Showing 210001 words to 213000 words out of 221978 words
Chapter 71 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
tunanin kiranku”. Ammie ta faɗa tana kallonsu. Amsa mata duk sukayi da Amin. Maanal ta matsa jikinta ta rungumeta. Kallonta tai da mamaki. “Lafiyarki kuwa Maanal?”.
Fuska ta ɗan ɓata, sai kuma ta kamo hannun Ammie ta ɗora a saman ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta. Kamar zatai kuka ta ce, “Ammie zuciyata ce ke bugawa da sauri, gabana kuma nata faɗuwa. Sai nake jin kamar wani abu babba na kusanto ni”.
Shiru Ammie kawai tai tana kallonta. Itama zuciyar tata na raunana. Dan bata raba ɗayan biyu kasancewar Ajwaad a gidan nan ya sakata jin hakan. Ya rabba wannan wace irin tarayya ce haka?. Amma dai bari tai mata tambaya. Fuskar Maanal ɗin ta shafa, cike da kulawa ta ce, “Dama yana miki haka?”.
Kai ta girgiza ma Ammien tana sake narke mata a jiki. Ammie ta sauke ajiyar zuciya, tare da shafa mata kai ta ce, “Kairan in sha ALLAH kinji my babie”.
Kai ta ɗagama Ammien sannan ta saketa saboda umarnin da Hajiya Majdiya ta basu na ɗaukar abincin da aka shirya su kai sashen Daddy. Manaal da Najma ne a gaba, sai dai Najma ɗin ma ta gota Maanal, dan itace ta fara shiga falon da sallama Maanal biye da bayanta. Da wani irin sauri Najma ce ta tsaya cak tana mai waro idanunta da faɗin, “Lah wa nake gani kamar su Yaya Fawzan da Yaya AA? Abah! Babban Yaya”.
Da wani kalar sauri itama Maanal ɗin ta tsaya, hakama su Amrah duk suka tsaya suna kallon inda Najma ɗin ke kallo, sai ma ta ajiye kular hannunta ta nufi inda suke cike da mamaki da farin ciki. Ba ƙaramin girgiza zuciyar Maanal tayi ba, dan nata idanun akan AA ɗin suka fara sauka. Kamar shima kuma ance ya kalletan sai nasa idanun a kanta. Da sauri ta janye nata zuciyarta na zallo. Cikin ƙarfin hali ta maida su akan Abah da ya furta, “Finaly yau dai gani ga Autan Oum”.
Ƙasa Maanal tayi da kanta tana murmushi, sai kuma ta cigaba da takowa cikin falon ta ajiye kayan hannunta inda su Amrah suka ajiye, gaban Abah taje ta durƙusa, har cikin ranta itama tana jin daɗin ganinsa. Abah ubane da bazata taɓa mantawa ba a rayuwarta. Ya nuna mata dukkan gata da soyayyar da ko ita ɗin a cikin ahalinsa ta fito iyaka kenan. Shiyyasa har gobe shine uba mafi kima da daraja da take kallo a cikin idannunta. Hatta da babu sunan mahaifi kawai yake amsawa a zuciyarta. Amma uba na gaske da bugun ƙirji a nunama duniya Abah ne farko. Cikin rawar murya alamar tahowar kuka ta shiga gaishe shi. Shima a mamakin duk wanda ke'a falon idanun Abahn cike suke da ƙwalla. Amma sai yay jarumtar sakin murmushi tare da kai hannunsa ya kamo nata. Kamar abinda take jira kenan hawayen suka shiga rige-rigen sakkowa.
“My daughter nima so kike nayi kukan?”. Ya faɗa cikin taushin murya da kulawa. Kanta ta girgiza masa. Kafin ta share hawayenta ta ɗago ta ɗan kallesa. Murmushi ya sakar mata, itama sai tayi murmushin. “Abah nayi kewarka matuƙa”. Ta faɗa a hankali. Gefe ya kauda kansa, yasa babban yatsarsa ya ɗauke guntun hawayen daya ciko masa idanu shima. Har cikin ransa yana ƙaunar yarinyar, ɗaukarta yake tamkar yaransa guda uku daya mallaka a duniya. Sake juyowa yayi gareta da murmushin dai. “Nima nayi kewarki Maanal. Bantaɓa kwana na tashi babu ke a zuciyata ba. A kullum ina ji a raina akwai wani giɓi da babu a cikin ƴaƴana. ALLAH yay miki albarka, ya kare rayuwarki, ya azurtaki da farin ciki mara yankewa. Ya rabbi kasa iyakar jarabawar kasancewa a nesa da juna da mukai kenan.”
Jiki a sanyaye kowa dake a falon ya amsa. Yayinda kan AA ke a ƙasa babu mai ganin fuskarsa balle yanayinsa. Gaishe da su su Aneesah sukayi suka fita, sai Najma da Manaal dake gaban Abah suna magana ƙasa-ƙasa da kowa baya ji. Dan hatta Daddy dake a kusa da su baya jin mi suke faɗa. Dai-dai nan Huznah ta shigo hannunta ɗauke da babban basket an shiryo abinci, sai yara biyu biye da ita da kayan ruwa da lemuka. Gaba ɗaya hankalinta akan AA da kansa ke ƙasa har yanzu yana latse-latsen waya. Babu ko kunyar mahaifinta dake a falon kanta tsaye gaban AA ɗin ta nufa ta dire basket ɗin, murya can ƙasa cike da iyayi ta ce, “Barka da zuwa gidanmu Sweetheart”.
Ɗan jimm AA yay zuciyarsa na kai da kawon wai da shi ake ko wa? Ga shi kamar yasan muryar. Sake yin magana da tayi ya sashi ɗagowa a karo na farko, manyan idanunsa da suka ɗan kaɗe ba kamar sanda ya shigo gidan ba da suke fari tas ya zuba mata. Harga ALLAH yayi mamakin ganinta anan ɗin, amma sai ya dake ya wani kalar janye idanunsa ya maida akan wayarsa. Duk da zuciyar tata ta raunana da salon nasa haka ta dake tare da basarwa ta juyo tana kallon sauran mutanen falon. Karon farko gabanta ya faɗi sakamakon saukar idonta akan Abah, ya ALLAH, wlhy batasan harda mahaifinsa ba, ai da ta kama kanta. Ita tsabar ganinsa ya firgitata duk zatonta abokansa ne ma. Zaram ta miƙe daga gaban AA ɗin ta nufi inda Abah yake. Sai da ta watsama Maanal dake mata kallon mamaki harara sannan ta durƙusa cike da girmamawa tana gaishe da Abah. Amsa mata yay cike da kulawa dan kamannin Daddy a bayyane suke gareta. Ya tambayeta sunanta ta gaya masa tana faman sinne kai wai ita taji kunya. Kafin ta juya tana gaishe da su Babban Yaya. Ta gane Fawzan dan haka bayan gaisuwar ta tambayesa ina Oum da Mamy.
Fawzan da al'amarin yarinyar ya ɗaurema kai ya bata amsa cikin dauriya. “Su Oum na tare da Ammie”. Zaram kuwa ta miƙe da faɗin, “Lah ai ban sani ba”. Kafin wani ya samu damar magana har ta fice. Tsabar mamaki daya lulluɓe Daddy ya saka shi suman zaune ya kasa magana. Sai kuma Huznah ɗin na fita Hajiya Basariyya da Maman Yaseerah suka shigo da sallama. Shi Abah ba wani sanin Maman Yaseerah yayi ba, duk da kuwa ƙanwarsa na matsayin kishiyarta. Koda suka gaishesu ya amsa ne da tunanin duka matan Daddy ne, dan kamanin Huznah yafi fitowa a fuskar Hajiya Basariyya. Fuskar Maman Yaseerah da murmushi ta ce, “To wai ni ina surukin namu anan?”.
Karan farko Daddy daya kasa daurewa ya ce, “Suruki kuma?”.
“Eh mana Alhaji. Ai baƙin Huznah ne, nazatama har sun sanar maka, shine muke maka batunsa kwanaki, har mukace ka shirya za'a kawo kuɗi kace a jinkirta a gama na Yazeed ko. Kamar AA naji tana ambatonsa da shi ita Huznahr”.
Wani irin ɗagowa AA yayi ya kalla Hajiya Basariyya mai maganar, yayinda Abah da su Babban Yaya duk suke kallonsa su kuma. Shi ko Daddy Hajiya Basariyya ya zubama idanun kawai. Sai falon yay shiru akama rasa mai iya yin magana. Wani irin takaici ne ya gama turniƙe AA, jiyay bazai iya daurewa ba, dan haka ya buɗe baki a fusace zai yi magana, amma sai Babban Yaya dake kusa da shi ya kama hannunsa ya riƙe. Dole yay shiru, tare da haɗiye maganar. Tsaf Daddy ya lura da abinda ke faruwa. Dan haka a dake ya cema su Hajiya Basariyya, “Okay naji, kuje zasuci abinci tukunna”.
Baki Hajiya Basariyya ta sake buɗewa zatai magana Daddy ya harareta, dole ta haɗiye. Suna fitowa Maman Yaseerah ta ce, “Kada ki wani damu shirin nan namu fa ya hau, kin san Malam akwai iya tsara abu”.
“Anya kuwa Aminiya, kina ganin yanda yaron ke kallon mutane babu ɗigon sassauci, wlhy sai yanzu na fahimci abinda Huznah ke sanar min a kansa. Lallai da ganinsa zai yi baƙin taurin kai.”
“Karki wani damu da taurin kansa, zamu bi dashi ne tsaf ya mata biyayya kamar babu gobe. Yanzu dai kawai muyi yaƙin shigarta gidan. Ammafa ni ina mamakin munene alaƙarsu da Asiya ne haka wai?”.
“Nima wlhy ina son sanin wannan dangantar, amma ki bari, akwai ta hanyar da zan bincika”.
★A ɓangaren Huznah ma tana can sashen Ammie, hatta Mamy tayi mamakin ganinta, amma sai ta basar. Cike da ladabin daya bama Ammie da su Amaal mamaki take gaishesu, sai wani sissinkuy da kai take. Ita Oum ma bata wani maida hankali a kanta ba, hirarsu suke da Maanal dake jikinta kwance. Dan itama tun shigar su Hajiya Basariyya falon Daddy ta baro can.
Saheeba dai da Nibras harara suketa antayama Huznah a kaikaice, dama kuma basu tanka ba koda tai gaisuwa. Bayan ficewarta cike da takaici Huznah tai tsaki da faɗin, “Ya akai tasan nan? Ko biyomu tayi ne? Nifa ban san ballagazanci wlhy. Yo ko mata sun ƙare mi Yaya Ajwaad zai yi da ita, balle ma yanada matarsa a hannu. Ai wlhy inaga sai Nuratu ta sake mata wani sabon zanen a fuska zata kiyayi mata saurayi”.
Da mamaki Oum ta ce, “Ban gane ba, ke ina kika san wannan ɗin Saheeba?”.
Batare da Saheeba ta kula kallon gargaɗin da Mamy ke mata ba ta ce, “Oum itace fa wadda sukai faɗa akan Yaya Ajwaad da Nuratu a Abuja”.
“Ikon ALLAH, ai ni ban ganeta ba sam wlhy. To ya akai tasan nan ɗin?”.
Amaal da Shaheeda da Ammie mamaki ya gama kashesu, Maanal kam yi tai kamar bata ji mi suke tattaunawa ba. Sai ma karanta saƙon da ya shigo mata a waya take wanda AA ne kuma ya turoshi akan tazo, amma ta masa reply da a (anƙi ɗin). Amaal ce ta bama Oum amsa da, “Oum ai anan gidan take, ɗiyar matar tsakkiyar gidan nan ce”.
“Oh shiyyasa na ganta a gidan Shahidah kenan. To ALLAH ya rufa mana asiri ”.
Da Amin kowa ya amsa aka saki zancen. Bayan sun kammala cin abinci ne Ammie da Oum da Hajiya Majdiya da Mamy sai Amaal, Shahidah da Maanal suka nufi sashen Daddy da yay kiran Ammie a waya. Sun samu suma sun kammala cin abinci, dan haka akai zaman gaisawa cike da mutunta juna. Abah nata tsokanar su Amaal. Dan yanda sukai jiki suka zama manyan mata ya bashi mamaki. Hakama yaransu da su Waleed duk suna zagaye da shi yanata sanya musu albarka da musu wasan jika da kaka. Sai da ya gama tsokanarsu yaran suka fito suka bar su Ammie can. Da wannan damar Abah yay amfani wajen bama Ammie haƙuri da neman gafararta akan abinda ya faru a baya. Ya ɗora da faɗin,..........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenm
u 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣2️⃣
______________
........“Nasan zakuyita mamaki akan rashin bin bayanku da bamuyi ba a wancan lokacin, a randa kuka wuce a ranar Fateema jikinta ya rikice matuƙa, dan yanke jiki tai ta faɗi, dole muka wuce da ita asibiti, amma sai suka turomu Abuja dan al'amarin nata banbane, paralysis na neman kamata. Tashin hankali yasa bamu tsaya Abujan ba kawai muka fara shirin fita da ita waje da tunanin bazamu daɗe ba zamu dawo sannan gwaggo ta huce, ashe wasa farin girki, dan shima Ajwaad sai ciwo mai ban tashin hankali ya samesa, ga depression. A haka suna cikin jiyyar su duka biyun Fateema ta matsa ni da Fadeel muka taho Nigeria domin ku, kai tsaye kuma Giro muka nufa, amma sai muka samu cewar wai ai suma sun wayi gari kun gudu, kuma an sanar dasu a majiya mai ƙarfi kuna dangin mamanki ba kuma a ƙasar suke ba. Bamu da wani dalilin ƙin yarda da su, dan haka muka juya muka koma. Amma Fateema naji tace ƙaryane, baki da wani dangi a ƙetaran Nigeria, ta sake tada hankalinta har takai jikinta dana Ajwaad yayi rikicewa mai ban tsoro, dan Ajwaad akwai daren da ma har mun gama yarda ya rasu, sai kuma ya farfaɗo gabannin asuba. Sai da akaita tausarta tare da mata alƙawarin a hankali zanta bincikenku sannan, muka maida hankali akan Ajwaad kuma. A lokacin ne kuma aka bani ambassador, shiyyasa bamu dawo Nigeria ba, amma inata ƙoƙarina batare data sani ba akan neman ku. Sai dai kuma ALLAH bai ƙaddara ba sai a dalilin samuwar aikin Maanal a kamfanin Ajwaad ta dalilin Rafeeq. Dan ALLAH mu yafi juna Asiya, mu ɗauka dukkan abinda ya faru ƙaddararmu ce babu mai canjata. Mu dawo da zumincinmu tamkar a baya can.”
Hawayen dake gudu a fuskarta Ammie ta share. Ta ce, “Babu komai Yaya komai ya wuce. Ni dama ban taɓa ƙullatarku ba wlhy. Sannan ban san ma Maanal a ina take aiki ba dan basu sanar min ba. Da tun kafin kuzo nan ma nice zanzo gareku, ban dan Rafeeq nada alaƙa da ku ba shi da Maman Najma. ALLAH ne kuma bai ƙaddara haɗuwar tamu ba shiyyasa, tunda gamu tare da Majdiya fin shekara huɗu”.
“Ikon ALLAH ai yafi gaban wasa. Wannan wata hikima ce ga UBANGIJI mai ɓoye al'amura ta yanda yaso, a kuma inda yaso. Shi kuma yasan dalilin yin hakan garemu”..
Haka ne. Kowa ya faɗa cikin jinjina kai....
_________★
Da yamma sosai su Abah sukai shirin wucewa, sai dai fa Oum tace suje ita sai gobe in sha ALLAHU. Jin haka AA yace shima ya fasa, ƙafar babarsa ƙafarsa. Wani irin takaici ne ya turniƙe zuciyar Mamy, dan haka kawai take ji a ranta wani abun Oum ke son ƙullawa. Sai kawai catai ai itama kuwa tana nan ɗin. Sam babu wanda ya kawo komai a ransa a tsakanin Oum da Ammie, sai AA ne yay wani iri. Daga baya kuma yace to kawai shi bari ya bisu. Yana ganin hararar da Mamy ke masa amma ya basar. Nibras kam wani sanyi taji a ranta, dan har hankalinta ya tashi da zaman AA a tsakiyar kuraye biyu da take kallo. Wato Maanal da Huzna😂, yayinda Huznah da keta dama-dama da AA ɗin taji kamar tayi kuka. Haka dai babu yanda ta iya suka wuce. Dama Maanal ko'a kwalar rigarta, sai ma hirarsu suke da Fawzan....
Da daddare akai gagarumar dinner ɗin datai tsawa da amsa kuwa a garin na Kaduna kamar yanda su Hajiya Sabuwa sukai fata. Yau ma su Ammie sunje, kuma harda Maanal. Inda rigima taso tashi a hall ɗin, saboda matsawar Hajiya Majdiya Maanal da su Shahidah sukaje yima amarya da ango liƙi. Aiko Yaya Yazeed ba kunya Maanal na liƙa musu kuɗi yana liƙa mata, sai kawai abokansa ƴan neman magana suka taso suka rufe Maanal da liƙi aka daina liƙama amarya. Nanfa masifa ta tashi, Aunty Sabuwa da Hajiya Yaya suka miƙe zuwa wajen. Wani kalar fisga da Hajiya Yaya taima Maanal kaɗan ya rage tai muguwar faɗuwa ALLAH ya taƙaita Yaya Yazeed ya tareta. Wayyo ina wuta su saka Maanal, nan fa ƙannen Yazeed sukai ma Maanal zobe wai zasu daketa, sai da Oum ta shigo tsakkiyarsu cikin ɓacin rai ta janye Maanal ɗin dan daga ita har Mamy sun halarci dinner ɗin suma. Gaba ɗaya suka bar hall ɗin banda Mamy data maƙale, dan dama damar hakan take buƙata na keɓewa da Hajiya Basariyya....
Abu kamar wasa tun a daren ƙawayen amarya da ƙannen Yazeed suka dinga posting hotunan Maanal a media suna faɗin maganar banza a kanta. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa abu yayta yawo. Kafin wayewar gari al'amari ya zama babba, dan tunda ahalin su Hajiya Yaya suka dawo daga wajen dinner sabon rikici ya dake ɓalle. Ga amarya an kawo amma bata batunta ake ba. Wannan tashin hankali ya saka Maanal ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzaɓi. Dole da safe Nene tai shirin wucewa da ita gidanta. Saboda wannan rikici ya zama wani babban al'amari daya bama kowa mamaki, wato zancen fyaɗe da akaima Maanal sai gashi a bakunan mutane harma da Media dangin Hajiya Yaya na gorantama Ammie da Maanal. Matuƙar tashin hankali Ammie da su Amaal da su Oum sun shiga, dan sun rasa daga ina wannan magana ta fita. Sirrine da babu wanda ya sanshi a gidan daga Daddy sai Yazeed. Ai sai fa jikin Maanal yay bala'in birkicewa, abinda ake gudun dai ya nema kaiwa ga faruwa, sai da akai gaggawar kiran likitanta abokin Yaya Yazeed dake anan cikin Kaduna..
Wannan fitina ba'a samu kwantawarta ba sai da Baban su Hajiya Yaya yazo gidan da kansa. Shine fa yay musu kaca-kaca yace kuma biki ya tashi kowa ya shirya ya koma inda ya fito tunda amarya ta shiga ɗakinta. Sauran shagali kuma ya soke su, wanda kuma yake ganin bai isa ba zai yi ga fili ga mai doki. Hakan ya ƙara baƙanta ran Hajiya Yaya da Aunty Sabuwa, sai dai babu yanda kuma suka iya..
Wannan masifa ta bama Oum mamaki, kishi kamar bala'i, ai sai taji ta sake ƙaunar Mamy a ranta. Ta kuma sake jin girmanta da kimarta, dan su dai irin wannan masifa basu taɓa shigar koda kwatankwacinta ba. (Nace Humm Oum ai gara irin su