Showing 15001 words to 18000 words out of 221978 words

Chapter 6 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

barka da gida sai kace wasu sa'oinki?”.
Cikin sake hasala Hajiya Yaya ta ce, “Kinga da yawa ai, idan batai iyayi ba ai bata cika jinin Asiya ba, Amma wai a haka Alhaji ke neman ƙaƙabama jinina ita”.
“Humm kar kiga laifinsa wlhy Yaya, tunda uwarta ta shanyesa kina ganin shima Yazeed ɗin zasu barsa ne. Balle suna ganinsa shine gidan da uban gaba ɗaya”. ta faɗa tana mai ballama Maanal wata shegiyar harara.
Tsamm Maanal ta miƙe kafin Hajiya Yaya ta bama ƙanwar tata amsa. Cikin ɗan sassarfa tabar wajen tana mai jin ɗaci da ciwo sosai a zuciyarta game da cin mutuncinsu ga Ammien ta. Tarasa mi Ammie ta tsare musu a gidan da su duka basa ƙaunarta...


Shikam Yazeed tana fita ya kife kansa a saman steering yana mai cije bakinsa da masifar ƙarfi. Kai bazai yiwu ba, dolene ya zigirgiɗi Daddy azo ayita ta ƙare a bashi matarsa. Dan gaskiya yana cikin tashin hankali, da yasan ma abinda gyaran jikin nan zai zame masa yanzun nan daya hana yarinyar nan yinsa ko kuma yaƙi komawa ɗakkota. Ɗan buga glass ɗin saitinsa da akai da ɗan ƙarfi ya sashi ɗagowa. Sai da ya ɗan saisaita kansa kafin ya sauke glass ɗin. Da Hajiya Yaya yaci karo, ai da sauri ya janye idanunsa da sukai wani irin kaɗawar da duk mai hankali idan ya kallesa zai fahimci halin da yake ciki. Ita kanta Hajiya Yayan sai da taji wani iri a ranta, amma ta dake cikin masifa ta ce, “Yazeed miye haɗinka da waccan yarinyar? A ina ka ɗakkota?”.
Ɗan gyaran muryarsa data koma can ƙasa yayi, kafin ya furta, “Mamma anan ƙofar gida ne mai napep ya ajiyeta shine nace ta shigo na ƙaraso ciki da ita. Wani abu ne ya faru?”.
Wata hararar bana son rainin wayo ta balla masa. Kafin cikin masifarta ta furta, “Yazeed! Yazeed wlhy ka kiyayen, ni zaka maida sakarai ko....”
“No Mamma ba hak....”
Hannu ta ɗaga masa cikin tsawa, “Bana son ji, ka sameni ciki yanzun nan”. Tana gama faɗa ta juya ta bar wajen. Iska mai kauri ya furzar daga bakinsa tare da sake maida kansa jikin steering yana mai lumshe idanunsa. Yafi mintuna biyar a haka sannan ya buɗe motar ya fita yana mai saka glass a idanunsa domin ɓoye abinda ke cikinsu. A falo ya sami mahaifiyar tasa da ƴar uwarta. Cikin girmamawa ya gaida innar tasa dake wani binsa da kallon ƙurilla kamar mai son gano halin da yake a ciki batare data amsa masa gaisuwarsa ba ta ce, “Yazeed! Anya kuwa kana son nemawa mahaifiyarka mutunci damu ƴan uwanta a gidan nan. Wai kai bazaka bar batun yarinyar nan ba ne shin ko yaya kake nufi?”.
Sai da ya ɗan haɗiye abinda ke masa yawo a maƙoshi sannan ya furta, “Aunty Please mun wuce maganar nan fa tuni. Dan ALLAH a barta kawai”.
“Anƙi a bari ɗin dan ubanka. Yazeed ni dai kake son cigaba da tozartawa ko? Ni dai mahaifiyarka dana sha baƙar wahalar rainon ciki ka da naƙudar haihuwarka da shayar da kai. Asiya dai ta fini muhimmanci a wajenka ko? Shike nan kaje kayi duk abinda kake ganin dai-dai ne agareka. Amma ka sani ko mutuwa nayi kurwata bazata barka zaman aure da yarinyar can ba. Dan na riga na maka mata kamar yanda na faɗa maka. Garama ka shirya tun kafin takaimu da bakanta a cikin gidan nan. Amma bari shi Alhajin dake ɗaure maka ƙugu ya dawo gidan ina dai-dai dashi wlhy”.
Kasa iya furta komai Yazeed yayi, sai wani irin haɗiyar zuciya yake acan ƙasan ransa dan mutum ne mai zuciyar tsiya dama. Haka suka cigaba da masa masifa bai iya sake cemusu komai ba har sai da ALLAH ya taimakesa Daddy yay kiran wayarsa sannan ya tashi ya fita domin amsawa. Daga haka bai koma wajen su ba ya gudu sashensa dan ya shirya gashi har yana neman makara....


________


A ɓangaren Manaal bata sanarma Ammie komai ba. Sai ma ƴan uwanta ne da suka zagayeta suna yaba irin ƙyawun da gyaran yay mata. Daga haka Ammie ta korata dan ta shirya kada su makara. Saboda tasanta da nauyin shiri. Aiko bata kammala shirin ba sai da Ammie tai mata tsiya-tsiya. Faɗan Ammien yasa ta fito ɗauko da ɗan box ɗin da take ajiye kayan ƴan kunne da makamantansu ciki a hannu tana neman agogon da zata saka da zobe. Su Amal ne dake musu dariya suka amsa suna duba mata. Dai-dai fitowar Ammie tana faɗin, “K muje ai ba dole sai kinsa wani agogo can ba bana son shiririta”.
Jin hakan ya sata miƙewa dan tasan kaɗan daga aikin Ammien ta maketa ma saboda bata ƙaunar jira, da sauri Shahidah da takamo hannunta ta ɗaura mata wanda ta zaro kalar silba kawai ta shiga ɗaura mata batare da su duka sun maida hankali akansa ba. Daga haka suka fice hannunta riƙe da ƴar bag ɗinta sai gwangwanin maltina data ɗauka saboda yunwan da take ji kasancewar bawani break ɗin kirki tayi ba ta fita gyaran jikin, yanzu kuma Ammie tace bazata zauna cin abinci ba aiba itace ta hanata ci ɗazun ba sai dai ta bari idan sunje gidan bikin taci. Itako tasan bazata taɓa iyawa ba cin abinci a gidan biki koda na wanda ta sani ne balle wannan, duk da kamar gidane can ɗin ma saboda alaƙar dake tsakanin mai gidan da uban amaryar mai matuƙar ƙarfi ce, ta wani gefen ma za'a iya cewa akwai zuminci. Koda yake su sai dai suyi kara saboda Ammie kawai amatsayinsu na ƴaƴanta...........✍️




✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖0️⃣9️⃣




______________




Lady's collection and more


Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko


08169307477


Address bayan gidan drugs katsina State. Kayanmu nada inganci da zasu birge mai saye fiye da yanda yake zato. Maza ku garzayo kada ayi babu ku.


_______________




.........Tunda suka fito ya zuba mata ido daga inda yake tsaye jikin mota. Itakam sam bata lura da shi ba tana ta ƙoƙarin gyara kayan data zubo a handbag ɗinta dataƙi rufuwa. Sai da suka iso gab da shi ta tsinkayi muryarsa yana gaida Ammie. Yayinda Amrah ta taɓota itama tana gaida Ammien. Ɗagowa tai ta dubi Amrah ɗin, suka sakarma juna murmushi, harta maida kanta sai kuma ta ɗan ɗago dan sai yanzu hankalinta ya kai garesa sosai. A take ta shanye murmushin saman fuskarta ziciyarta na takurewa waje ɗaya a ƙirjinta. Tabbas da tasan tafiyar nan tare zata kasance musu ALLAH duk yanda zatai da sai tayi ta zame kanta a masu yinta. Amma yanzu babu yanda ta iya dole ta dake. Ganin su Ammie sun shige itama ta fara ƙoƙarin shiga kusa da su amma sai Amrah tai saurin rufe murfin tana faɗin, “Kije wajen Yaya mana gashi can ya buɗe miki”.
Tsaye tai kawai tama gagara cewa komai, koda ta saci kallon Ammie sai taga ta ɗan harareta, dole ta shiga kusa da shi ɗin tana faman sauke ajiyar zuciya. Ɗan karkatowa yay inda take kaɗan kamar zai ɗauka abu a ƙasan ƙafafunsu. Cikin raɗa ya furta, “You look so good dear”. Kasa cemasa komai tayi, sai ma takurewa data ɗanyi jikin kujerar, yayinda shi kuma ya ɗaga yana gyara zamansa tamkar bashi yay maganar ba dan fuskarsa sam babu wani walwalan kirki.
Sun fara tafiya shiru motar babu mai magana. Sai da suna gab da barin titin anguwar gaba ɗaya kamar ance ta kalla hannunta idanunta suka sauka akan agogon da Didi Shahidah ta ɗaura mata. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yay ba har kana iya ganin yanda maƙoshinta ke kaiwa da komawa a wuyanta. Ta ƙurama agogon ido wani abu mai shegen nauyi na sake saukar mata a dukkan illahirin jikinta. Bata masan wani ƙarfi yazo mata ba tasa ɗayan hannunta ta fincike agogon, kamar zatai wurgi da shi waje sai kuma ta daure ta ɓalle bag ɗinta ta jefashi ciki batare data zuge zip ɗin ba ta maida kanta ta nannaɗe cikin ƙafafunta data ɗage gaba ɗaya zuwa saman kujerar. A take wasu hawaye masu zafin gaske da raɗaɗi suka fara zirara mata. Yanda tayi ɗin sai sukai tunanin ko barci take, musamman Ammie da tasan bawani barcin kirki ta samu ba a safiyar yau dama daren. Shima Yazeed daya ɗauka barcin tayi sai kawai ya farama Ammie hira. A haka har suka iso Zaria kasancewar tafiyar ba wata mai yawa bace ba. Da yake Yazeed yasan hanya basu wani sha wahala ba nan ma suka iso. Sun sami anguwar kanta da mutane sosai balle ƙofar gidan daya kasance masha ALLAH dan har Ammie na faɗin, “Anya Yazeed zamu iya keta mutanen nan zuwa cikin gidan kuwa?”.
Amsa ya bata da faɗin, “Ammie zaku iya shiyyasa ma nai parking tanan ganin yafi ƙarancin mutane. Zan bidaku ta baya ne akwai wata ƙofa dana sani Uncle na amfani da ita nasan zata kasance buɗe yau kodan baƙinsa”.
Cikin gamsuwa Ammie ta ce, “To Alhamdullah hakan ma yayi”.
Sun firfito yayinda a kallo ɗaya Ammie ta fahimci Manaal tayi kuka duk da gilashin dake a idonta. Sai dai ta fassara kukan nata da zaman gaba da aka sakata yi ne dole. Dan haka ta watsar da ita tama haɗe fuska. A wannan yanayin suka shiga gidan ta inda Yazeed ɗin ya faɗa. Aiko sai suka samu sauƙi jama'a anan sai falon Uncle ɗin ne ma da mutane dan akwai takalma kusan ƙafa bakwai a wajen masu ƙyau. Wucewarsu sukai zuwa cikin gida dan itama Ammien ba wannan ne zuwanta na farko ba. Hakama Amrah. Maanal ce dai bata taɓa zuwa ba dama sai yau ɗin. Amma ta ɗan san yaran gidan saboda suna zuwa can gidan nasu lokaci-lokaci...


★-----------


Babu jimawa da shigewar su Maanal tawagar ango da abokansa suka iso ƙofar gidan. Cikin tsari da nutsuwa tarin motocinsu suka layantu dai-dai inda Yaya Yazeed yay parking motarsa. Firfitowa duk suka shiga yi, kowa ka kalla shar da shi cikin dakakken yadi mai shegen ƙyau da tsada, wasu kuma shaddoji. Sai shima ango dake sanye da shadda fara ƙal tanata maiƙo da ɗaukar idanu. Sun gama firfitowa sai motar dake kusa data Yazeed ce kawai wanda ke ciki baida alamar fitowar, sai da angon ya juya yana ɗan kalle-kalle da faɗin, “Wai Uncle fa?”.
Duk motar suka kalla. Kafin wani a cikin abokan yace, “Bai kai ga fitowa ba kamar ma suna magana ne da Uncle Nass”.
“Oh ai fa an haɗu. Ni dai suyi su fito kar a fara neman waliyyai aga duk basa kusa. Bara ma na taɓa su Uncle Fawzan suma”.
Dariya abokan nasa suka sanya masa da shaƙiyanci. Yayinda yay gefe yana dariya. Wanda dai ya ambata da Uncles basu fito a motar ba sai kusan bayan mintuna talatin, suma ɗin dai ba tsoffi bane, matasane da shekarunsu ya haura talatin kaɗan, ɗaya ma zai iya girman ɗayan. Wanda bai kai shekarun ba dake sanye cikin yadi milk ne ya fito ta sashen da motar Yazeed take. Ɗan jingina yay da motar yana amsa waya kansa a sunkuye ta yanda ko fuskarsa ba'a wani gani da ƙyau. Yaci fin mintuna biyu a haka kafin ya katse wayar yana mai kai wa duƙe ya ɗauki abinda idonsa ya sauka a kai tun fitowarsa dake yashe a ƙasa. Agogo ne silver na mata mai ƙyau sosai, juyawa yay ya kalla motar daya jingina batare da yayima agogon wani kallon tsaf ba. Har ya kai hannu zai aza agogon saman motar da tunanin maybe masu motar ne suka yadda sai kuma ya fasa. Tunanin ajiyewa yay a hannunsa dan maybe su haɗu da masu motar sai ya basu, kada ya ajiye kuma wani ya ɗauka dan a ɗan kallon fisha da yay ma agogon ya fahimci mai daraja ne da za'a iya sayensa da kuɗi masu yawa. Motar da suka fito ya buɗe ya jefa agogon sit ɗin mai zaman banza daya zauna dan ɗayan ne yayo driving ɗin. Daga haka ya juya abinsa kawai....


______________★


Duk da yawan taron jama'a bai hana ai musu tarba ta musamman ba da girmamawa da mutuntawa. Dan can ƙuryar ɗakin amaryar gidan aka kaisu tare da musu sauka ta musamman da abinci da kayan ciye-ciye irin na biki. Sai nan nan Hajiya Majdiya keyi da Ammie dan tuntuni take son su jone su zama ƙawaye Ammien ce dai bata maida hankali ba. Ita kuma ba komai yasa hakan ba sai sanin uwargidanta jone suke da Hajiya Yaya 5&6, ko bikin nan ma dan na yarinyar matar tsakkiya ce shiyyasa Hajiya Yayan bata zo ba saboda suna matuƙar adawa da juna. Ita kuma aminiyar Hajiya Basariyya ce dan ita tun sassafe ma tana nan Zaria ɗin da duka yaranta kuma kwana zasuyi dan har Abuja inda za'akai amarya zasuje ma.
Ƙorafin da take tayi yasa Ammie bama su Maanal umarnin cin abincin. Amrah ce ta zuba ma Ammie sannan ta zuba musu. Maanal na cewa ta ƙoshi Hajiya Majdiya tace, “Haba ɗiyata kada kimin haka mana, idan kuma baƙya sonshi na canjo miki wani ko na dafo miki yanzun nan”.
Da sauri ta ɗauki spoon ta saka cikin abincin, hakan ya saka Amra kwashewa da dariya. Sunci abincin Ammie da Hajiya Majdiya na hira sai ga wata budurwar yarinya ta shigo ɗakin. Zasu iya zama sa'anni dasu Maanal, tayi ƙyau cikin lass da nake ƙyautata zaton ankonsu kenan dan ƴammata da yawa na dashi a wajen bikin. Tafawa suka ɗan yi da Amrah alamar sun san juna sosai sai kuma ta ɗan zunguri Maanal cike da tsokana ta furta, “Kurman Ammie”. Hararta Maanal ta ɗan yi duk da ba wani sabo sukai ba gaskiya, dan ko gidan sukaje iyakar Maanal ɗin da su gaisuwa ne. Cikin dariyar da suke ta gaida Ammie, yayinda Amrah ke faɗin, “Amma fa sunan nan ya dace da ita sosai, Najwa kin iya saka suna ALLAH”.
Dariya Ammie da Hajiya Majdiya suka sake yi. Nan dai suka cigaba da tsokanar Maanal ita da Amrahn. Bayan sun tsagaita ta dubi Maman nata tana faɗin, “Ummy Uncle Rafeeq fa ya iso”.
“Oh Masha ALLAH har ya ƙaraso, da'alama gudun nashi na tsiya yayi kenan. Yana ina?”.
“Na kaisa ƙaramin falonki wai yunwa yake ji, sai yaci abinci zai fita wajen ɗaurin aure”.
Ƴar dariya tai da faɗin, “Acici kenan mala'ikun tauna. Ga key dama na haɗa masa abincin ai. Idan kin ɗauka ki rufe min kitchen ɗin, sai ya gama sai nazo mu gaisa”.
Amsa tai tana miƙewa, sai kuma ta kalli su Amrah, “Ku taso muje kunzo kun ƙunshe a nan. Amrah karfa ki bari Maanal ta koya miki halinta”.
Da sauri Amra ta ce, “Da naga takaina. Maanal fa ko maijego bazata faɗa mata zaman ɗaki ba, magana kuwa yakan iya sati batayi da kowa ba”.
Hararar su Maanal tayi batare data motsa ba ko yin magana. Ganin haka suka fahimci bazanje ba. Dan haka Najma tai saurin kai ƙararta wajen Ammie. “Ammie kinga wai bazata ba”.
Kallon Maanal Ammie tayi dole ta miƙe badan taso ba suka fita. Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauka basket ɗin da aka shirya kayan abincin sanan suka bi wani ƙofa, roƙonsu take akan suje kai amarya Abuja dan ALLAH. Yayinda Amrah ke bata amsa da basuzo da wasu kaya ba. Dai-dai zasu shiga take cewa baga nata kayan ba tasan zasu musu ai, kokuma idan zasu wuce Abujan su tsaya kd ɗin su ɗauki kayan. Shigarsu tasa babu wanda ya bata amsa. Falone ƙarami amma yayi ƙyau sosai cikin tsari.
“I'm sorry Uncle na barka kana jira”. Ta faɗa dai-dai tana ƙarasawa gaban mutumin dake zaune ya ɗan juya ma ƙofa baya ta yanda basa ganin fuskarsa da ƙyau. Juyowa yay ya kallo ta inda suke cikin sigar harara, sai idanunsa cikin na Maanal.
Cak kuwa ta tsaya kamar wadda aka buge mata ƙafafu da sanda, hakama numfashinta sai da yay rawa. Shima ɗin da wani kalar mamaki ya zuba mata idanunsa har yana ɗan warosu waje na kasa ɓoye mamaki. Sai yanda yay ɗin ya saka su Amrah kallon Maanal ɗin suma cike da tambayoyi.
Lips ɗinsa ne suka ɗan motsa a hankali ya faɗi abinda ita da su duk basu ji ba. Yayinda Najma ta furta, “Uncle ko ka sansu ne?”.
Maimakon amsa mata sai ya saki wani ƙayataccen murmushi kawai da kai hannu ya ɗan shafo sajensa siriri yana lumshe idanu da kauda kansa gefe. Itama Maanal janye nata idanun tayi a hankali daga garesa, sai kuma ta juya da nufin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login