Showing 147001 words to 150000 words out of 221978 words
Chapter 50 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
da Abba da Oum, kasancewar su ɗin iyayen nasu aurene na zuminci, zumuncin ma na kusa kusa sosai, shiyyasa suke kamanni ɗaya, dan duk family ɗinsu haka suke da wannan kamannin. Su har alfahari suke indai ɗa na tsatsonsu ne koda an auro uwarsa bare baya ɗakko kamanninta sai nasu saboda ƙarfin jininsu. Koda Babban yaya ya gaishe da Aba ya maida hankalinsa akan Ajwaad da son taimaka masa ya amshi Maanal ɗin dake bayansa kansa ya girgiza alamar ya barta.
Hakan ya saka Babban yaya da Aban yin murmushi kawai. A haka suka ɗinguma zuwa ga mota. Driver ya gaida Abba cike da girmamawa sannan suka shiga, Abba da Ajwaad da Maanal dake barci a kusan jikinsu su biyun na baya. Shi kuma babban Yaya ya shiga gaba kusa da driver. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gida, inda suka samu tarba daga Oum da Mamy da Fawzan. Sai dai Oum tayi mamakin ganin harda Maanal, dan batai tunanin zasu bari a taho da itan ba kamar yanda Ajwaad ke faɗin da ita zai dawo gida. Mamy dai bata tanka ba, dama kuma babu wanda yay tunanin tankawar tata dan dama haka take ita shiru-shiru. Ba komai ne zakaji bakinta a gidan ba. Garama idan suna hira da Oum ko Aba zaka jita cike da nishaɗi kamar ba ita ba. Amma akan yaran babu ruwanta da sabgarsu. Sosai take nuna kawaici da kara bama zaka taɓa tunanin tana da wata alaƙa da su ba...
Ɗakin Oum Ajwaad ya kai Maanal, Oum ta taimaka masa ya kwantar da ita bisa gado. Kwanciya ta gyara mata da rufa mata duvet dan ɗakin akwai ac. Batare daya zauna ba ya ce, “Oum naje wanka, jikina duk babu daɗi”.
Murmushi Oum ta masa, dan kowa yasan Ajwaad da tsaftar tsiya dama a gidan. Idan yana wani ƙalƙalin saika rantse ba yaro bane ƙarami ɗan shekara sha... Komai nashi zaka samesa kwaf-kwaf da kulawa kamar wani babban saurayi maji ƙarfi. Idan Ajwaad yay ado dole ka tsaya kallonsa. Sam bai damu da manyan kaya irin namu na malam bahaushe ba. Dan duk juma'a ma sai ankai ruwa rana da shi yake yarda ya saka. Garama idan Maanal ta saka masa rigima ta ɗakko da kanta tace ya saka sai ya saka. Dan duk da baya so Aba bai taɓa tsamesa a ɗinkin manyan kaya ba. Yanda akema su Fawzan da Babban yaya haka shima ake masa su, shiyyasa ya tarasu tab wadrobe yana ado dasu.
Yana shiga ɗakin nasu Fawzan Sarkin tsokala ya fara tsokanarsa da dariya. “Ah-ah kaga baban soyayya, kaga Auta na Auta, Besty kuma na Besty. Wai yanzu nan dan ALLAH ko kunya baka ji ba Auta kaje gidan surukai ka ɗakko Lilly? Oh kai wannan wane kalar abin kunya ne haka?”.
Harara ya ballama Fawzan ɗin yana wucewarsa bayi batare da ya tanka masa ba. Aiko Fawzan ya shiga kwasar dariya har sai da Babban yaya ya shigo ya tsagaita. Koda ya maimaita na Babban yaya dalilin dariyar daya tambaya murmushi kawai yayi shima, dan shi kansa soyayyar autan nasu da Bestynsa na ƙayatar da shi, da. Haka yana musu fata da addu'ar ɗorewa a haka har girma su kuma kasance ma'aurata kamar yanda kowa ke tofa albarkacin bakinsa akan dangantakar tasu.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣4️⃣
______________
.........Duk suna a d/table suna dinner Maanal ta fito tana faman murzar ido alamar yanzu ta tashi. Fawzan ne ya fara ganinta. Dan haka cike da shaƙiyanci ya furta, “Oyoyo Bestyn Auta, bada kanki a sare kije gida kice ya faɗi. Kaga surukar Oum da Abah”.
Daina susan idon Maanal tayi ta tsaya tana kallon sa da farko kamar mai mamakin ganin kanta a nan ɗin. Yayinda suma duk suka zubo mata ido suna kallonta musamman Ajwaad. Oum kuwa da Abah murmushi suke yi, hakama babban yaya. Mamy kuwa kamar bata a wajen abincinta kawai take famar ci. Hannu Oum ɗin ta miƙo mata alamar tazo gareta. Da gudu kuwa ta iso ta shige jikin Oum ɗin, sai kuma ta saki kukan shagwaɓa.
Shi ko Fawzan ya wani tuntsure da dariya yana faɗin, “Oh oh yau naga ikon rabbu surukar Oum shagwaɓaɓɓiya kenan, an dawo zakuma a ɗaura daga inda aka tsaya ko”.
Rankwashi Oum ta kai masa sakamakon ɗagowar da Maanal tayi cike da taɓara da tsiwa ta ce, “Oum kinga Yaya F ko, kice ya daina ni Babynki ce ya bar cewa suruka bana son sunan”. Yanda tayi ɗin sai da ya bama kowa dariya. Dan shi kansa Bestien nata wani guntun murmushi ya saki kawai ya cigaba da kallonta. Ita ko ta cika tayi fam dan duk zatonta ma surukar wani mugun sunane da ake gudu. Gwalo Fawzan ya mata da faɗin, “Anƙi a daina ɗin, da wani bakinta kamar na tsuntsu”.
Kuka sosai ta buɗe baki zata sanya, Abah ya saka hannu ya ɗauketa cak yana hararar Fawzan. “Kinga ƙyalesa kinji babyn Oum ɗinta. Kin san dama shi bashi da aiki sai neman faɗa da mutane in dai Fawzan ne. Shiyyasa ma bazanje da shi saudia ba sai ke da bestyn ki kawai”.
Cike da farin ciki Maanal taima Fawzan gwalo da harara. Sai kuma ta hau murna za'aje dasu saudia ita da Bestyn ta. Da wannan lallashin Abah ya kashe rigimar, ya saka mata spoon a abincinsa sukaci tare...
Bayan sun kammala cin abincin ta gama tsiyaya musu surutunta Oum tajata zuwa ɗakinta tai mata wanka. Kaya gareta fal a gidan, anan ɗakin Oum da ɗakin su AA a cikin kayansa. Tana cikin shiryata Ajwaad ɗin ya shigo hannunsa riƙe da kayan tsifa. Tana ko kallon hannunsa ta ɓata rai dan bata ƙaunar kitso sam. Fuska a marairaice kamar zatai kuka ta ce, “Besty kaina na ciwo”.
Harararta ya ɗan yi yana kaiwa zaune a bakin gadon Oum da faɗin, “Idan an gama zaki sha magani”. Sosai ta tura baki gaba, sai kuma ta kalla Oum dake gumtse dariya. “Oum dan ALLAH kaina bada zafi ba? Taɓa kiji ma”. Dariya sosai Oum ta fashe da shi tana taɓa kan, “Gaskiya Babyn Oum babu wani zafi, kanki yayi datti ki daure a tsefe kinji, jibi ƙasa a cikinsa tule. Ko baki son kuje Saudian da Abah yace?”. Jiki a sanyaye ta ce, “Ina so Oum”.
“Yauwa ton daure kinji ƴar albarka. Ai Auta bazai miki da zafi ba kin sani ko? Gama chocolates bari na baki kije anayi kina ci baza kiji ma anayi ba har a gama”.
Da wannan lallashin ta yarda badan taso ba. Haka suka fito hannunta ɗauke da ɗan bowl da Oum ta haɗa mata kayan kwaɗayi, ɗayan kuma Ajwaad ya riƙe mata. Tsakar gida suka fito tacan baya inda garden ɗin gidan yake, wajen akwai ni'ima sosai dan an gyara shi yanda ya kamata. Ga kujeru an shirya domin hutawa harda na yara, sai lilo da dai kayan wasan yara. Koda suka zauna sai da ya ɓare mata chocolate ɗin ya bata wayarsa sannan ya fara mata tsifar. A hakan ma yana farawa ta ɓata fuska zatai masa kuka. Sai da shima ya ɓata fuskar da faɗin, “Oh nacema Abah ɗin mu wuce mu barki?”.
Da sauri ta girgiza masa kai.
Ya ce, “To oya malama nutsu”.
Baki ta tura gaba da faɗin, “Niba sunana malama ba”.
Murmushi yay a karo na farko, tare da jan hancinta ya ce, “To Bestyn bestyn ta ko?”.
Cike da jin daɗi ta ce, “Yes”.
Ƙaramar dariya yayi, sai kuma ya buɗe baki alamar ta bashi chocolate ɗin. Cirowa kuwa tai ta saka masa a bakinsa, ganin ya ɗan ɓata mata yatsun yasa shi kama hannun nata ya lashe wadda ta maƙale. Murmushi tai da faɗin, “Kwaɗayi”.
“Ai ke kika koya min”.
Ya bata amsa yana murmushin shima. Sannan ya fara mata tsifan. Tana kallon cartoon ɗin daya sanya mata tana masa surutu da juyowa ta bashi chocolate ɗin da sauran kayan ciye-ciyen. Shi ko yana biye mata. Dama in kaga Ajwaad na zuba surutu da murmushi to lallai Maanal na a wajen kuwa tabbas. Baya wasa da al'amarinta ko kaɗan. Idan ka gansu dole su birgeka kamar ba yara ba. Haka dai aka gama tsifan, wajen taja kuma aka hau faɗa, sai da ya riƙeta da ƙyau sannan ya iya taje mata, ita ko tana kuka da faɗin babu ruwanta da shi kada ya sake kulata. Dariya ya dinga yi shi dai bai kulata ba sai da ya gama ya ɗaure mata da ribbon duk da yayi datti. Dan cikinsa uban ƙasa ne na faɗan data dinga kwasa a Giro, a hakan ma wai kusan kitso na fin biyar ne akan nata a zuwansu. Koda suka dawo cikin gidan fushi ta dinga masa, sai ta koma kula Fawzan shiko Ajwaad ɗin ya sharesu. Hakan da yake yi idan tana tare da wani a cikinsu yake sa suke faɗin suma yana kishi da su akanta..
_____________★
Washe gari suna gama breakfast Ajwaad ya tasa Maanal gaba zuwa wajen kitso. Ita ko tana faman kuka da faɗin bafa zataje ba. Sai da ƙyar Oum ta lallaɓata ta yarda bayan ta mata alƙawura. Koda suka fito tsakar gida inda ɗan kekensa yake sai da ya hau itama ta hau daga gabansa tanata cika baki da iska. Shi dai bai kulata ba yaja keken suka fito. Ai tun daga gida har zuwa shagon Aunty Saloon duk inda suka gitta sai an musu magana. Dan Maanal fa cele ce a anguwar tasu saboda tsabar fitinarta da neman faɗa. Yara ɗai-ɗai ne batai rigimar da taja Ajwaad ya jibgesu ba.
Da farin ciki Aunty Saloon ta tarbesu tanama Maanal oyoyo da dawowa. Itako ta ɓata fuska taje jikin Ajwaad ta maƙure idanunta cike da ƙwalla. Dariya Auntyn ta fara yi da faɗin, “Maanal ke baki girma da ƙin kitso? Haba ƴar gatan Ajwaad Bestyn ta. Shi gashi yana son yaga ana gyara masa ke da kitso ke kuma baƙya so”.
Baki Maanal ta sake turawa gaba da kallon Ajwaad, shima kallon nata yake yi. Sai ta sake ɓata fuska zatai kuka. A hankali ya kai durƙushe gabanta ya dai-dai tsahonsu hannayensa duka akan kafaɗarta cike da lallashi ya ce, “Ba kin min alƙawari bazakiyi kuka ba? Ko kina son yaran anguwar nan su ganki su samu abin raina ki da tsokana”.
Kanta ta girgiza masa hawayen dake cike a idonta na gangarowa. Hannu yasa ya share mata, “To kada na ƙara ganin hawayen nan. Inba hakaba kuma na fasa shiga secondary ɗin tare dake”.
Da sauri ta haɗiye kukan, cikin rawar murya ta ce, “To bana bari ba”.
“Yauwa my sweet Besty. Faɗa min mi kike so naje na saya miki? Ko awaran can?”. Ya nuna mata waje can tsallaken titi da mai awara ke ta soyawa. Kanta ta jinjiina masa. Shima sai ya miƙe tare da kama hannunta ya kaita saman kujerar wanke kan ya zaunar, fita yayi tana kallonsa daga nan. Bai wani jima ba ya dawo da awaran a leda. Lokacin har Auntyn Saloon tayi shirinta na fara wankema Maanal ɗin kai. Dan duk ta fito da kayan shampoo ɗinta da suka zo dasu a cikin ƴar bag. Haka komai na Maanal a tattale yake ga Ajwaad. Sam bai yarda a mata amfani da kayan wankin kan wajen saloon ɗin ba, duk abinda yasan ana buƙata idan sukaje shopping da Abah ke kaisu duk ƙarshen wata zai ɗakkosa. Dan shi dama ko a wajen shopping ɗin zakaga duk abubuwan da yake ɗakkowa na Maanal ne. Ƙalilan zaka samu nashi. Kujera ya jawo gabanta sosai ya zauna, dan yasan bazata yarda ba sai anyi darun. Bai bata awaran ba ya ajiye gefe yacema auntyn Saloon ta fara. Kuka Maanal ta fara ƙoƙarin farawa ya girgiza mata kansa, sai tai shiru. Haka dai aka wanke kan yana riƙe da hannunta da lallashi kamar wata ƴar mitsilar yariya can ba ƴar shekara kusan takwas ba. Koda aka gama shi da kansa ya goge mata kan da towel ɗin da sukazo da shi ya ɗaure mata shi, sannan ya dinga bata awaran a baki ana busar da kan. Da aka zo kitso kam daru aka sha na haƙiƙa, dan dole sai da ya riƙeta, amma a hakan yasha cizo a hannu da bibbigewa. Kitson ma ba wani mai yawa ba dan shikku ne. Sosai ya mata ƙyau aka saka mata bet. Maanal akwai gashi Masha ALLAH, dan sun biyo Ammie ne cikar gashi da tsaho kamar ba nasu ba.
Sai faman sauke ajiyar zuciya take idanu sun yi jazur saboda kuka ta kama hannunsa tana dubawa, dan duk sayin ƙananun haƙwaranta. Sake fashewa tai da kuka tana shafa cizon da kallonsa, shima idon nasa duk ya kaɗa saboda kukan nata. A hankali ya ce, “Minene kuma? Ba'an gama ba?”.
Hannunta na bin wajen cizon ta ce, “Da zafi ko? Muje na amshi magani wajen Oum na baka”.
Murmushi yay mata da girgiza kansa, sai kuma ya shafa kitson nata da yay ƙyau sosai ya ce, “Babu zafi fa. Jiba yanda kanki yay ƙyau. Ya kamata ki daina kukan kitso Besty kin girma.”
“To ai Oum ta ce idan na girma zan daina ”.
“Wane girma kuma ya rage Besty. Secondary fa zamu shiga ai kin girma ko. Ba kiga ni idan kika rakani wajen aski bana kuka ba”.
A sanyaye ta ce, “Zan bari. Besty muje gida zanyi barci”.
Kansa ya jinjina mata tare da miƙewa. Cikin girmamawa ya kalla Auntyn Saloon dake kallonsu cike da sha'awa da mamakin irin wannan al'amari tamkar ba yara ƙanana ba. Godiya ya mata ya ɗauka bag ɗin sannan ya duƙa Maanal dake faman lumshe ido ta hau bayansa. Kekensa ya kalla sai kuma ya kalla Auntyn Saloon ɗin. “Aunty zanje na kaita sai na dawo na ɗauka”.
“To babu damuwa Ajwaad sai ka dawo. Ka gaishe da Hajiya. Maanal daru sai kuma next”.
Maanal dai bata kulata ba, sai ma sake lafewa da tai a bayansa dan barci take ji sosai. Tana fita wanda ke a cikin shagon suka fara gulma. Aunty Saloon dai dariya take yi da sake basu labarin wannan shaƙuwa ta Maanal da Ajwaad dake birge kowa a layin tamkar ba yara ba...
Kafin su iso gida har tayi barcin. Oum da Mamy na falo suka shigo. Muskar Oum da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Ai na sani dama da barci zaku dawo gidan nan. An sha darun ma yau kenan?”.
Fuskar Ajwaad da murmushi shima ya ce, “Tab Oum miza'a fasa. Duk na sha cizo”.
Dariya Oum ɗin tayi da faɗin, “In ba Bestien taka ba wazai cijeka a zauna lafiya Auta. Maza jeka ka kwantar da ita to”.
Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, sai da ya rage acn ɗakin ya cire mata ɗab hijjabinta sannan ya fito. Oum na tambayarsa ina kuma zaije yace zai ɗakko kekensa ne. Daga haka ya fice. Mamy dai bata saka musu baki ba. Yana kuma fita suka ɗora da hirarsu da suke yi ita da Mamyn hankali kwance cike da farin ciki kuma kamar ba kishiyoyi ba. A haka Ajwaad ya sake dawowa ya samesu. Ɗakinsu ya wuce yana tambayar ina su Fawzan. Oum tace sunje aikan datai musu ne. Daga nan zasu duba malaminsu na islamiyya suji yaushe zasu koma. Dan tun wancan satin ya kamata su koma matar ya sayyadin ta haihu, haihuwar kuma tazo da matsala shine ya ƙara hutun, sai dai bai sanar da ranar komawar ba taka maimai. Ciki ya shige suma su Oum ɗin suka miƙe dan lokacin salla yayi.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣5️⃣
______________
.......Abah bai samu zama da su Oum ba sai daren yau akan batun daya faru a Giro. Komai bai ɓoye musu ba daya faru A to Z har hukuncin daya yanke akan Fadeel da Fawzan. Sosai tausayin Ammie ya sake baibaye Oum. Dan tamkar ƙanwa uwa ɗaya take jin Ammie a ranta ba maƙwafciya kawai ba. Ɗari bisa ɗari kuma ta bada goyon baya ga hukuncin mijin nasu. Ta kuma yabama dattakonsa. Itama dai Mamy ta jimanta al'amarin ƙwarai da gaske. Akan batun yara kuwa ta nuna kawaici kamar yanda ta saba.