Showing 21001 words to 24000 words out of 221978 words
Chapter 8 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
ƴan uwanta zagaye da ita. Hakkanne ya sake ƙarfafata zuwa bayan la'asar tace suje ta rakasu gidan mai gyaran jikin zata iya. Koda sukace a'a sai Ammie tace suje ai fitar zata saka ta sake jin ƙarfin jikinta ta kuma warware. Da wannan shawarar sukai amfani suka tafi........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣1️⃣
______________
Abubuwan da nake saidawa
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
_________
.........Fitarsu babu jimawa ashe masifar Hajiya Yaya ta jiya bata ƙare ba. Dan yau yinin nan guda bata gidan, sai yanzu zuwa yamma sai gata ita da ƙanwarta da suke kira Aunty Sabuwa a gida da yaranta ƴammata guda biyu. Nan fa wata sabuwar fitinar ta tashi dan har sashen Ammie suka sameta wai sun sake zuwa mata gargaɗi ita da Maanal akan Yazeed. Yayinda aka nuna ƙaramar ƴar Aunty Sabuwar wai itace Yazeed zai aura dan haka sai Maanal da Ammie su maida maitarsu a kansa. Ba ƙaramin zafi kalaman sukaima Ammie ba. Ga shi lokacin su Manaal ma basa gidan taje raka su Shahidah gidan mai gyaran jikin da za'ai musu. A yanzun kam kasa daurewa Ammie tai ta yayyaɓa musu magana. Fuskarta kuma ɗauke da murmushin da yake ƙona zuciyarsu ta kalli Sabuwa mai kora bayanin..
“ALLAH sarki ai mu wannan abin farin cikinmu ne Sabuwa. Ina kuma taya Yazeed murna da fatan alkairi dan ko bai auri Maanal ba har gobe ɗa yake a gareni tunda ina auren mahaifinsa. Daga ke har Yaya kuma ku daina ɗagama kanku hankali akan Maanal, dan ita dama sam bata buƙatar wannan haɗin, ta karɓa ne kawai dan maida alkairi da hallaci. Har miye abin kace nace da ɓacin rai akan abinda ALLAH ne maiyi kawai. Wani rabon zafi ne da shi musamman ma na aure, idan aka tsananta sai ya kawar da rayuwa kuma ayi abinda ba'a son a bayan ran masu adawar”.
“Oh kina nufin zaki kawar damu kenan ki aurama Yazeed ƴar ki?”.
Hajiya Yaya da kalaman Ammie suka shige ta ta faɗa a hargitse. Murmushin Ammie ta sake yi da faɗin, “Rayuwa da mutuwa ai na ALLAH ne kawai Hajiya. Ina fargar da kune dan ikon ALLAH yafi gaban wasa, ku daina matsawa da yawa dan ALLAH”.
Wannan fa kalamai na Ammie sune suka sake tunzura wutar wannan harmutsi. Dan takai har Hajiya Yaya na iƙirarin maka Ammie a kotu wai tace zata kashe su ta aurama Yazeed ƴarta. Haka ta kira maigidan tana zazzaga masifa. Ta gama ta fice zuwa gidansu ita da ƴar uwarta suka sanar da mahaifinsu. Lokacin da su Manaal suka dawo gidan sun tadda komai a hargitse matuƙa. Ga su Hajiya Basariyya ƴan biki sun dawo daga Abuja ita da yaranta. Aiko ta shiga tai kane-kane tana ƙarama wutar fetur a bayan fage. A yau kam Maanal data jima da mutuwa mai rashin ragi ga duk wanda ya taɓata sai gata ta dawo. Wani irin ɓacin rai ya rufe idanunta. Cikin razananniyar tsawa ta ce, “Kai haba ya isa haka mana. Nace ya isa!! Ya isa!!!. Wai shi Yazeed ɗin anyisa da gold ne ko diamond ko tagulla ko azurfa ne? Ko na taɓa ce muku dama ina son aurensa ne? Gashi nan ku tambayesa ko sau ɗaya nata amsa masa ina son sa? Shin Yazeed na taɓa cewa ina sonka? Ka faɗa musu mana ko zasu kama kawunansu. Ni nan da kuke ganina bama Yazeed ba kowanne namiji bana buƙata, domin Manaal ta jima da amincewa zata rayu a matsayinta na MACE kawai batare da kowanne NAMIJI ba takowanne fanni. Kun taɓa ganin wanda ya mutu yana son kasancewa da rayayye? Mi matacce zaiyi da rayayye? Ko shi rayayyen mi zaiyi da matacce?. Dan haka idan kunso ku aurama Yazeed mata huɗu a rana ɗaya ko duka matan duniya shine zaku birgeni ko kanku dan ALLAH, damuwarku ce wannan. Ku daina fakewa da maganar Yazeed kuna cin zarafin Ammien mu, idan ba haka ba wlhy wlhy zakuga ainahin Maanal kuwa. Dan kaf ɗinku sai kunsha matuƙar mamaki ba tsoro yasa ake ƙyaleku ba girmama kaine da darajar shi Yazeed ɗin da Daddy. Saboda ina girmama waɗan nan mutanen guda biyu a cikin TARIHINA. Zan iya ce muku sune suka saka zuciyata banbanta sunan MAZA daga jam'in da nai musu. Amma tunda kunce ku baku san kawaici ba kumuje zuwa daga yau a gidan nan ni daku ɗan halak ka fasa. Na fiku iy.....”
“Manaal!!”.
Ammie ta faɗa cikin tsawa tana ƙoƙarin riƙota. Kanta ta shiga girgizawa sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tana cigaba da faɗin, “Ammie ki barni na gaji, nagaji haka nan Ammie. Mi mukayima rayuwa ne? Mi muka tare musu ne? Mi mukayi musu da zafi haka da kowa ke son ganin ya wulaƙanta rayuwarmu, na taɓa ce musu bazan rayuwu ba sai da wani NAMIJI ne Ammie?. Basa tunanin kafin su ina dake ba! Basa tunanin ba dole bane sai mace ta rayu da namiji zata amsa sunan mace? Basa tunanin na haƙura da wanda ma yay sanadin kawoni wannan duniyar bisa izinin UBANGIJI balle su, su ɗin nan da ba komai ba a rayuwata. Su ɗin nan da zan iya canjawa da ire-irensu a duk lokacin da naso. A tunaninsu dole-dole sai da sune zan RAYU?! Ko babu su zan rayu Ammie, zan rayu dake kaɗai da ƴan uwana kun isheni, kun wadatar dani a wannan rayuwar, bana buƙatar kowanne namiji, suje, suje ban buƙatarsu.....” kuka ya sarƙe ta sai tari. Ɓull!!! Ɓull!! Jini ya dinga ambulowa ta bakinta ta hanci.
Wani irin firgitaccen kukan tashin hankali Ammie ta saki jikinta dake riƙe dana Maanal na rawa. Tuni Shahidah, Manaal da Yazeed sun yo kansu a ɗari. Su kansu su Hajiya Yaya da tawagarta da sauran jama'ar gidan al'amarin ya matuƙar firgitasu. Dan a wai-wai suke jin Maanal nada matsalar ciwo mai haɗari, amma basu taɓa ganinta a ciwon ba, kai zasu ma iya rantsuwa basu taɓa ganin ana aman jini ba sai yau musamman wannan da takeyi ta baki ta hanci.
Kowa ya rikice an rasa mai cewa a tafi asibiti. Sai baba maigadi ne daya iso wajen a hargitse yake faɗin asibiti ya kamata a tafi. Da wannan magana tashi suka zabura gaba ɗaya. Cak Yazeed ya ɗauki Maanal daketa aman jini ya nufi hanyar gate a maimakon motocin gidan saboda tsabar yanda ya rikice. Shahidah, Amal, Ammie suka take masa baya sai Amara da itama ta zabura ta bisu tana kuka. Fitowar Yazeed dai-dai da isowar RK ƙofar gidan, dan haka a cikin rikicewa Amal ta buɗe motar RK ɗin kawai tana cema Yazeed ɗin ya shiga batare data tantance motar waye ba itama. Shima bai wani tantance komai ba ya saka Maanal a ciki, da sauri itama Ammie ta shiga ta rungumeta tana kuka da faɗin, “Haba Maanal ya zaki mun haka, dan ALLAH kiyi haƙuri kada ki tafi ki barmu mu muna sonki, muna tsananin ƙaunar Maanal. Muna buƙatar ki a duniyar mu Maanal...”
Wannan furuci na Ammie shi ya zaburar da RK da ya tsaya yana kallon ikon ALLAH, sai kuma lokacin ya gane Ammie da Amra dake kuka. Duk da halin da Maanal ke ciki itama bai gagara ganeta ɗin ba. Ai da wani irin tashin hankali ya tada motar, Yazeed ya shiga kusa da shi suka bar anguwar. Napep Amal da Shahidah da Amrah suka tare suma suka bi bayansu....
Yazeed ne ya faɗa masa asibitin da zasu je, inda Maanal ke ganin likita kenan. Asibitin kuɗin ne, kasancewar kafin su isa ma Yazeed ya kira abokin nasa doctor Nazeer ya sanar masa zuwansu suna isowa suka samu nurses har huɗu da Doctor Nazeer ɗin kansa na jiransu a waje. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Manaal daga jikin Ammie. A kallo ɗaya idan kai mata zakai tunanin bazata sake rayuwa ba. Dan yanda take yunƙurowa ƙirjinta na ɗagawa tana aman jinin kaɗai ke nuna akwai sauran numfashi a tare da ita. A haka dai aka shiga da ita ciki kowa a kiɗime. Dai-dai nan suma su Shahidah da suka biyosu a napep suka iso...
Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan yanda doctors ke shiga da fita ɗakin da aka shiga da Maanal basa ko sauraren kowa zai tabbatar maka al'amarin yayi tsamari da yawa. Dan har zuwa goman dare babu wani bayani mai daɗi. Zuwa sannan Nene ta iso, (Nene ƙanwar mahaifiyar Ammie ce da yanzu take kallo kamar mahaifiya. Zamu iya cewa ma ta sandinta Ammie da ƴaƴanta suka zo cikin Kaduna. Ita a anguwar dosa take, ita da zuri'arta. Dan itama yaranta huɗu duk maza a yanzu haka duk suna da aure da ƴaƴansu suma, sai ɗaya ce kawai mace itama dai tayi aure).
Har wannan lokacin RK na asibitin, hasalima tuni ya shige cikin likitocin da shi ake bama Maanal taimako kasancewarsa shima ƙwararren likita masani a fannoni da dama daya shafi aikin. I'd card ɗinsa kawai ya nunama Doctor Nazeer ya amince masa shiga cikinsu aka rufu kan Maanal. Haka shina Yazeed tsaye yake da ƙafafunsa. Duk abinda akace ana buƙata kafin wani dogon lokaci zakaga ya kawosa. Sai su Ammie suka kasance ƴan addu'a da share hawaye. Daga can gidan dai babu wanda ya biyo bayansu, sai dai Yazeed ya kira mahaifinsu ya sanar masa. Ya kuma tabbatar masa a yau ɗin nan zai baro inda yake zuwa Nigeria. Domin shima hankalinsa yay matuƙar tashi bana wasa ba. Koda yasa Yazeed ya haɗashi da Ammie kasa magana tayi sai kuka data fashe masa da shi kawai. Sai hakan ya sake birkita masa lissafi gaba ɗaya babu shiri ya fara neman ticket ta online......
___________
Alhaji Usman Chalawa bai iso ba sai washe gari wajen misalin ƙarfe ɗaya na rana. Babu wanda yasan da dawowar tasa a cikin matansa, dan hatta ita ma Ammien bai sanar mata ba. Sai Yazeed kawai ya sani. Shi kuma tashin hankali ya mantar da shi sanar ma kowa sai da Daddyn ya tura masa saƙon yazo ya ɗaukesu sun kusa sauka sannan ya tuna. Ya bar asibitin ne dai-dai lokacin RK na bada shawarar yima Maanal transfer zuwa Abuja. Dan gaskiya jikin nata sam babu daɗi. Su kansu likitocin sun fara karaya, RK ɗin ne ma ke ƙarfafasu duk da shima gwiyawunsa a sare suke yana dakewane kawai da ƙarfafa kansa...
Kai tsaye asibiti Yazeed yayo dasu Daddyn. Rungume Ammie su Waleed sukayi, yayinda take kallon mijin nata cikin karaya idanunta cike da ƙwalla. Cike da kulawa ya girgiza mata kansa alamar kar tai kuka. Sai kawai tai ƙasa da kanta tana mai rungume Hameed da Waleed sosai a jikinta. Idanun nasa ya ɗauke cike da damuwa ya maida kan su Shahidah dake gaishesa. Ya amsa musu da kulawa yana tambayarsu mai jiki. Maimakon amsa sai suka fara hawaye suma. Jiyay gaba ɗaya zuciyarsa ta ƙara karaya, da ƙyar ya iya gaishe da Nene, sannan ya wuce office ɗin doctor inda suke meeting shi da su RK. Doctor ne yay ma RK bayanin matsayin Daddy a wajen Maanal duk da tare da Yazeed suka shigo, dan RK bai ɓoyema doctor alaƙarsa da Maanal ɗin ba. Cikin girmamawa RK ya rissina ya gaishe da Daddyn. Nan ma doctor ya sanarma Daddy RK likita ne, ya kuma masa bayanin shawaran da suke akai yanzu haka game da maida Manaal ɗin Abuja. Babu wani musu Daddy ya yarda, tare da ƙarfafasu cewar ayi komai yanda ya kamata ama bar ɓata lokaci, bari yaje ya bincika ko akwai jirgi mai wucewa yanzu sai su wuce a ciki zaifi mota sauri....
Hakan kuwa akayi, dan zuwa la'asar an gama shirya Maanal zuwa tashar jirgin ƙasa. Zasuyi gaba harda Nene da su Shahidah. Ammie kuma sai zuwa gobe in ALLAH ya kaimu da safe zasu bisu ita da Daddy kamar yanda ya buƙata.
Suna isowa Abuja ambulance ce tazo ta ɗauki Maanal dan tuni RK ya gama booking komai. Shi da Yazeed ne suka bi ambulance ɗin, yayinda mijin Shahidah da yazo shima ya ɗauki su Shahidah ɗin da Nene da Amal. Yaran duk suna Kaduna sai gobe idan ALLAH ya kaimu Ammie zata taho da su nan. KK HOSPITAL asibiti ne mai tsanani ƙyau da kowa ya sani a cikin Abuja. Suna da ƙwararrun likitoci da suka san aikinsu ƙwarai da gaske. Suna ƙoƙari matuka wajen bama mara lafiya kulawa yanda ya kamata, ga sauƙin kashe kuɗi dan talaka da mai arziƙi duk zasu iya biya. Babu wani ɓata lokaci cike da kulawa aka shiga da Maanal, yanda ake girmama RK a asibitin yasa suka fahimci eh lallai yana da wani matsayi babba a wajen.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣2️⃣
______________
Abubuwan da nake saidawa
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
__________
.......Yau kwanakin Maanal biyu a KK HOSPITAL. Zamu iya cewa Alhamdullahi abubuwa sun fara dai-daita, duk da dai har zuwa yau ba'a barin kowa shiga inda take sai doctors kawai. Tun a jiya su Ammie suka iso suma ita da Daddy. Tsabar munafunci na Hajiya Basariyya sai ta ce zata biyosu taga jikin Maanal ɗin. Dan a waccan ranar da Daddy ya dawo tunda ya koma gida ya rufesu da faɗa ita da Hajiya Yaya akan ƙin zuwansu asibiti, sai dai faɗan nasa yafi tsamari akan Hajiya Yaya data zama itace sanadin komai, dan yama sanar mata ya haramtawa Sabuwa zuwa masa gida, idan kuma tai gigin zuwa ALLAH sai ya saka jami'an tsaro sun kamata. Itama kuma ta jira hukuncinsa bayan Maanal ta warke dan yanzu baida lokacinta. Tofa wannan abu da Hajiya Basariyya dake laɓe taji yasa ta dawo ta lallaɓa Daddyn ta bashi haƙuri akan nata laifin daya faɗa naƙin zuwa asibiti kawai, ta kumaji duk halin da ake ciki akan maida Maanal Abuja shine ta maƙale itama zata bisu. Ammie bata san da batun ba sai da suka fito zasu wuce taga Hajiya Basariyyan. Sosai ta sake jinjina makircin matar a ranta, dan ta jima da gane wacece Basariyya, sai dai bata taɓa nuna mata ba ta barta da halinta. A lokacin ma murmushi kawai tai batace komai ba, hakan kuma sai ya ƙonama Hajiya Basariyyan rai, ta rasa wacece Ammie, ta rasa ta inda zata kamo lagon matar, ta rasa ta inda zata shiga jikinta kamar yanda take shiga jikin Hajiya Yaya tasan sirrinta. Amma ba komai, idan tasan wata ai bata san wata ba.
Anan Abujan itama ta kwana dan Daddyn nada gida anan ɗin dan yana harkar sayen gidaje da sayarwa ne. Kasancewar komai akwai a gidan yasa sauka kawai sukai anan ɗin. A yanzu ma haka tana a asibitin tare da su. A ɗakin da aka kwantar da Maanal ɗin ɗakine na musamman kamar palor da bedroom, dan haka duk suna a palor ɗin zaune itama Maanal na daga ciki babu mai shiga sai dai su leƙata ta jikin ƙofar glass ɗin. Shahidah da Amal suka iso ɗauke da abinci, bayan duk sun gaishesu suna ƙoƙarin zama Daddy da RK suka shigo ɗakin sai wani ba'indiyen likita da shine akan case ɗin Manaal ɗin ma. Gaishe da Daddy su Shahidah sukayi, sannan suka gaisa da su RK da suma suke gaida su Ammie. Su RK na ƙoƙarin barin wajen kamar daga sama sai Hajiya Basariyya cewa tai, “Nikam likitan nan kamar na sanka”. Yanda tai maganar idonta akan RK ya sakashi fahimtar da shi take, kallonta ya ɗan yi sai kuma ya rissinar da kansa tunda bai san matsayinta ba a garesu ya ce, “Mommy zata iya yiwuwa. Sai dai ban san a ina kika sanni ba”.
Batare data damu da kallon harara da Daddy ke mata ba ta ce, “A zaria gidan Alhaji Saminu Ashafa”.
Cikin jinjina kai RK ya bata amsa da, “Ni ƙanin amaryarsa ne Majdiya”.
Kafin Hajiya Basariyya ta samu yin magana Ammie da Daddy suka dubeshi. Abinda ya faru a ranar da sukaje ɗaurin aure gidan Alhaji Saminun ya shiga dawo mata a rai. In dai batai kuskuren fahimta ba shine yaron da Hajiya Majdiya ke mata bayanin yana son Maanal kenan. Wani irin sanyi taji a ranta, dan koba komai ita dai yaron ya shiga ranta a lokaci guda, sannan ta samu karɓuwar addu'ar ta akan al'amarin Maanal ɗin da Yazeed tunda ga raba gardama yazo.. Shikam Daddy murmushi yayi cike da nuna mamaki ya ce, “Ikon ALLAH ashe ma kai ɗin na gida ne doctor. Ai nasan Hajiya Majdiya kuwa sosai saboda Alhaji Saminu aminine kuma ɗan uwana ta fanin mahaifiya, zan iya cemaka