Showing 114001 words to 117000 words out of 221978 words
Chapter 39 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
nufi ɗakko towel ɗin, dai-dai da dawowar Nibras. Sai faman hawaye take, dan ji take kamar ta maido ciwon kanta ko zata ji sassauci. Babban Yaya ne ya amshi ruwan da towel ɗin yana faɗin, “Oum kuje falo bari nai masa. Dan jikin nasa ma ya ɗau zafi duka yana buƙatar ruwan sanyin”.
Oum dake hawaye bata musa ba. Sai dai Nibras ba haka taso ba. Dan takaici har ɗan hararar babban yaya tayi ta gefen ido. Ganin yanda Oum ɗin ke hawaye Fawzan ya kama hannunta cike da lallashi, dole itama Nibras ɗin ta biyosu badan taso hakan ba. Sai dan tasan rijiya ba wajen wasa makaho bane ba. Shima babban yayan kamar AA yake baya ɗaukar raini..
Tsaf babban yaya ya gogema AA jiki yana tofa masa addu'a, a hankali jikin ya dinga hucewa shi kuma yana sauke ajiyar zuciya. Sai da ya koma sanyi ƙalau barci ya fara ɗaukarsa sannan ya barsa haka. Kaya marasa nauyi ya ɗakko a closet ɗinsa ya canja masa, dan ya zame waɗan can duka da boxer kawai ya barsa sanda yake goge masa jikin. Koda ya sanar ma su Oum suka shigo itama zama tai a ta ɗayan gefen tana tofa masa addu'a, hakama Fawzan na daga wajen ƙafafunsa yana tausa masa su da tofa masa addu'ar kamar yanda babban yaya da Oum keyi. (😀AA ɗan gata kenan). Tsahon lokaci suna a hakan kafin barci mai nauyi yay awon gaba da shi, wannan addu'ar da suke masa ce kawai mafita, dan in irin wannan ciwon kan ya bugesa sam maganin asibiti baya masa. Ba kuma dan ciwon bana asibitin bane, kawai dai ita addu'a dabance, maganin kowacce irin masifa ce.. Yanda yake sauke numfashi kaɗan-kaɗan ya sakasu dinga sauke ajiyar zuciya suma. Yayinda Nibras dake ta hawaye ta kasa haƙuri sai da ta tambayi Oum cikin dauriya, dan ji take kamar ta shaƙeta kota tureta daga zaman datai kan AA a saman cinyarta. Kishin matar take ji, tsananin kishinta mai zafi. Bama ita ba, duk wanda zai raɓar mata AA bata ƙaunarsa sam musamman mace. Kai hatta Mamyn ma haushinta take ji, dan ta jima da fahimtar daga Mamy har Oum ɗin dukkan soyayyarsu akan AA tafi ƙarfi. Dan kowa nayi ne bakin rai bakin fama duk da Mamy na ɓoye kurwanta wa kowa sai su da suka sani ita da Saheeba da ƙalilan ɗin mutane......
_____________★
WASHE GARI ba ƙaramin tashi hankalin RK yay da ganin yanda idanun Maanal suka kumbura ba. Gasu sunyi jazur. Amma koda ya tambayeta sai tace barci ne bata samu isashe ba sai gab da asuba. Badan ya yarda ba ya barta. Zama yay da kansa ya haɗa mata tea kamar yanda yay a kwana biyun nan, amma sai tace ta ƙoshi, ita so take dai su sallameta.
“Karki damu in dai sallama ce in sha ALLAHU yau za'a sallameki. Amma dan ALLAH ina son muyi magana Maanal”.
Yanda ya kira sunan nata in serious yasa ta kallesa. Sam kuwa babu wasan data sani akan fuskar tasa. Sai hakan ma yaso bata mamaki, kamar ba RK sarkin tsokana ba. Itama nutsuwar tayi yanda ya kamata. Kofin shayin ya miƙa mata, babu musu ta amsa. Tare da cema “Thanks” a hankali.
“Karki damu wannan aiki na ne. Maanal ina son muyi magana akan lafiyarki. Dan haka a matsayin likitanki nake tare dake anan.”
Kanta ta jinjina masa. Shi kuma ya sake gyara zama sosai da sake nutsuwa. Maanal kin yarda da ALLAH?”.
Nan ma kanta ta jinjina masa.
Ya ce, “Alhamdullah, ina son yanda kika yarda da ALLAH shi kaɗai bashi da wani abokin tarayya ki yarda da cewar komai naki a hannunsa yake. Kuma shi mai iko ne akan komai. Maanal magana ta gaskiya ciwon dake tare dake baya buƙatar komai ƙanƙantar tashin hankali daga gareki, domin ciwo ne mai haɗarin gaske. Nasan rayuwa bata kasancewa sai da JARABAWOYI a cikinta, domin suna tafiya ƙafa da ƙafa ne da fitar numfashin mu. Amma duk sanda abu ya faru damu ya wuce yana da ƙyau mu manta da shi kamar ba'ayi ba. Tabbas ban san minene lulluɓe da rayuwarki ba, sannan ban san minene musabbabin ciwonki ba. Amma ina roƙonki ko sau ɗaya ki samu wani ki tattauna damuwarki da ita nauyin zuciyarki zai ragu. Sannan ki sake miƙa al'amuranki ga ALLAH, ki ƙara ruɓanya ibadarki da addu'oi muma in sha ALLAHU zamu tayaki kinji. Amma ki kwantar da hankalinki, ki daina barin damuwa na miki yawa akwai haɗari, dan ciwonki na neman kaiwa wani mataki musamman a tsakanin nan da yake yawan tashi. Dan ALLAH ki cire komai kinji. Ke mai haƙuri ce na sani, kuma jarumace dan a ɗan zamana dake na karanci ƙyawawan halaye daga gareki masu yawan gaske. Ƴan uwanki na sonki, ki daure ki bama kanki farin ciki, suma zasu samu farin ciki”.
Murmushi tayi a karo na farko, sai kuma ta kallesa wani abu mai nauyi na narkewa daga cikin ƙirjinta. Tabbas zuciyarta bata son kowane ɗa namiji da sunan soyayya. Amma abubuwa da yawa daga RK na birgeta. Mutum ne shi mai sauƙin kai, sam bai ɗauki rayuwa da girma ba. Komai nashi so simple, burinsa ya bama kowa farin ciki koda shi bazai yi farin cikin ba, ko a wajen ma'aikatan asibitin nan takan ji suna hirarsa da yabonsa akan tausasawa kowa duk da kasancewar asibitin MALLAKINSA....
“Nifa wannan kallon ALLAH narka ni yake yi Baby”. Ya faɗa yana wani karyar da kai. Murmushi ta saki a karo na farko, sai kuma ta kauda idanunta a hankali ta maida su ƙasa ta rissinar har lokacin da murmushi a kan fuskarta. Kusan minti ɗaya sannan tai magana batare data sake kallonsa ba.
“Nagode sosai Yaya Rafeeq. Nagode da irin kulawar da kake bani batare da gajiyawa ba. Nagode da irin haƙurin da kakeyi da ni duk da abubuwa da nake maka da dama....”
“No! no no please ni ban taɓa miki abu dan ki gode min ba. Dan haka kibar gode min. Kuma yaushe na zama Yayanki ne ma?”.
“Yanzu mana”.
Ta faɗa tana ɗan waro idanunta dake a kumbure sosai, gasu da ja har yanzu. Dariya sosai ya shiga yi, da sauran dariyar a fuskarsa ya ce, “A'a nagode a barni a matsayin da na kawo kaina dai. Ke duk tarin yayun nan naki. Ga Yazeed, ga Fadeel, Fawzan, AA, Uncle Sadeeq, Uncle Hamza haba ai sai daɗin ya miki yawa idan na ƙaru”.
“Kai dai kace baka son yin ƙanwar da ni kawai na haƙura”.
“Ni bance ba. Amma dai a barni a wancan matsayin, idan ma zan zama yayan a bari sai anan gaba kin shigo daga ciki”.
“Hummm”.
Kawai tace tana cigaba da juya spoon a cikin shayin daya bata. Fin minti ɗaya sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa. Ganin kallonta yake shima sai ta ɗan kauda idanun ta. “Yaya Rafeeq ka shirya yin aure yanzu?”.
Mugun faɗuwa gabansa yay dan abin yazo masa a bazatar da baiyi zaton ji daga gareta haka cikin sauƙi ba, duk da bai san ma'anar yimasa tambayar ba. Cikin nutsuwar ban mamaki ya ce, “Miyasa kika mun wannan tambayar Maanal?”.
Ƙasa ta ƙara yi da kanta, tana mai kokawar ƙarfafa kan nata da danne dukan abinda ke neman rinjayar shawarar data gama yanke ma kanta tun a daren jiya. Ajiyar zuciya taja mai nauyi kafin ta saki murmushi mai ciwo. “Ka amsa min kawai, ka shirya yin aure yanzu?”.
“Ban san miyyasa kika min wannan tambayar ba Maanal, amma tabbas na shirya yin aure, dan na isa yinsa, da ban shirya yin aure ba ALLAH bazan tunkareki da sunan soyayya ba. Saboda alƙawari naima kaina bazan taɓa ɓatama kowacce yarinya lokacinta ba in har ba aurenta zanyi ba. Na daɗe ina addu'ar a duk sanda zan so wata ɗiya mace ya kasance aurenta nake so zanyi”.
Sosai ta kafesa da ido, sai kuma ta wani lumshesu da sake buɗesu a kansa. Cikin son taushe muryarta dake neman fara yin rawa ta ce, “Ina son zuwa Kaduna a weekend ɗin nan. Kuma ina son na ɗan huta a can....” sai kuma ta ɗan yi shiru. Cikin zaƙuwa RK yace, “Uhumm ina jinki”.
Murmushi ta sake saki mai ciwo idanunta dai na kallon ƙasa. “Na baka dama kaje ku gana da Daddy akan batun auren mu”.
Ai ba zuciyar RK ba, hatta ɗakin ma ji yay yana masa girgiza. Yayinda wasu irin hawaye masu azabar zafi suka silalo da gudun tsiya a kumatun Maanal. Ƙarar tarwatsewar abu da basu san ko minene ba ta ratsa kunnunwansu. A tare duk suka dubi ƙofar, dan tanan ne abun yay ƙara. Plates ɗin abinci ne suka watse a ƙasa.
Dubansu suka maida ga wanda alama ta nuna daga hannunsa plates ɗin suka suɓuto...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣0️⃣
______________
.........“Subahanalillahi Naufal ya akai haka?”. Oum ta faɗa tana kallon Naufal first born ɗin babban Yaya kenan da a safiyar yau suka dawo daga Kano shi da sauran ƙannensa biyu ƴammata. Kafin Naufal da yay ƙwalƙwal da idanu alamar zai yi kuka ya bata amsa ta maida dubanta ga AA da yay tsaye a ƙofar duk ya tare ko'ina babu ma ta yanda zata iya shigowa. Sake leƙo fuskarsa tayi daga bayan san da take sai kuma ta kalla direction ɗin daya zubama idanun. Kallon cikin ido suka zubama juna shi da Maanal.. sai dai kafin ta iya yin wani yunƙuri RK da tuni ya baro inda yake yazo ya kama Naufal ya ɗaga gudun kar ya taka fasashshen plate ɗin daya tarwatse shi kaɗai ya katseta da faɗin, “Alhamdullahi ai babu ma abinda ya zube kamar plates ɗin ne suka suɓuto kawai daga basket ɗin, inaga tuntuɓe yayi ne”.
“Ai kasan Naufal da wautan tsiya. Tun da naga ya figo basket ɗin da gudu nasan komai zai iya faruwa. Baka dai ji ciwo ba ko?”. Tai maganar tana kallon Naufal ɗin dai. Kansa ya ɗaga mata cike da shagwaɓa ya ce, “Oum Uncle ne fa ya kusa sawa mu faɗi”.
Yanda yay maganar yana kallon AA yasa duk suka kallesa suma. Taɓa AA Oum tayi, dan gani tai ma kamar baya motsi, sai dai kuma tana taɓa shin ya juyo ya kalleta, hannunsa ta kama cikin nata ta rumtse da ƙyau, sai kuma ta juya ga Naufal da RK kema dariya da faɗin, “Ko kuma kai ka kusa sakawa ku faɗin ba. Aunty ai banyi zaton yanzu zaku ma taho ba.
“Rafeeq ai bana wasa da Baby na sam. Balle kace yau za'a sallameta shiyyasa nace in sha ALLAHU da wuri zanzo. Sai kuma Auta da nake son yaga likita yau shima”.
Karo na farko RK ya dubi AA sosai. Ganin yanda idanunsa sukai masifar kaɗewa ya ce, “Ya Salam badai kan nasa bane har yanzu?”.
“Shine kuwa wlhy yaƙi sauka, jiya haka ya kwana a wahale”. Ta bashi amsa tana jan hannun AA ɗin zuwa gaban gadon da Maanal take. A kwance take yanzu ta juyama ƙofa baya, hakan yasa Oum zama a bakin gadon kusa da ita. Shi kuma yay tsaya kawai daga gefen Oum yana kallon ƙofa dan yaƙi sake kallon Maanal. Kujera RK ya tura masa cike da kulawa ya ce, “Zauna anan bara na duba Doctor Rasheed ɗin muga. Ai da kun sanar min da gida yazo ya samesan”.
“Yayi ƙoƙari ne ai Rafeeq, kwana biyun nan yanata zaryar zuwa gidan, kuma dama yace idan bai sauka ba yau asibiti ya kamata yazo ya duba shi da ƙyau shiyyasa”.
Jajantawa RK ɗin ya sake yi kafin ya juya ya fita yana jaddadawa AA ya zauna. Sai dai ko kallonsa yaƙiyi balle ya zauna ɗin. Yana daga tsayensa duk da hajijiyar da yake ji na jujjuya masa kai. Oum kuwa data riƙo hannun Maanal a hankali ta shiga kiran sunanta. Hakan yasa cikin dauriya da jarumta Maanal da tuni ta goge hawayenta tas ta juyo ɗin. Suna haɗa ido da Oum ta sakar mata murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta shige jikinta cike da shagwaɓa ta ce, “Oum ni nayi fushi sai yanzu”.
“Oh oh my baby kada kiyi fushi kinji, ayima Oum afuwa yaya jikin naki?”.
“Naji sauƙi Oum. Yaya Rafeeq ma yace zasu sallameni yau”.
“To Alhamdullah ALLAH ya ƙara afuwa. Tun jiya naso zuwa shima sai Auta ya kwanta shiyyasa”
“Hy Aunty”.
Naufal ya faɗa yana ɗagama Maanal hannu fuskarsa da murmushi. Murmushin itama Maanal ɗin tai masa. Sai kuma ta ɗaga masa hannun itama ta ce, “Hy Handsome”.
Farin ciki ne ya kama Naufal jin an kirasa Handsome, dama Uncle AA ne kawai ke kiransa da sunan. Gaban gadon ya ƙaraso sosai. Ya ce, “Nagode Aunty da kika kirani Handsome. Kun zama biyu kenan ke da Uncle.” yay mata nuni da AA.
Batare data kalli AA ɗin ba taima Naufal murmushi kawai. Gaisheta yaron yay da tambayarta yaya jiki, ta amsa masa da kulawa tana zaunar da shi kusa da ita. Sai kuma ta kalla Oum tana faɗin, “Yana kama da babban Yaya sosai”.
Dariya Oum tayi a karo na farko, idonta akan Naufal ta ce, “Kodai Auta. Dan komai na Naufal Auta ne sak, duk da dai dama suna kama da Fadeel ne shima ɗin, amma Fadeel ai fari ne, shiko Naufal irin fatanku gareshi ke da Auta”.
Maimakon Maanal ta amsa zancen sai ta basar ta hanyar shagwaɓe fuska ta ce, “Oum mi kika dafo min?”.
Dai-dai Oum zata bata amsa RK ya shigo. Idonsa a kansu sai kuma ya kalla AA, da kulawa ya ƙarasa garesa yana faɗin, “Wai baka zauna ba. Ko duk ƙulafucin Oum ɗin kaka ne kazo ka tsaya mata a kai kamar zaka koma ciki kai da ɗayar Autar tata. Common malam zauna kada ka faɗi”. Yanda baiyi magana ba tunda ya shigo yanzun ma bai tanka ba, sai dai ya zauna ɗin dan shima yasan in ba hakan yay ba tabbas gab yaje da zubewa a ƙasa, sam kuma baya son cigaba da tada hankalin Oum, dan kwana biyun nan da baida lafiyar nan har rama tayi, ga shi itama tana fama da kanta.....
____________★
A Kaduna kam shirin kai lefe ake gidan su amarya. Shi ango ma baya nan yana Lagos kwana takwas kenan. Kaya ne na garari aka shirya na kuma fariyya. Jiya yini guda masu shiryasu na aikin nan. Akwatina set ashirin daa huɗu cif, kaloli daban-daban. Kuma kowane set zaka samu kusan akwati biyar ko uku harda masu goma sha biyu. Ga galleliyar mota new model a 2023 sabuwa dal a ledarta. Hajiya Basariyya dai tana nane dasu a gabanta ake komai duk da zuciyarta a ƙuntace take, amma yafi yarda data danne ayi komai akan idonta, Ammie ko yanda ba'a gayyaceta ba bata saka kanta a sabgar ba daga ita har Sakina da har yanzu take a gidan. A yau ɗin ma sai suka ƙirƙiri zuwa gyaran jiki abinsu. Duk bidirin shirin kayan da akai basa nan. Aiko Hajiya Yaya da ƴaƴanta suka samu na zaginsu wai Ammie tana hassada ne saboda ba ɗiyarta bace ba. Koda suka dawo gidan haka suka cigaba da habaice-habaicen su Ammie tayi kamar ma bata jisu ba...
Washe gari tun sassafe gidan ya fara tara dangin Hajiya Yaya. Sai wasu a dangin Daddy dake ɗan ɗasawa da Hajiya Yayan. Yanda gidan ya cika saika ɗauka bikin ne ma ya fara. Har lokacin kuma babu wanda ya zo ya cema Ammie tazo ga lefe kota shirya zuwa kai lefe, ita kuma tayi biris da kowa bata saka kanta ba. Bayan sallar azhar suka cika motoci goma cif sai ta amarya dake tsakkiya da toyota hilux da aka zuba kayan lefen a ciki. Haka suka tafi a jere gwanin sha'awa, duk inda suka gitta sai an tanka kuwa. Dama haka suke so, gari ya ɗauka ko'ina ayi zancen wannan aure. To ALLAH ya cika burinsu dan kuwa an fara, sakamakon ƙannen Yazeed kaf da wasu a dangi tun jiya sun gama watsa wannan lefe a kafafen yanar gizo tako ina.. A can gidan Aunty Sabuwa ma gida cike yake tanƙam da ƙawayenta ƴan duniya da dangin mijinta. Anyi abinci kala-kala domin tarbar baƙi duk da kuwa aurene na dangin juna. Cikin abinda baifi mintuna ashirin ba anguwar ta gama rikicewa, dan kuwa kiɗa suka saki sosai da dj ɗinsu da suka tanada. Kafin a ɗan sarara a shiga buɗe kaya, masu video