Showing 9001 words to 12000 words out of 221978 words
Chapter 4 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
kullum zaidinga juyuwa 💰
Kubiyoni domin Jin cikekken labarin 52U don koda kudinka saida rabonka abin na yan baiwane
52U ba platforms bane networking ne kuje kuyi bincike kafin kuyimin magana
08031507345
___________
______________
........Idanu Manaal ta ɗan rumtse kamar zatai wucewarta sai kuma ta dakata saboda hararar da Ammie ta watsa mata, cikin sanyinta ta furta, “Yau ne Yaya, ina yini”.
Batare daya amsa ba ya sake furta, “Ai da yake ke baƙya zumunci ko a waya sai kinso ake jinki. ALLAH ya sanya albarka to”.
Kasancewar ta fara tafiya a taƙaice ta amsa masa da Amin. Ganin da gaske barin falon zatai kuma harga ALLAH dan ita yazo ya dakatar da ita da sake faɗin, “Zoki bani abinda kuka girka anan ɗin naci”.
Cak Maanal ta sake tsayawa zuciyarta na wani kalan harbawa da sauri-sauri, sai kuma ta yunƙura zata cigaba da tafiya ranta na wani kalar jin zafinsa da mamakin rainin hankalinsa. Ba abinci suka samu yana ci a sashensu ba? Shine dan guntun kutsugu zaizo nan kuma yace a bashi abinci......
“Wai nikam ba dake ake magana ba halan?”.
Ammie ta katse mata hanzari cikin kaushin murya. Jitai kamar zata saki ihu, sai dai babu yanda ta iya dole ta furta, “Ammie nafa amsa“ daga haka ta nufi kitchen a maimakon hanyar bedroom ɗinta. Abincin ta zubo mata tana faman ƙannan magana a ranta. Itafa wlhy da tasan ma yana gidan bazata dawo ba. Kuma ko yanzu idan taji zai jima a KD ɗinne gara tabi Didi Shahidah Abuja har sai ya tafi ta dawo kawai. Da wannan tunanin ta dawo da abincin. Tana ƙoƙarin nufo falon ya miƙe yana faɗin, “Bani anan”.
Kallon dining ɗin daya nufa tayi, sai kuma ta kalla Ammie kamar zata saki kuka. Ganin Ammien ta ɗauke kanta ta maida dubanta gasu Didi Amaal. Da baki Amaal tai mata nuni da Ammie. Hawayen da suka cika mata ido kawai ta haɗiye kafin ta taka a hankali ta ƙarasa inda yake zaune yana jiranta. Tray ɗin ta ajiye a gabansa. Tana niyyar barin wajen ya dakatar da ita da faɗin, “Dawo ki zauna”.
Yanda yay maganar babu wani wasa kuma a gadarance ya sake kunna zuciyarsa. Sai dai kuma babu yanda zatayi dole ta koma ta zauna dan tun fil azal shi baya wasa dasu. Sannan kaf ɗin gidan nan babu wanda zai ce baya tsoron Yaya Yazeed. Mutum ne bamai yawan shiga sabgar kowa ba, amma baya ɗaukar raini. Abincin ya ɗan fara ci a nutsensa yana lumshe ido, sai da yay kusan lauma uku ya ɗago yaɗan kalleta. Fuskarsa babu wani walwala ko alamar wasa ya furta, “Abincin Ammie dabanne a gidan nan Manaal. ALLAH dai yasa ki gadota iya girki dan ina son abinci sosai. Idan ko kina wasa da koya ki ƙara dagewa sosai kinji”.
“Hummm” ta faɗa kawai batare da tace komai ba. Manyan idanunsa ya ɗan zuba mata yana ɗan sake tsuke fuska. “Miye wani hummm. Kin san fa bana son halayyar nan naki ai ko? Tom zamu fara ai kenan. Dama baki son ina fushi dake bane. Tunda nai tafiyar nan baki taɓa nemana a waya ba why?”.
Rasama mizata ce dashi tayi, tsahon lokaci bata tanka ba har sai da ya sake tsareta da kaifafan idanunsa sannan ta motsa lips ɗinta da ƙyar ta amsa masa da “Ai ban san da wane layi zan sameka ba”.
“Hummm dama ba niyyar kiran nawa kike da shi ba. Ni wannan halin miskilancin naki ban san yaya zan kwashe da shi ba Maanal. Amma ba komai zanyi maganinki ai. Yanzu ke miya samu naki layin da ban samunki kwana biyu, ko blocking ɗina kikayi?”.
Nan ma ta jima bata amsashi ba. Kafin ta nisa da ƙyar ta amsa masa a taƙaice. “Matsala ya samu, mizaisa nayi blocking ɗinka”.
“Sai kuma kika gagara zuwa ki gyara ko?”.
Shiru tai ta ƙi bashi amsa. Shima sai ya bar zancen dan yasan ɓacin rai kawai zai ƙarama kansa. Abincinsa ya cigaba da ci, sai da yana gab da gamawa ne yake sake kallonta da faɗin, “Lokaci fa yayi da zaki cireni a gidan gandun nan. Dan kasa isasshen barcin daren nan da nake ya fara isata haka nan Manaal”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa cikin ƙosawa da mamaki kuma, sai dai muryarta acan ƙasan maƙoshi da kuma sanyi. Idanunsa da suka ƙanƙance lokaci guda ya ɗan lumshe mata ya sake buɗewa. Sai kuma ya wani maidasu ƙasa-ƙasa tare da muryarsa ya furta, “Saboda ina buƙatarki a gefena. A tsakanin nan a matse nake da buƙatarki a kusa dani. Dan haka zanma Daddy magana a tada zancen aurenmu tunda kin kammala karatu harda sarvese ai nayi ƙoƙari sosai”.
Wani irin mugun bugawa ƙirjin Maanal ya shigayi. Yayinda jikinta ke wani tsuma. Cikin rawar murya da sake bayyanar rauninta ta ce, “Yaya Yazeed Please ka ƙara min lokaci mana, ka......”
Spoon ɗin hannunsa ya ajiye cikin tsatstsareta da idanunsa da suka hanata cigaba da maganar tata. “Manaal lokaci kuma? Miyyasa baƙya tausayina. Kin san shekarata nawa kuwa a duniya? 35 fa nake ƙoƙarin cikawa. Kin san kuwa nakai maƙurar ƙurewa da buƙatar abokiyar rayuwa ko? A wancan karon kince kina son kammala karatu, nayi miki wannan alfarmar, kika kammala kika sake roƙon haɗa masters naki na sake kauda kaina saboda Dadday, yanzu harda su sarvese duk bance komai ba amma ki sake cewa na baki lokaci. Ko kina son sai an samu matsala na far miki a cikin gidan nan ne saboda halin da nake ciki?”.
Zuciyarta ce ta sake harbawa da sauri, duk da kuwa bawani fahimtar zantukan nasa take ba kasancewar hankalinta ya gama rabuwa biyu. Shima ganin tunaninta na neman yin nisa da shi ya kira sunanta murya a ƙasan maƙoshi. Ajiyar zuciyar dawowa cikin hayyaci tayi, sai kuma takai hannu ta goge ƴar ƙwallar dake neman gangaro mata. Cikin rawar muryar kuka ta ce, “Yaya Yazeed!”.
Idanunsa kawai ya zuba mata batare daya amsa ba. Dan shima dai miskilin ne kamar yanda ake zaginta akan natan. Sai dai ita ɗin ta takashi ta shanye. Dan shi yakanyi magana a inda yaso idan yaso hakan. Ganin taƙi cigaba da magana ya ce, “Ke nake saurare.”
Maganar take son yi sai kuma ta kasa, sai faman wasa take da dogayen yatsunta masu ɗauke da farce masu haske dan babu ɗigon lalli a jikinsu duk da kuwa ita ma'abociyar sonshi ce. Nuni ya mata alamar ita yake saurare. Itama saita ɗaga masa kanta tana ƙoƙarin shanye abinda ke mata kaikawo ta cigaba da faɗin, “Mamma!. Ya kamata ka....”
“Maanal Please, kema kin san an wuce da wannan matsalar tuni, Mamma tsakaninta da Daddy ne bada mu ba. Mizai sa ki ɗauka ki saka hakan a tsakkiyar rayuwarmu. So please indai ba so kike ki sake jana a ƙasa ba kuma bayan na baya ki bani haɗin kai. Ina buƙatar abokiyar halitatta Maanal. Ina cikin takura matuƙa akan hakan kada kisa na cutu”.
Idanunta ta rumtse da ƙarfi, kalamansa na mata wani kalar kuɗa a zuciya da ƙirji. Yayinda ta wani gefe suke maimaita kansu a sigar ƙaddararta ta ƙuruciya. Rawa jikinta ke neman farayi saboda abinda ke neman jijjigo gyanbon ƙasan ziciyarta da kowa ke tunanin ya jima da warkewa. Kamar wanda ke karantarta ya ce, “Okay na baki dama kije kiyi shawara dama duk wanda kike ganin zakiyi. Kafin nan dai kafin Daddy ya dawo ki tsaida min zance ɗaya. Idan ba haka ba sai dai kiji batun saka rana. Zuwa anjima ina son ganinki a garden, ki zo min da layin naki dakeda matsala zan saka a dubashi”. Ya ƙare maganar yana miƙewa abinsa. Har yay sallama dasu Ammie ya fice a sashen Maanal na zaune kamar gunki da aka dasa don tarihi a dining area ɗin ta kasa tasowa. Saima wata irin zufa ce data cika mata gaban goshi. Yayinda hawaye ke ambaliya a saman ƙyaƙyawar fuskarta. Amaal da dama tun ɗazun hankalinta ke kanta ce ta ƙaraso wajen da sauri. Kamota tai cikin rawar jiki tana tambayarta mike faruwa? Maimakon amsa sai ta faɗa jikinta kawai ta rungumeta tsam ta saki wani sirrin kuka mai ban tausayi. Rikicewa Amaal ɗin tayi, hakama Didi Shahidah tuni ta taso ta nufosu. Ammie ce dai kallo ɗaya ta musu ta kauda kanta gefe, dan ta ɗaura ɗammarar itama bazatai sanya a wannan karon akan Maanal ɗin ba. Ta gaji da zamanta haka gara ai auren nan ko hakan zaisa ta manta da baya. Tana jiyo yanda ƴan uwanta ke sake jera mara tambayoyi a rikice batabi takansu ba tama tashi tabar falon zuwa bedroom ɗin ta. Bakin gado takai zaune tare da fara sarrafa wayarta, sai kuma ta kaita kunne alamar kira tayi. Babu kuwa jimawa aka ɗaga daga can, bayan sun gaisa da tambayar juna iyali ta fara magana kamar haka.
“Nene na kiraki ne akan ƴar gidanki, yau dai ta dawo an kammala service”. Ta ɗan yi shiru alamar saurare. Sai kuma tai murmushi da cigaba da faɗin, “Shine ma dalilin kiran naki Nene. Dan anyi sa'a shima Yazeed ɗin yana gida yazo wani aiki kuma zai jima kamar yanda ya sanar min. To sai nake ganin hakan damace da za'ayi kawai a huta. Dan nagaji da wannan ɗage-ɗagen saka ranar auren nasu shi kuma Baban nasu na biye mata. Gara ayi a huta, idan taga abin bawasa bane tama ƙarasa nutsuwa. Saboda na fahimci Maanal fa bazata taɓa kasancewa a yanda ake buƙata ba a haka gaskiya. Amma shi idan suka je can zai san ta yanda zai ƙarasa mantar da ita komai dan yaron nada hankali da nutsuwa. Banga abinda Yazeed bai mallaka ba da mace bazatai alfahari da shi ba ako'ina matsayin miji”. Nan ma tai shiri tana saurare. Ta jima kafin ta amsa da, “Ni abun sake bani tsoro yake. Yanzu haka bakiga yanda ta dawo a fige ba wannan karon kamar kazar fakat. Al'amarin Maanal na tayar min da hankali Nene wlhy”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa.
“Hakane Nene ina kan yimata iya ƙoƙari na. Dan ko sadakar nan wlhy kusan don itane bana iya jinkirtawa. Amma dai a aiko mata da ruwan addu'ar ma sai ta cigaba da sha. ALLAH ya kawo iyakar komai ya kuma bama yaron nan ƙwarin gwiwar kwantar mata da hankali ta sake manta komai”.
In sha ALLAHU Nene bana jin Yazeed. Yarone mai addini da sanin yakamata tamkar mahaifinsa. Dan sam baida halin mahaifiyarsa, baya kuma biyema al'amarinta kamar ba daga jikinta ma ya fito ba.”
“To Amin ya rabbi sai kin shigo ɗin ma ƙarasa”. Daga haka sukai sallama.
★★“Auta dan ALLAH kibar kukan nan haka. Wlhy yana ɗaga mana hankali. Ki mana bayanin mike faruwa ne? Ko wani abu yace dake mara daɗi?”.
Kanta ta shiga girgiza musu tare da share hawayenta. Sai kuma ta tashi daga kwanciyar datai a jikin Didi Shahidah ta koma ta jingina da fuskar gadonta. “Didi dan ALLAH ku taimakeni, wlhy bana son auren nan bana buƙatarsa dan bazan taɓa yin aure ba wannan alƙawarine da naima kaina. Amma su Ammie da Yaya Yazeed sun kasa fahimtata. Wlhy kosun matsa nayi auren nan GANGAR JIKINA kawai zai aura, sannan bazan taɓa biyayya irin ta aure ba a gareshi, bama shi ba ga kowanne ɗa namiji. Didi miyyasa bazai fahimta bane, Maanal ta jima da mutuwa babu ita a wannan DUNIYAR ta mutane. Duk gangar jikin dake rayuwa da matacciyar zuciya bashi da wani amfanin rayuwa. Amma sun kasa fahimta, sun kasa min uziri, dan ALLAH ku ku fahimtar dasu maybe zasufi saurin yarda daku idan ni basa gane yarena. Koku fahimtar da Yaya Yazeed shi maybe ya fisu gane illar yin AJIYA A DUHU da yayi, cigaba da matsawarsa kuma zai zama ƙonewar komai daga hasken fitilar da yake ƙoƙarin haskawa don lalubo abinda ma babu shi koda a cikin duhun....”
“Maanal Please...”
Didi Shahidah ta faɗa tana kamota jikinta ta sake rungumewa. Itama cikin murya da lallashi ta ce, “Please ki kwantar da hankalinki mana. Kin san ba wani lafiyace ta isheki ba. Ciwonki baya buƙatar irin waɗannan abubuwan kinfi kowa sani. Maanal iyayenmu suna son taimakon rayuwarki ne ba cuta miki ba. Sannan Yazeed babu abinda ya rasa daga zama cikakken Namiji. Yana kuma matuƙar kaunarki, duk da boren mahaifiyarsa akan al'amarinku bai taɓa canjawa ba. Miyyasa bazakiyi haƙuri ki manta da komai ba ki amshi wannan ƙaddarar?......”
“Saboda ƙaddara tana tafiya ne da rayuwa Didi, ni kuma na riga na jima da Mutuwa, mi zaiyi da gawa? Mi zai yi da gangar jikin da babu zuciya? Mi zaiyi da wadda labarinta ya jima da rubutuwa da ƙarewa? Tuni fa Maanal ta gama mutuwa, na mutu! ni tamkar hawace Didi..”
“Keba gawa bace Maanal, ya kamata ki fahimci bafa komai a rayuwa kake samu hundred percent ba, dole sai kayi haƙuri da wani abun sannan kake mallakar wani. Please ki amshi ƙaddararki a karon na biyu, nasan zaki ji daɗin zama da Yaya Yazeed wlhy mutumin kirki ne, tunda kin san dai babu yanda za'ai a barki haka babu aure. Kuma Yazeed ya dace dake matuƙa”.
“Didi ban musa miki kirkinsa ba ko nagartarsa ko cancantarsa. Duk abinda kuke hange min nasan fiye da haka gareshi, sai dai bana buƙatar kowanne namiji a rayuwata gaba ɗaya ku fahimta mana dan ALLAH”..........✍️
_Tofa, mace kuwa zai yiwu tace bata buƙatar namiji a cikin rayuwarta?????. Shin jama'a mike damun Maanal ne haka?????🏃🏃🏃🏃🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣7️⃣
.......Hawaye ne suka cika idon Amaal, yayinda Shahidah ke ƙoƙarin shanye nata itama. Tausayin ƴar uwar tasu na ƙara cika musu zuciya. Dai-dai nan Ammie ta shigo, kallo ɗaya tai musu su duka ta kauda kanta. Sai kuma tai gyaran murya. A tare duk suka kalleta, Maanal ta share hawayenta da ƙoƙarin kaiwa kwance, amma sai Ammie ta riƙota tana kaiwa zaune kusa da ita da faɗin, “Auta wai yaushe zaki bar shagwaɓa ne?”.
Baki Maanal ta tura gaba da yin narai-narai da idanu zata sake sakin sabon kukan Ammien tai mata hararar wasa. “Kina sakin min kuka zan zaneki ne tas a ɗakin nan”.
A tare suka kwashe da dariya, dan yanda Ammie tai maganar sai ya tuna musu baya. Kai Maanal ta zuba fitina a rayuwarta, ga tsoron dukan masifa. Dan duk rashin mutuncin da zata zuba da Ammie tace zata zaneta take nutsuwa. Ammie data ji daɗin ganin damuwar tasu ta kau sai ta cigaba da jansu da hira. Idan ka gansu abin sha'awa kamar wata babbar yayarsu can ba mahaifiyarsu ba. Dan Ammie an mata aure da ƙarancin shekaru ne, kuma ALLAH ya bata haihuwan da wuri, shiyyasa idan baka sani ba sai ka ma ɗauka ba itace ta haifi su Shahidah ba, dan za'afi ganin Maanal a ƴar farinta kamar. Kamar wasa suka sha hira sosai sai da aka kira Magrib Ammie ta fita. Babu wanda ya sake tada batun auren Maanal ɗin har dare. Sun idar da salla Shahidah da Amaal suka shiga kitchen, yayinda Maanal ta nufi ɗakin Ammie dan tana son tambayarta gobe in sha ALLAHU da wuri zata fita gyaran jiki. Ta samu Ammie akan abin salla tana waya da mijinta, dan haka ta haye gadonta ta kwanta tana saurarenta. Sun jima kafin suyi sallama ta juyo ga Autar tata tana tambayar, “Mi kuma ya faru ƴar shagwaɓar Ammie?”.
Murmushi Maanal ɗin tayi, cikin yanayinta na miskilaye da shagwaɓa ta ce, “Ammie ina son naje gyaran jiki gobe in ALLAH ya kaimu, ban sani ba ko kina da kuɗi. Jibafa yanda jikina duk ya bushe ga kaina sai ƙaiƙayi yake mun”.
“Uhm ko bani da kuɗi auta ai dole na nemosu, ke idan fitinar gyaran jikin nan naki ya tashi ai duk fatarata baƙya raga min”.
Sosai Maanal takema zancen Ammien murmushi. Yayinda Ammien ke kallonta cike da jin daɗi, idan taganta cikin farin ciki haka daɗi take ji, sai ta dinga ganin asalin Maanal ɗinta ta baya sarkin rikici da kwaramniya, amma yanzu duk ta zama sanyi-sanyi ga miskilanci, sam bata son sabon yanayin nata na wannan shekarun, sai dai babu yanda zatai tana mata addu'a. Katse mata murmushin tai da faɗin, “Ke duba wayar nan taki tun ɗazun take haske alamar kira”. Amsa Maanal tayi da faɗin, “Inaga Zezaa ce ko Anees....” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda ganin number mai kiran, dan ko saving batai ba, amma nacinsa yasa tuni ta haddace lambarsa a kanta. Fuska ta ɗan tsuke, har zata maida wayar ta ajiye sai kuma ta dakata, dan tasan shegen nacinsa ba lallai ya