Showing 150001 words to 153000 words out of 221978 words

Chapter 51 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Daga ƙarshe ma miƙewa tai tana faɗin, “Wannan maganarku ce Oum, mu ƴan ALLAH ya sanya alkairi ne”. Daga haka ta fice tabar falon.
Da kallo duk suka bita. Kowanne na sake jin ƙaunarta a cikin ransa daga Oum ɗin har Abah. Mamy abar alfahari ce a garesu, dan suna matuƙar alfaharin shigo da ita cikinsu. Tana da wasu irin nagartattun halaye masu matuƙar ƙayatarwa a zahiri. Oum da Abah sun cigaba da tattaunawa, kafin suma su miƙe bayan sun gama yanke yanda zasu fahimtar da yaran nasu batare da sunga an ƙasƙantar da su Shahidah a idanunsu ba.



A ɓagaren Mamy kuwa koda ta shiga ɗakinta kasa tsaye da zaune tayi. Ta jima a haka kafin ta ɗauka waya tayi kira. Ba'a wani jimaba kuwa aka ɗaga. Sallama tayi tana kaiwa zaune. Sai kuma ta ɗora da gaisuwa.
“Yaya mutanen nan ban san mi suke so dani ba. Shike nan ni bani da wani ƙarfin iko akan ƴaƴana ma. Daga mijin har matar kamar tare suka auro ni? Nifa na fara kaiwa gaɓar da zan nuna ma matar nan ina buƙatar ƴaƴana nima. Sai dai ya sakan ko itama tayi zuciya ta haifi nata.......” kuka ya sarƙeta.
Numfashi aka sauke mai nauyi daga can, kafin cikin isa a furta, “Kamila! Dama wannan shine abinda aka dinga guje miki tun farko. Amma kika kasa fahimta soyayyar mutumin nan ta rufe miki idanu. Daga baya aka sake nusar dake illar sakar mata yaran nan tun suna zanin goyo nan ma kika kasa fahimta ke wai neman soyayyar miji. Ai gashi nan, ƴaƴan da mijin duk suna a hannunta ke baki amfanu da komai ba sai baƙin ciki da damuwa. Kin san wacece Hajiya Fateema kuwa akan mijin nan nata? Dukkan fa bincike sai da nayi a kansu. Akwai matsananciyar soyayya da shaƙuwa a tsakaninsu tun ta ƙuruciya. Tun fa tana ƴar shekara goma sha a duniya aka aura masa ita. Shi ya raineta, gida ɗaya suka tashi, shi ya koya mata komai taya dama kike tunanin zaki shiga wannan gidan ki samu farin ciki? Haihuwa da kike ganin bazatayi ba? Humm irin su Alhaji Aliyu Darma da kike gani ba wannan bane a gabansu....”
“Yaya ni dai naji. Koma minene dai ya riga ya faru ai. Kawai yanzu ina buƙatar dawo da yarana hannuna kota ƙarfin tsiya. Musamman Ajwaad. Wlhy yaron nan yi yake tamkar ma bai san muna da alaƙa ba. Har tayata kishi yake fa. Dan ALLAH ki taimkeni”.
“Hummm ai wannan yaron taƙadari ne daga gani. Kuma ba kowa ya busar masa da zuciya ba sai ita. Ga shegiyar yarinyar nan da suke ƙalatar juna ƴar maƙwaftanku, kai na tsani yarinyar nan da uwarta wlhy saboda aminiyar Fateema ce”.
“Wlhy Yaya na fiki tsanar Asiya. Dan haka koma mi za'ayi sai dai ayin wannan haɗin auren bazai yiyu ba. Sai kace ma ita na haifamin ƴaƴan kenan”.
“A da'alama kam ita ɗin kika haifamawa. Ba kuma makircin kowa bane sai na Hajiya Fateeman. Kinga idan yaran sun auri ƴaƴan Asiyar ai itace zata cigaba da juyasu ko. Ke wannan fa ƙulline babba wlhy. Amma karki damu zamuyi maganinsu. Kizo ki sameni gobe”.
“Aunty sai dai weekend. Dan yanzu ina cemasa zan fita zai iya zargin wani abu kin dai sanshi da kaifin tunani. Amma weekend zan tambayesa zuwa kitso sai na zo”.
“To hakan ma yayi ALLAH ya kaimu. Kidai kwantar da hankalinki”.
“Humm Yaya kenan, amma in sha ALLAHU zan yi ƙoƙari sai anjima”....


___________★


SU WAYE SU OUM?.


Abah da Oum jini ɗaya ne. Makusanta sosai dan kuwa da mahaifiyarta da mahaifinsa uwa ɗaya uba ɗaya suke. Kunga kenan su cousins ne. Asalinsu ƴan jihar Adamawa ne, a wata ruga da ake kira RIGAR DARMA. Baffa Ishaq Darma da Gwaggo Halima sune tushen zuri'ar. ALLAH yayma Baffah Ishaq Darma arziƙin kiwo da noma matuƙa gaya. Dan yana da shanaye, tumaki, awaki, raƙuma, harma da dokuna da shi kansa bai san adadinsu ba. Sannan yana noma da ake kira noma ba wasan yara ba tun duniya na kwance. Yaransu huɗu. Mata biyu maza biyu. Abubakar shine babba, suna kiransa da suna Sardauna. Sai Umar, sai Maryam, sai auta Khadijah. Baffah Ishaq baiyi karatun boko ba daga shi har matarsa. Amma hakan bai saka ya tauye yaransa ba daga yi. Su duka sunyi karatun boko mai zurfi har matan. Kafin Sardauna ya fara aure bayan kammala degree ɗinsa na farko. Ya auri ƴar aminin Baffa Ishaq da yakema kallon tamkar ɗan uwa. Ansha shagali matuƙa irin na nunama tsara a wancan lokacin, amarya da ango suka tare acan cikin garin Adamawa. Bayan auren Sardauna da kusan shekara huɗu sannan Umar shima yayi tare da Maryam a rana ɗaya. Shima Umar ya auro ne daga ɗiyar dangi anan cikin Rigar Darma, ita kuma Maryam aka aura mata wani ɗan Alhaji da suke huɗɗa da baffah tsahon shekaru. Yana zuwa ya sayi dabbobi masu yawan gaske a duk ƙarshen shekara, a hankali zuminci ya ƙulle tsakaninsa da Baffan har suna kallon kansu tamkar ƴan uwa (mutanen da kenan masu girmama alkairi). Shi wannan Alhaji dai yana zuwa daga jihar Kano ne, asalinsa kuma ɗan garin Kura ne. Ɗansa ɗaya tal a duniya mai suna Kasheem. Yana karatu a turai. Yazo wani hutu gida Nigeria ya biyo babansa nan Adamawa shine ya ga Maryam itama a lokacin tazo hutun makaranta daga Yola. Aifa yace yaga mata, Baffa kuma yace ya bashi halak malak. Ansha biki nan ma na nunama tsara, Umar ya tare da matarsa anan Rigar Darma, ita kuma Maryam aka wuto da ita Kano. UBANGIJI mai hikima shakara ɗaya tak ALLAH ya sauki matar Umar lafiya, har kuma lokacin yayan su Sardauna ALLAH bai bashi haihuwa ba shi. Dan matarsa ko ɓatan wata ma bata taɓa yi ba. Kaf family sunyi murna, sun kumayi farin ciki, an sha shagalin suna shanaye sun sha wuƙa da ƙananun dabbobi yaro yaci suna Aliyu (Abah kenan😂👍).
UBANGIJI mai rahama matar Abubakar bata yaye Aliyu ba sai ga wani cikin. Dole aka cire Aliyu daga nn, sai kawai matar Sardauna ta amshesa ta yaye. Daga wannan yaye ne kuma bai sake dawowa wajen iyayensa ba su Baba Sardauna suka cigaba da riƙo tunda su har lokacin ALLAH bai kawo iyaka ba. Matar Umar ta sake haihuwar namiji yaci sunan Hamza, shima bata yaye ba ta kuma samun wani cikin. A taƙaice dai sai da ta jera yara huɗu duk maza sannan itama Maryam ALLAH ya kawo ciki. A kusan tare kuma suka sake haihuwa da matar Umar da tai mace a wannan karon. Itama dai Maryam ɗiya mace ta haifa da taci suna Fateema (Oum kenan😂👍).
Itama Maryam matar Babban Yaya wato Sardauna suka kawoma yayen Fateema. Bakuma su sake waigawa ba dan a lokacin ne ma suka bar ƙasar. Hakan da sukai na nufin suma sun barma Sardauna Fateema har abadan. Wannan abu ya saka Sardauna da matarsa kukan farin ciki da sake jin ƙauna da soyayyar ƴan uwansu. Basu haihu ba amma gashi suma sun mallaki ƴaƴa. Bayan nan itama Auta Khadijah tayi aure anan cikin garin Adamawa. Itama kuma babu jimawa ta fara haihuwar. Itama kuma ɗanta na fari haka ta mallakama Sardauna shi kamar yanda sauran ƴan uwanta biyu sukayi. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH fin shekara goma sha sai ga matar Sardauna da ciki. Zamu iya cewa wannan zuri'a basu taɓa tsintar kansu a irin farin cikin da suka samu kansu ba na wannan tsakanin. Dan tuni Maryam ta baro ƙasar waje tazo gida Nigeria. A lokacin yaranta biyu da Kasheem Kura bayan Fateema da sukai ƙyauta. Majdiya, Sulaiman. Itama Khadijah nada biyu bayan Sa'eed da sukai ƙauta ma Sardauna. Sai matar Umar nada biyar bayan Aliyu da sukaima Sardauna ƙyauta suma. Ansha matuƙar shagali da bidiri na wannan ciki har ALLAH ya kaishi haihuwa aka haifo ƴan biyu duk maza. Kwantata muku irin shagalin da akai ai bashi misaltawa. Musamman Aliyu da Fateema da Sa'eed da akai ƙanne.
Zuwa yanzu Aliyu ya fara zama saurayi, dan yana da shekara kusan goma sha bakwai a duniya. Yayinda Fateema keda goma sha ɗaya cif. Akwai wata irin shaƙuwa da ƙaunar juna a tsakanin Fateema da Aliyu mai ban mamaki. Sun tashi tamkar wasu tagwaye duk da Aliyu ya bata shekaru sosai. Soyayyar ce mai ƙarfi irin wadda zaman rubutata ma jan lokaci ne. Gashi suna matsanancin kamanni dan ita Fateema ta ɗebo dangin mahaifiyarta ne gaba ɗaya. Sauran yaran Maryam kuwa sun biyo mahaifinsu Kasheem Kura sosai. Hakama yaran Umar ƙannen Aliyu kaf ɗinsu sun ɗebo gida ne, babu wanda ya biyo mahaifiyarsu, suma yaran Khadijah duk suna kamanni da danginta. Sai su ƴan biyu. Wannan yasa suke jin alfahari akan su jininsu nada ƙarfin da suke ɗebo kamannin gida ne. Yanda su iyaye ke kamanni da juna haka suma ƴaƴan duk suka ɗebo. Hatta da yaran Maryam dake kamanni da mahaifinsu sun ɗebo wasu abubuwan nasu, ita dama Fateema gaba ɗayanta sune.
Soyayya da shaƙuwar Aliyu da Fateema yasa Baffah Ishaq bama ƴaƴansa shawarar haɗe yaran aure saboda gudun shaiɗan a tsakaninsu, dan shaƙuwar tayi yawa matuƙa komai zai iya faruwa. Babu kuwa wanda yayi musu akayi hakan. Fateema nada shekara goma sha biyu da wasu watanni, Aliyu nada goma sha tara da wasu watanni aka ɗaura musu aure. Akai kuma shagalin biki irin na gata sai dai sun tare anan gidan Baba Sardauna ɗin dan yace yaransa bazasuyi nesa da shi ba. Balle kuma gasu yara ƙanana basu kai ƙwarin da za'a barsu su kaɗai ba tukkuna. Soyayya ta ƙara ƙarfi a tsakanin Fateema da Aliyu, yayinda a gefe suke ta karatunsu ga kuma kulawar iyaye. Aurensu nada shekara uku ALLAH yayma gwaggo Halima rasuwa. Kaf wannan zuri'a ta Darma sunji wannan mutuwa matuƙa, sunyi kuka har sun rasa hawaye musamman ma Baffa Ishaq Darma daya rasa mata ƴar uwa uwar ƴaƴansa. Bayan rasuwar tata kuma shima duk sai lafiya tai masa ƙaranci. Shekara biyu tsakaninsu shima yace ga garinku nan. Matuƙar ruɗani wannan family sun sake shiga, har takai Baba Sardauna da Baba Umar sun kasa jin daɗin zaman garin Adamawa sukayo hijira zuwa Kano. A lokacin shekarun auren su Aliyu biyar cif a duniya. Fateema nada sha shida, Aliyu nada ashirin da uku. Ya kammala karatunsa na jami'a, ita kuma zata shiga ss a sakandire.
Shekarar da Fateema ta kammala sakandare a shekarar ALLAH ya bata ciki. Murna da farin ciki ba'a magana. Dan wannan zuri'a na matuƙar son haihuwa. Sosai cikin ke bata wahala, kullum tana nane da Ummanta. (Matar Sardauna) Dan soyayya take musu ta haƙiƙa da sam bama su san ainahin ba itace mahaifiyarsu ba sai lokacin da akai musu aure. Hakan kuma bai sa sun canja daga soyayya da ƙaunar da suke mata ba. Itama kuma haihuwar da tai baisa ta sassauta soyayyar da take musu ba a matsayin ƴaƴa har gobe. Haka dai akai wannan rainon ciki Fateema kullum na sashen iyayensu. Har abun na damun Aliyu dan idan yana son ya kasance da ita sai yayi mata wayo da ƙyar tazo nasu sashen da aka ware musu a gidan. A haka ALLAH ya kai wannan ciki lokacin haihuwa. Sai dai yazo da doguwar naƙuda. Tun ana hasashen haihuwa a kusa har al'amarin ya fara bama kowa tsoro aka yanke shawarar yimata theater. A wancan lokacin matuƙar tsoron theater akeyi dan kodai a rasa ɗa ko a rasa uwa. Dole da wahala cikin biyun nan ɗaya bai kasance ba sai idan duk suna da tsohon kwanan ne uwar da ɗan. Aliyu kuka ya sanya akan bai amince ba, sai da likita yayta lallashinsa da su Baba Sardauna sannan da ƙyar ya amince aka shiga theater da Fateema.......✍️


_(Ina fatan dai kuna gane kan labarin😆. Fateema itace OUM a yanzu, Aliyu ne ABAH a yanzu😂👍)._






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖6️⃣6️⃣




______________


.........Alhamdullah bayan dogon zaman jira da fargaba da kasancewa a tashin hankali an samu nasarar ciro yara ƴan biyu a jikin Fateema duk maza. Sai dai ɗaya bashi da rai, rabin jikinsa ma har ya ɗan fara ruɓewa. Wannan yanayi ya saka farin ciki da alhini a wannan zuri'a duk a lokaci guda. Sai babbar damuwarsu sanin halin da Fateema ke a ciki kuma. Dan Doctors ɗin dai since su basu lokaci. Haka suka sake koma a yanayin damuwa da taraddadi musamman ga Aliyu har zuwa washe garin safiyar ranar. Dan wajen ƙarshe sha biyu aka samu nasarar farfaɗowar Fateema. Dama wannan shine tsaikon da likitocin suka samu na zahiri. Zuwa yanzu kam kowa ya warware, farin cikin kowa ya fito a bayyane, anatama juna barga da addu'a ga jaririn da ya rage, wanda ma bai zo da ran ba ana masa addu'a.....


Watan Fateema ɗaya cif a asibiti aka sallesu, jikinta da sauƙi sosai, sai dai yanayin cs na wancan lokacin ba dai-dai yake dana yanzu na zamani ba. Sai ya kasance wasu tsarabe-tsarabe kan biyo baya da har mutum kan iya ɗaukar dogon lokaci yana mafa da jiyya sama-sama har komai ya zama normal. Zuwa lokacin tuni an raɗa sunan jariri da aka barsa da sunansa wato Hussain. Dan Hassan ɗinne baizo da rai ba kasancewar shi aka fara cirowa. Raɗin suna kawai akai, sai bayan sallama aka shirya taron suna. Ansha shagalin kam mai birgewa da nunama tsara, sai dai maijego na dauriyane kawai dan sam bata jinta cikin isashiyar lafiya har lokacin. Sai dai bata son ɗagama mijinta da ƴan uwanta da iyayenta hankali, shiyyasa ta cigaba da daurewa har taro ya tashi lafiya ta cigaba da wankan jegon da Umma ke mata da kanta. Wato matar baba Sardauna. Sun gama wankan jego lafiya, dan kusan ma arba'in biyu sukayi, ta ɗan zaga dangi harda Saudiya ita da Aliyu sukayo sati uku sannan suka dawo. Abin ƙaddara satinsu biyu da dawowa Hussain ya fara wata mura mai ban tausayi, murar fa ko numfashinsa da ƙyar yake fisga. Hankali tashe suka wuce asibiti da yaron, sai dai UBANGIJI shi mai hikima ne, a daren shima yabi ɗan uwansa. Kuka rurus Aliyu ya dinga yi, amma a mamakin kowa Fateema ko ɗigon hawaye, sai ma ta koma itace ke lallashin mijin nata kuma ɗan uwanta. Bayan rasuwar Hussain da kusan wata biyar sai ga Fateema ta fara laulayin sabon ciki. Murna a wajen Aliyu ba'a magana ko kwatantawa. Hakama sauran ahalinsu kowa na fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya inganta. Sosai wannan ciki yazo ma Fateema da tsanani fiye dana ƴan biyu, dan bata sati guda a gida sai a asibiti, ƙarshe dai suka riƙeta a asibitin domin samun bedrest. Dan haka kawai saita dinga bleeding, doctors sunyi iya ƙoƙarin ganin sun shawo kan matsalar amma al'amarin ya gagara, har takai mahaifin ta dake matsayin babban likita a saudia wato Kasheem Kura ya nufo Nigeria da kansa. Shine ya tsaya akan matsalar, inda ya fahimci ƴar tasa tana fuskantar babbar ƙaddarane mai girma. Ya shiga tashin hankali amma haka ya daure ya jure ya fito fili yama uban riƙonta da uwar riƙon ta da mijinta bayani akan dole ne fa a raba Fateema da wannan ciki, dan sam mahaifarta bazata iya riƙeshi ba. Hasalima sai an rabata da mahaifar kanta sakamakon ciwo mai haɗari data kamu dashi, in ba hakaba kuma ciwon zai fara girma wataran a wayi gari ya harbi dukkan illahirin jikinta. Amma idan sunyi ƙoƙarin cirewa yanzu in sha ALLAHU an rabu kenan.
Wannan al'amari ya matuƙar ɗagama kowa hankali, musamman ma Aliyu. Amma lafiyar matarsa tafi masa duniya da abinda ke cikinta. Dan haka babu wani ja'inja ya amsama Abbu cewar kawai a cire ɗin. Haka kuwa akayi, aka cirema Fateema cikin da dama bai wani zauna da ƙyau ba, aka kuma cire mata mahaifa. Wannan shine ya kawo mata sanadin yin doguwar jinya ta kusan watanni takwas, kafin ALLAH ya bata lafiya komai ya daidaita tamkar ma ba'a taɓa yi ba. Har kuma lokacin bata taɓa sanin an cire mata mahaifa ba. Bayan samun lafiyarta abu na farko shine nema mata gurbin shiga jami'a da Baba Sardauna yayi ana BUK. Dan danan kuwa ta fara karatunta. Dan Fateema yarinya ce mai hazaƙa matuƙa da son karatu.
A randa ta fara shiga makarantar ɗaukar darasi a ranar suka fara haɗuwa da matashiyar budurwa da bazata wuce sa'arta ba, in ma ta girmeta baifi da shekaru uku zuwa huɗu ba. Kamila Shu'aibu ƙyaƙyƙyawar yarinya, baƙace amma baƙinta mai ƙyau ne. Tana da matuƙar sanyin hali da rashin son yawan magana. Wajen zama ya fara haɗa su da Fateema a ranar farko, Fateeman ce kuma ta samu Kalima. Bayan ta mata sallama fuskarta da murmushi tai nuni da kusa da ita tana faɗin, “Sis... Kozan iya zama?”.
Murmushi mai sanyi Kamila tai mata itama, tare da nuna mata wajen ta ce, “Bismillah mana ki zauna”.
Murmushi Fateeman ta sake mata sannan takai zaune da faɗin, “Thanks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login