Showing 138001 words to 141000 words out of 221978 words
Chapter 47 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
dawo gareta ba. Sai dai kuma babu yanda ta iya, dan Haruna ya tabbatar mata idan tai masa hauka sauran matan huɗu ma da take dasu zai kwashe ya bama su Umar ita kuma ya saketa. Wannan furuci ya tada mata da hankali dole tai shiru, amma ta koma yima Lubabatu habaici da gorin haihuwa dan ita tun wancan haihuwar bata sake ba har yanzu. Yanda take mata gorin haihuwa haka sauran matan gidan suma suka fara, sai ya zam sam kwanakin da sukai a Giro bai mata daɗi ba, bama su gama cika kwanakin ba tace ita dai zata koma. Haƙuri malam Ibrahim ya dinga bata kamar ba surukarsa ba. Ita kuma tace ba komai baba. Haka dai suka dawo Giro harda Habibu. Ashe ALLAH mai rahama mai jinƙai tana maƙale da ciki harna wata biyu.
Ta raini cikinta cikin aminci da yarjewar UBANGIJI, babu kuma wanda yasan da shi sai da ya shiga wata takwas Baba Haruna yazo Kebbi ya ganta da shi. Ya taya ɗan uwansa murna matuƙa, yana dawowa Giro kuwa ya fasa zance. Ashe shi Baba yasan da cikin, dan Umar ya sanar masa amma yay shiru dan ya fahimci yanda Umar yake rayuwa a cikin yan uwansa da matansa, da yanda itama matarsa ke fuskantar ƙyara da hantara wajen surukansa. Aiko wannan batun ciki sai da ya ɗaga musu hankali, musamman Talle, dan da farko ma saida ta jefa cikin da mummunar kalmar data saka Haruna marinta. To babu dai yanda suka iya, haka ALLAH ya sauki Lubabatu lafiya, ta haifo ƴarta mace. Habib yafi kowa farin ciki dan ya samu ƙanwa. Giro baba yace su dawo ai suna, haka kuwa akayi duk da Lubabatu bata so ba, amma darajar baba zata iya yin komai. Shagalin suna akai na garari na faɗa aji, dan Umar ya kashe kuɗi batuƙa, ta yanda a lokacin kowama ya fahimci lallai ya kama ƙasa, dan lokacin tabbas kuɗi na shigo masa Alhamdullah. Sosai mahassada su kuma suka zuba hassadarsu, dan su Talle dai habaici suke. Wai ai ta banza, idan ana son nuna musu anyi kuɗin miyyasa bata haifi namiji Magaji ba. Babu wanda ya kulasu, dan sune jahilai. Bayan suna da sati ɗaya suka shirya komawa Sokoto saboda makarantar Lubabatu data Habib, amma sai Talle tai tsalle ta dire Habib bazai koma ba. Nan ma ubansa Haruna yace bata isa ba tayi kaɗan. Haka tana ji tana gani suka tattara suka wuce suka barsu da ƙunar zuciya...
Bayan haihuwar Asiya Lubabatu bata sake ko samun ciki ba, dan haka ta maida hankalinta akan yaranta biyu, wato Habib da Asiya. Gata suke musu matuƙa daga ita har Umar ɗin. Ga tarbiyya suna samu mai inganci. Sosai Habib ke son Asiya, dan ita yake kallo a matsayin ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ba ƙannansa na Giro ba. Yakan je Giro ɗin, wani lokacin ma harda Asiya. Amma sam babu mai nunama Asiya soyayya sai baba kawai da Baba Haruna. Sai ko shi Habib ɗin dake zama yayta kaffa-kaffa da ita duk da kuwa hakan baya hana Talle dukanta da hantararta. Dan gaba ɗaya ƙiyayyar da takema Lubabatu da Umar ta koma kan Asiya yanzu. A haka Umar ya kammala karatunsa. Ya nuna yana sha'awar aikin ƴan sanda. Aiko babu musu Baba Umar ya sama masa. Ya fara aikin babu jimawa Asiya ta kammala secondary ta fara jami'a itama. Sai kawai Baba Umar ya yanke shawarar haɗasu aure, koda ya tuntuɓi Lubabatu murna tayi sosai, dan acewarta wa suke da shi bayan Habib ɗin dazai riƙe musu yarinya, Habib tarbiyyarsu ne hakama Asiya, suna ƙyautata musu zaton alkairi. Wannan magana tata ta ƙara masa ƙwarin gwiwa ya nufi Giro da batun. Anan ma Baba yayi matuƙar murna da sanya masa albarka, hakama baba Haruna. Amma sai Baba yace suyi shiru da zancen kawai sai ranar ɗaurin aure. To dama akwai bikin jikokin gidan da za'ayi har su bakwai, saboda yawan family ɗin da wahala kaga an tashi auren yara an aurar da ɗaya ko biyu. Hakan kuwa akayi, aka fara taron biki batare da kowa yasan dana Habib da Asiya ba. Har ita Asiya da Habib ɗin kuma. To dama yanzu indai za'a aurar da yara a gidan Baba Umar shike yin komai na hidimar batare da gajiyawa ba, duk da ƴan uwansa basu taɓa gode masa ba sai ma zaginsa akan kullum baya musu. Baba Haruna ne kawai mahaifin Habib ke ganin ƙyautatawarsa.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣0️⃣
______________
........Ba ƙaramin tashi hankalin kowa yayi ba lokacin da akaji a ɗaure-ɗauren aure harda Asiya da Habib, tab ɗin jan inji mata. Ai a ranar kowa yaga ainahin Talle a wannan gida. Tayi tujara ta fitar hankali, tai tsalle ta dire akan bata yarda ba kuwa. Aiko Baba Haruna yace idan bata yardaba kuwa sai dai itama ta koma gidansu da zama. Ansha rikici kam bana wasa ba, harma wanda basu san ainahin matsalar gidan ba da takurar da Umar ke fuskanta da iyalansa kowa ya sani yanzu. Baba ne dai yasa Baba Umar da Lubabatu da tsirarun danginta da sukazo biki, dan ƙanwartace ma kawai Shamsiyya da itama yanzu tayi aure a Kaduna harda yaranta biyu. Sai dai mijinta yana tafiya da ita Lagos shiyyasa sukan daɗe basu haɗu ba.
Dama dai an tsara ma amarya da ango gidan zamansu anan Kebbi, dan haka can suka tare su. Sudai suna musu addu'a da fatan zaman lafiya da zuri'a mai albarka. Alhamdullah Habib na nunama Asiya kulawa, duk da kuwa a yanayin nasu kamar dai babu wanda ke son ɗan uwansa da kalmar soyayya sai dai ƴan uwantaka, kawai iyayensu sun musu shigar sauri ne tunda basu tambayesu ba. Amma kuma bazasu taɓa iya musu da su ba dan haka suka haƙura suka amshi juna kamar babu komai. A farkon zaman tarbiyya da ilimi ne kawai ke jagorantar zaman auren, amma a hankali sai Asiya ta fara son Habib, so kuwa mai tsananin gaske, tun bai fahimci ƙanwarsa ta faɗa soyayyarsa ba har ya fahimta. Dan haka ya sake ninka kulawar da yake bata. Bawai shima Habib baya son Asiya bane ba, yana sonta shima sosai, sai dai shi Talle mahaifiyarsa itace matsalarsa. Dan yana samun matsi a gurinta a duk sanda yaje Giro akan sai ya saki Asiya komai daren daɗewa. Irin wannan abubuwan yasa yake jin bai son zuwa Giro ɗin ma, Asiya kuwa tunda sukai aure bai yarda taje ba. Sai ya fake da karatun da take yi. Baba ne kakansu idan ya samu lokaci yana shigowa Kebbi, shima Baba Haruna haka, dama ko zasuso zuwa sai dai domin su. Itama dai Asiya ta mayi mahaifiyarta Lubabatu, dan sai da tai shekara biyar harta kammala karatunta ma da service sannan ALLAH ya bata ciki, babu irin tujarar da Talle batayi ba akan wannan rashin haihuwa amma kowa yay uwar watsi da ita har shi ɗan nata Habib. Dan yanzu ma ba'a Kebbi suke ba an maida shi aiki Zamfara can suke da Asiya. Sosai Baba Umar da Mama Lubabatu sukai farin ciki da samuwar cikin ƴar tasu, hakama kakansu Baba Ibrahim da Baba Haruna mahaifin Habib. Gambo kuwa sai taita aibanta cikin har sai da Baba ya tsawar mata.
Ciki ya girma suka dawo Kebbi haihuwa, inda ALLAH ya sauki Asiya lafiya ta haifo ƴarta mace mai kama da ita da kakarta Lubabatu. Babu ta inda yarinya ke kama da Habib gaskiya. Oho hakan bai damu Habib ba, farin ciki yake shima ya samu ɗiya jininsa. Hakama Lubabatu da Baba Umar da Baba Haruna suna farin ciki da samun jika. Giro aka koma akai suna saboda Baba, sunan daya haɗa hargitsi da farin ciki duk a lokaci ɗaya, dan kuwa Talle ana kai mata ƴa ko taɓawa batai ba sai cewa tai ba ƴar Habib bace, dan babu ta inda tai kamanni da shi. Wannan magana ta tada ƙura matuƙa, ƙura irin wadda a karo na farko Baba Umar ya zuba tsiya irin wadda ba'ayi zaton ya iya ba. Dan sai da Talle ta raina kanta kuwa. Murmushi Baba yay tayi dan shi kansa daya haifi Baba Umar bai san ya iya faɗa haka ba, saboda bayayi, shi mutum ne mai sanyi da nutsuwa. Wannan tujara da Baba Umar yayi tasa aka samu sassaucin ƙarasa taron gagarumin sunan lafiya.
Ana kammala taron suna suka tattara suka koma, Habib ya wuce Zamfara yabar Asiya anan tana wankan jego ita da jinjirarta mai suna *_Shahidah_*, sai ya koma zuwa musu weekend har suka kammala wankan ta koma can Zamfarar wajensa. Bayan komawar tata ne ALLAH yay ma mahaifin mama Lubabatu rasuwa. Hankali tashe suka wuce Minna ita da Baba Umar. Wannan tafiya itace ta canja komai daga rayuwar Asiya Umar Ibrahim Giro (Ammie) itace ta canjata daga sarauniya ƴar gata zuwa baiwa da ƙaddarorin rayuwa suka zagaye, dan kuwa a hanya Baba Umar da Mama Lubabatu suma sukai haɗari, babu kuma wanda ya shura a cikinsu tun a wajen dan gawawwakinsu aka kawo Giro. Kamanta irin tashin hankalin da Baba da Baba Haruna da Habib da Asiya suka shiga ma ɓata lokaci ne. Dan Asiya komawa tai kamar ta zare ma. Sauran jama'ar gidan kuwa bazaka iya cewa ga abinda ke cikin zukatansu ba akan wannan rashi. Bayan rasuwar su Baba Umar da sati biyu shima Baba ALLAH yay masa rasuwa. Dan tun da yaga gawar Baba Umar da Lubabatu a kwance jikinsa ya rikice, abinka da dama ga tsufa. Asiya tayi kuka har ta rasa hawayen zubarwa. Dan tasan ta rasa dukkan gatanta a family ɗin su sai Baba Haruna kawai ya rage mata sai kuma Habib da ƴar ɗiyarta. Haka dai aka sha alhini komai ya lafa. Habib ya ɗauka Asiya dan su koma Talle tace bai isa ba, ai kuma Asiya ta dawo Giro da zama kenan. Hankalinsa yay matuƙar tashi hakama na Asiya. Gashi ta kafa matsa tsaurara dokoki ciki harda in Baba Haruna ya tambaya yace shine yace zai barta ta ɗan huta. Idan ba hakaba ALLAH sai ta tsine masa. Wannan kalma ta girgiza Asiya Ammie tace zata zauna kawai. Ta dinga lallashin mijin nata. Haka badan yaso ba ya shirya ya koma Zamfara ya barta a Giro.
Rayuwa a Giro ga Ammie rayuwace mai tsanani da takura da damuwa. Tasha wahala matuƙa a hannun Talle da suke kira Gwaggo. Gaba ɗaya Ammie ta fita a hanyyacinta kamar bata taɓa shiga ajin makaranta ba. Ga Baba Haruna baya iya magana a yanzu saboda Talle ta danne masa kai a gidan teacher. Habib na zuwa weekend, amma bai isa sauka ɗakin Asiya ba. Ko da dare idan ya shiga domin kwanciya babu kunya Gwaggo ke zuwa ta buga musu tace ya taso ya koma ɗakin soro ya kwanta, inda ɗakin Baba kakansu yake. Haka babu yanda zai yi zai fito. Tom dai kuma UBANGIJI ya nuna mata ita bata isa hana abinda ya hukunta ba. Dan kuwa sai ga Asiya Ammie da ciki, gashi bata yaye Shahidah ba. Ta shiga tashin hankali, dan mutanen gidan ƴaƴa da iyaye sun tasata a gaba da zagi da habaici wai mayyar miji jarababbiya tayi gwanne. Abin kuma tsoro da firgici Gwaggo tace ai ciki bana Habib bane tunda ba kwana yake a ɗakin ba, dama ai Shahidah ma ba ƴarsa bace. Magana kamar wasa ta nema zama babba. Dan har gari ya ɗauki wannan zance. ALLAH gafurin rahimun sai ga Baba Haruna ya dawo hankalinsa a lokacin, dan kuwa asirin Gwaggo ya sakesa. Shine ya bama Asiya kariya har ya sake yina Gwaggo saki ɗaya. Ya rage saura igiya ɗaya a tsakaninsu kenan. Wannan saki shine fa ya sake haddasa wutar ƙiyayya tsakanin Gwaggo da Ammie. Da ƙyar dai Mahaifiyar Baba Haruna tasa ya dawo da Gwaggon dan ƴar ƙanwarta ce dama auren zumunci akai musu. Gwaggo ta dawo amma ta ƙara ninka ƙiyayyarta ga Ammie, sai dai a yanzu Baba Haruna na tsaye akan al'amarin Asiyar, dan ya ma fara shirin Asiya tabar giro tabi mijinta. Amma sai ta haihu kodan yanayin samun cikin.
Haka Asiya taita rainon ciki cikin matsi da takurar surukarta. Ga Shahidah dake ta fama da ciwo. Babu mai taimaka mata a gidan har tsoffin gidan saboda Gwaggo ta zama boss ga kowa. ALLAH ya sauki Asiya lafiya ta sake samun mace mai kama da ita itama kamar Shahidah. Aiko Gwaggo ma ta sake aibanta jinjira tace ba ɗiyar Habib bace. Sai da Baba Haruna yay mata tas. Baba Haruna shine ya tsaya akan komai akai suna yarinya taci suna Lubabatu, amma sai suke kiranta Amaal koma ace Asiya da Habib ke kiranta. Dan su dai ƴan gidan Lubabatu suke cewa. Zuwa lokacin an ma Habib transfer zuwa Maiduguri. Dan haka ana gama bikin suna ya sake shirya komawa. Sai Baba Haruna yace ya ɗauki matarsa su tafi. Hankalin Gwaggo ya tashi akan hakan amma Baba Haruna yace bata isa ba kuwa Habib kamar ya tafi da iyalinsa ya gama. Hakan yama Habib daɗi, ya ɗauka Asiya da yaransa biyu suka wuce abinsu, suka bar Gwaggo na tujara.
Wannan tafiya ita ce ta samawa Ammie sauƙi, suka koma Maiduguri da zama ta samu damar rainon yaranta cikin aminci, anan ta koya gyaran jiki da haɗin turarruka. Shekararsu biyu a Maiduguri aka sake masa transfer zuwa jihar Nasarawa. Nan ma ya kwashesu suka koma. Anan ɗin ma shekararsu uku aka sake maida shi Sokoto, zuwa lokacin kuma bata sake haihuwa ba. Yaransu Shahidah da Amaal sunyi ƙyau abinsu yara kamar ka lashe, dan Ammie ma ƙyaƙyƙyawa ce kamar mahaifiyarta. Dole kaga yaran nan sai ka tanka, dan kamar wasu ɗiyan hamshaƙin mai kuɗi bana ɗan sanda mai ƙaramin muƙami ba. Shima Habib yana son yaransa, sai dai irin mutanen nan ne shi da bai cika jan yaro a jiki ba, komai dai na buƙatar rayuwa yana tsaye a kansu. Dan ko ita Ammie bazata ce ga wata soyayya a bayyane da yake nuna mata ba. Baya dai takura rayuwarta ko hanata duk abinda take so, ba kuma ya nuna mata tsantsar soyayya a zahirance. Ga wanda ma bai sansu da ƙyau ba idan yaga rayuwar zamansu sai ya ɗauka tana a cikin matsin rayuwa ne. Sun tattaro sun dawo Sokoto, a lokacin Shahida nada shekara bakwai, Amaal nada shekara biyar da wasu watanni dan tsiransu da Shahidah kaɗanne. Saida sukai sati biyu a Sokoto sannan suka je Giro. Babu wanda bai firgita da canjawar Asiya da yaranta ba. Dan ta koma ƴar gayunta kamar batai rayuwar Giro ba. Tuni kishinta da hassada ya shiga zukatan jama'ar gidan kamar yanda suka dingama mahaifiyarta Lubabatu. A ɓangaren Gwaggo ma babu abinda ya canja, dan ƙiyayyar Asiya sai wacce tai gaba. Haka su Shahidah ko kallo basu isheta ba dan tace ita ba jikokinta bane ba uwarsu dai tasan inda ta samo su. Hakan na ma Habib ciwo amma baya cewa komai. A wannan zuwa kuma Gwaggo ta tsira sai Habib ya ƙara aure, dan a haifa masa namiji. Kai tsaye ya nuna mata bashi da wannan ƙarfin, dan shi dai bamai kuɗi bane, dukiyar da yake juyawa kuwa kowa yasan ta Asiya ce da iyayenta suka bar mata duk da ma dangin nasu sun kusa cinye rabi da kwata. Aiko ta tujaresa da masifa da bala'in daya sashi tattara matarsa da ƴaƴansa suka koma abinsu. Sai kuma suna komawar sai ga Asiya da ciki. Yayi farin ciki matuƙa, ya kuma shiga addu'a da fatan ALLAH yasa Asiya ta haifa namiji dan shima fa yana son a haifa masa namijin, ga maganar mahaifiyarsa ta sake kwaɗaita masa abun a rai. Kawai dan bashi da ƙarfin aure ne. Amma tabbas a ransa yana son ƙara auren ma. Dan yana ɗan neman mata batare da Asiya ta sani ba, tun kafin yay aure yake yi, bayan aurensu ya rage sosai sai dai kuma ita dama zina masifa ce. Faratane mara wuya, amma indai ka fara sai ALLAH ya soka da rahama kake dainawa.
Ammie tayi rainon cikinta cikin aminci da kulawa, har ALLAH ya kai cikin watan haihuwa ta haihu lafiya. Ta samu ƴa mace ma a wannan karon. Sai da Habib yaji wani iri a ransa, sai dai kuma yana ɗaura idonsa akan yarinya yaji ƙaunarta ta shigesa. Dan ita kam tayo kamannin mahaifiyarta da ƴan uwansa, ta kuma yo kammaninsa ta bangarori da dama da suke a bayyane........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣1️⃣
______________
.........Wannan karon ma dai Giro suka koma suna, sai dai babu wanda ya nuna murna da wannan haihuwa kamar ta Amaal daga Baba Haruna sai uban jegon sai kuma su Shahidah dake murna an haifa musu ƙanwa. Wannan karon dai Gwaggo babu damar aibanta yarinya tunda tana kama da ubanta a abubuwa da dama. Amma hakan bai hana sako batun haihuwar ɗa namiji ba data fahimci yana tasiri a zuciyar ɗan nata. Haka dai akai bikin sunan babu wani