Showing 144001 words to 147000 words out of 221978 words

Chapter 49 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Da mamaki Shahidah ta ce, “Aban Kano wai?”.
Cike da zumuɗi Amal ta amsa mata da “Eh”.
Ba ƙaramin waro ido Shahidah tayi ba. Yayinda Ammie ta saki murmushi mai faɗi tana rufe idonta sai ga hawaye sharrr. Da sauri tasa hannu ta goge kafin yaran su gani, wata irin ƙaunar Oum na ratsa mata zuciya da ruhi. Kallon Maanal dake barci sukai, Shahidah ta ce, “Lallai yau da bidiri a gidan nan ga Bestyn Maanal a Giro”. Dariya Amal tayi tana matsawa kusa da Maanal ɗin ta shiga tadata. Da faɗa kuwa ta tashi, dan dama faɗan sukai da wata yarinya a gidan ta fasama yarinyar baki shine Ammie ta daketa tai barcin dole. Dan uwar yarinyar har sashen tazo tana faɗin bazata yarda ba sai ta daki Maanal, yarinya duk tabi ta addabar musu yara. Haƙuri Ammie taita bata amma matar nan sai da ta gama cima Ammie mutunci da gori sannan tabar sashen. Hakkanne ma ya saka Ammie kasa cin abinci dan kanta wani irin ciwo yake mata mai zafin gaske......

A cikin gidan ma tuni labari ya kai musu daga bakin yaransu. Kasancewar duk suna a ainahin babban tsakar gidan kowa na ayyukansa. Masu surfe, masu sakar mahucin kaba, bamu hira, masu sana'oinsu. Sun ɗauki ƙus-ƙus ɗin zance sai ga wani almajiri ya shigo hannunsa niƙi-niƙi da kaya wani matashin yaro biye da shi. A zahirance dai yaro ne, dan dudu bai wuce shekaru goma sha ba. Sanye yake cikin ƙananun kaya na jeans daga wandon har jacket ɗin saman duk sky blue. Sai rigar ciki data kasance red haka ma belt ɗinsa da boot ɗin takalmansa. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa sakaye da farin siririn gilashi mai shegen ƙyau da a kallo ɗaya zaka fahimci mai tsada ne duk da kuwa na ƙarin gani ne. Tafiya yake a nutse babu hayaniya balle garaje, kallo ɗaya kuma yayma tarin matan dake cike da tsakar gidan ya kauda nasa idon ganin yanda suka zuba masa idanunsu har yana jin tsigar jikinsa na tashi.
Cikin muryarsa mara ƙarfi da hayaniya ya gaishesu a jimlace batare da ya damu da sunji ko basu jin ba, shi dai yana biye da almajirin nan da kai tsaye ya nufi sashen Gwaggo. Suna gab da shiga sai ga Maanal a guje ta fito har tana ture almajirin. Kanta tsaye Ajwaad tanufa, shima da ya jiyo ihunta tuni ya tsaya cak yana kallonta. Ko damuwa da yanda jikinta yay buɗu-buɗu da ƙasar danben da sukai kafin tayi barci ma baiyi ba. Tuni ya buɗe mata hannayensa tazo ta shige jikinsa. Yako ɗagata camak sama yana juyi da ita illahirin fuskarsa na washewa da wani irin sassanyar murmushi daya bama ƴan gidan mamaki. Dan daya shigo sam babu alamar fara'a a tattare da shi. Sai da yay juyi sosai da Maanal dake ƙyalƙyala dariya kafin ya sauketa, sai kuma ta sakar masa kuka. Zuru yay yana kallonta, sai kuma ya kai duƙe a gabanta dan ya fita tsoho sosai, duk da kasancewarsa yaro shi ɗin dogo ne kamar sauran yayunsa da mahaifinsu. Tuni fuskarsa ta koma ta tsuke daga murmushin da yake, idanunsa farare tas da kamar an watsa madara sun fara canja launi.
“Is something bothering you?”. Ya tambaya kamar wani babba yana tsatstsareta da idanunsa. Ƙara ɓarkewa Maanal tayi da kukan iskanci, tare da faɗin, “Ni tare dakai zan koma. Bana son nan mugaye sunyi yawa. Kullum su Safare sai sun dakan, Ammie ma haka, su Didi ma suyita zaluntata. Wicked old woman ɗin can taita min harara da zagina tana cemin shaiɗaniya. Kowa cutata yake anan ƙauyen Baffa ne kawai ke sona da saya min kayan daɗi. Kuma dama na faɗama su Lami duk randa kazo saika rama min duk abinda suke min.”
Sosai ɓacin rai ya bayyana a fuskar Ajwaad. Har yama ji ya kasa magana. Dan shi fa idan kana son kaga ainahin fushinsa to kuwa ka taɓa Maanal. Ko Ammie da Babu dan baida yanda zayi ne kawai....
“Ajwaad!”.
Sassanyar muryar Ammie ta saka shi janye idanunsa daga kallon Maanal ya maida ga Ammien. Murmushi ta sakar masa da faɗin, “Kaga tashi kaji karka biyema wannan ibilishiyar. Kadai san halin mutuniyar taka maza taso”.
Dan Ammie ce kawai ya tashi, hannunsa riƙe dana Maanal suka shiga. Su Shahidah na masa sannu da zuwa yana faman balla musu harara. Amaal daba barin saita kwana take ba itama tai saurin faɗin oh har an kai maka munafuncinmu kenan?”.
Caraf Maanal dake naniƙe da shi ta murguɗa mata baki da faɗin, “E ɗin an faɗa, kuma duk abinda kuka min sai ya rama min har ma Ammie ko Besty?”. Tai maganar tana kallon AA. A hankali ya jinjina mata kansa, sai kuma ya ce, “Amma banda Ammie”. Fuska ta ɓata sai kuma ta sanya kuka tana turza ƙafafu. “Ni dai harda ita Besty, kullum fa sai ta dakan, yanzu ma ta daken ta sani barcin dole.....”
“An dake kin, oh ni Asiya nima ƙarar tawa kika kawo wajen Ajwaad ɗin?”. Ammie ce tai maganar tana ajiyewa Ajwaad ruwa a gabansa. Sai kuma ta zauna idonta na harar Maanal ta ce, “Karma ka bari ta ɓata maka rai kaji Ajwaad. Yarinyar nan tabi ta fitini ƴaƴan mutane a gidan nan, kullum babu ranar banza saita fasa kan wani ɗan kota jawo min magana. Fitinar Maanal ta isheni wlhy. Kuma ALLAH in baki min shiru ba zan miki duka agaban Ajwaad ɗin”.
Sarai Maanal ta san halin Ammie, tanada zafi akansu, sanyinta akan Babu ne kawai da mutanen gidan nan nasu. Muƙut ta haɗiye kukan tana mai lafewa a jikin Ajwaad. Cikin maganar nan tasa sanyi-sanyi ya ce, “Ammie kiyi hakuri, amma idan bata ramawa ai sai suyita dukanta. Yanzu ma jiba duk yanda ta rame tai baƙi”.
Baki Ammie ta saki tana kallonsa. Yayinda Shahidah da Amaal ke kwasar dariya. In dai Ajwaad ne zai yi fiye da haka akan Maanal, dan haka Ammie ta ce, “Shike nan ai dama kai ke ɗaure mata ƙugu, amma dai kubi a hankali, dan ina tsoratar muku randa hajar mai gari zata tsinke”.
Babu dai abinda Ajwaad yace, amma Maanal sai tura baki take yi. Koda aka kawo masa abinci bai iya ya nutsu yaci ba sai da ya dinga bama Maanal a baki. Itama sai ta dinga amsar spoon ɗin tana bashi. A haka Baabu da Aba suka shigo. Suma dai tsayawa sukai kawai suna kallonsu, sai kuma suka kalli juna suna murmushi. Al'amarin yaran na ƙara tasiri a zukatansu. Cike da farin ciki Maanal ta tafi ta rungume Aba. Shima ya ɗauketa yana dariya da faɗin, “Oh oh my Baby, Autar Oum kuma Bestyn Auta”.
Dariya Maanal ta sanya da jin wannan kirari na Aba, hakama Ammie da Baabu. Zama Aba yay da ita a jikinsa tana masa surutu, shiko yana biye mata dan harga ALLAH yana ƙaunar yarinyar, yanama ɗansa sha'awa da fatan wannan kusancin da shaƙuwar ya kasance musu har girma su kasance ma'aurata, duk da shi fa ko'a yanzu da su Baabu zasu amince wlhy baiƙi a ɗaurama yaran aure ba kawai. Yana dannewa ne kar ace ya cika azarɓaɓi, ba kuma asan mi gobe zata zo da shi ba.........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖6️⃣3️⃣




______________


.........Sai da Aba yasha furar da Ammie ta kawo masa sannan suka zauna tattaunawa. Gently Ajwaad ya miƙe idonsa akan Maanal dake tama Aba surutun Giro har yanzu. Nuni ya mata data tashi, ta maƙe masa kafaɗa bakinta a sama. “A'a ni ban gama ba Aba labari ba. Ka zauna na ƙarasa masa sai muje na nuna maka su Hanne dake dukana ɗaya bayan ɗaya ka musu duka har ɗakunan uwayensu”.
Harararta Ajwaad yayi, sai kuma ya sake tsuke fuska. “Idan baki taso ba ALLAH nan zan barki mu wuce ni da Aba”.
Ai baima gama rufe baki ba ta miƙe zaram, sai kuma ta kalla Aba kamar zatai kuka. “Aba ai dai dani zaku tafi ko?”.
Da ƙyar Aba ya gumtse dariyarsa da faɗin, “Sosai kuwa. Ai ƙafar bestynki ƙafarki har Kano. Oum ɗinku ma tace karna sake na baroki”. Sosai ta shiga dirga tsallen farin ciki, sai kuma ta nufi Ajwaad ta kama hannunsa. “Besty muje kafin Aba ya gama kama yaran can su Hanne jina-jina. Dan bazan tafi ban bar fuskokinsu da tabon da zasu dinga tunawa da ni ba, dole kuma asan Bestyna mai ƙarfin ILIYA ƊAN MAI ƘARFI YAZO”.
Komai bai ce ba ya riƙe hannun nata shima suka fice. Kai kawai Baabu ya girgiza, yayinda Abah ya fashe da dariya. Ammie ma murmusawa kawai tai da jerama Maanal ɗin addu'ar shiriya a zuciyarta. Bayan sun tsagaita da zancen su Maanal Aba ya gyara zama yana fuskantar Ammie.
“Ammien Amal ki kwantar da hankalinki, dan mun tattauna da su kuma ga shi Habib ya fahimta. Duk da dai an kai ruwa rana akan batun su Shahidahn gaskiya. Dan sai da nai katoɓarar nuna musu ai su Shahidahn nada mazaje a hannu, ba kuma su kowa bane sai yarana Fadeel da Fawzan sannan suka amince, amma da sharaɗin nan da wata shekarar za'ayi biki”.
Cikin matuƙar mamaki da ruɗani Ammie ke kallon Aba da Baabu. Muryarta har harɗewa take wajen faɗin, “Amma Yaya sufa su Fadeel ba'asan ra'ayinsu ba”.
“Ai basu ya dace asan ra'ayinsu ba Ammien Amaal. Su su Shahidah sune ya dace asan nasu ra'ayin saboda sune mata sune zasu zauna da su. Suko maza ne ai, sannan ni nasan daga Fadeel har Fawzan basu da bakin ƙin yarana zuƙa-zuƙa masha ALLAH, sai ma godiya ya kamata suma ALLAH da samun su a cikin sauƙi dan Shahidah da Amaal duk matan manya ne”. Ya ƙare maganar cike da barkwanci. Ammie zata sake magana Aba ya katseta. “Aifa magana ta ƙare Ammien Amaal, fatanmu ki saka albarka kawai dan ALLAH. Sai kuma batun shi Habib, ina son ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri kiyi koyi da ƴar uwarki Fateema, zai ƙara aure bawai yana nufin ya bar sonki bane ba. Mu maza ALLAH ya saka mana son ku ku mata kuma fiye da ɗaya a zukatanmu. Wani lokacin ba gazawarku bace ba, daɗin zama da kune ke kawo hakan. Kiyi haƙuri kinji, in sha ALLAHU sai kinci ribar haƙurinki kuma na tabbatar miki bazan taɓa bari Habib ya wulaƙantaki ba. Shima kuma nasan bazai ko kwatanta hakan ba koda da wasa ma.”
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke a hankali, dan ta fahimci dai shi nashi auren na nan daram. Fuskarta da murmushi ta ce, “Wlhy babu komai yaya. Ni dama ba nashi bane damuwata. Karatun yaran nan ne da kuma banbanci wannan rayuwar da basu tashi a ciki ba. ALLAH ya sanya albarka ya bamu zaman lafiya baki ɗaya. Baga Aunty ba ita da Mamy ai kosu ababen koyine a gareni idan ma ban tashi naga mhaifiyata da abokiyar zama ba. Dan haka ku daina tausata ma dan bashine dalilin son kuzo ɗin ba”.
“Na sani Asiya, ko shi Habib ya yabi ƙyawawan halayenki yanzu a gaban iyayenku, in sha ALLAHU kuma zakiyi nasara a rayuwarki”.
Murmushi Ammie tayi, hakama Baabu. Sai kuma Aba ya haɗasu ya cigaba da musu nasiha su duka biyun. Daga ƙarshe yace shi zai wuce dan zasu kwana a Sokoto da safe su kama hanyar Kano in sha ALLAHU. Idan kuma sun sami jirgi a daren nan ma zasu wuce. Sai dai kuma da Maanal fa zasu koma bazai bar Auta a cigaba da dukar musu ita ba.
Dariya sosai Ammie da Baabu suka sanya. Baabu ya ce, “Humm kaima kasan rigimar ƴar taka ai, ALLAH ta addabi kowa a gidan nan. Hatta da Gwaggo bata bari ba. Dan bata tsoron kurarin Gwaggo sam, shiyyasa kullum sai sunyi faɗa.”
Sosai Abba ke dariya. Yana mai sake jinjina rashin jin Maanal. Dan shi dai a ƴar fahimtar da yayma Gwaggon a iya yau kawai yaga kamar tana da zafi sosai. Sannan rashin ƙaunar da takema Ammie da yaran nasu a bayyane suke. Dan da ƙyar fa aka tankwarata akan batun su Shahidah ɗin nan. Shiko batun auren Baabu cewa tai idan yace zai bijire sai ta tsine masa wlhy. Dan haka da sauri Abban yace ai bama za'ayi hakan ba wannan kam sun karɓa. Shi yana ɗauki alƙawarin yin komai. Shine fa aka rabu lafiya, koda yake ko yanzu da suka shigo sashen nan yana kallonta tana harararsa, dan suna yin sallama ta shige ɗaki abinta kamar bata gansu ba. Amma a hakan Aban yace zai shiga ya sake gaisheta. Badan Baabu yaso ba ya masa rakkiya har cikin ɗakin, anan ɗin ma sama-sama ta amsa musu duk da kuwa Aban na janta da hira tana basar da shi.....


★★


Maanal da Ajwaad kam koda suka fito haka ta dinga nuna masa yara abokan faɗanta, har cikin ransa yaso rama matan amma baba Haruna da ALLAH yakai idonsa ya janyesu su duka biyun zuwa ɗakinsa. Shi yayta jansu da labari bayan ya basu zuma da magani a cikin a wani ɗan ƙoƙo yace su sha duk da su basu fahimta ba sun ɗauka zumarce kawai. Daga Maanal har Ajwaad na matuƙar son zuma, dan wajen shi ma za'ace Maanal ta koya. Aiko hankali kwance suka hau sha, ko nace Ajwaad na sha yana bama Maanal Baba Haruna na musu labari. A haka Aba da Babu suka fito suka samesu. Maanal na jin zasu tafi ta fara kuka itafa sai tabi Besty. Babu kalar lallashin da Baba Haruna bai mata ba tace ina itafa sai Kano. Haka dole suka sake komawa cikin gidan aka shiryata tai sallama da mutanen gidan hannunta maƙale a cikin na Ajwaad. Dan ko shirin ma shine yay mata da kansa, su Amal ma dai da basu san yanda aka canja komai ba yanzu idanunsu duk sunyi ƙwal-ƙwal, ji suke kamar suyi ta Maanal ɗin amma babu dama. Zuma da dabino da mazarkwaila mai yawa Baba Haruna ya haɗama Ajwaad da Maanal na tsaraba. Haka aka musu rakkiya har cikin mota. Ko'a kwalar rigar Maanal bata damu da barin su Ammie da Babu da sauran ƴan uwanta ba, tana baya a tsakkiyar Aba da Ajwaad suka wuce tanata ɗagama ƙawayen faɗanta hannu dan tace sun shirya ta yafe musu😆..


__________★


Bayan wucewar su Maanal sabuwar tujara Gwaggo ta kafa a gidan, dan sai da taima Ammie zagin ƙare dangi na fitar hankali. Daga ƙarshe tace an sake matso da bikin Baabu nan da kwana huɗu juma'a kenan. Duk da abin na dukan Ammie haka ta dinga dannewa. Sai ta shiga ɗaki tai kuka. Dan ma yaranta na tausarta da lallashi dan Baabu kam ma dai takan yini bata sakashi a ido ba. Ba'a nan yake kwana ba. Tunda sukazo Giro bai kwana tare da ita ba. Ita da yaranta suke kwana, sai dai ya ɗan shigo musu a tsaitsaye saboda tsoron Gwaggo ma baya jimawa yake ficewa. Sai dai in suna buƙatar abu tai kiransa a waya. Idan kuma ya sayo sai dai a shigo da shi a ɓoye kosu Shahidah suje su amso su ɓoyo a hijjab. Maanal ce kawai ba'a ƴar haka da ita. Dan itafa bata tsoron Gwaggo. Idan tai mata tsawa ta murguɗa baki da ƙugu tai gaba abinta, haka Gwaggo zataita rantsuwar sai ta dake ta, sai ta sumar da ita. Duk kuma yanda zatai lambon kamata bata yarda, dan tsaf take cajama Gwaggo kai. Duk da taji haushin tafiya da akai da ita taji daɗi ta wani fannin, dan ta hutama da fitsararta...


Yau ɗin ma dai kuka sosai Ammie taci kafin ta dake zuciyarta, dan Babu tun daga rakkiyar su Aba har yau bai dawo gidan ba. Da alama ma Sokoto ɗin zai kwana....


_________★


Alhamdullah su Aba sun iso Kano lafiya. Duk da a lokacin anata shirin shiga sallar isha'i ne. Dan basu baro Sokoto ba sai da akai magrib. ALLAH ne ya taimake su suka samu jirgi mai zuwa Kano a daidai lokacin. Tuni Maanal tayi barci a jirgi, dole Ajwaad ya goyota suka fito tana a bayansa, sai Aba riƙe da ledar tsarabarsu dan ma sunƙi ɗakko kayan da yawa. Dan dama jirgi suka bi da zasu je. A sokoton ne abokinsa kuma ɗan uwansa ƙanin Oum amma cousin da suka fara sauka a gidansa ya bada mota driver ya kaisu Giro dan shi anan Sokoto yake zaune da iyalinsa. Aiki ne ya cillarosa nan kuma.
Alhamdullah nan ma sun samu babban yaya (Fadeel) da drivern dake kaisu school na jiransu a airport ɗin. Yana hangosu yay saurin nufosu, shima baida yawan fara'a, dan halinsu kusan ɗaya da Ajwaad. A fuska ma sunfi kamanni, duk da dai su duka ukun suna tsananin kamanni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login