Showing 183001 words to 186000 words out of 221978 words
Chapter 62 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
da girman naki a titin mutane to Madam Maanal Giro”.
Sam ba fahimtar inda zancen nasa ya nufa tai ba. Amma taji a ranta akwai shaƙiyanci a ciki. Bata kulashi ba ta sanya belt ɗin ta sake tada motar. Hanyar anguwarsu ta ɗauka, dan gara ta masa yanda yake so su rabu lafiya kawai.....
Ganin hanyar da Maanal ta ɗauka ya saka Nurry dake binsu a baya tun daga shagon Saloon saurin dannama Mamy kira. Bugu biyu ta ɗaga, ko sallama batai ba ta ce, “Yauwa Mamy ga su nan sun nufo nan gidan, kuma itace ma ke tuƙasu, amma kamar baida lafiya ma”.
Kai ta jinjina tana sauraren abinda Mamyn ke faɗa daga can, kafin ta yanke kiran sannan taja motar zuwa hanyar nasu gidan. Ƙawarta ta ce, “Amma Nurry baƙya tsoron ya gane kece kika faɗa ma mamansa”.
“Bazai gane ba, shiyyasa nake so ta gansu da idonta ai.”
Kai kawai ƙawar tata ta jinjina alamar gamsuwa.....
A ƙofar katafaren gate ɗin gidan nasu ta tsaida motar, hakan ya sashi buɗe idanunsa ya kalleta. Ganin tana ƙoƙarin kunce belt ya ce, “Yanaga kin tsaya anan? Ki shiga mana”.
“No ka ƙarasa da kanka, ni zan koma daga nan”.
“Bazaki gaida su Oum ba?”.
“Next time”.
Kansa ya jinjina kawai ya cire nasa belt ɗin. “Kije da motar zan aiko driver ya amsa”.
“A'a zan hau taxi”.
Dakatawa yay daga ƙoƙarin fitar da yake, ya ɗan juyo yana kallonta. “Kin san fa bana son musu, taxi kuma na haramta hawanta daga yau”.
Komai batace da shi ba saboda yanda ya tsatstsareta da idanu. Shima sai bai sake cewar ba ya buɗe ya fita. Sai kuma ya ɗan duƙo ta glass ɗin windown. “Kije gida magrib ta kusa. Kuma kiyi tuƙi a hankali”.
“Ni Company zan koma ɗaukar kayana”.
“No ban yarda ba kije gida. Driver zai taho miki da su. Ki kula da kanki”.
“ALLAH ya ƙara lafiya”.
Ta faɗa itama tana maida glass ɗin ta rufe duka tare da yin baya. Yana tsaye yana kallonta har sai da ta ɓace masa. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da furzar da iska. Sai kuma ya shafa cikinsa yana yamutsa fuska kaɗan. A hankali ya juya yay knocking gate ɗin gidan nasu. Maigadi ya leƙo yana tambayar waye. Ganin AA ya sashi haɗiye sauran maganar, mamaki fal ransa na ganinsa a ƙafa. Bai dai ce komai ba ya gaisheshi. Shi kuma ya amsa masa yana wucewa ciki. Da Mamy ya fara cin karo zaune a gaban sashen Oum, sai Naufal da Anum dake wasa da keke. Yanda ta wani zuba masa idanu tun daga nesa ta sashi janye nasa da ga kallonta. Cikin dauriya ya ƙarasa inda taken, su Naufal da sai yanzu suka gansa suka sheƙo da gudu suna masa oyoyo. Daurewa yay ya tarbesu, sannan ya shiga gaishe da Mamyn. Bata amsa ba, sai mugun kallo da take jifansa da shi.
“Ina motar taka?”.
Ta jefa masa tambaya a bazata. Bai iya ƙarya ba, ya kuma tsani mai yi, amma ya fahimci yau dolensa ma ya yi tan. Batare daya yarda sun haɗa ido ba ya ce, “Tana gareji Salihu ya kaita. Nima taxi na biyo”.
Rasama abin cewa Mamy tayi, dan yayi wani kicin-kicin da fuska, sai kawai ta zuba masa idanu. Shiko ya sake ciɗin-ciɗin da fuska. Batare daya yarda ya sake kallonta ba ya saki hannun su Naufal ya nufi sashensa dan ruwa kawai yake buƙatar sakarma kansa. Ko Oum baya son ta gansa a wannan yanayin. Ita kanta Mamy ɗin bai so ta ganshi a hakan ba....
A ɗan tsawace ta dakatar da shi, dole ya tsaya yana mai lumshe idanunsa, sai kuma ya dawo da baya inda take. Miƙewa tai batare data sake kallonsa ba cike da bada umarni ta ce, “Anjima ka sameni zan yi magana da kai”. Daga haka tai wucewarta. Da kallo kawai ya bita, wani abu mai nauyi na masa kai-kawo a cikin wuya da maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sosai. A hankali ya furzar da iskar numfashi, sai kuma ya nufi sashen nasa....
__________★
Baki a wangale maigadi ke kallon Maanal daya buɗema gate. Taja motar a hankali zuwa cikin gidan. Bawai tuƙin nata ne ya bashi mamaki ba, dan yasan tana jan mota idan tazo. Ganin ɗirkekiyar motar da take ja ɗin ce da kuma sanin da yay mata bai taɓa ganin ta tuƙa wata mota ba sai ta gidan ya sashi a mamakin....
Turus itama ta tsaya tana kallon motar RK lokacin da take fitowa. Sai kuma ta ɗan leƙa gaba kaɗan. RK ɗin ne shima da kansa zaune a cikin motar tasa ya zubama motar data ajiye ido ko ƙyaftawa bayayi. Ta tabbatar kallon ƙurillar da yakema motar ya gane ta wacece ne. Sai kawai ta dake abinta ta ƙarasa garesa. A hankali ya janye idanun nasa daga kallon motar ya maida kanta. Batare da ya amsa sallamar da take masa ba ya furta, “Dama kina jan mota haka?”.
Guntun Murmushi kawai tai masa ta ce, “Uhmm!”.
“Masha ALLAH, kinyi ƙyau kuwa da motar”. Ya faɗa yana fitowa da ƙyau daga motarsa.
“Oh harda zolaya ma abin kenan?”.
“Babu wata zolaya gaskiya na faɗa miki. Naje ɗaukarki a office AS ɗin Boss ɗinki yace kun fita tare tun la'asar. Shiyyasa na wuto nan dan na matsu na ganki”.
Murmushi tayi batare data tanka maganarsa ta farko ba ta ce, “Kamar wanda ya shekara bai ganni ba?”.
“Miye maraba my queen. Kwana huɗu fa. Ya kuka baro su Ammie?”.
“Lafiya Lau suke, suna gaisheka. Ya aikin?”.
“Alhamdullahi munata fama. Shi AA ɗin yana office kenan?”.
Murmushi ta saki a taƙaice, dan ta fahimci dole dai so yake sai anyi maganar AA ɗin nan. Sai kawai kanta tsaye ta ce, “Yana gida baida lafiya. Dan da wajenka ma zan kaishi yace na dai ajiyesa a gida”.
“Mike damunsa?”.
“Kamar ciwon ciki yace”.
“ALLAH ya bashi lafiya, yasa kaffara ne. Bari nai salla zanje na duba shi.”
“Okay ai ni dama da motar tashi ka wuce, sai driver ya bika da ita”.
“A'a, bashi ya baki ba da hannunsa”.
“Dama yace zai turo driver ya ɗauka ne. Ni kuma bana ma so Didi taga motar a gidan ne”.
“Dan mi to?”.
“Kawai”.
Shiru kawai yay yana kallonta. Yasan ƙarshem zancen kenan. Yau ma ai babu laifi an amsa masa magana da tsaho sosai. Ajiye zancen yay shima gefe ya fara wanda ya kawo shi ganin magrib na sake gabatowa. “Magriba na gabatowa. Ga shi inada uziri da daddare. Kuma ina son muyi magana yanzu ALLAH yasa ban takura ki ba”.
Kanta ta jinjiina masa alamar eh. Shima sai ya cigaba da faɗin, “Maanal na karanta diary ɗinki duka. Ba kuma zanja wani zance ko neman ƙarin bayani ba daga gareki ko daga wani, ina son ki bani dama magabata su shigo cikin al'amarinmu. Idan kuma babu damuwa ina son bikin anan kusa”.
Duk da wani irin motsawa da zuciyarta tayi haka ta dake. Tai ƙasa da kanta tana sakin miskilin murmushi. Sai kuma ta jinjina kan batare data kallesa ba tace, “Duk da ƙaddarar data shiga cikin rayuwata da mutunci na ka amince zaka aureni a haka Rafeeq?”.
“Maanal! Ke nake so ba jikinki ba. Kuma kema kince ƙaddara ai. Ƙaddara kuma babu wanda ya isa faruwarta ga kansa balle wanninsa. Haka ALLAH ya tsara miki rayuwa ai. Dan haka ki manta da baya kamar ma bata faru ba. Ni ke nake so Maanal, ke nake so ki zama uwar ƴaƴana. Halayenki, tarbiyyarki sune gaba a komai. Yanda na fara sonki ban san ke ɗin wacece ba, sanin ke wacece bazai sa na taɓa canjawa ba. Ni dai kawai fatan da nake da roƙo ki soni koda kwatar soyayyar da nake miki ne, wanda nake mikin ta ishemu rayuwa in sha ALLAHU”.
Karan farko Maanal ta ɗago tana kallonsa, idanunta na zubar da hawaye. “Nagode Rafeeq. Nagode sosai da ɗunbin soyayyar da kake min. Kuma ni ban taɓa ƙinka ba, ba kuma zan taɓa ƙinka ba. Sai dai kasan akwai ƙalubale a gaban mu”.
Sai da ya miƙa mata handky ɗinsa sannan ya ce, “Nami?”.
“Yaya Yazeed, ya taka rawar gani sosai a rayuwata, shima bai gujeni ba duk da yasan wacece ni. Wasu dalilai ne yasa kawai nake gujema aurensa domin samun zaman kafiyarsa shima. Amma a yanzu ban san yanda zan tunkare shi shi da mahaifinsa ba, kai har ma Ammie”.
Ta faɗa tana share hawaye. Murmushi ya saki mai faɗi har haƙoransa na bayyana. Sai kuma ya gyara tsaiwa sosai. “Sweetheart na fahimce ki, kuma abinda kika faɗa gaskiya ne. Amma muyi addu'a, da. ban taɓa kallon Yazeed a ƙalubalena ba game dake dama. Duk da ina fargabar kada ki zaɓesa ki barni, ta wani gefen kuma jin rawar daya taka a rayuwarki ta ƙara sani ganin girmansa da jin kimarsa a raina fiye da da. Amma tunda kece kika bani dama a yanzu da kanki na samu dukkan ƙwarin gwiwa. Zan iya karawa da kowa domin mallakarki. Karki wani damu zanyi maganin wannan matsala ɗin in sha ALLAHU. Ke dai kawai ki kasance cikin shirin zama amaryar Rafeeq Kasheem Kura anan kusa kaɗan”.
Murmushi tayi da juya masa baya. Shima sai yay dariya. Leda ya ciro a mota ya miƙa mata. “Ga wannan ki shiga da shi ciki bara naje, idan na gama da wuri zan dawo. Idan kuma dare yayi a shirya mini lokaci na musamman zan kira waya mu ƙarasa anan. Amma dan ALLAH bana son ganin hawayen nan masu daraja suna fita. Baki ji yanda nake jin zafin a zuciyata ba”.
Kai ta jinjina masa kawai. Ta amsa ledar tai godiya. Sai da taga ya shiga mota sannan ta nufi ciki, ya ɗan bita da kallo ta cikin mirror yana murmushi. Sosai yake jin zuciyarsa na ƙara samun nutsuwa. Tabbas yana son yarinyar nan. Ba kuma yajin akwai wani abu da zai bari ya rabasu. Alaƙarta da AA ta baya ko a ƙasan slippers ɗinsa bai ji ta damesa ba. Tunda a kaf labarin bai ji a inda ko sau ɗaya AA ya furta yana sonta ba ko ita tana son shi. Daga ƙarshe ma da bakinsa yace shi baice yana son aurenta ba. Hakan na nufin babu soyayya kenan shaƙuwace kawai da kowa kema kallon soyayyar. Da wannan tunanin ya fice a gidan.....
__________★
“Hajiya! magana ta gaskiya yaron nan al'amarinsa nada matuƙar nauyi da tsauri. Ni kaina na shiga mamaki da ruɗani da Hajiya ta sanar min aikin da duk mukai masa bai shigesa ba. Shiyyasa na tsananta bincikena a kwana biyun nan, dalilin ma ce miki ki dakata da zuwa sai yau kenan”.
Cikin matuƙar damuwa Hajiya Basariyya ta ce, “To malam yanzu yaya ake ciki kenan? Dan gaskiya yarinyata na sonshi sosai. Kuma nima ina mata sha'awar aurensa”.
Ƴar dariya malam yayi, sai kuma ya kalla Huznah da keta faman kuka a jikin Maman Yaseerah. Janyewa yay ya maida ga Hajiya Basariyya. “Hajiya ku kwantar da hankalinku komai zai yi dai-dai. In har za'abi dukkan matakan da zan bayar zata aureshi. Sai dai akwai ƙalubale babba a gabanta....”
Cikin sauri Huznah da tun da malam ya ce zata iya auren AA ta ɗago da sauri ta ce, “Kowane irin ƙalubale ne zan iya ɗauka Malam, wlhy ina son shi, zan iya ɗaukar komai in har zan zama mallakinsa”.
Dariya malam ya sake yi da faɗin, “Kin tabbatar zaki iya?”.
“Ko miye kuwa Malam”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya miƙa mata zabgegen carbin hannunsa. Da sauri ta amsa, zaɓar ɗaya yace tayi, tako zaɓa ɗin. Amsar wanda ta zaɓa yayi ya rufe idanunsa yana muy-muy da bakinsa. Su dai duk idanu suka zuba masa kawai.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣0️⃣
______________
.......Fin mintuna uku ya buɗe idanun nasa tare da ajiye carbin sannan ya dubi Maman Yaseerah. “Wato Hajiya babban ƙalubalen shine akwai wadda ke'a zuciyar yaron gaskiya da jimawa. Dan haka yaƙi biyu kawai da zamuyi zai sa ta samu damar aurensa. Na farko shine cire yarinyar daga zuciyarsa gaba ɗaya, ba kuma zamu iya yin hakan ba sai mun san wacece ita. Na biyu zamuyi aiki akan iyayensa, ta yanda ko baya so zasu sakashi dole amsarta. Mu kuma idan ta shiga daga ciki sai muyi aikin karɓa mata zuciyarsa ta yanda bazai sake kallon wata mace ba a duniya sai ita. Kai hatta uwar data haifesa wlhy sai dai tabi bayanta”.
Gaba ɗayanzu babu wanda fuskarsa bata washe da murmushi ba. Sai Hajiya Basariyya ce ta ce, “Amma malam taya zamu san wadda ke cikin zuciyar tasa ne to? Sai naga kamar hakan zaiyi wahala”.
“Bazaiyi wahala ba Hajiya. Wannan aikin na yarinyarki ne. Ita zata bincika mana ai”.
“Karka damu Malam zanyi ƙoƙarin hakan. Sai dai akwai wata yarinya Nuratu da muka haɗu, itama tana sonshi, ban sani ba ko ita ce a zuciyar tashi, dan har ciwon nan itace ta jimin shi”.
“Nuratu!”.
“Eh malam”.
Ɗan jimm yay, sai kuma ya sake ɗaukar carbi ya bata. Amsa ta sake yi ta zaɓa. Kamar dai ɗazun yanzu ma ido ya rufe na wasu mintuna sannan ya buɗe. “Gaskiya ba ita bace. Abinda na gani a kanta mahaifiyarta ke son ta aureshi da wata ta kusa da ita dake a cikin gidan su yaron. Suma kuma suna aiki a kanshi sosai, a yanzu haka ma suna shirin yin mai zafin gaske duk dan itama ya aureta.”
“Eh lallai, ashe suma waɗan nan shegun kansu ne. To aiko Malam ai mana maganinsu, dama nace bazan yafe mata ciwon da ta jima Huznah ba. Jiba yanda ta maida min da fuskar yarinya kamar ƴar yarbawa ko goburawa. Ashe itama ba sonta yake ba shegiyar yarinya kawai”.
“Karki damu da wannan Hajiya nasu mai sauƙi ne. Yanzu zan haɗa mata abubuwa taje ta cigaba da amfani da su. Nan da kwanaki uku zan kammala aikina nima. Itama sai tai ƙoƙarin samo mana wadda ke'a zuciyar tashi”.
Godiya suka shiga jera masa kamar shine mai basu biyan buƙata. Maybe ma basu samun lokacin yima UBANGIJIN dake basun magiya irin haka ba. Gidan su Maman Yaseerah suka koma, dan anan zasu yini zuwa anjima su koma Kaduna......
___________★
Bayan sallar magrib AA ya baro massallaci. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa. Bai sameta a falon ƙasa ba, dan haka ya haye sama. Sai da yay sallama a ƙofar bedroom ɗinta ta amsa da bashi izinin shiga sannan ya shiga. Tana zaune kan abin salla, tunda ya shigo kuma ta zuba masa idanu. Hakan ya sashi tsayawa yay shiru. Wani irin ɓacin rai taji ya tokare mata maƙoshi, a kausashe ta ce, “Ni zan taso kenan”.
Komai bai ce ba ya ƙarasa takowa har gabanta ya zauna a saman lallausan carpet ɗin wajen ya tanƙwashe ƙafafu. Kansa a ƙasa ya gaisheta. Kai da ka gansa kasan babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Sai ma shakka da girmamawa irin ta na sama akan na ƙasa. Sai da ta gama shan ƙamshinta cikin kaushin harshe ta furta, “Ajwaad miye matsayina a wajenka?”.
Idanunsa ya lumshe a hankali, maƙoshinsa na kaikawon ɓacin rai a cikin wuyansa. Da ƙyar ya iya amsa mata da, “Mahaifiya”.
“Ai baka ɗauke ni a mahaifiyar ba. Saboda Fateema ta fini. Inda ka ɗauke ni da ban sharɗanta maka sharaɗi ba harda ALLAH ya isa kaƙi bi. Ya mukai dakai a shekarun bayan akan wannan shegiyar yarinyar ƴar matsiyata?”.
Kasa bata amsa yay, sai dai fuskarsa tai masifar rinewa. Mamy ta daka masa tsawa jikinta har yana rawa. “Wlhy zan mareka. Wane alƙawari ka ɗauka min akan Maanal! Da zaɓin matar aurenka?”.
Karan farko ya kalleta da rikiɗaɗɗun idanunsa da sukai masifar kaɗewa, sai kuma ya maida kansa ƙasa. Cikin kwantar da murya da girmamawa ya ce,