Showing 165001 words to 168000 words out of 221978 words
Chapter 56 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
Ana idar da sallar Asr ɗin shima Ajwaad ya nufo gida. Dan hankalinsa duk yana kan Maanal. Kansa tsaye ɗakin Oum ya nufo, hakan yay dai-dai da farkawar Maanal a firgice. Silmiyowa tayi daga saman gadon Oum ta durƙushe ƙasa, hakan yasa Ajwaad ƙarasowa gareta da sauri yana tambayarta. Sai dai batako samu bashi amsa ba ta shiga kwara amai. Gaba ɗaya duk sai ya rikice yanata jera mata sannu. Itako aman take sosai. Sai da ta gama ta koma gefe ta kwanta yaraf tana maida numfashi. Sannun yaketa jera mata, yanda fuskarsa ta koma sai ka ɗauka ma shike ciwon. Sai kuma ya miƙa mata hannu yana faɗin, “Tashi muje ki wanke baki”.
Kanta ta girgiza masa. Da ƙyar ta iya furta, “Zan huta tukkuna”. Bai matsa mata ba, ya fita ya ɗakko abu ya fara gyara wajen. Ya gama ya maida komai zai dawo ɗakin yaci karo da fasa ƙararata. Ai a ɗari ya ƙarasa faɗowa ɗakin. Tana a inda ya barta, sai dai kallon hannunta take da duk ya ɓaci da jini. Hannun ta nuna masa tana sake fashewa da kuka, sai kuma ta miƙe a galabaice tana kallon gadon. Ashe har nan akwai jinin lurane basuyi ba tun ɗazun. Ganin tana niyyar nufar ƙofa yay saurin riƙota. Cikin son ganin ta kwantar da hankalinta ya ce, “Relax!”.
Kuka ta sake fashe masa da shi tana ƙoƙarin fisge hannunta, “Na shiga uku Besty jini fa? Jini Oum kizo jini”.
“Nace ki nutsu ko!!”.
Ya faɗa a tsawacen daya sakata nutsuwar dole. Sai dai jikinta rawa yake sosai tana cigaba da kallon hannun. Bakin gadon yace ta zauna amma taƙi, sai ya ƙyaleta kawai. Batare daya kalleta ba dan haka kawai yaji kamar yana jin nauyinta ya ce, “Ki jirani anan ina zuwa”. Daga haka ya nufi toilet ɗin Oum. Ruwa masu zafi ya haɗa mata, sannan ya sake dawowa inda take. Har yanzu tanata kallon hannun tana hawaye. Murya ya kwantar kamar bashi ke faɗa ba ɗazun.
“Kinga ki nutsu Besty ba wani ciwo bane ba fa. Dama doctor ya sanar mana zaki fara proud ne shiyyasa kike jin ciwon ciki. Shine sai yanzun yazo. Ki tashi kije bayi ga ruwa can na haɗa miki ki cire wannan kayan ki gyara jikinki kafin Oum ta dawo taje wajen Ammie ne. In kuma kina son sai kowa yazo ya ganki a haka ne to?”.
Da sauri ta girgiza masa kai tana miƙewa ta faɗa Bayin........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣2️⃣
______________
........Ajwaad bai ji ƙyanƙyami ba ya cire bedsheet ɗin samman gadon Oum ɗin ya samo ruwa da omo da towel ya goge inda katifan ta ɗan ɓaci. Haka ya ɗaga katifan shi kaɗai ya juyata sannan ya ɗauka sabon bedsheet ya canja. Wadrobe ɗin Oum ya buɗe side ɗin da kayan Maanal suke a cike fal ya ɗauka mata kaya, tare da pant. Sannan yaje bakin toilet yana sanar mata idan ta fito ga kaya nan ta saka, ta kuma bar kayan data cire ɗin zai zo ya wanke”. Bata dai amsa shi ba ya nufi hanyar fita. Har yaje ƙofa sai kuma ya dawo da baya sakamakon saukar idonsa akan ledar da Oum ta aiki Amaal ta kawo mata ɗazun, Ledar ya ɗauka ya buɗe ya ciro abinda ke ciki. Bai fahimci miye ba, dan haka ya karanta bayanin jiki. Ganin audigar mata ya sashi maidawa ya ajiye, sai kuma ya sake ɗauka ya sake buɗewa. Ledan ya fasa ya ciri ɗaya ya ɗauka pant ɗinta sabo da ya aje ya saka kamar yanda ya fahimta. Daga haka ya fice.
Bayan tsahon lokaci Maanal ta fito jin motsin fitarsa. Kasa zama tayi gudun karta ɓata wajen, sai dai tanata bin gadon da kallo ganin ya canja kamar komai bai faru ba. Haka jiki a sanyaye ta ƙarasa ga kayan daya ajiye mata. Sai idonta ya sauka akan pant ɗin da ya sakama part ɗin. Sosai tawaro idanunta waje, sai kuma ta tunzura baki gaba da faɗin, “Besty ALLAH baka da kunya”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki, sai kuma ta ƙarasa ta ɗauka pant ɗin ta saka dan tana ganin yanda Didin ta suke amfani da shi ai. Kayan ta saka tsaf tanata kumbure-kumbure. Sai kuma ta ɗauka wayarsa data riga tasan password ɗin ta buɗe. Hayewa gadon Oum tai ta sake kwanciya. Dan wani kalar jirin barci take ji sosai. Takai mintuna goma da kwanciya akai knocking ƙofar. Umarnin shigowa ta bada sai ga Bestyn ta. Ɗauke yake da tray a hannu, suna haɗa ido ta risinar da nata. Shima baiyi magana ba ya ajiye abincin kawai ya wuce toilet ɗin Oum ɗin kamar wasu masu jin kunyar juna. Kayan data cire ya tattare hadda p ɗinta dake a ɓace sosai. Tsabar rashin hankali da rashin wayo irin na Maanal maimakon ta wanke sai shima ta bar masa saboda yace tabar masa kayan data cire. Abin mamaki Ajwaad Sarkin ƙyanƙyami da tsantseni sai gashi tsaf ya wanke kayan har sau biyu kafin ya sakasu a injin wanki harda bedsheet ɗin Oum ya wanke fes. Sannan ya wanke bayin ya fita da kayan can backyard ya shanya amma banda p ɗin daya shanya anan toilet ɗin. Zuwa lokacin Maanal ta jima da komawa barci. Sai ma ɗauke tray ɗin abincin yay ya ajiye gefe sannan ya fice ɗakinsu domin yin wanka...
★Rai a ɓace Oum ta dawo gidan tare da Ammie dake wani irin kuka mai ban tausayi saboda abinda ya faru a gidansu Maanal ɗin. Da farko bata lura da canja kayan Maanal ɗin ba dana bedsheet sai da ta zauna idonta akan trayn dake ajiye. Hannu takai ta taɓa wuyan Maanal, sanyi ƙalau zazzaɓin ya sauka. Barcinta take hankali a kwance. Ajiyar zuciya ta saki mai kauri, sai kuma ta maida dubanta ga Ammie.
“Kiyi haƙuri Asiya kukan nan ya isa. Kada kanki yazo yana miki ciwo. Tashi ma kiyi wanka ki shirya gidan baba zamuje. Dan na fahimci wannan karon sai na dangana al'amarin Habib da baba tukkuna, tunda baya gane yaren Aban su Fadeel da nawa.”
Kai kawai Ammie ta jinjina mata, ta tashi ta shiga toilet. Ita kuma ta buɗe wadrobe ta ɗakko mata wata sabuwar atamfa da bata taɓa sakawa ba da gyale da duka abinda zata buƙata sannan ta fita. Harta nufi ɗakin Mamy sai taci karo da Ajwaad. Sannu ya mata, ta amsa tana kallonsa ganin shima ya sauya kaya. “Fita zakayi ne Auta naga ka canja shiga?”.
Kansa ya girgiza mata, “A'a Oum, wancan sun ɓaci ne”.
Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, “Mamy fa?”.
“Tana ciki tunda kika fita. Oum ina kikaje wai?”.
“Naje nan wajen Ammien ku ne, yanzu ma zamu sake fita da ita gidan Baba. Idan Mamy ta tashi ka sanar mata, ga kuma Maanal nan na barci.....”
Kansa kawai ya jinjina mata. Ita kuma ta juya ta koma ɗakinta ranta duk a dagule.
__________★
Shigar Baba Sardauna a cikin al'amarin Ammie yasa aka samu sauƙi tsakaninta da Babu a lokacin. Ga gwaggo ne dai babu abinda ta fasa wulaƙanci yima Ammie take iya iyawarta. Tunda kuma ta ƙyalla ido taga Maanal ta fara jini sai ta fara surutai, yara duk sun zama iyayen mata miye-miye. Saboda ƙwaɗayin Ammie kuma duk sun laƙema masu kuɗi, indai kwaɗayi abun yine suyi tayi watarana sai amma yaran cikkunan shege a titi. Babu wanda ya kula gwaggo da zatunkanta sai Maanal, rashin kunya ta mata sosai ranar har sai da ta saka Gwaggon kuka. Sai Ajwaad ne yazo yasa Maanal barin gidan da ƙyar. Aiko gwaggo ta haɗata da Babu yace sai ya daketa. Jin haka Maanal ta daina shigowa gidan har kwana huɗu.
A yammacin ranar Maanal ta nema jini ta rasa. Tana son gayama Oum tana jin kunya. Gashi bata shiga gidansu saboda Babu yace zai daketa. Kawai saita yanke shawarar samun Ajwaad, ɗakinsu ta leƙa, babu kowa sai babban yaya dake barci, dan haka ta fito. Can harabar gidan ta nufa, inda ta wuce Mamy da ƙanwarta da suke kira Maman Saheeba suna hira. Kallon banzar da Maman Saheeba ke mata yasa ko gaisheta bayi take ba idan tazo gidan. Dan haka yanzun ma bata kulasu ba har Mamy ɗin ta wuce garden neman Ajwaad. Tasan shi baya yawo, indai ba aikensa akai ba to zaka samesa ne a garden yana karance-karance daya ɗaukama kansa yanzu. Wani lokacin har faɗa suke yi dan ita karance-karance haushi yake bata, ya rage bata kulawa, bata san miyyasa ba bai son su cika kaɗaicewa daga ita sai shi a yanzu. A hankali ta zare novel ɗin dake a hannunsa, fuska ya yamutse tare da ɗago idanunsa ya saukesu a kanta. Zama tai kamar zatayi kuka tana kallon littafin, sai kuma ta sake kallonsa idanun nata cike da hawaye.
“Besty wai mike damunka kwana biyun nan. Sosai ka canja min, musamman tsakanin nan. Ka ɗauka dukkan hankalinka ka maida ga karatun novels. Baka son mu zauna muna hira mu kaɗai, ko assignment zamuyi sai kace sai a gaban Oum ko Mamy. Kana yin abu kamar ma baka son ganina.”
Maimakon amsa mata sai kawai ya lumshe idanunsa masu haske sosai ya sake buɗewa a kanta. Tsohon lokaci kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta, “Babu komai yanayi ne kawai”.
“Yanayi?”.
Kansa ya jinjina mata kawai. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Fuska taɗan shagwaɓe tare da faɗin, “Besty akwai matsala fa?”.
Cikin ɗan tsireta da idanu ya ce, “Tami?”.
Sake shawaɓe fuska tayi ƙasa-ƙasa kamar mai tsoron a jita ta ce, “Na daina ganin jinin, kuma ALLAH kunyar faɗama Oum nakeyi. Ina son zuwa wajensu Didi ina tsoron Baabu ya kama ni”.
“Oh nine baƙya jin kunya?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu.
Sai da ta waro idanunta waje sosai sannan ta ce, “Kai kuma zanji kunya Besty? Kai fa Besty nane. Ni dan ALLAH ka gaya min yaya zan gane ya ɗauke ɗin kenan naje nai wanka. Kuma ai irin wankan da aka koya mana a islamiyya zanyi ko?”.
Idanunsa kawai ya rumtse yana datse laɓɓansa da ƙarfi da haƙori. Miyyasa yarinyar nan bata ganewa ne wai? Taɓa shin da tai ya sashi dawowa hayyacinsa. Ta sake marairaice fuska. Sai kawai ya samu kansa da bata amsa. “Naji zan faɗa miki. Amma lokaci yayi da zaki fara fahimta”.
“Fahimta? Mizan fahimta?”.
“Ba komai”.
Ya faɗa yana miƙewa. Tashi tai itama ta bishi, amma sai yay mata nunin ta koma ta zauna. Zaman tayi, shi kuma ya fice a garden ɗin. Babu jimawa ya dawo da takarda ya bata. Kafin yace mata, “Tashi kije na rubuta miki komai”.
Batai musu ba ta miƙe, hannu ya miƙa mata. Idonsa akan novel ɗinsa dake hannunta. Sai da ta tura baki gaba sannan ta miƙa masa ta wuce....
Kwana biyu dayin haka zazzaɓi mai zafi ya kwantar da Ajwaad. Zazzaɓin daya sanya har sai da ya kwanta a asibiti. Kwanansa biyar aka sallamesa. Ana sallamarsa kamar jira itama Maanal ta fara nata ciwon. Tasha jiki sosai kafin itama ALLAH ya bata lafiya..
_________★
Zancen da Fawzan yayma Oum itama ta samu Abah da shi, shi ba mutum bane mai son takurama yaransa. Sannan yakan nutsu akan abu idan sunzo masa da shi ya dubi halaccinsa da haramcinsa a wajen UBANGIJI. Sosai yay nazari akan batun ya kuma nema shawarar Baba Sardauna. Ɗari bisa ɗari Baba Sardauna ya bada goyon baya shima akan hakan, dan tunda har Fawzan ɗin ya furta ai masa auren ai masan kamar shine yafi komai dacewa. Dan haka su Abah suka shirya zuwa Giro. Sun kuwa je. Alhamdullah Baba Haruna ya basu auren Shahidah da Amaal, basu baro ba kuma sai da suka bada komai har sadaki. Aka kuma tsaida ranar aure. Kasancewar Baabu ya zama abinda ya zama yasa sai da suka dawo Abah ya sanar da su daga shi har gwaggo. Wannan al'amari yay matuƙar ƙona zuciyar gwaggo dan itafa duk wani jin daɗin duniya bata son ganin Ammie a cikinsa.
A ɓangaren Mamy kam komai batace ba, sai ma addu'a datai da sanya albarka kawai. Haka ƴan uwanta ma albarkar suka saka. Babban Yaya ya koma makaranta, haka Ajwaad da Maanal ma. Yayinda akema Fawzan nasa shirin yin sabuwar jarabawa shi da Amaal. A haka aka shanye watanni kusan biyar, su Amal sun kammala exam, akai bikin saukar Maanal da Ajwaad tare da walimar data ƙayatar. A wajen wannan walima ne Baba Sardauna ya ɗarsa nasa burin akan Ajwaad da Maanal. Sai kuma bayan kwana biyu dayin walimar yazo har gidan abinda bai cika yi ba. Zaunar da Oum da Abah da Mamy yayi, bai ɓoye musu komai ba akan batun da yazo da shi na son haɗa auren Ajwaad ɗin da Maanal tare da ƴan uwansu. Ya kuma kawo musu hujja mai ƙarfi akan abinda ya hango game da shaƙuwar yaran. Dan gara ya kasance akwai igiyar aure a tsakaninsu gudu sharrin shaiɗan saboda kusancinsu yayi yawa. Gashi kuma suna a wata gaɓa ce mai ban tsoro akan duk wani yaro dake a wannan shekarun musamman ma shi Ajwaad da Babban Yaya ya sameshi ya warware masa komai akan halin da Autan yake ciki tun kafin ya koma, shiyyasa ya saka ido shima ya fahimci komai ya ya kuma tabbatar. Su duka ukun babu wanda ya musa ko jayayya akan abinda Baba Sardauna yazo da shi. Sun kuma gamsu da cewarsa akan ai shiru da batun kada a sanarma Ajwaad ɗin da Maanal. Su kuma barsa da Baabu shi zai yi magana da shi.
Haka kuwa akayi, Baba Sardauna ya kira Babu har gidansa sukai magana ta fahimta. Ya kuma gamsu shima ya bada goyon baya. Bayan haka Baba Sardauna yay kiran Baba Haruna shima a waya suka tattauna. Shima kuma ɗari bisa ɗari ya gamsu. Daga haka aka fara shirin bikin ƴan gata su shidda. A ɓangaren Babu babu wani ƙwaƙwƙwaran shiri, dan gwaggo da Amaryarsa sun gama zugesa tsaf ta bayan fage. To dama dai Abah yayi niyyar shiryama yaransa biyu gida da kansa. Shi ko Ajwaad dama sai sun kammala secondary za'ayi biki. Oum kuwa duk wani abu da uwa ya kamata tayi ta ɗauki ɗammarar yin komai, duk da haka Ammie ta sameta da abinda ke a hannunta, ta kuma nema shawararta akan tunkarrar Babu da gadonta da iyayenta suka bari. Oum ta bata goyon baya badan zata amshi kuɗin a hidar yaran ba, sai ɗan abinda take shiryama zuciyarta. Tana shiri akan in har aka kammala bikin yaran to lallai koma miza'ayi dole Babu ya saki Ammie. Dan ta gaji da ganinta cikin wannan zaman zaluncin da ƙuncin. Ita ba kwanciya da miji ba, ita ba ƴancin aure ba, duk ta lalace ta rame ta fita hayyacinta. Kamar ba Ammie ƴar gayu ƴar ƙwalisa ba. Sarkin tsafta da gyara jiki. Tofa dole ne su taya mata ta amshi hakkinta a wajen Babu tun yanzun.
Babu wasa kuwa Ammie ta tunkari Babu da batun kadarorinta da komai ma da iyayenta suka bar mata akan son yin hidimar biki, abinda ya tadama Babu hankali kenan, dan kuwa ya salwantar da kaso biyu bisa ukun wannan dukiya, suma kuma dangi sun ci. Shi kansa kaso ɗayan daya rage ma yana a ƙila wakala ne kawai. Ƙin cema Ammie komai yay a lokacin, face kalmar “Yaji”. Yay gaba abinsa. Bata damu ba, ba kuma ta kawo komai a ranta ba tunda rayuwar daya ɗauka ma kansa kenan a yanzu..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣3️⃣
______________
........Matakin farko na shirin biki shine shirya zuwa Dubai da Oum tayi tare da Umma (Matar baba Sardauna) da Gwaggo Khadijah. Sai dai zasu fara zuwa suyi umrah ita da Ajwaad da Fawzan da Maanal. Amaal da Shahidah kuma za'a fara musu gyaran jiki dan ita Maanal bazata tare ba sai sun kammala secondary. Sunyi wannan tafiya Maanal na'a cikin ɗunbin farin ciki, dan wannan shine karonta na farko hawa jirgin sama. Fawzan ya tasata da tsokana da dariya. Itako ko'a jikinta. Sai mutum nata data dama da surutu wato Ajwaad, yana ɗan biye mata sama-sama batare da tasan dalilin komawarsa hakan a gare ta ba yanzu. Sunyi Umrah Alhmdllh, inda suka samu kwanaki goma sha biyu kafin su nufi Dubai, can suka haɗu da Umma da Gwaggo Khadijah