Showing 102001 words to 105000 words out of 221978 words

Chapter 35 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

nasa mai shegen girman kai.
Lokacin da suka iso su biyun Abah nata ƙoƙarin gwada key a ƙofar bedroom ɗin AA ɗin, yayinda Oum ke duba sauran bedrooms ɗin da ɗazun rikicewa ta mantar da ita dubawa. Dama bedrooms uku ne a saman, ƙasa ma uku. Ɗaya a main falo biyu a ɗayan falon.
“Abah lafiya kuwa?”.
Fadeel daya iso ya faɗa a rikice. Batare da Abah ya dubesa ba ya amsa masa da, “Ban san mike faruwa ba nima Fadeel. Oum ɗinku ce tazo hankali tashe tana sanar min Ajwaad ya kulle kansa a ɗaki”.
Kafin Babban yaya ya samu damar cewa wani abu ƙofar ya buɗe. Su duka afkawa sukai ciki har Oum da matar babban yaya data iso yanzun nan. Aiko tuni hankalinsu ya sake tashi dan ganinsa a bargo, yayinda tuni Oum da babban yaya sun haura saman katafaren gadon nasa dake a dunƙule kamar zero. Oum ce ta yaye bargon dan har fuskarsa ya rufe, hucin zafin zazzaɓinsa ne ya bugeta, sai kuma rawar sanyin da yake faman yi. Cikin fashewa da kuka Oum ta kamo hannunsa ta damƙe cikin nata tana kiran sunansa......


________★


Kusan zamu iya cewa a position ɗaya AA da Maanal suke a ciki. Dan itama bama ta san a yanayin data iso gidan ba. Sai maigadi ne ya biya taxi drivern daya kawota. Itako tuni ta shige ciki tana layi saboda nauyin da ƙirjinta yay mata har numfashinta na seizing. Batama ko ƙarasa shiga cikin ainahin falon ba ta zube a ƙofa tana ƙoƙarin kiran sunan Shahidah sai dai muryarta sam bata fita. ALLAH ne ya taimaka Linda ta fito dan tana ƙoƙarin jera abincin su Barrah a d/table kasancewar suna gab da dawowa daga school. Idanu ta zaro tare da dangwarar da abinda ta ɗakko ɗin ta nufi Maanal da gudu. Ganin numfashinta na neman barin gangar jikin ta yasa Linda kwara ihu. Ai a guje baba magajiya ta fito daga kitchen tana tambayar Linda mike faruwa?. Ganin Maanal dake kakarin mutuwa yasa itama ta fasa ƙarar. Sai kuma ta runtuma waje a guje tana kiran maigadi. Cikin sa'a ta samesa tare da drivern yara da yazo ɗaukar mota zai tafi ɗakkosu. A guje suka koma ciki su ukun, Linda da Baba magajiya suka cicciɓi Maanal suka fito, a mota aka sakata, baba magajiya ta shiga itama driver yaja suka fice aka bar maigadi da Linda dan bazai yiwu subar gidan babu kowa ba kuma.
Maigadi ne ya tunatar da Linda cewar ya kamata ta kira Hajiya ta sanar mata. Sai yanzu itama ta farga da haka. Lokacin da ta kira Shahidah tana tsaka da aiki, amma haka ta wancakalar da komai cikin tashin hankali ta fice zuwa asibiti bayan ta kira RK. Cikin tashin hankali ya sanar mata isowar su Maanal ɗin a yanzu haka. Kana jin muryarsa kasan shima ya gama gigicewa, sai Shahidah ta ƙara ruɗewa itama.


★ A wannan karon ma dai ansha matuƙar wahala kafin ceto numfashin Maanal, sai dai sam babu aman jini idan ka cire wanda ya ɗan ziraro mata ta hanci kamar haɓo. Shima kuma basuyi wahala wajen tsaidashi ba. Su Dr Ranjet basu samu nitsuwa ba sai bayan isha'i, dama shi RK wannan karon ma kasa komai yayi bakamar wancan karon da akai komai da shi ba. Sai dai yana a bakin ƙofar tare da Shahidah da mijinta da shima ya iso suna zaman jiran tsammani. Fitowar su Dr Ranjet ya saka su dukansu miƙewa. RK kamar ba likita ba ya nufesa da sassarfa yana tambayarsa yaya take?. Cike da kulawa Dr Ranjet ya dafa shi yana faɗin, “Calm down doctor, everything is fine”. Kusan su ukun a tare suka sauke ajiyar zuciya mai matuƙar nauyi. Yayinda Dr Ranjet ya sake kwantar musu da hankali.....


__________★


A ruɗe Oum tacema Babban yaya yay mata kiran Uncle ɗinsu yana sashenta. Fita yay kuwa da sauri, sai dai yana fitowa motar RK na fita a gidan da gudu. Dan dai-dai ya nufo sashen AA da nufin jin damuwarsa saboda tunaninsa Oum na wajen mijinta kamar yanda tace masa zataje, sai dai yana gab da shiga sashen ne Dr Ranjet yay kiransa cewar gafa Maanal an kawo asibiti. Shine ya juya a guje ya faɗa mota ya fice. Fitar tasa dai-dai da shigowar motar Fawzan shima daga wajen aiki. Matarsa na a gefensa dan itama tana fita aikin, motarta ta samu matsala ne ta barta a office tai kiransa ya biya ya ɗakkota suka nufo gida. Ganin babban yaya ya sasu fitowa da sauri Fawzan na tambayar ko lafiya yaga Uncle Rafeeq ya fita a guje?.
“I don't know why! Na fito kiransa ne nima fa”.
“A da alama gaskiya babu lafiya, dan kamarma waya yake hankali tashe. Maybe asibitine suka kirashi kasan Uncle da patient ɗin nan nashi. Amma lafiya kuwa?”.
“Auta ne babu lafiya”.
Ai Fawzan ma bai samu damar sake cewa komai ba suka nufi sashen AA su duka ukun. Sai dai Babban Yaya na ƙoƙarin kiran layin family doctor ɗinsu a waya da shima ke aiki a KK HOSPITAL ɗin. Kafin doctor ya iso su duka sun rufu a kansa hankalinsu duk a tashe. Kallo ɗaya zakaima wannan taron kasan AA ɗin ɗan gatan dangi ne. Dan amaryar Abah ce kawai babu a wajen. Sai da matar babban yaya ta ɗaga waya tai kiranta sannan sai gata ta iso. Kusan tare suka shigo da doctor. Itama dai macece ƙyaƙyƙyawa, tana da ɗan jiki na ƙiba dan har tafi Oum ma. Sai dai Oum ta fita tsayi da haske dan ita fara ce kamar yanda Abah ke fari tas. Kai hasalima suna kama sosai da Abah ɗin tabbacin auren zuminci ne a tsakaninsu. Hakama duk yaran kama suke dasu, idan ka cire AA da yake da duhun fata sai dai kamanin fuskar Oum da Abah ɗin na tare da shi shima.
Duk fitowa sukai aka bar Oum da Doctor yana duba shi. Duk da cikin faɗa yake mitar shi abarsa kar doctor ɗin ya taɓasa. A barshi haka baya buƙatar kowane magani. Hawaye Oum take tana ƙoƙarin tausarsa da shafa lallausar sumarsa daya tara take cin kuɗaɗe. Yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin yaron nata dan gaba ɗaya yanayinsa ya nuna alamomin tashin ciwonsa. Sam bata fatan hakan, bata son abinda ya shuɗe suke murna ya dawo. Sun azabtu matuƙar azabtuwa da halin da AA ya shiga a shekarun baya. Da ƙyar da addu'oi abubuwa suka sassauta. Sai tabon dake zuciyarsa da sun san har ya koma ga ALLAH bazai warke ba kamar yanda suma nasun yake zaune daram. Sai kuma gashi ƙaddara na neman sabunta abubuwa cike da ban al'ajabi da mamaki a duka ɓangarorin biyu.........✍️












✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖4️⃣5️⃣




______________


.........Sai da Doctor yay masa allurai masu matuƙar ƙarfi a cikin drip ɗin da aka saka masa har kala uku a tare sannan barci ya ɗaukesa. Cikin kwantar ma su Oum da hankali yace musu karsu damu in sha ALLAHU komai zaiyi normal. Dan dama akwai malaria ne a jikinsa sai kuma damuwa data saka jininsa haurawa sama sosai, kuma da alama ya kwana biyu da damuwar a ransa amma ya cigaba da jigata kansa da sabgogi kuma.
Hankalinsu ya ɗan kwanta jin abun da sauƙi, sai dai a ƙasan ran kowa maganar damuwar da yake ciki ta damesu. Oum da Fawzan ne kawai da suka fahimci musabbabin damuwar zuciyarsu ke suya. Sai dai basuce komai ba akai dan ko Babban yaya daya dawo Kano basu gaya masa zuwan Maanal gidan ba. Bayan sun shiga sun gaggansa yana barci fuskar nan fayau sai dai a takure na rashin wal'wala tamkar yana ido biyu. Yayinda Oum ke zare masa takalman ƙafarsa a hankali. Amsa Babban yaya dake kusa da ita yay ya ajiye gefe, batare daya zare masa socks ɗin ba ya maida duvet ɗin ya rufe masa ƙafafun a yanda suke. Tie ɗinsa da tuni ya sassautoshi da kansa dama Oum ta ƙarasa zarewa shima. Sai ƴar rigar saman long sleeve shirt ɗinsa itama ta ɓalle botiran. Itama shirt ɗin ta rage botira uku na sama. Su dai sauran duk suna tsaye suna kallonta, musamman Abah dake mata kallo cike da so da ƙaunarta. Matarsa dabance a cikin mata, idan yace daban yana nufin daban ɗinne a cikin daban. Har yanzu bai iya samun abinda zai kwatanta Fateeman sa da shi ba. Murmushi ya saki mai sanyi sakamakon haɗa ido da sukai da babban yaya da shima ke murmushin, sai kuma duk suka janye ya ɗan kalla amaryarsa itama. Itama dai Oum ɗin take kallo fuskarta da ɗan murmushi. Jiyay itama so da ƙaunarta na sake dasuwa a ransa. Kai shi kam ya gode ALLAH da samun mata nagartattu na ƙwarai. Su ɗin aljannar duniyarsa ne.
Sallar magrib ce ta fita da su a sashen, amma Oum bata fitan ba sai ma umarni ta bama Fawzan akan ya kawo mata kayan sallarta nan. Da girmamawa ya amsa mata yana fita. Yayinda Abah dake kallonta cikin marairaice fuska ya furta, “Amma baiwar ALLAH tunda ɗan naki ya samu barci ai ƙyaji tausayina kizo ki bani abinci”.
Ɓata fuska Oum tayi tana girgiza masa kai, “Ni dai gaskiya babu inda zanje nabar yarona a wannan halin, in dai abinci ne ai na kammala Mamy ta shirya maka kuje ku ƙarata”.
Dad daya rasa ma abin cewa juyawa yay yana kallon Mamy, murmushi ta masa kawai da faɗin, “Kaima kasan ba kulamu za'ai ba ɗan gwal babu lafiya. Mu rufama kammu asiri muje muci abinci dan nikam har uku huɗu nake ganin mutane”.
Ɗan hararar wasa Oum tai musu tana murmushi. “Eh kwaji da gulmarku dai, dan kawai kanwa na kawo sai na bar yarona a halin ciwo na koma kanku”.
Dariya sosai Abah ya kwashe da shi, sai kuma ya nunama Mamy hanya yana faɗin, “Kinga Kamilah muje dan na kula itama uwar ɗan sai a hankali. Dama haka ɗan ya ɗakkomu a airport yana mana mazurai kamar sabon dan doka da mai laifi.”
“Kwaji dai da shi, ba kulaku zamuyi ba sai mun warke”. Oum ta faɗa tana murmushi. Ficewa sukai suma suna dariya. Dama tuni matan su Fawzan sun fice. Dai-dai nan Fawzan ɗin ya shigo da kayan sallar Oum. Ajiye mata yay shima ya fita dan kar ya rasa jami'a.


__________★


Alhamdullah washe gari su dukansu jikin nasu da sauƙi. Musamman ma AA da Oum ke faman riritawa kamar wani ƙwai. A yanzu haka tana zaune ne bakin gado kusa da shi tana bashi breakfast, sai faman mata shagwaɓa yake ita ko tana lallaɓashi. Su Fawzan duk sun wuce aiki bayan sun shigo sun duba shi, hakama Abah tunda ya shigo ya gansa ya fita dan yana da uziri. Mamy ma ta shigo ita da matar babban yaya. Sai dai bata wani jimaba ta tafi tabar Oum da matar babban yayan dan ita bata aiki Bussines takeyi na kawo kaya daga Chaina tana rabama ma'aikata. A yanzu haka ma da Oum ke faman lallaɓa shi tana zaune tana faman musu dariya. Shi dai ba wani kulata yake ba dan tsakaninsa da matan yayyan nashi gaisuwar girmamawace da mutuntawa. Amma ka gansa yana hira dasu ko wani wasa da dariya abune mai wahalar gaske dan duk ƙanne suke a gunsa. Kai shifa mai ganin dariyarsa yanda ya kamata daga Oum sai ƴan uwansa, musamman Fawzan ma da suke kamar wasu friends ba brothers kawai ba. Dan shi Fawzan akwai barkwanci kamar Abah, saɓanin babban yaya da kusan halinsa ɗaya da AA ɗin.
“Oum Please ki bari haka zanyi amai”. AA yay maganar a hankali yana kwantar da kansa a kafaɗar Oum ɗin cike da shagwaɓa. Murmushi itama tayi da kai hannu ta shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake luf-luf duk da yau ko gyara bai samu ba.
“To shike nan an barsa haka, ai kamayi ƙoƙari, kaida in baka da lafiya abinci ya zama maƙiyinka duk sonka da shi. Yanzu sai mi kake buƙata?”.
Cikin lumshe idanu da sake maida muryarsa can ƙasa ya ce, “Barci”.
“To Alhamdullah karɓa wannan ruwan addu'an kasha, Mamy ce tayo maka”.
Ɗan jim yay yana kallon kofin, sai kuma ya ɗauke kansa da faɗin, “Oum ga naki ma ban shanye ba. Ki bari saina gama da shi”.
“No naƙi wayon, shima kasha ai ba'asan inda za'a dace ba”.
Fuska yaso ɓatawa amma dai ya amsa yasa kofin a baki, bayan yayi bismillah ya shanye yana miƙa mata kofin. “Yauwa ko kaifa ɗan albarka. Shike nan kwanta abinka ka huta nima bara naje na idan abinda ya rage kafin ka tashi na nema maka lunch”.
Kansa kawai ya gyaɗa mata yana zamewa a gently ya kwanta. Dai-dai tana tattara kwanikan matar babban yaya mai suna Saheeba na tayata. Knocking akai tare da sallama, Oum ta amsa tana bada izinin shigowa dan su duka sun gane mai muryar. RK ne ya shigo cikin takunsa na nutsuwa, suna haɗa ido da AA ya saki murmushi cikin tsokana ya furta, “Ayya my son ashe an kusa a gangara”.
Harararsa AA ɗin yay yana ɗauke idanunsa a kansa. Yayinda Oum ke dariya Saheeba na tayata. Sai da ya kai zaune a bakin gadon ya gaida Oum, Saheeba ta gaisheshi da tambayarsa aiki ya amsa mata da kulawa da tambayarta ina yara. Amsa ta bashi da cewar suna Kano basu dawo ba sai gobe da sassafe zasu taho da mamanta. Ya jinjina mata kai kawai yana maida hankalinsa ga AA.
“Sorry my dear Son ai ban san abun haka ya kasance ba, sai ɗazun Fawzan ke sanar min ashe jiya ina ƙoƙarin fita ana kirana na dubaka. ALLAH ya ƙara sauƙi yasa ya zama kaffara”.
Batare da AA ya buɗe idanunsa ba ya jinjina masa kai kawai. Dai-dai nan Oum ke faɗin, “Ai na kira wayanka da dare ma bayan ya samu barci switch off, ALLAH yasa dai lafiya dan fitan naka a jiya duk sai da ya dame mu”.
“Wlhy tashin hankali yasa har cajin wayar ya kare ban kula ba Aunty, dama saura kaɗan sanda nazo nan jiya. Ƴarki ce babu lafiya sukai kirana gata an kawota asibiti, shine fa na tafi hankali tashe kin san ciwon nata nada haɗari”.
A rikice Oum ta ce, “Wai kana nufin Maanal?”.
Da wani irin mugun sauri AA ya buɗe idanunsa a karo na farko tun shigowar RK ɗin. Idanunsa masu kaifi da masifar haske kamar an watsa madara duk da halin ciwo da yake a ciki ya zubama bakin RK dake faɗin, “Yes ita Aunty, wai daga wajen aiki ta koma kawai ta yanke jiki ta faɗi”.
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un yaya jikin nata?”. Oum ta faɗa tana kallon AA, suna haɗa ido yay wani saurin lumshe nashi ya juya musu baya.
“Da sauƙi Alhmdllh, dan yanzu haka ma na barta tana barci. Shiyyasa nace bara nazo naga Autan ki shima”.
Addu'a sosai Oum take ma Maanal, yayinda Saheeba ke amsawa zuciyarta na kai kawo da maimaita sunan Maanal ɗin. Can dai taga zata gaza ta tattare kayan data kwashe tana faɗin, “Oum bari naje dasu a wanke, ki huta zan masa lunch ɗin kawai”.
Kai Oum ta gyaɗa mata da sanya mata albarka. Daga haka ta fice da ɗan saurin da su Oum ɗin sam basu lura ba. Kai tsaye sashen Mamy ta nufa, shima dai komai ya haɗu ga wani ƙamshi na musamman na tashi, tana a falonta na biyu zaune da waya a hannunta alamar magana ta gama yi. Shigowar surukar tasu kuma ɗiya a wajenta dan Saheeba ƴar yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya, zama a iya cewa itace ta haɗa aurenta da Fadeel ɗin. Ɗan ɗagowa tai ta dubeta sai kuma ta maida ga wayar tata tana faɗin, “Saheeba lafiya kuwa?”.
Zama Saheeban tai kusa da ita gab fuskarta na nuna matuƙar ruɗani. “Mamy inafa lafiya. Kin san ina can wajen Yaya Ajwaad kamar yanda kikace naje na zauna komai ayi a gabana, sai ga ƙaninta yazo shine naji wata magana data ban mamaki.....” tsaf ta zayyane mata duka abinda aka tattauna a sashen AA ɗin. Cikin matuƙar mamaki Mamy ta sake maimaita sunan. “Maanal kuma Saheeba?”.
“Tabbas Mamy sunan nan naji, duk da nasan akwai Maanal da yawa a duniya zuciyata ta kasa yarda ba waccan yarinyar bace da Yaya Ajwaad ke ƙula fuci. Kin dai san makirci da munafuncin matar nan, musamman idan kika duba ƙaninta ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login