kamo hannunta cike da lallashi. “Dan ALLAH ki fahimceni ƙanwata, badan na tozarta Nuratu bane ko ƙuntata mata. Dan babu wata ɗiya da za'a auro da zata kasance a sama da su jinina. Shiyyasa ko'a yanzu a komai kin san kema Saheeba tafi Nibras a gareni. Dan yanzu haka ma al'amarin Nibras ɗin ya fara kaini wuya wlhy. So nake shima Fawzan ya ƙara aure. Ya duba tsakanin Barirah da Mabrooka ya zaɓi ɗaya. Shekara kusan shida babu wani bayani, sai rikici ya haɗosu ta dinga zuba masa gori kamar ance mata shine baya haihuwar. Shekaran jiya kamar Ajwaad zai daketa, kin sanshi akan ƴan uwanshi ba ragi babu ragowa. Ƴar tsirkun gidan tamu dai da Abahn su suka kwakkwaɓe shi da ƙyar. To gara yay auren mu tantance ina matsalar take.”
“Tab ɗin amma Aunty kin fa san halin Hajiya Rahane, zata iya komai akan wannan taɓararriyar ƴar tata mace tilo guda ɗaya”.
“Nima kuma zan iya komai akan nawa ɗan Gambo. Fawzan nada haƙuri a cikin ƴan uwansa. Sannan matsalar rashin haihuwar nan tashi na damuna wlhy”.
“Dole akwai damuwa kam, ALLAH ma yasa ba munafukar gidan naku ce tai masa wani abun ba kamar ita dan kada ya haihu, kai ni hatta rashin auren Ajwaad ina ji a raina a kwai lauje cikin naɗi. Dan komai matar nan zata aikata tunda ba ƙaunar yaran take ba, kawai munafunci ne su kuma sun kasa ganewa sam. Tunda ba gashi ta dake dawo da mayyar yarinyar nan rayuwarsa ba”.........✍️




_Nifa bara na faɗa gaskiya, bana son babar Saheeba ɗin nan wlhy. Idan nazo wajenta kamar na jawota na fallasa mata maruka haka nake jin raina🥺☹️🙄😲🏃._




















09032345899






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖8️⃣7️⃣




______________




........“Humm taya zasu gane tunda ba haka nan ta barsu ba. Kedai kawai a rufe rufau. Shiyyasa yanzu a shirye nake kan batun dawowarsu wajena. Auren Ajwaad ɗin kawai nake jira na fara ƙaddamar da komai na shiri na.”
“Ina bayanki wlhy ALLAH kuma ya taya miki. Sai kuma ya ran nan su Naufal uwar tace min kwana biyun nan hankalin yaran ya fara karkata a kanta.”
“Hummm nima na fahimci hakan. Kin santa kamar mayya take, amma zan sake sabon shiri akan su suma. Yanzu dai ki shirya muje Kano ɗin tare Please”.
“A'a Yaya Kamila kada muyi haka dake. Ai idan suka gammu tare zasu iya zargin wani abun. Kidai je ko ke da Yaya Raliya mana”.
“Kema kin kawo shawara. Bari zan yi magana da Yaya Raliya ɗin..”


_________★


Da mamaki Maanal dake sauka a taxi take kallon Abideen dake tsaye a ƙofar gate ɗinsu. Yana ganinta shima ya tashi tsaye sosai daga jinginar da yay da mashin ɗinsa roba-roba. Da girmamawar data bata mamaki ya ce, “Barka da dawowa sister Maanal”.
Ɗan zuba masa idanu tayi, sai kuma cikin kasa daurewa ta ce, “Abideen lafiya kuwa? Mi kazo yi gidan mu?”.
Murmushi yayi tare da shafa kansa. “Magana nazo muyi dan ALLAH ki daure ko mintina biyar ki bani”.
Shiru kamar bazata ce masa komai ba, sai kuma ta jinjina kanta. “Okay shigo ciki”. Ta faɗa tana shigewa....


A cikin rumfar bunun da akai adon gidan da ita har uku suka zauna. Ya sake gaishe da Maanal da girmamawar da take sake ɗaure kanta.
“Humm Abideen ni wlhy sake ɗaure min kai kake. Wai wannan sissinkuy da kan na miye haka?”.
“Girmanki ne Sister Maanal. Nazo nan ne domin neman afuwarki dan ALLAH. Sannan na roƙeƙi ki bama boss haƙuri kota hanyar Dr RK ne na koma kan aiki na, na san na aikata kuskure. Kuma wlhy sharrin shaiɗan ne dana zuciya. Amma in sha ALLAHU bazan sake ba. Dama ban taɓa aikatawa ba sai yanzu, kuma Alhamdullahi bamma kai ga ƙarasa badu abinda suke buƙatar ba sai wasu kaso a ciki”.
“Su wanene? Mi kuma suka buƙata ka basu kai kuwa. Ni sai sake rikitani ma kake, miye alaƙata kuma da boss da zan saka shi ko roƙonsa ya maida ka wajen aiki...”
“Humm Sis... Maanal kenan. Bara dai na buɗe miki zancen. Kusan sati biyu kenan idan baki manta ba ranar wata laraba mun fito daga company ni da ke da Yaqub bayan an tashi, sai ke kika shiga taxi keda Yaqub ni kuma nace zan ƙarasa wajen ɗan uwana a ƙafa dake aiki a companyn AREWABOOKS”.
Kai Maanal ta jinjina masa alamar eh anyi haka.
“Yauwa to bayan wucewarku wani dattijon Alhaji mai suna senator Bukar ya tareni da buƙatar son yin magana da ni. Da farko ban damu ba, saboda mutane da yawa irinsa sun sha biyo ma'aikatanmu mata domin suna son su ko sanin inda suke. Ya buƙaci na shiga motarsa, shine yake tambayata miye sunanki? Babu wani damuwa na sanar masa. Ya tambayen aikinki a Mawaad nan ma na faɗa masa har kaɗan daga halayyar ki dana sani. Shine yamun godiya tare da ɗaukar maƙudan kuɗi ya bani, ya kuma ce na bashi number ta dan zan masa wani aiki a kanki. Kin san zuciya bata da kashi, ganin kuɗin daya bani daga tambaya kawai na bashi amsa da batafi ƙwara huɗu ba sai ban masa masu ba na bashi. To tun daga ranar fa duk wani motsinki a Company sai na tura masa. Ina miki video batare da kin sani ba da ɓoyayyar camara ina tura masa kullum. Wlhy ban san taya boss ya gane ba shine jiya yake tuhuma ta akai. Kuma jiya kamar yanda kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login