Showing 219001 words to 221978 words out of 221978 words

Chapter 74 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Tunda ku dukanku ba muhallin zama kuka rasa ba. Babu kuma wanda bai da abinyin da idan yau akace za'ayi nasan zaku shiga ku fito. Balle ma bama buƙatar komai daga kowanneku, ku shirya tarbar matayenku kawai. Magana ta ƙarshe akwai zaman da mukai shekaru uku da suka wuce a wannan falon game da Ajwaad na auren yarinya da aka bashi wadda ta fito daga ke ɓangarenki Kamila”. Da sauri Mamy ta kalla baba Sardauna ranta fal farin ciki amma tana ɓoyewa. Cigaba yay da faɗin, “To ban manta ba, dan haka zamu tuntuɓi iyayen nata in sha ALLAHU. Sai yarinya daga Kaduna da ƙanin mahaifinyarta da kansa ya kirani itama yazo da batunta akan tarayyar su da Ajwaad ɗin dai suka kuma bamu damar zuwa tsaida magana itama in har ya shirya zamuje ayi magana tunda shi da alama da mata biyu zai fara, ya nuna mana duk ya fimu gwarzantaka har mu dake iyayen naku”. Yanda yay maganar da ƴar raha ya saka wasu yin dariya. Yayinda mamaki ya gama lulluɓe wasu, Ajwaad ne wai da auren mata biyu lokaci ɗaya, duk wannan jin kan nashi tab ɗin. Oum kam suman zaune tayi, burinta su haɗa ido da AA amma yaƙi yarda. Haka Abah da su Babban Yaya ma. Ran Mamy kam fes. Haka dai akai addu'a taro ya tashi.........✍️




_Humm wlhy kuna bani dariya da yanda kuka matsu da al'amarin Mamy dama sauran mutanen da mukema kallon ƙalubale a wannan labarin. Shin wai mun taɓa ganin rayuwar da babu ƙalubale a cikinta ne?. Ni da ku mu koma cikin rayuwarmu mu kalla mana, itafa rayuwa gaba ɗayanta ma jarabawace, mukance ai rayuwa rayuwace, rayuwar novel kuma rayuwar novel ce kana karantawa ne dan nishaɗi da farin ciki. Eh hakane kam banyi musu ba, amma mu sani mutane da yawa na ɗaukar darasi da fahimtar tasu rayuwar a dai wannan rayuwar novels ɗin da mukema kallon nishaɗi da labarin hikayoyi kawai. Da ace labarin akan soyayyar su AA da Maanal ce kawai, ƙalubalen rabuwar ma bazai shigo ba, Sai kawai suyi rayuwar ƙurciyarsu suyi aure shike nan miya rage. To koma ita kanta soyayyar ai duk daɗinta ƙalubalen cikinta yafi yawa koda a zahirin ne. To amma ni akwai saƙon da nake son isarwa a labarin gaba ɗayansa. Idan kukai haƙuri za'akai fiye ma da inda kuke tunani. Ka aikata alkairi ma yaka ƙare balle akasinsa a wannan rayuwar. Dole ne mu yarda akwai farin ciki, akwai kuka a rayuwa. Duk yanda muke tunanin mu masu gaggawane duk gaggawarmu muna tafiya ne bisa zartarwar hukuncin UBANGIJI. Dan haka dan ALLAH ku barni na isar da sakon da nake son isarwa dan masu buƙatar hakan su amfana. Ni da nake wahalar rubutun da hana kaina barci da wasu muhimman abubuwan rayuwa nafi ku ƙagauta naga nakai gacci, dan banƙi na runtse ido naga na kammala ba. Fatan alkairi a gareku baki ɗaya🙏_


_Maanal kuma sai Uncle RK ko Abuja babu kowa ehe🤪🏃🏃🏃_




09032345899


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖9️⃣5️⃣




______________






.........Zaman wannan meeting na Kano ya matuƙar saka Mamy a farin ciki. Yayinda Oum da Babban Yaya ke cikin damuwa da zaman neman mafita. Abah da Yaya Fawzan kuwa sun mugun ƙullatar AA. Shiko tunda suka dawo Abuja yay bala'in maida kansa busy. Sam baya zaman gida, yakan fita da safe sosai, sai ya kai goma kuma bai koma gidan ba. Sam yaƙi bada wani space da Oum zatai zaman yin magana da shi balle su Babban Yaya. A kamfani ma ya toshe duk wata hanya da zata haɗa shi da Maanal. Itama kuma a nata ɓangaren haka ne. Duk hanyar da zata haɗata da AA ta toshe ta. A wannan halin aka shiga shirin bikin ƙaddamar da agogonsu. Taro na farko kuma kenan da kamfani zai yi Maanal na nan. Ita da RK normal ne, dan tuni shima ya dawo Abujan, amma ya ɗauke ƙafarsa da zuwa gidan su AA gaba ɗaya. Hasali ma tunda ya dawo babu wanda zaice ya ganshi a cikinsu. Ga Abah ya kafama Oum takunkumi akan cewa RK ɗin komai. Dan shi yana bayansa ɗari bisa ɗari.
A haka aka shiga satin bikin kamfani, wanda ke nuni da daura sati biyu kacal gagarumin bikin auren da familyn Darma ke shirin yi na ƴaƴa biyar cif. Ana cikin wannan shirye-shirye Ammie tazo Abuja tare da Daddy. Zai ɗan yi wani aiki na kwana biyu anan tace zata biyoshi dan ta ɗan huta da hayaniyar gidan su, daga nan su ɗanyi shawara da Shahidah. Sai dare Shahidah da Manaal suka je gaishesu dan da rana suna wajen aiki. Sai kawai Maanal ta maƙale anan zata kwana wajen Ammie. Dan haka su Shahidah suka wuce suka barta. Washe gari Daddy ya cema Ammie ta shirya ya kaita ta gaida Oum gaskiya. Dan bai kamata ta shigo Abuja ta fita bataje ba tunda komai ya wuce. Tayi farin ciki da hakan sosai kuwa. Bayan sallar juma'a Maanal ta taso aiki sai kawai suka tafi tunda ita ta san gidan.
Sanye take cikin Abaya fara tas da tai mata ƙyau sosai. Sai ɗan kwalliyar golden kaɗan a jikinta. Kasancewar zuwan na surprise ne sun matuƙar saka Oum a farin ciki. Nan fa ta shiga kai-kawon musu hidima. Sunfi mintuna goma da zuwa sai ga Yaya Fawzan da Babban Yaya da su Naufal sun dawo massallaci. Suma sunyi farin cikin ganin su Ammie ɗin. Cike da girmamawa suka shiga gaida Ammie, dan shi Daddy yana ajiyesu ya wuce akan sai an jima in ya dawo ɗaukarsu ya zai shigo. Gaishesu Maanal tayi itama. Fawzan ya tasata da tsokanar daya saba mata Babban ya na tare mata. Ita dai yau murmushi kawai take ta kasa maida masa. Suna cikin haka AA ya shigo shima. Yana sanye cikin mayan kaya da suka masa ƙyau. Sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci irin ramar da yayi, ga ƙasumbar daya tara sosai yanzu baya gyarawa. Yana yin sallama idonsa akan Maanal ɗin ya fara sauka. Ɗan turus yayi kamar yanda itama tayi duru-duru, sai kuma ya janye idanun nasa cike da basarwa ya ƙarasa shigowa. Itama natan ta janye tana mai danne komai. Oum dake kallonsu ta cije lips, hakama Yaya Fawzan sai da ya taɓe baki. Ammie kam kallonsa take fuska ƙawace da murmushi. A mamakin kowa sai sukaga shima ya saki murmushin, tare da cigaba da takowa a hankali cikin nutsuwarsa ya nufi kujerar da Ammien take Oum a gefenta. Saman carpet ɗin ya zauna a gaban Ammie gab, sam ya kasa haɗa idanunsa da Ammien, wani irin kunyarta mai girma da bai taɓa ji ba a shekarun baya yake ji a yanzu duk da kuwa ko randa suka haɗu a Kaduna ma yaji hakan, amma sai yaji na yau yafi na waccan ranar girma kodan daga su sau su ne oho. Sai da ƙyar ya iya dai-daita nutsuwarsa ya shiga gaisheta. Kasare Oum da su Babban sukai suna kallonsu...
Gaisheta ya farayi cike da nutsuwa da girmamawa. Murmushi mai sanyi Ammie ta saki, cikin danne komai cike da kulawa ta amsa tare da faɗin, “Ikon ALLAH Ajwaad baka da lafiya ne? Irin wannan zabgewa haka lokaci ɗaya?”.
Idanunsa ya ɗan lumshe tare da sakin murmushi mai sanyi. Yanzun ma kansa a ƙasa ya bata amsa da, “Lafiya Lau nake Ammie. Kai kawo ne kawai na yau da kullum kin san muna shirin fitar da project ɗin mu da Maanal tai aikin sa”.
“To, to ALLAH sarki ai ban sani ba. Kasan ƴar uwar taka ta koya miskilanci yanzu ko labari bata bani ba. ALLAH ya sanya albarka yasa a fitar a sa'a”.
Da Amin duk suka amsa, yayinda AA ya ɗago ya ɗan kalla Maanal. Suna haɗa ido ta hararesa da taɓe baki ta ɗauke kanta. Karan farko ya saki wani ɗan murmushi shima ya ɗauke nasa idon, sai suka sake haɗa ido da Fawzan alamar yana kallonsu shima kenan. Harararsa shima AA ɗin yayi. Fawzan yay dariya yana ɗauke kansa da faɗin, “Gulma ajali”. A fili. Dan haka kowa ya kallesa. Ganin duk sun watso masa idanu sai ya nuna AA, ya ce, “Dafa wancan yaron nake”.
Sake harararsa AA yayi, Ammie dake murmushi ta ce, “Fawzan har yanzu dai baka canja ba ashe”.
Dariya yayi shima, ya ce, “Kai Ammie ALLAH na canja sosai, ɗanki ne dai yana nan da baƙin halinsa.” ya ɗan kashema AA ido.
“A'a Fawzan Ajwaad mutumin kirki ne. Shi dai ba mai yawan magana bane kawai”.
Murmushi sosai AA yayi saboda jin furucin Ammie, matar da yakema kallon uwa bayan iyaye biyu daya mallaka a duniya. Wato Oum da Mamy. Hakama Oum da Babban Yaya duk murmushi sukayi. Babban Yaya ya kalla Fawzan tare da faɗin, “Kasan shi Auta ɗan gatan iyayensa ne, basa taɓa yarda da laifinsa in dai Ammie ce da Oum”.
Dariya Ammie tayi da faɗin, “Kaima harda kai Fadeel. Shike nan munji ɗin”.
Haka sukaita hirarsu cikin nishaɗi gwannin sha'awa. Yayinda Maanal ta ƙirƙirarma kanta barcin ƙarya, aiko Oum tace ta tashi taje ɗaki ta kwanta. Babu yanda ta iya ta miƙe, duk da koba komai ta gujema idanun AA ai....


Bayan sallar la'asar Oum ta tafi raka Ammie sashin Mamy, a ranta tana mamakin rashin shigowar Mamy ɗin su gaisa da Ammien. Dan Saheeba da Nibras sun shigo. To ko basu faɗama Mamy ɗin bane?. Tunanin hakan yasata kauda zancen a ranta suka fice. Sun bar Maanal tana salla, itama bayan ta idar sai ta fito da nufin bin bayansu kamar yanda Ammie tace mata.. Harga ALLAH ita ba sanin sashin Mamy ɗin tayi ba tunda wancan karon da duka zo bata ma gidan. Dan haka ta fara canki canka a tsakanin sassan gidan.
“Mi kike nema?”.
Muryarsa mai sanyi ta faɗa a bayanta. Da sauri ta juyo dai-dai da shigewar ƙamshin turarensa cikin hancinta. Yitai kamar ta daburce, ta dai samu ta saita kanta, idannunta ta janye daga kallonsa tare da furta, “Sashen Mamy”.
Sashen Mamy ɗin ya ɗan kalla. Sai kuma ya janye idanun nasa ya sake maidosu a kanta. Yatsunta da taketa faman matse gefen veil ɗin abayarta ya zubama idanu kafin ya kauda yana ɗan cizar gefen lips ɗinsa.
“Idan babu damuwa ina son muyi magana”.
“Magana? Tami kuma?”. Ta faɗa a sanyaye. Idanunsa dake ƙyalli kamar ruwa na taruwa a cikinsu ya janye daga kanta. Shima cikin sanyin ya ce, “Plesse”.
“Okay ina jinka”.
“Ba'a nan ba”.
Ya bata amsa yana barin wajen. Bayansa tabi, sai da suka ɗan zagaya can baya ya buɗe wata ƙofa sai ta gansu a wani kyakkyawan waje, ga ƙaton swimming pool da kujerun gefen ruwa. Daga can gefe furanni ne da ƙamshinsu ya sake ni'imta wajen matuƙa. Baka jin komai a wajen sai kukan tsuntsaye masu ƙyau farare tas daketa kai-kawo. Matuƙa wajen ya ƙayatar da ita, sai faman kalle-kalle take. Wajen zama ya nuna mata a wasu rukunin fararen kujeru bayan yaja kujera ɗaya baya. Sai da ta zauna sannan shima ya zauna. Tsawon sakanni baiyi magana ba itama kanta a ƙasa, kafin a hankali ya furzar da iska ya ɗan gyara zamansa.
“Maanal!”.
Ya kirayi sunanta abinda bai cika yi ba. Sai ko da taji tsigar jikinta ta tashi, amma sai ta dake ta amsa masa da, “Na'am” batare data ɗago ba.
“Kin tabbatar kina son Rafeeq?”.
Harga ALLAH sai da hanjin cikinta suka yamutsa, kanta yay mata wani irin nauyi amma dai ta dake ta jinjina masa kanta. Sai da ya lumshe idanunsa ya sake buɗesu a kanta. Yayinda maƙoshinsa keta faman kai-kawo a cikin wuyansa, sun jima shiru yana kokawa da kansa kafin yay murmushi irin na takaici mai sauti, ya ce, “Shike nan Alhamdullahi. ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a masu albarka. Ki riƙe min shi amana. Rafeeq mutumin kirki ne, yanda kikaga halayen Oum shima haka yake, yana da sauƙin kai da daɗin zama. In har kika zama mai biyayya a gareshi zaki ci ribar zama da shi matuƙa. Kema na sanki da ƙyawawan halaye tuni, dan ALLAH kada ki canja, ki zama mai yin koyi da Ammie azaman haƙuri da miji. Ina miki waɗan nan nasihihin ne kasancewata yayanki, zakuma ta iya yiwuwa shine zama na ƙarshe da zan yi da ke. Dan zanyi tafiya mai nisa ne....”
Yanzu kam Maanal ta kasa riƙe hawayenta, shaaaaa haka suke zubowa suna sauka. Muryarta na rawa ta ce, “Ina zakaje?”.
Murmushi ya yi kaɗan, yana mai kauda idanunsa da suka gama kaɗewa jazur a kanta. “Zanje wani wajene mai nisa”. Ya sake faɗa a dunƙule. Batare da ya jira amsarta ba ya cigaba da faɗin, “Akwai saƙo zan bama Rafeeq zai baki daga baya, abu na ƙarshe zan damƙa amanar MAWAAD a hannunki.....”
A firgice ta ɗago tana kallonsa jikinta na tsuma ga hawaye. Harshenta har harɗewa yake wajen ambaton, “Mawaad? Kana nufin kamfani? Saboda mi?”.
Kansa ya jinjina batare daya kalleta ba. Sai kuma ya miƙe dan yakai maƙurar da bazai iya cigaba ma da mata bayanin ba, sannan baya son taga abinda ke ƙoƙarin fito masa ta hanci. Sai da ya juya mata baya yasa handkacheff ɗinsa da sauri ya tare hancinsa. Tsawon sakan biyu ya goge tsaf sannan ya juyo. Ganin kallon da take masa ya sashi sakin murmushi. “Duk kin maida kanki raguwa yanzu. Komai kuka. Shike nan na fasa yin bayanin zan ajiye miki komai a rubuce. Ina fatan dai kin gama shiryama bikin nan na gobe? Dan kin san kece tauraruwar taron”.
Hannu tasa ta share hawayenta, batare data masa magana ba ta miƙe zata bar wajen. Sai da tai taku biyu sannan ta ce, “Ni bazan zo ba”.
Da sauri yasha gabanta. Cike da kwantar da murya ya ce, “Ashe baki so nima naje kenan Besty?”.
Da matuƙar mamaki take kallon, hawaye na cika mata ido. Ya jinjina mata kansa. “Tabbas idan baki je ba nima bazanje ba”.
Wani kalar kuka ta sakar masa, sai kuma ta zagayesa da gudu ta fice a wajen gaba ɗaya. Idanunsa kawai ya lumshe ya cigaba da tsaiwa a wajen, kafin ya kai hanky ɗinsa saman hanci jin abun zai zubo.....


Banɗakin Oum Maanal ta shige tasha kukanta, gudun kada suzo su kamata ta fito ta hau gadon Oum tayi kamar mai barci. Sai ALLAH ma ya taimaketa suka jima a sashen Mamy ɗin. Dan sun tarar itama wai kanta ke ciwo ne shiyyasa bata zo sun gaisa da Ammie ba. Koda suka dawo ganinta tana barci data tashi lokacin baisa sun zargi komai ba, sai suka ɗauka barci da tayi ne.
Sai bayan sallar isha'i Daddy yazo. Nan fa suka haɗu da Abah da su Babban Yaya. AA dai baima fito ba, koda Daddy yayi jajensa sukace maybe baya gidan ne. Zuwa goma suka tafi gida suka bar Oum da kewa. Taso Maanal ta kwana anan amma taƙi, wai zataje tayi shirin taron gobe. Haka dole Oum ta barta tunda tasan taron nada muhimmanci ga Maanal ɗin kasancewar aikinta ne zai fita....


WASHE GARI.


Yau ɗin ta kasance asabar. Tako wane ɓangare masu alaƙa da Mawaad Company sun tashi da shirin babban taron ƙaddamarwa na project ɗin da aka ɗauki tsawon watanni sanyinsa. Anan cikin Companyn za'ayi taron. Yako sha gyara ɗan gaske. Ko'ina ka kalla sai ka ƙara kallo dan ƙyau. Masu himma har sun fara isowa. Irin wannan taron yakan kasance an gayyaci manyan ƴan kasuwa na ɓangarorin duniya da Mawaad ke mu'amular kasuwanci da su. Tare da na cikin ƙasa Nigeria. Sai ma'aikatan companyn da ƴan jarida. Wasu a manyan ƙasar musamman daya kasance a wannan gaɓar AA nada muƙamin gwamnati na shugaban matasa na ƙasa gaba ɗaya da shugaban ƙasa ya bashi shekara ɗaya da wasu watanni kenan. Kafin tara waje ya gama haɗuwa, dan taron za'a fara shi ne goma a tashi ƙarfe ɗaya batare da an takurama mutane ba.
A ɓangaren Maanal sai da Ammie da Shahidah sukai mata jan ido sannan ta shirya. Tayi matuƙar ƙyau kuwa kamar ka saceta ka gudu. Suna ƙoƙarin tafiya sai ga Rafeeq babu zato. Zuwan nashi yasa tsarin tafiyar ya canja. Ammie da Shahidah da mijinta da Daddy suka tafi tare. Maanal kuma tabi RK. Lokacin da suka iso wajen taron ya gama cika, dan har su Oum sun iso suma tare da uban gayya AA Darma.
Su Ammie an basu wajen zama na musamman, yayinda Maanal ta wuce inda aka tanada dominta da sauran ma'aikatansu. RK ma tare da su Oum ya zauna. Sai wani dama-dama Mamy keyi da shi, ta yanda Oum tama gagara ko yimasa kallon banza balle zazzage masa abinda ke ta faman cimata zuciya..........✍️






09032345899




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login