Showing 72001 words to 75000 words out of 221978 words

Chapter 25 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

ma Maanal kayayyakinta. Wannan shine abu na biyu daya faru tsakanin Boss da Maanal ko yace na uku harda kaita gida da sukai jiya. Shi sai ma ya rasa kalar tunanin da zai yi akan al'amarin.
Sauran ma duk sun ma Maanal sorry, kanta kawai ta jinjina musu da ɗan yin murmushi ta wuce zuwa office ɗin Director Mustapha. Bayan tayi knocking aka bata iznin shiga. Ta gaishesa da girmamawa kamar yanda ta saba yima kowa. Shiko ya amsa fuskarsa da murmushi tare da nuna mata kujera. Kanta ta ɗan girgiza masa da ajiye document ɗin hannunta saman desk ɗinsa.
“Sir dama na kammala ne shiyyasa nace bara na kawo maka sai ka duba”.
“Yauwa sister Maanal dama kamar kin san yanzu nake shirin nemo ki, dan ban jima da baro office ɗin CEO ba akan batun. Woow ai sai naga ma kamar waɗan nan sunfi ma wancan ɗin ƙyau”.
Ita dai Maanal komai batace da shi ba kanta a ƙasa, sai da ya gama santinsa sannan ya sallameta akan ta zama cikin shiri koyaushe za'a iya nemansa a conference room. Koda ta koma saita samu har gulmar abinda ya faru tsakaninta da CEO ɗin taje can. Dan ta wuce wasune nayi batare da su sun farga da ita ba. Kowa bata kula ba har abokan zamanta da wasu ke ɗan ƙus-ƙus ta zauna ta cigaba da aikinta.


Bayan anje break daga massalaci Maanal ta dawo kan aikinta, dan tunda tazo companyn bata taɓa zuwa kitchen cin abinci ba. Kullum da abinda zata ci take zuwa daga gida, dan haka bata taɓa maida hankalinta ba. Tana cikin aikin ta samu kira daga head of design office ana nemanta a conference room. Tashi tai ɗauke da drive ɗin data haɗa abinda zata gabatar ta wuce. Batayi mamakin ganin duk manyan companyn a wajen meeting ɗin ba, dan ta fahimci project ɗin nada matuƙar muhimmanci. Sai da ta gaidasu cikin girmamawa sannan ta zauna a kujerar da aka nuna mata. Kusan zaman mintuna biyu sannan CEO ya shigo AS nashi biye da shi. Dukansu miƙewa sukai domin girmamawa, sai da ya zauna a kujerar da AS ya gyara masa sannan yay musu nunin su zauna. Duk zaman sukayi, ita dai Maanal bata yarda ko inda yake ta kalla ba. Sai da Director Steven ya mata magana sannan ta tashi. Kamar waccan ranar yau ma ta gabatar da sabbin zanenta, tare da bayanai akan yanda zai iya kasancewa. Yau ɗin ma dai kowa ya yaba mata matuƙa, dan hatta shi kansa CEO ɗin a mamakinta ya wani zuba mata ido, ita dai kame kanta ta ƙarayi. Tattaunawar ta cigaba da gudana, musamman ta ɓangaren Head of design and engineering da R&D Director da Sales and Marketing Manager sai shi CEO ɗin dake ɗan saka baki. Sun kwashi kusan awa ɗaya da rabi kafin a tashi, yau kam Maanal ita ta fara fitowa daga conference room ɗin tana sauke numfashin gajiya. Har ga ALLAH ta gaji sosai, dan surutun nan na wahalar da ita matuƙa. Kai tsaye elevator ta nufa. Koda ta fito floor ɗinsu sai ta samu anata ƙus-ƙus, bata fahimci ƙus-ƙus ɗin na minene ba sai da ta ƙarasa group ɗinsu. Sama-sama take tsintar gulmar da su Zaharadeen suke suma, wai wata ƙyaƙyƙyawar budurwa ce tazo neman CEO. Sai dai an hanata shigowa kasancewar yana meeting tana a reseption dan tace ko zai kwana a meeting ɗin zata jirasa. Abinda ya kawo gulmace-gulmacen kuwa securitys da suka hanata shigowa taima tas tare da sanar musu cewar basu san matsayinta bane shiyyasa, to itace matar da CEO ɗin zai aura. Wannan furuci nata shine dalilin ƴan ƙananun maganganun dan kowa dai yasan wanene CEO ɗin akan mata. Hatta hoton dake zagaye da duka offices ɗin companyn kowa yayi gulmarsa ya bari dan babu wanda yasan matsayin mai hoton ko sanin wacece ita. Musamman ma daya kasance bawani gane ainahin wanda ke'a hoton ake ba sam. Abinda kowa ya yarda da shi kawai koma wacece tanada muhimmanci a wajensa. Sai kuma ga ita wannan budurwa tazo da sabon zancen daya ɗauki hankalin kowa.
Shigowar wani abokin aikinsu sai dai ba'a rukuninsu yake ba ya sakasu maida hankali wajensa su duka banda Maanal da kunnenta ne kawai ke wajen. Cikin gulma yake sanar musu gafa shi can AS na CEO yazo ya shiga da budurwar nan da'alama zancen dai gaskiya ne ita ɗin matar da CEO ɗin zai aura ɗin ce. Duka sosai zuciyar Maanal take yi, sai da ta dinga ambaton sunayen ALLAH da sauri-sauri sannan ta ɗan fara jin dai-daituwa. Daga haka taji gaba ɗaya aikin da take yama fita mata a rai........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣3️⃣




.........Yau kam za'a iya cewa itace ta riga kowa fara tattara kayan tashi tun lokaci bai gama cika sosai ba. Dan zuciyarta gaba ɗaya a ƙuntace take. Ga ƙirjinta ya mata wani irin nauyi sosai. Tamkar an saita sai ga kiran RK ya shigo mata. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta ɗaga, sallamarta kawai ya amsa yace ta fito gashi a waje yana sauri ne bazai shigo ciki ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da amsa masa da gata nan. Daga haka taima sauran sallama kamar yanda ta saba ta wuce.
“Kai mutuniyarku kamar fa yanayinta ya sake canjawa tunda akace ga budurwar CEO”. Zaharadeen yay maganar yana gumtse dariya.
Caraf Yusuf yace, “ALLAH nima na lura da hakan, anya kuwa itama bata faɗa tarko ba? Kasan CEO da farin jini wajen matan kamfanin nan kamar ya musu turaren asiri”.
Dariya suka kwashe da shi, Ema dake jin hausar sama-sama dan da Hausa suke gulmar ya ce, “Baku ji labarin ɗazu ba, itama sonshi take shiyyasa take mana wulaƙanci, in dai CEO ne duk zasuyi su gama maitarsu”.
Tsaki yakub yayi tare da miƙewa yana faɗin, “ALLAH ya shirye ku, kuna maza amma gulma ta riga ta muku katutu. Haka kawai kuna ma baiwar ALLAH ƙazafin abinda baku da ilimi a kansa.”
Caaa suka yo masa da masifa suma, bai kulasu ba yay wucewarsa ya barsu....


★ ★★ ★


“Baby anya kinyi murna da dawowata kuwa?”.
RK dake kallon Maanal cikin wani yanayi ya faɗa murya a raunane. Karo na farko ta ɗan dubesa, sai kuma tai murmushi da bata cika yi ba. Shi kansa saida ya lumshe idanu saboda yanda murmushin nata ya wani ratsa masa zuciya. Idanunta ta ɗan janye daga kallonsa ganin yanda yake wani ƙanƙance nasa idanun. “Daga dawowa zaka fara rigimar taka ko”. Ta faɗa ƙasa-ƙasa batare da tunanin zai jita ba.
Amma a mamakinta sai taji ya saki ƙaramar dariya da faɗin, “Oh ashe kallon rigimamme ake min ni Rafeeq”.
Murmushi kawai ta sake yi batace komai ba. Shima sai ya tada motar suka fice a kamfanin. Sun ɗan yi nisa da tafiyar yanata mata labarin inda yaje. Ita dai bata cewa komai shi kuma bai damu ba. Sai da suna gab da shiga anguwar su Shahidah tace masa, “Yaya jikin Aunty kuwa? Kaƙi dai bani address ɗin naje na dubata”.
“Ayya! Amin afuwa gimbiya. Kin san tafiyar nan ce da babu shiri kawai ta kawo tsaikon. Amma idan babu damuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dai ki shirya nazo muje bayan sallar magrib”.
Ɗan jimm tai sai kuma ta ce, “Okay ALLAH ya kaimu, zan dai fara sanarma Didi yanda tace”.
“Ba damuwa hakan ma yayi”. Ya ƙare maganar dai-dai yana horn a ƙofar gate ɗin. Da sauri maigadi ya wangale ƙofar bayan ya leƙo yaga shine. Sun saba sosai saboda RK akwai sauƙin kai ga ƙyauta, da wannan halayen nasa yake saurin saye zuciyar mutane da yawa. Mutum ne mai sauƙin kai matuƙa, da wahala ka zauna da shi bai shiga ranka a lokaci ɗaya ba. Sai da ya gama dai-daita parking idanun Maanal suka sauka akan motar Yazeed. Motar ta zubama idanu na tsayin sakanni, sai kuma ta buɗe ta fito. Shima RK ɗin fitowar yayi hannunsa ɗauke da ledar da bata san da ita ba, sai lunch box ɗinta daya haɗa ya ɗakko. Ganin inda take kallo shima sai ya kalla wajen, a take fara'ar fuskarsa ta canja, har zai miƙa mata kayan dan baida niyyar shiga ciki amma sai ya fasa. Cike da basarwa yace mata, “Muje”.
Kallonsa tayi, sai ya ɗauke kansa. Baki ta buɗe kamar zatai magana amma sai ta fasa, dan ta tabbatar sai ya shiga ɗin tunda yaga Yazeed ɗin na ciki. Ita kam bata san yaya zatai da wannan mutanen ba ƴan rigima. A tare suka shiga falon tana gaba yana biye, Yazeed kuwa na zaune tare da su Barrah kasancewar yau babu islamiyya alhamis ce. Tunda ta shigo shima idonsa kyam a kanta, sai dai yana ganin RK ya tsuke fuska. Jitai kamar ta fasa ihu, amma ta daure dai ta ƙarasa, sannu da zuwa tai masa tare da gaishesa. Shima RK sai ya miƙa masa hannu a ɗage. Shima Yazeed ɗin a ɗagen ya bashi nashin suka gaisa sama-sama. Daga haka RK ya kai zaune yana janye ra'ayin su Haneeff. Shi kuma Yazeed sai ya maida hankali ga Maanal duk da dai yanzu babu fara'ar data shigo ta ɗan gani a fuskarsa. Dama dai can shima ɗin kamar ita ne ba gwanin fara'a bane ba.
Magana Yazeed ɗin ke mata ƙasa-ƙasa tana bashi amsa cikin yanayinta na rashin son magana. Yanda RK ya maida hankalinsa akan shirmen su Barrah sai ka ɗauka bai damu dasu ba, sai dai gaba ɗaya kunnesa da hankalinsa na akansu. A haka Shahidah tai sallama ta shigo falon. Wata irin ajiyar zuciya Maanal ta saki acan ƙasan maƙoshi, kamar an saita sai ga Huznah itama ta shigo, sai dai ita tana cin karon da Yazeed tayi wani turus na ɗan firgici, shima ɗin kallonta yake da mamaki. Cikin ɗari-ɗari ta gaida shi gefe kuma tana satar kallon RK da tunda yay mata kallo ɗaya ya ɗauke idanunsa ya maida ga Maanal. Amsa mata Yazeed ɗin yay da faɗin, “Ke daga ina haka? Yaushe kika zo Abuja?”.
Daburcewa Huznah tayi, dan duk fitsararsu suna tsoron Yazeed kasancewar baya ɗaukar raini dukansu uban kowa yake ci a gidan. Cikin ɗan sarƙewar murya ta buɗe baki zata masa bayani Shahidah ta tari numfashinta.
“Ayya yaya Yazeed zumunci tazo yi mana. Jiya ta iso zata mana hutu ne”.
Shahidahn ya kalla kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Da wannan Huznah ta samu ta gudu ɗaki cikin sassarfa. Maanal nason shigewa ta ɗan watsa ruwa babu dama, sunzo sun sakata tsakkiya. Haka dole ta haƙura har ALLAH yay balling ta akai kiran sallar magriba sannan suka miƙe dan zuwa massalaci. RK dai ya mata sallama alamar bazai dawo ba. Amma Yazeed baice komai ba, hakan ba nufin shi yana nan kenan.
Sanda ta shiga ɗaki baje-baje ta iske Huznah a gado tana waya. Sai ƙyalƙyala dariya takeyi. Komai Maanal batace da ita ba ta wuce bathroom. Daga cikine take ɗan jiyo hirar Huznah ɗin.
“Ai ki bari kawai guy ɗin nan ƙarshe ne. Ga ƙyau, ga aji, ga kuɗi ga iya wanka. Kin san ALLAH yau jinai kamar na rungumesa.”
Dariya ta ƙyalƙyale da shi alamar ana magana daga can, caraf ta cigaba da faɗin, “Ai gara kam kuyi sauri ku kaini kada naja muku abin kunya a gari, wlhy har gida yasa aka kawoni a wata azababbiyar motarsa. Wa ai gobe ma komawa zanyi dan ya tabbatar da ƙarfina na shigo”..
Kai kawai Maanal ta girgiza da taɓe baki, sai ma ta ɗauke hankalinta daga sauraren zantukan shirmen. Ita dama tasan ba banza ta kawo Huznah Abuja ba, ashe kuwa namiji ta biyo. Kai wannan abun kunya dame yay kama mtsoww!.


__________★


Washe gari sai ga Yazeed wai yazo kaita office da kansa. Rasama abin cewa Maanal tayi, tadai cigaba da cusa breakfast ɗin da Shahidah ta tsareta yi saboda shan magani. A haka yazo ya samesu. Ta gama shan maganin tana tattara kayanta sai ga maigadi yazo yana sanar mata ga RK yazo, wai ya kira wayarta switch off. Gaba ɗaya sai Maanal ma ta kasa motsi, idanunta cike da ƙwalla ta kai dubanta ga Shahidah da abin yama fara bata dariya. Dan ita kam Yazeed da RK ɗin yanzu dariya al'amarin nasu ke bata. Kowanne baya iya ɓoye kishinsa akan Maanal. Ta wani gefen kuma tausayi suke bata su duka ukun ma. Inda Yazeed yake Shahidah ta juya, sai ta samu wayam alamar ya fita.
“Tofa, shi kuma Ya Yazeed yaushe ya fita”.
Da sauri Maanal ta juya inda Yazeed ɗin yake, itama ganin wajen empty sai ta ɗan waro idanunta tare da maida kallonta ga Shahidah. “Didi ina kuma yaje?”.
“Wajen abokin takararsa mana. Ai wannan samari naki Maanal na kula kowanne da zafinsa yake. ALLAH dai yasa a rabu lafiya kawai. Kinga muje kawai ni na saukeki da kaina sai a raba rigimar. Ya kamata ma su duka ki hutar dasu zuwa kaiki da ɗakkokin nan dan na fahimci abin yana neman ɗaukar wata hanya ne a tsakaninsu”.


Koda suka fito sun samu rayukan Yazeed da RK ɗin duk a ɓace, kallo ɗaya Maanal tai musu ta wuce ga motar Shahidah tai shigewarta. Sai ita Shahidahn ce ta ƙarasa wajensu. Maanal bata san mi yayar tata ta sanar musu ba, koda ta dawo motar kuma batai mata bayani ba ta tayar suka fice.
Haka ta kasance a office babu wani walwala a tare da ita. Dan fuskarta tafi kowacce rana kasancewa a tsuke. Yau ma anyi zama tsakaninta da Marketing and sales manager, sai Head of operation da quality control manager, bayan sun gama meeting akai kiranta da mata tambayoyi akan dai wannan zane nata da company zai fitar. Yau ma da yake bata buƙatar kowa yazo ɗaukarta da wuri ta tashi. Ta fito harabar companyn hankalinta akan agogon hannunta tana kallon lokaci suka kusa cin karo da assistant ɗin CEO. Haƙuri ya shiga bata itama ta bashi. Ta raɓesa zata wuce idonta ya sauka akan AA Darma ɗin dake tsaye shi da wani dattijo suna magana. Yau dai sanye yake cikin farar shadda ƙal datai masa shegen ƙyau da sake fitowarsa a cikakken bahaushensa ɗan arewaci dan harda hula. Da sauri ta kauda kanta tare da ƙara sauri a takunta duk da hakan bai hanata kasancewa a nutsenta ba.
Sarai AA Darma ya ganta shima. Amma ya basar ya cigaba da maganarsa da Alhaji Wakili. Alhaji Wakili tamkar uba ne a wajensa, dan kuwa abokine ga mahaifinsu, sai kuma huɗɗar kasuwanci ta haɗasu, dan yanzu haka ma akan wannan project da zasuyi wanda Maanal tai zanen agogon Alhaji Wakili ɗinne ya kawo mutanen....


Dai-dai Maanal ta fito gate ɗin da nufin samun abun hawa wata taxi ke ƙoƙarin shiga cikin Companyn. Sai dai securitys sun hana mai taxi ɗin shiga, sun tabbatar masa da dole wanda ke ciki sai dai ya fito ya ƙarasa ciki da ƙafarsa. Yanda aka buɗe ƙofar motar a fusace ya ɗan ja hankalin Maanal, a mamakinta sai taga Huznah ce ke fita a motar. Jitai ma gaba ɗaya ta ƙame a wajen ganin yanda Huznah ɗin ke musu masifa da tabbatar musu akanta zasu iya rasa aikinsu. Sukuwa dai securitys ɗin sunce bafa zasu bar mai taxi ya shiga ba dan dokar companyn ce hakan. Ko ma'aikatan wajen indai motar haya suka shigo ƙa'ida anan suke sauka su ƙarasa ciki da ƙafarsu.
Ran Huznah ya kai maƙura a ɓaci, kuma dole ta haƙuran ta sallami mai taxi ɗin ta ƙarasa da ƙafar zuwa ciki. Ga ma'aikatan sun fara fitowa sai kallonta ake ana ƙus-ƙus, itako tana wani yauƙi da taku ɗai-ɗai. Maanal dai tuni ta shige taxi ɗin da Huznah ɗin ta fita. Haka ta iso gida al'amarin nata mata kaikawo. Har jitai ta ƙagara Didin ta ta shigo. Zuwa duba Auntyn RK yasata watsar da komai bayan tayi wanka ta shiga kitchen. Da taimakon Linda ta fara haɗa cake da wasu ƴan kalolin snacks da suka shirya zatayi dan dubiyar ita da Shahidah. Suna tsaka da aikin Shahidah ta shigo tare da yara data biya ta ɗakko a makaranta yau da kanta. Dama haka take musu duk juma'a sai dai idan aiki ya mata yawane tabar driver ya ɗakko su kamar yanda ya saba.
Joining ɗinsu tayi a kitchen ɗin, anan ne Maanal ke labarta mata batun Huznah. Itama mamaki sosai tayi Shahidahn, sai dai basu iya hasaso abinda ya kai Huznah Maawad company ba, har kuma suka kammala aikin bata dawo gidan ba. Dama ba kowa take sanarma zata fita ba, ko jiya Shahidah bata san da fitar tata ba hakama yau ɗin. Ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login