Showing 84001 words to 87000 words out of 221978 words

Chapter 29 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Ta raɓashi tai wucewarta fuuuu.
Baiyi wani yunƙurin dakatar da ita ba a yanzu, dan bai ma motsa daga yanda yake tsayen ba harta gama ficewa. Sai lokacin yay wani irin kai hannu ya hankaɗar da flower base ɗin dake ata bayan kujerar mai tsananin ƙyau da ƙayatarwa. Jikake tatsatsa ya tarwatse a ƙasa komai ya zama pieces.
“I will teach you lesson”.
Ya faɗa da tsananin kaushin murya dake bayyana dukkan fushinsa. Daga haka ya juya zuwa cikin bedroom ɗinsa. Kayan jikinsa ya fara zarewa kawai yana wulli da su, kafin ya wuce cikin closet ɗinsa ya ratsa ya shige bathroom. Ƙaton gaske ne shima. An kuma tsarashi da kayayyakin toilet masu ƙawa tamkar ba banɗaki ba. Ƙarƙashin shower yaje kawai ya buɗe duka ukun ruwa suka fara saukar masa a jiki shaaaaa!! Tamkar irin ruwan samar nan mai zuwa babu zato. Hannayensa kawai ya dafe a jikin glass ɗin da aka zagaye wajen wankan da shi ruwan na cigaba da saukar masa. Yafi mintuna talatin a haka dan har numfashinsa ya fara fisga alamar ruwan ya masa yawa sannan ya kashe, a haka ya cigaba da tsaiwar ruwan daya saukar masa na kwararewa musamman na cikin sumarsa dake lashe kuɗaɗe da shi kansa bai san adadi ba. Ada shi ba ma'abocin tara suma bane, amma wasu dalilai suka sakashi fara tarawar harta zama ɗabi'arsa. Ba tara sumar kawai ba, abubuwa da yawa ya ɗabi'antu da su ne daga baya bisa wasu dalilai. Kuma a yanzu sun zama halittarsa kuma jinin jikinsa da shi kansa bai taɓa tunanin raba kansa da su ɗin ba...
Ya jima a hakan, dan sai da zuciyarsa ta koma ta kwanta cikin ƙirjinsa luf kafin yayi wanka kamar yanda ya saba da brush ya fito, idanun nan sunyi matuƙar juyewa da komawa jajaye. Gaban mirror ya tsaya yana goge jikinsa, kafin ya shafa mansa mara hayaniya ya feshe jikinsa da sprys ɗinsa masu ƙamshin tsiya da saka zuciya nutsuwa. Ya kuma gyara kansa da kwantaccen gashin dake lafe a kumatunsa, ya sama bakinsa ƙamshi. Tausasan kayan barci farare tas ya sanya, ya sake feshe jikinsa da turarurrukansa na barci tamkar ba kwanciya zaiyi ba sannan ya nufi katafaren bed ɗinsa dake a wani kalar dunƙule waje guda tamkar zero. Zama yay ya jingina da gadon tare da kai hannu ya rage fitulun ɗakin ya maida mai duhun haske sai bed side lamp kawai dake kunne itama ta gefensa. Sai da yaja lallausan duvet ɗinsa ya rufe ƙafafunsa zuwa ƙugu sannan ya ɗauki eyeglasses ɗinsa dake ajiye kusa da novel ɗinsa dake a bed side drawer ɗin ya saka, novel ɗin shima ya ɗauka. Alamar daya saka a inda ya tsaya ya sashi buɗewa kai tsaye ya fara karatu cike da son kauda komai dake cinkushe da zuciyarsa.....


___________★


Kamar yanda ta saba damunsa a kowanne dare da sakwanni yau ma tsaf ta kammala shirin barcinta ta faɗa saman gado. Jinta take wani free yau ita kaɗai a ɗaki babu Maanal. Sai hakan ke sakata nishaɗi tun ɗazun. Yayinda tuni ta kaima uwarta gulmar fitar Maanal ɗin da saurayi da rashin dawowar tata. Nan sukasha gulmarsu da aibanta Maanal ɗin wai tana can an kaita hotel yawon fasiƙanci dai aka fake fa dubiya. Bayan sun kammala wayar ne tai abubuwan da malam ya bata tai shirin barci shine ta ɗauki waya. Kai tsaye data ɗin ta ta buɗe. First WhatsApp ta fara shiga, duk da ta fahimci kamar bai cika damuwa da WhatsApp ɗin ba sam. Amma tanan take saurin gane idan yana online. Koda yake da wahala ma kaga ya kashe data shi kam. Yanzun ma dai kamar yanda tai fata yana online ɗin, cike da farin ciki ta tura masa sallama da gaisuwa kamar yanda ta wajabtama kanta a yanzu. Ganin fin minti biyar babu amsa ta shiga masa WhatsApp call. Amma har ya kashe ba'a amsata ba. Fita tai ta koma ta tura masa ainahin massege, nan ma mintuna biyar shiru. Sai tai direct call kawai tana fatan ya ɗauka koda bazai ce mata komai ɗin ba kamar yanda ya yi mata. Dan data taki sa'a ya ɗauka har sau kusan uku data kira shi, sai dai daga sallama da amsa mata gaisuwa a cinkushe baya sake cewa komai zai barta taita surutunta harna tsahon mintinan data fahimci batasu yake daga haka a takaice yace goodnight ya yanke wayarsa. Kota sake kira kuma bazai amsa ba. Sau biyu yana mata haka, sakamakon roƙon wannan alfarmar datai a garesa jiya data bisa office, a lokacin bai tanka mata ba, amma data kira ɗin bayan ya gama bata wahala sai ya amsata a jiyan, hakama yau da safe. Shine ta samu hope ɗin sake kiransa yanzu ma da fatan ya ɗaga ɗin dan tanada yaƙinin aikin malam ya fara karɓuwa. A wajen bikin Yaseerah ko kallo bata ishesaba fa, amma a wannan karon gashi ya kulata har a office data samesa ya kuma bada mota aka maidata gida, ai dole tace aikin malam yayi.
A kasalance ta ajiye wayar ganin kira har uku babu amsa, amma sai zuciyarta sam bata gajiyaba, har yanzu tana jin zalama da fatan ya amsa ɗin. Sake tura masa text massage tayi har uku na roƙon ya ɗaga kiran, ta watsap ɗin ma ta tura masa, sannan ta sake kira. Sai dai yanzun ma babu alamar zai ɗaga mata. Idanunta na zubar da hawaye ta tura masa tsararren sabon saƙo masu kalamai masu armashi da kashe zuciya sannan ta kwanta badan taso hakan ba. Ta jima batai barci ba hawaye na bin fuskarta. Ita kanta bata san irin son da takema bawan ALLAHn nan ba. Amma tabbas mai zafi ne. Matuƙar zafin da ta tattabar idan bata mallakesa a matsayin miji ba akwai ƙura......


___________★


Maanal bata koma sashen Oum ba sai da ta tabbatar ta daidaita kanta da nutsuwarta a waje. Dan sai da tasha kukanta sannan ta share hawayenta tsaf ta koma sashen Oum ɗin. A falo ta sameta mai aikinta na kwashe su Barrah da sukai barci za'a kaisu ɗaki ai musu shirin barci kamar yanda taji Oum ɗin na bada umarni. Komai batace ba, sai zama tai tana murmushi da faɗin, “Oum duk munzo mun sakaki wahala”.
Harararta Oum tayi cikin sigar wasa. “Oh haka kike ɗauka shiyyasa kika kasa sakin jiki dani. Gaba ɗaya kamar ba Lillyn babban yaya ba, kamar ba Autar Oum ba, kamar ba Bestien Auta ba. Maanal kin canja min, matuƙar canjawa da mamakin hakan ya kasa barina”.
Kai kawai Maanal ta duƙar tana murmushinta mai sanyi, sai kuma ta furta, “Nama manta banga Babban Yaya da matarsa da Mamy da Abbah ba?”.
“Uhm sai yanzu kika tuna da su? To suna nan abinsu. Mamy tana tare da Abbanku ne a ƙasar Oman, Amma ina ƙyautata zaton nan da kwana biyu suna hanya insha ALLAHU. Babban yaya kuma da matarsa da matar Fawzan da yara suna Kano ana bikin ƴar ƙanwar Mamy ɗin ne kin san kuma itama Saheeba kamar ƙanwa ce a wajenta. Shine matar Fawzan ta mata rakkiya shima yau Babban yaya ya wuce da yammar nan dan yana fita kuna shigowa. Ɗaurin auren safe ne shiyyasa yaje ya kwana sai ya dawo goben idan ALLAH ya kaimu. Su kuma sai biki ya tashi, Fawzan da Auta aiki ya hanasu zuwa, ni kuma jikin nawa ne sai a hankali”
Cikin gamsuwa Maanal ta jinjina mata kai batare data sake cewa komai ba, sai dai tayi mata addu'ar lafiya mai dorewa. Daga haka itama Oum ɗin ta zuba mata ido kawai. Sai kuma zuwa can ta katse shirun nasu da faɗin, “Rafeeq ɗin ya wuce kenan?”.
Batare data ɗago ba ta ce, “Eh wai ana jiransa a asibiti ne”.
“Uhm ai ya riga da ya ɗaurama kansa irin aikin Papa. Gashi nan gaba ɗaya nauyin ya koma kansa yanzu, dan ma Papan na ƙoƙarin rage masa wasu abubuwanne. Mu kuma so muke shi ya huta saboda tsufa, dan ma ALLAH ya bashi jiki mai ƙyau ne da kuma zuciyar taimakon al'ummar. Tun yaushe kuke tare da Rafeeq Maanal?”.
Matuƙar dukan zuciyarta tambayar tai, dan har sai da ta motsa mata a cikin ƙirji, maƙoshinta ya ɗan bushe saida ta haɗiyi yawu da ƙyar. Yanzun ma bata ɗago ba kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta bama Oum ɗin amsa cikin Muryar tan nan ƙasa-ƙasa.
“Shekara ɗaya kenan Oum, a Jos inda nayi sarvese”.
“Oh iko ALLAH, dama kece yaketa bani labarin ya samu a Jos ashe. ALLAH mai girma kenan. Ya jima yana faɗa mana ni da Majdiya, sai dai bamu maida hankali ba saboda sanin halinsa sarai. An jima ana fama da shi akan aure yana botsarewa da faɗin shi baiga wadda tai masa ba. Har Papa ya fusata zai haɗashi da wata yarinyar abokinsa sai gashi da zancen ki. Amma sai babu wanda ya ɗauka serious ne. Ko kwanciyar asibitin nan naƙi zuwa ne saboda ban wani yarda da gasken yake ba duk da Majdiya ta sake tabbatar min. Ashe nayi sake da tuni naga ɗiyata da ƴar uwata. Nayi kewar Asiya matuƙa Maanal. Haka ke da su Amaal, idan na tunaku a raina har hawaye nake wani lokacin. Bana fatan ALLAH ya sake maimaita min abinda ya faru a baya”.
Hawayen da suka cika idonta suka gangaro. Hannu tasa ta sharesu da sauri tana murmushi mai ciwo. Sai kuma ta miƙe tana faɗin, “Kinga tashi muje kiyi shirin barci ki kwanta. Dan Rafeeq ya jaddada min ki kwanta da wuri”. Ta ƙare maganar tana ƴar dariya da kama hannun Maanal ɗin da jikinta yay wani kalar sanyi ƙalau.........✍️










✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣8️⃣




______________




https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥💃💃 Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....🔥⭐⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑royal jelly na fidda shape din mace...💃💃⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥⭐👑💃🏼💃🏼 Haseer supplements ta kawo muku supplement kaloli sai wanda ranki keso hajiya a cikin farashi mai sauqi Phone: 08038796871


_________




........A haɗaɗɗen bayin Oum Maanal tayi wanka. Ita dai sai bin ko'ina take da kallo. Tun can baya tasan su Oum nada kuɗi, amma komai nasu ya sake canjawa daga sanin datai masan. Ita kanta Oum ɗin ta sake gogewa ko tsufa batayi. Da waɗan nan tune-tunen ta fito a wankan. Rigar wanka ce dan haka bata ɗan ji takura ba sosai, koda yake Oum bata cikin mutanen daya kamata acema tana jin kunya, to mi zata ɓoye mata, matar da tun bata san kanta ba take mata wanka harda goyo. Tasha kwana a gadon Oum daga ita sai pant. Oum da Bestyn ta ne suka fara sanin jinin haila yazo mata. Kalmar (Besty) ta sake maimaita kanta a cikin zuciyarta, sai kawai taji zuciyar tata ta mata nauyi. Ture tunanin tayi da ƙarfi ta maida hankalinta ga bin ɗakin da kallo. Oum ta fita, sai kaya da aka ajiye a saman gado. Kayan ta matsa ta ɗaga. Wando da riga ne na barci, sunada yalwar da bazasu matseta ba ko kaɗan. Bata wani ɓata lokaci ba ta sanya, tana gama sanyawa Oum ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da wani ɗan basket mai ƙyau golden. A gefen Maanal ta ajiye, Maanal ta kalleta tana mata sannu sannan ta kalla kayan. Mayukane da zasuyi dai-dai da fatarta, ba daidai da fatarta kawai ba ta jima da saninsu, dan dasu take amfani ada, bayan ita kuma mutum ɗaya tasan yana amfani da su a gidan....
Kamar Oum tasan mi take tunanin ta katseta da faɗin, “Nasan nawa bazasu ma skin ɗinki ba. Shiyyasa na kira Auta ya kawo miki nasa dan nasan fatanku yana ɗaukar mai iri ɗaya ne, sai kuma akai sa'a irin wanda ma kike amfani da su ne. Maza ki shafa kada jikinki ya bushe bara nima nai wankan”. Daga haka Oum ɗin ta miƙe batare da ta jira cewarta ba. Maanal ta jima bata motsa ba idanunta akan kayan shafar, wani abu ne mai nauyi ke tsikarar mata zuciya. Yayinda tunaninta ke kai kawo da tambayar kanta miyyasa ya cigaba da amfani da irin manta? Miyyasa wasu abubuwa nashi har yanzu suna a yanda ta sansu, waɗansu kuma a baya suke yawan faɗa akan tana so yayi su yaƙi yi. Amma a yanzu duk sai taga yana yin su.....
Knocking ƙofar da akayi ya sata ture tunaninta gefe ta kalla ƙofar, jin an ƙara na biyu yasa ta miƙewa ta ɗan gyarama su Barrah bargo sannan ta nufi ƙofar, duk zatonta cikin masu aikin Oum ne. Sai dai tana buɗewa taci karo da abinda bashi tai zato ba. Muƙut ta maida abinda tai niyyar faɗa ta haɗiye abinta tare da janye idanunta daga kansa taja jikinta baya ta koma tai zamanta a inda ta taso. Sai lokacin ya ƙarasa shigowa ɗakin hannayensa duka biyu zube cikin farin wandon kayan barcin sa. Tafiya yake cike da ƙasaita, ga mayataccen ƙamshinsa duk ya rikita ɗakin. Baiko kalleta ba ya wuce closet ɗin Oum kansa tsaye kuma hankalinsa kwance. Ƙasa-ƙasa Maanal ta bisa da kallo, tana mamakin mi kuma ya kawo shi yanzu. Bata da mai bata amsa, sai ma kira daya shigo wayarta a dai-dai lokacin. Wayar dake acan saman mirror ta ɗan zubama ido, sai ta tsinta kanta da jin nauyin jiki har kiran ya tsinke. Wani kiran ne ya sake shigowa, sai hakan yay dai-dai kuma da fitowar AA hannunsa ɗauke da wata bag ƙarama. Har ya wuce batare daya kalleta ba itama ta miƙe da nufin ɗaukar wayar sai ta hangesa agaban mirror ɗin kamar mai neman wani abu. Komawa tai ta zauna, sai kawai jin ƙarar wayarta tai a ƙasa. Da sauri ta ɗago, wayar tata ce kuwa, yayinda shi kuma yake duƙe yana duba abu a drawer ɗin jikin mirror ɗin tamkar ma baiga abinda ya faru ba. Oum dake fitowa ta ce, “Subahannahi kako yaddoma Auta waya Auta”.
Tsabar rainin hankali irin na AA sai ya juyo irin as bai lura ɗin nan ba ya ɗauki wayar yana jujjuyawa, ƙarasowa itama Oum ɗin tai inda yake ta amshi wayar ta duba. Gaba ɗaya tayi tatsa-tatsa. Screen ɗin yay wani irin zuuuuu alamar ya tashi aiki shima. Babbar waya ce, dan SS ce babba Daddy ya saya mata ita gift ɗin kammala karatun ta.
“Auta kayi ɓarna”.
Oum ta faɗa tana sake jujjuya wayar. Fuskarsa dake a tsuke ya yamutsa babu alamar damuwa a tattare da shi ya ce, “Oum ban lura bane. Kawo zanba Ahmad da safe ya gyaro”. Yay maganar yana miƙama Oum hannu. Kanta kawai ta girgiza da ɗora masa wayar a hannunsa. Shi kuma batare daya ce komai ba ya ɗauka bag ɗinsa ya fice. Ajiyar zuciya Oum ta sauke tare da juyawa ta dubi Maanal. “Karki damu kinji Auta, nasan in sha ALLAHU zai bada a gyara kafin wucewar mu goben”.
Murmushin yaƙe kawai Maanal taima Oum. “Babu komai Oum”. Itama Oum ɗin sai tai murmushi tana jinjina mata kanta. Haka sukai shirin barci suka kwanta. Dan har Oum ɗin kwanciyarta tai a gadon tana faɗin, “ALLAH ya yarda yau zan sake kwanciya gado ɗaya da Babyna”.
Siririyar dariya Maanal ta saki, yayinda Oum ke tayata itama zuciyarta cike da nishaɗin yanayin.....


__________★


Washe gari da safe bayan sunyi wanka suna dining da shirin karyawa harda Ya Fawzan AA ya shigo. Da mamaki Oum daya fara gaidawa take kallonsa. Dan a shirye yake tsaf cikin baƙaƙen suit da suka sake fiddo ainahin cikar haibarsa da madarar ƙyau.
“Yau ba Saturday ba na ganka da shirin office?”. Oum ta faɗa cikin kasa haƙuri. Hannu ya miƙama Yaya Fawzan yana bata amsa da, “Oum project ɗin nan da nake gaya miki yau zamu fara aikinsa da Engineers ɗinmu”.
“Okay aina ma shafa'a, ALLAH yasa ayi cikin nasara ya kuma ɗaga darajarsa. Maza to zauna ka karya dan bazaka fita da yunwa ba”.
Agogon hannunsa mai matuƙar nauyin kuɗi da zama designer daba ako ina zakaje ka samesa ba sai ga wanda ya isa ya kalla. Cikin ɗan ɓata fuska ya ce, “Oum Please zansha coffee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login