Showing 78001 words to 81000 words out of 221978 words

Chapter 27 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

sauri ya miƙe ya ƙarasa kusa da Oum ɗin ya zauna, tare da kai bakinsa saitin kunnenta ya ce, “Oum idona ne kokuwa dai kaina ne ya kwance da gajiyar aiki? Wai kin san wa nake gani kuwa? Little fa, Bestyn Auta?”.
Kai Oum ta jinjina masa fuskarta na ɗan komawa damuwa, itama a hankalin ta ce, “Itace Fawzan, Maanal ce. Itace kuma Rafeeq ya kawo mana matsayin wadda zai aura”.
Ai zaram sukaga Fawzan ya miƙe yana faɗin, “What!!” gaba ɗaya idanunsa a waje sosai, sai kuma ya juya yana kallon AA daya wani share kowa yana sauraren surutun Haneeff, idanunsa kuma nakan novel da tunda su Maanal suka shigo ya daina fahimtar labarin. Sake ɗaukewa yay daga kan AA ɗin ya maida ga Maanal daketa ƙoƙarin saisaita kanta. Murmushi ta sakar masa mai sanyi, cikin muryarta mai zurfi da rashin son hayaniya ta ce, “Yaya F”.
Maimakon amsawa sai yakai zaune jagwab a kujera yana faɗin, “Ya ilahil'alamina da gaske Little ɗin ce dai Oum. Ni abin ma sai yake min kamar mafarki wlhy”.
“Bakai kaɗai ba Fawzan, ni kaina kallon komai nake kamar a mafarki, yau Rafeeq ya haɗa zuminci sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi. Kalla yaran nan yaran Shahidah ne su duka, macen sunana aka saka mata ma”.
Kallonsa ya maida ga yaran, sai kuma ya kalla Maanal. “Little! Su Shahidah duk sunyi aure kenan?”.
Kan Maanal a ƙasa ta ce, “Eh yaya. Itama Didi Amal yaranta biyu”.
Wani murmushi ya saki mai kama dana damuwa, sai kuma ya jinjina kansa, “ALLAH sarki rayuwa komai sai kaga yana faruwa kamar a mafarki. Oum jiba dai Autar ki duk ta canja, komai na Little ya canja kamar ba ita ba. Ji yanda ta zama shiru-shiru, ba surutu yanzu, komai nata ya canja, ta girma ta ƙara tsayi”.
Murmushi sosai Oum tayi itama idonta akan Maanal datai ƙasa da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta. “Sosai kam Auta ta canja Fawzan, badan fuskar na nan ba ma sai nace an canja min ita gaba ɗaya. Girma yazo”.
“A girma yazo kam Oum, ko'a mafarki akace min little zata koma shiru-shiru haka za'a kwana gardama dani ban yarda ba. Little ina Ammie da Abbah fa?”.
“Lafiya lau Yaya, Ammie na Kaduna itama”.
“Ban gane ba, kun dawo Kaduna ne yanzu?”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa. Cikin mamaki ya ɗan juya ya kalla Oum, itama shi take kallo, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda maganar da RK yayi....
“Nifa gaba ɗaya sai sake sakani a wani irin dogon tunani mai rikitarwa kuke wlhy Aunty, wacece Maanal a wajenku dan ALLAH? Ya akai kuma ni ban santa ba?”.
“Ai kwantar da hankalinka Uncle kada ka wani ruɗar da kanka. Maanal dai ɗiyar Oum ce, mu kuma ƙanwa ce. Abinda yasa baka santa ba lokacin da mukai zaman Kano ne, kai kuma sannan kuna Paris”.
Da mamaki RK yace, “Kenan har AA ya santa?”.
Su dukansu juyawa sukai suka kalla AA ɗin da furucin RK ɗin ya wani daki zuciyarsa, hakan ya sashi tsayawa cak da karatun da yake duk da dama tun ɗazun ba fahimta yake ba. Kai Fawzan ya jinjinama RK. Sai kuma ya ce, “Tabbas ya santa”.
Cike da mamaki RK da ke kallon AA ya ce, “Lallai, amma gaskiya na sake yarda kai abin tsoro ne AA. Amma shine koda wasa baka nuna min kasanta ba. Aunty kusan fa 3 weeks da fara aikin Maanal a companynsa shiyyasa kikaga inata ƙara jinjina mamakina ai”.
Kallon juna Oum da Fawzan sukayi, sai kuma suka kalla AA ɗin da har yanzu dai yana a yanda yake, sai ka rantse baya falon ko kuma baya jin mima suke faɗa akansa. Fawzan ya girgiza kansa kawai da murmusawa, “Ai autan Oum sai addu'a Uncle. Little kice har an kammala karatu?” ya maida hankalinsa ga Maanal.
Idanunta ta janye daga satar kallon AA ɗin itama. Ta amsa ma Fawzan da, “Eh Yaya har sarvese nayi”.
“Kai Masha ALLAH, kinga rigimarki ta saka kin kammala karatu da ƙarancin shekarunki, kai Little rigima”.
Hannu Maanal tasa ta rufe fuskarta dan tuna baya. Yayinda Oum keta dariya itama tana tuno abubuwa kamar labarin Film. A mamakin su sai sukaga AA ya miƙe batare da yacema kowa komai ba ya nufi hanyar ficewa daga falon. Da kallo kawai suka bisa.... Sai da ya taka step na farko batare daya jiyo ba ya ce, “Oum na wuce massalaci”. Murmushi Oum tayi da masa addu'a, yayinda RK ya miƙe yana faɗin, “Ɗan rainin hankali shine bazakace mu tashi lokacin salla yayi ba”. Fawzan ma miƙewa yay yana dariya. Sai kuma ya fara raira waƙar Hamisu breaker _Ƴar Arewa_.
“Duk wanda yay gamo da abin ƙauna baisan rabewa, in dai ko ya rabe duk nishaɗi nai yay tarwatsewa.
Sirrin farin ciki soyayya in ba takurawa, mai so aso shi kanso babu abinda bazai iyaba.
Na durkusa akan gwiwata idan kuskure nai. Kiyafiya gyaran dan kamin har maganai.
Nemanki na karaɗe kauye na koma birane, fito na ganki Ni kallon kauna kinji yar arewa...
Sissiran dake cikin raina duka ne zan baiyyanawa. So yayi tsitstsige na takawa yay min illatarwa.
Ni bani fasa yarda domin kin zam rayuwata, manta dake hakan ban san yaushene zan iya ba
Kukan da ni nake da kishirwa bata gushe ba, duk da na sani rabuwa bata zamto mutuwa ba.....
Harara mai lasisi AA ya wurgama Fawzan tare da wucewa da sauri-sauri kan stairscase ɗin. Hakan yasa Fawzan kwashewa da dariya Oum kuma na murmushi. Shi ko RK da bai fahimci inda waƙar Fawzan ɗin ya nufa ba sai ca yay “To ɗana kodai kaima waƙa zaka koma ne?”.
Shi dai Fawzan dariya kawai yake yi yana cigaba da bin AA da har ya gama sauka daga steps ɗin da kallo...


Haka suka fice harda Haneeff. Oum kuma ta shiga da Maanal da Barru ɗakinta. Gaba ɗaya idanun Oum sun kasa daina kallon Maanal da dukkan motsinta har suka idar da salla. Tana son mata tambayoyi sai dai yanayin Maanal ɗin yasata haɗiyewa, sai ɗan abinda ba'a rasa ba dai da take tambaya Maanal ɗin na bata amsa. Kiran Shahidah yasa Maanal cema Oum zasu tafi gida. Amma sai Oum ɗin ta amshi wayar tai kiran Shahidah back.
Koda Shahidah ta ɗaga taji ba muryar Maanal bace sai tayi ɗan jim. Cikin girmamawa ta shiga gaida Oum. Itako ta amsa mata tana murmushi. “ALLAH sarki Shidan Abba an girma, an zama iyaye”.
Da wani irin zabura Shahidah ta dafe ƙirji da faɗin, “Oum!”. Sai kuma ta cire wayar daga kunnenta tana sake duba number ɗin. Da gaske no ɗin Maanal ce dai, amma kuma sunan da aka kirata da shi mutum ɗaya ke kiranta da shi a duniyar nan, sake maida wayar tayi kunnenta ta ce, “Maanal!”.
“Ni ɗin ce dai har yanzu Shahidah. Oum ɗinku ce, yau gani ga ɗiyata a kusa dani Rafeeq ya kawo min ita har gida”.
Ba ƙaramin motsawa zuciyar Shahidah tayi ba. Ai babu shiri ta furta, “Oum kenan kece auntyn Rafeeq da Maanal suka zo gaidawa?”.
“Tabbas nice Shahidah, kinga wata hikimar UBANGIJI kuma ko. Dan haka ina roƙon a bar min ɗiyata da jikokina su kwana anan, gobe in sha ALLAHU da kaina zan maidosu gida tunda weekend ne”.
Koda wasa Shahidah bazata taɓa iya musu da Oum ba, dan haka babu jayayya ta sallama. Sai dai tana yanke wayar ta maida akalar kiran nata ga Amaal.


★★

“Ni wlhy gaba ɗaya kin hatgitsani Didi wai dan ALLAH da gaske kike yi?”.
“Humm Amaal wlhy nima a hargitsen nake. Kema kin san bazanyi miki wasa da wannan zancen ba”.
“Tofa wannan fa shi ake kira da rikita-rikita. Kenan fa idan lissafin yayi dai-dai Rafeeq Uncle ɗin Ajwaad ne? Amma ya akai bamu san Rafeeq ba duk yanda yake da kusanci da Oum haka?”.
“Nima wannan tunanin nakeyi, sai dai kuma wani abu yazo raina. Kin san iyayen Oum na ainahi a lokacin basa Nigeria kamar. Idan baki manta ba muntaɓa jin tana sanar ma Ammie riƙonta akai a gidan Alhaji Abdulkarim Sardauna. Kingako kenan Rafeeq a lokacin baya Nigeria.”
“Tab ɗin, UBANGIJI mai hikima. Didi ni wlhy ma sai yanzu nima wani abu ke dawo min a rai. Kin manta randa muka fara gabin Hajiya Majdiya nake cemuku kamar tana min kamanni da wani amma na manta mai fuskar. Ke da Ammie kukace na cika ƙwaƙwale-ƙwakwalen cewa mutane na kamanni da wasu. To ALLAH kamanin Oum na gani a tare da ita”.
“Ya ALLAH, tabbas anyi haka kuwa Amaal. Kigafa wani al'amari mai ban mamaki, an rabu amma ashe ana tare da juna ta inda sam ba'a sani ba. Ni yanzu ma yaya zamu tunkari Ammie da zancen nan Amaal?”.
“Abinda nake hasasowa a zuciyata kenan, Ammie zatai matuƙar farin ciki. Sai dai kuma Auta Didi, ita nake tausayi da tunani a wannan gaɓar, dan dole ne ɗayan biyu, rabuwa da Rafeeq duk da dama bawani ta amshesa bane, sai kuma auren Yazeed”.
“Humm Amaal kenan, na fahimci kumafa har yanzu kun kasa fahimtar Ajwaad na'a zuciyar Auta daram, shiyyasa ta kasa amsar kowane namiji a rayuwarta. Abinda ya faru ne kawai ke danne soyayyar da tsiya-tsiya.”
“Na sani Didi, sai dai kema kin san kafiyar Maanal. Kin san idan har tace tabar abu tofa ta barsa ɗin kenan, kuma shi kansa Rafeeq alaƙarsa da Ajwaad sai shi zaisa ta rabu da shi rabuwa ta gaske a yanzu. Kinga kuwa babu wata mafitar data rage mata kuma sai na auren Yazeed, dan dama shigowar Rafeeq ɗin rayuwarta ne kaɗai hope ɗin mu. Babu shi kuwa da kunya a tunkari Daddy da batun ƙin auren ɗansa ko?”.
“Wato Amaal wannan batun na buƙatar zama gaskiya. In sha ALLAHU next week zan shigo kd. Badan ma Oum ɗin tace gobe zata shigo nan ba da goben zanzo.”
“Hakan ma yayi ALLAH ya kaimu, dan nima ban jima da zuwa Abujan bane, yanzu ko nace zanzo sai Abban Munaya yata mita.”
“Ai yama yi ƙoƙari, tsakanin nan kunsha zarya sosai. Ki bari zan shigo ɗin kawai. Bara naje kin san ƴar iskar yarinyar nan na nan gashi babu su Maanal sai Linda kawai, da safe mayi waya”.
“Okay ba damuwa ALLAH ya tashemu lafiya”....


________________


“Ranka ya daɗe nazo ne domin sanar maka sakamakon binciken ne daman”.
“Rabilu da wuri haka har komai ya kammala?”.
“Ai naga kamar kana buƙatarsa ne da wuri ranka ya daɗe shiyyasa nima nai himma”.
Dariya irin ta manya Sen.. Bukar Kaugama yayi, cike da jin dadi ya ce, “Lallai Rabilu kana son cin mota ashe kuwa”.
Wani kalar daɗi ne ya mamaye fuskar Rabilu. Bakinsa a washe matuƙa ya ce, “To ALLAH ya cidani ranka ya daɗe. Yarinyar dai sunanta *_Maanal Habeeb Giro_*. A gidan Alhaji Sadeeq Busam take zaune, dan matarsa yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya. Sai dai bawani ta daɗe a gidan bane bama, duk da dama tana yawan zuwa tai hutu a wasu lokutan. Tana aiki a companyn Mawaad ne......”
“Oh! Kace shegen takema aiki shiyyasa ashe?”.
Senator ya faɗa cikin katsesa.
“Eh tabbas a kamfaninsa take aiki, amma bata wuce ma 3 weeks da farawa ba. Kuma an tabbatar min yaron wajen Doctor KK ne ya samar mata aiki kuma koda yaushe suna tare da shi ma, yanzu haka zancen da nake maka ya ɗauke ta zuwa can gidan Ambassador Aliyu Darma”.
“Ɗan gidan Doctor Kasheem Kura?!”.
“Eh kwarai ranka ya daɗe”.........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣6️⃣




______________


https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥💃💃 Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....🔥⭐⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑royal jelly na fidda shape din mace...💃💃⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥⭐👑💃🏼💃🏼 Haseer supplements ta kawo muku supplement kaloli sai wanda ranki keso hajiya a cikin farashi mai sauqi Phone: 08038796871


_____________


..........“Alhaji Aliyu Darma ba shike auren babbar ɗiyar Dr Kasheem Kura ba kuwa?”.
“Eh shine, kamar ma itace ta haifi shi yaron nan AA Darma ɗin ai”.
“Okay! Ok! Ok na gane. Yanzu ita yarinyar minene aikinta a kamfanin?”.
“Eh wannan ne dai nake kan bincike ranka ya daɗe. Amma in sha ALLAHU a cikin satin nan zan kammala shima. Na fara kawo maka wannan ɗin ne dai”.
“Ba damuwa Rabilu, hakan ma kayi ƙoƙari. Amma ina son ka binciko min ainahin mahaifin yarinyar shima”.
“To ranka ya daɗe in sha ALLAHU an gama. Wannan itace lambar wayarta”.
“Ok ka samu Oler a waje zai baka kuɗin zuba mai”
“Nagode sosai ALLAH ya ƙara girma da ɗaukaka Ranka ya daɗe”. Rabilu ya cigaba da jera godiya kamar ba gobe...


Yana ficewa Sen.. Bukar yay wani murmushin ƙasaita, tare da shafo sajensa da furfura ta gama yima ƙawanya. Tabbas love at first sight ne ya shigesa na yarinyar nan. Dolene ta shigo a cikamakin matansa uku matsayin ta huɗu, koba komai ya samu ta sakawa a gaban mota dan amaryarsa ya fahimci itama yara sun fara tsofar da ita. Dan ta bari ƙiba ta fara zama mata, shiko sam baya ƙaunar mace tayi ƙiba, hakanne ma ya sakashi ƙara aure na biyu saboda uwargidansa itama haka ta zama rabkekiya, yayi yayi suje a rage mata ƙiba taƙi, sai kawai yayi ta biyu. Itama ɗin dai kwana biyu ta ƙibe masa. Haushi ya sashi auro ta uku, amma abin mamaki itama yaga yanzu ta ɗakko hanyar yin ƙibar, to gara tun kafin ma suje ga hakan yayma tufkar hanci. Dan Maanal zatai dai-dai da ra'ayinsa, gata ƙaramar yarinya. Murmushi ya sake saki, yana jin kamar ya tashi ya fara taka rawa. Dan babu abinda yake sai siffanta surar Maanal a zuciyarsa......


Tofa, Maanalu sarkin farin jini, ga shuger daddy mun samu🏃🏃🏃.


___________★


Tsaye yake kawai ya zubama harabar gidan ido hannayensa duka a cikin aljihun baƙin wandonsa. A kallo ɗaya zaka fahimci yayi matuƙar yin nisa a duniyar tunani. Dan har Fawzan daya shigo sashen nasa ya iso inda yake babu alamar yasan da shi. Sai da ya kai hannu saman kafaɗarsa ya ɗan bubbuga sannan ya juyo...
Murmushi Fawzan yay masa tare da masa alamar minene? da idanu. Sake tsuke fuska AA yay tare da kauda kansa ya ce, “Nothing”.
Ƙaramar dariya kawai Fawzan yayi yana mai girgiza kansa. Sai kuma ya matsa jikin ƙarfen balcony ɗin ya jingina tare da harɗe hannayensa a ƙirji shima ya zubama AA ɗin idanunsa. “Auta kenan, kai kasan ko zaka ɓoyema kowa kanka banda ni nan. Dan na sanka fiye da yanda nasan yunwar cikina ai ko?”. Ya ƙare maganar da wani ɗan ɗage gira sama.
Idanu AA ya lumshe tare da buɗewa duk a lokaci guda. Kamar zai yi magana sai kuma ya maida bakinsa ya tsuke. Murmushi Fawzan ya saki sai kuma ya juya ya kalla inda idanun AA ɗin suke kallo, flat ɗin Oum ne dan haka ya sake maido kallonsa ga AA ɗin.
“Ajwaad nasan har yanzu kana sonta, ba kuma zaka taɓa daina sonta ba. Wannan dama ce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login