Showing 192001 words to 195000 words out of 221978 words
Chapter 65 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
mata auren gata, shiyyasa ma ranar juma'a ɗin nan zamuje Kaduna ɗin. Mijin Asiyan na aurar da ɗa kuma ya gayyaceni, sai muyi amfani da wannan damar muje gareta duk da ina jin matuƙar kunya wlhy”.
Fuska sosai Oum ta ɓata tana kallon Abah. Idonta cike da ƙwalla ta ce, “Amma ya kamata ku mana uziri, ku fahimci Ajwaad, sannan ita kanta Maanal tana son shi ai, ka zauna da shi kuma zakaji ta bakinsa. Zuwa Kaduna kuma ALLAH nima kunyar sake haɗuwa da Asiya nake yi, shiyyasa naketa tufka da warwarar tunkararta. Dama Majdiya ta faɗa min zancen bikin. Amma dan ALLAH ka duba al'amarin nan na Ajwaad a sassauta masa”.
“Ai in dai bashi ne ya kawo min zancen ba bai isa na masa ba. Kema kuma ban yarda ki saka shi ya min ba. Ki barsa ya mangantu a karan kansa ni naga ƙarshem miskilanci.”
“Amma Gadanga.......”
Kai ya girgiza mata tare da ɗaura yatsarsa akan lips ɗinta. Idanunsa a cikin nata ya ce, “Please Fateema ki fahimceni, in dai maganar Ajwaad ce na gama ta a gidan nan. Zuwa Kaduna kuma ku shirya ku duka zamu je”.
“Na fahimceka, amma hukuncin ya mana nauyi a sassauta mana”.
“Sassaucin a hannunku yake ai. Sai dai ina sake gargaɗi bana buƙatar fargarwa daga gareki a kansa.”
Rasama abin cewa Oum tayi, sai kawai ta zubama Abah daya miƙe ido. Sallama ya mata ya fice yana sanar mata ya koma wajen aiki...
Da sauri Saheeba tabar kitchen ɗin Oum ɗin ta baya, da alama duk tattaunawar Abah da Oum a kunnenta ne. Kai tun zaman RK da AA ma tana a sashen. Ta shigo ne wai zata amsarwa su Naufal abinci dan ita yau ta makara da girki, masu aikin sashen Mamy kuwa ba wani iya abinci sukai ba, ita ko Oum da kanta take girki bata saka masu aiki. Shine taci karo da hirar RK da Oum. Mai aikin Oum ta bama abincin su Anum tace ta kai musu, idan kuma takai kada ta dawo kitchen ɗin sai ta kirata. Shine ta laɓe tana saurare. Bayan fitar RK harta fito sai ta hangi Abah daya dawo, shine itama ta dawo da sauri ta sake laɓewa taji komai nan ma.
Da sassarfa ta isa sashen Mamy, masu aiki ne keta faman gyara, ganin bata a ƙasa ta haye sama nemanta. Acan kuwa ta sameta zaune a dining zata karya. Zama tayi itama a saman dining ɗin ta gaisheta. Mamyn ta amsa tana kallonta, dan yanayinta ya nuna da zance tazo. Saheeba kuwa ta cigaba da faɗin, “Humm Mamy da ga sashen matar can nake. Yau dai mun sami tabbacin itace ta dawo da yarinyar nan rayuwar Ajwaad. Tana can tana tsara Abah akan Ajwaad ya auri yarinyar shi kuma yana botsare mata. Wai ashe kin san bayan samun lafiyar Ajwaad tafiyar da yace zai yi ɗin nan ya barmu a can Nigeria yazo neman yarinyar nan”.
“Nigeria?”.
“Wlhy kuwa Mamy nan yazo ya dinga nemanta lungu da saƙo. Ni wlhy yanzu ma wani tunani yazo min, wai minene ma'anar sunan kamfaninsa na agogo?”.
Tsai Mamy tai tana kallon Saheeba zuciyarta na wani kalar tsaitsinkewa. Sai kuma a hankali ta girgiza kanta. “Ban sani ba Saheeba. Ban kuma taɓa maida hankali akan na sani ba. Wani abu su Fateeman sukace akan sunan kamfanin?”.
“A'a, basu ce komai ba. Nice dai nayi tunanin yanzu.”
Ture plate ɗin abincin Mamy tai gefe, batare data sake cema Saheeba komai ba ta miƙe. Bedroom ta nufa, hakan yasa Saheeba rakata da idanu tana wani ƙyaƙyƙyafta su. Sai kuma ta miƙe tana murmushi. Sashenta ta nufa. Tana zuwa tai kiran uwarta a waya ta zayyane mata komai. Daga can mamanta tai ƴar dariya da faɗin, “Kai Saheeba ALLAH ya shirya min ke. Yanzu to mi tace?”.
“Tashi tai ta shige ɗaki Umma. Wlhy na fahimci idan ba wuta-wuta mukai mataba yanzu zata canja ra'ayinta ne akan auren Nuratu da Ajwaad maƙiya sumana dariya. Kin dai ji abinda malam ya faɗa ai yarinyar can Huznah take komi shegiya ita da uwarta ba zaune suke ba. Ga kuma wannan maƙallaiyar mayyar Maanal ɗin da danginta, munafukar can kuma ta ɗaure musu ƙugu, idan ba munafunci ba ta bari ƙanin nata ya auri yarinyar mana ba sai suje suyi zumuncin ba da ƙyau”
“Ke ko tayi haka tunda tasan burin yarinyar da iyayenta cin dukiya ne, ai gara aci wadda ba tasu ba. Ta ƙaninta kuwa aita ubansu ce akwai gadonta a ciki. Ai Yaya Kamila ta tafka babban kuskure a rayuwarta wlhy da gyarashi sai dai ALLAH kawai. Yoni ina zan iya mallakama kishiya ƴaƴana dan neman wata soyayyar mijin banza can. Gashi nan har yanzu bata sami yanda take so a mijin ba ƴaƴa kuma sun nuna basu santa ba”.
“Ai Umma sai ma kina gidan nan zakiga ikon ALLAH. Jiya dai mai aikina ke faɗa min rigima Fawzan yasha da wacan sakaran. Ban dai gane kan zancen ba sai na bincika dan wai har ga haɗa kaya zata bar gidan ita Mamyn ta hanata, a sashen uwar tasu akai shari'ar, taga kuma Ajwaad ɗin ya fito a fusace”.
“Hummm ita wannan gaɓuwar ai ban san irinta ita da uwarta ba. Kamila ce bata jin shawara, amma sai da aka faɗa mana yarinyar sakarai ce gata da boko sun maidata shashasha amma tace zata bari ai. ALLAH ya ƙara suyita yi mu ƴan kallo ne”.
“Wlhy kuwa Umma. Bara naje anjima zan kiraki”.
“To shike nan sai na jiki”......
___________★
Tun daga gate kowa ke faman bin motar da kallo. Bawai dan basu san motar ba ne. A'a kowa ai yasan ta boss ce. Dan mota ce fitacciya kasancewar irinta a Abujar kaɗan ce ma, ba kuma ko yaushe yake hawanta ba shi kansa. To amma boss kusan mintunansa goma da isowa tuni ma har ya shige office. Mamakin waye kuma ya zo da motar a yanzu ya sakasu binta da kallon ƙurulla. Guri Manaal ta samu tai parking a parking space ɗin da boss ne kawai ke ajiye motarsa. Batai mamakin ganin motarsa a fake ba, dan tasan ya isa shigowa, saboda ita ta ɗan makara yau ɗin. Fitowar ta a motar yasa kallo ya koma sama ga kowa. Tayi ƙyau sosai cikin riga bubu ta lass ruwan toka da ratsin orange, sai ƙaramin veil shima orange data yana a kanta. Fuskarta tayi wani irin fayau saboda ƙitson da tasha jiya. Yanda ɗaurin nata ya ɗan zama baya kamar ta saka hula ya bayyana kitson kaɗan. Ga ƙamshinta mai sanyi na tashi da har sai ka kasance a kusa da ita gab zaka ma iya jinsa. Kamar yanda ta saba duk wanda ta haɗu da shi takan gaisheshi ta wuce abinta, yayinda su kuma suka fara ƙusƙus na gulma akan ganin ta a motar boss. A Maimakon Office ɗinsu kai tsaye sama ta nufa, bayan ta shiga cikin elevator ta gaisa da wanda ta samu ciki kasancewarsu manyan ta.
Yanda AS ya wani gaisheta kafin ita ta gaisheshi yaso bata mamaki, amma sai ya dake ta amsa masa tare da ajiye key ɗin hannunta a gabansa. A taƙaice ta ce, “Kaba boss”. Kafin ya ce komai ta juya abinta ta fice. Da kallo AS ya bita, tabbas yasha ganin ƴammata ƙyawawa masu ji da kansu suna zarya a companyn nan saboda boss, kuma yasha ji a ransa sun dace da shi, amma magana ta ALLAH shi da kansa ya yarda yarinyar nan ta musamman ce, irin musamman ɗin da komai nata yay dai-dai da boss. Inama ace zai so ta. Hummm ALLAH sai yafi kowa murna. Da wannan tunanin ya miƙe tare da ɗaukar key ɗin ya nufi CEO office ɗin. Sai da yay knocking aka bashi damar shiga sannan. Kamar kullum sarakin na zaune cikin kujerar office. Baƙaƙen suit ɗin jikinsa sun wani sake ƙawata cikar kamalarsa, yanda yay busy sosai zaka san aikin gabansa mai muhimmanci ne matuƙa. Dan ko ɗagowa ya kalla AS bai ba. Kansa a duƙen ya furta, “Lafiya dai Ahmad?”.
“Eh lafiya Lau sir, dama Sister Maanal ce ta kawo key wai a baka”.
Cak ya tsaya daga aikin da yake yi, kafin ya ɗago manyan fararen oily idanunsa gently ya saukesu a kan AS. Dole AS ya rissinar da nasa, dan kallon ya masa nauyi da yawa. Shima AA ɗin sai ya janye nasan ya maida ga aikinsa.
“Ita bata san hanya bane zata aiko ka? Ka maida mata ta kawo da kanta”.
Murmushi ne ya so kufcema AS, amma ya dannesa da ƙyar. Cike da girmamawa ya ce, “Okay sir, na barka lafiya”. Daga haka ya juya ya fita. Ɗagowa AA yay ya ɗan zubama ƙofar ido, sai kuma ya shafi ƙasumbarsa ka ɗan ya sake maida hankalinsa kan aikinsa....
_________★
Zaune take tana aiki ita da Yaqub daya jawo kujerarsa kusa da ita, nuna mata wasu abubuwa yake da take neman ilimi a kansu a cikin computer ɗinta. Yayinda munafukan nasu su Deeni ke faman zinɗensu da baki. Sai da AS yay knocking duk suka ɗago, batare da ya jira umarninsu ba ya turo glass door ɗin ya shigo. Kai tsaye ya wuce inda Maanal ɗin take bayan ya musu gaisuwar gaba ɗaya. Murmushi ya ɗanyi tare da ajiye mata key ɗin a gabanta da ƙaramar takarda daya rubuta abinda boss ɗin ya faɗa, dan haka kawai yaji shi kam bazai iya maimaita mata da bakinsa ba. Kallon key ɗin Maanal dake binsa da kallo tayi, sai kuma ta sake maida idanunta a kansa. Takardar AS ya nuna mata kawai, batare da yace komai ba ya juya ya fita. Suko duk suka rakashi da idanu, sai kuma suka dawo da dubansu ga Maanal ɗin data basar kamar komai ma bai faru ba ta cigaba da aikinta. Ba kuma ta taɓa key ɗin da takardar ba. Ji suke kamar su taso su ɗauka su buɗe suga mike a ciki, dan suma dai gulmar zuwan Manaal ɗin a motar Boss harta iskesu. Kai yau hatta da Yaqub ji yake kamar ya ɗau takardar ya duba. Amma dai sai ya dake.
Haka suka cigaba da ayyukansu har lokacin break yayi. Maanal da tasan ba salla zatai ba bama ta motsa ba. Dan da safen nan taci karo da baƙonta na wata. Sai dai koda Yaqub yace ta taso suje catai masa yaje tana nan zuwa zata ƙarasa wani abu ne. Badan yaso ba ya fita, suma sauran duk sun fice sai ita kaɗai. Aikinta ta cigaba da yi, dan Maanal akwai himma da nacin aiki, kamar yanda take da nacin karatu. Can idonta ya sauka akan takardar nan da key, ɗan zuba mata ido tai, sai kuma ta kai hannu ta ɗauka ta warware. _Kiyi hakuri boss ne yace na dawo da shi ki kai masa da hannunki_. Iya abinda aka rubuta kenan. Kanta kawai ta girgiza ta naɗe takardar ta jefa a kwandon sharar su dake office. Shi kuma key ɗin ta jefa shi a wani ɗan basket mai ƙyau da take zuwa kayan sweet da take sha, sai dai yanzu babu komai a ciki dan ta shanye ta kuma mance tazo da wasu. Ta sake maida kanta a aiki bayan ta ɗauka meat pie ɗaya ta fara ci. Kamar abin almara taji ƙamshin mayataccen turarensa na sake ƙarfi a hancinta. Da farko ta share da tunanin iska ce ko hancinta ne. Sai kuma dai taji abin na neman wuce wuri dan haka ta ɗago.
Samun zuciyarta tai da girgizawa sakamakon saukar idanun nata a kanshi, sai kuma ta janyesu da gudun tsiya ta hau waige-waige a office ɗin nasu alamar dai tabbatar da babu kowa dai ko........✍️
🤣Ko waye oho.
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣4️⃣
______________
........A hankali ya wani kalar taɓe baki. Cikin halin ko'in kula da ganin yanda ta ke waige-waigen ya ƙarasa shigowa cike da izzar nan tasa da ƙasaita hankalinsa a kwance. Sai da yaje jikin desk ɗinta ta kashe-kashen daya kasance daga ita babu kowa sannan ya tsaya. Kaɗan ya ɗosana jikinsa a desk ɗin yay irin tsaiwar maza tare da harɗe ƙafarsa akan ɗayar daya dogara, gaba ɗaya ƙarfinsa naga desk ɗin. Idanunsa har yanzu akan Manaal da kamar tayi suman zaune ne ma oho mata😂.
Babu wani ko ɗar balle tunanin wani ya shigo ya gansa ya kai hannu ya zare meat pie ɗin dake hannunta da take ci. Bakinsa ya kai ya gutsira, ya lumshe idanu yana mai taunawa a hankali...
“Amma kasan hakan na nufin sakani a masifa ko? Dan ALLAH dan mi zaka zo nan a wannan lokacin da kowa ke can yana salla kai kana nan ɗaukar magana?”.
Shiru kamar bai jita ba. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe lumsassun idanun nasa a kanta. Cikin halin ko'in kula ya cigaba da cin meat pie ɗinsa hankali kwance. Marairaice masa tai sosai idanunta na cika da ƙwalla, dan ta fahimci masifar bazata kaita ba. “Please dan ALLAH ka fita kada wani ya shigo ya ganka anan ka jamin surutu. Salla fa akeyi”. Da kaga yanda take maganar kasan bata da nitsuwa, dan sai leƙe-leƙe take kamar mai shirin yin satar naman miya a gidan soja.
Baki ya sake taɓewa da janyo bowl ɗin da meat pie ɗin yake ya sake ɗaukar wani. “K miya hanaki zuwa sallar?”.
“To ina ruwanka dan ALLAH da abinda ya hanani, ni dai dan ALLAH ka tafi kada ma'aikatanka su sakani a bakin duniya”.
“Tunda babu ruwana da abinda ya hanaki zuwa salla. Kema ina ruwanki da ganina anan to. Naga dai company na ne, ina da damar shiga duk inda nake so a lokacin da nake so ko”.
Yanzu kam sosai hawayen suka ciko mata idanu, ta tsatstsaresa da kallon da bama tasan tana yi masa ba. Cike da rauni ta ce, “Kadai fi son ka ganni a masifar ko Ajwaa....” ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya watso mata. Baki ta sake tunzurawa sosai. Baki ya ɗan laɓe ya janye idanun ya sake kai hannu zai ɗauka meet pie ɗin da ya rage saura biyu kawai. Ai babu shiri ta kai hannu ta buge nasan cike da tsiwa ta ce, “Malam wai miye haka zaka cinye min abinci”.
Bai kulata ba ya ɗauke bowl ɗin ma gaba ɗaya, sai da ya gutsira sannan ya kalleta cike da iskanci yana wani ƙanƙance su ƙasa-ƙasa ya furta, “Ko mai meat pie ɗin ta kama ba sai na.....”
“Na shiga uku. Sai kayi mi?..” Maanal ta faɗa tana mai waro dukkan idanunta a kansa. Kaɗan ya rage ya kwashe da dariya. Amma dai ya dake ya basar. Sai ma dan neman magana ca yay, “Ni kibar min wannan kallon karna ƙware. Sannan miye wani kin shiga uku bana son fassara zance. Sai nayi ƙyautarki nake nufi”.
Harara ta watsa masa ta koma kan kujerarta ta zauna. Dan ta fahimci idan ta biye masa ALLAH zama ta iya zubewa a wajen. Pretending ɗin danna keyboard ta koma yi, shi kuma ya cigaba da cin meat pie ɗin yana duba drawing papers na zanen da tayi dake yashe a desk ɗin. A haka ya kammala cinye mata tas babu ko tausayi balle ya rage mata, ya ɗauka ruwan da tasha ta rage ya shanye. Sannan ya maida gaba ɗaya hankalinsa ga papers ɗin. A bazata taji saukar furucin sa cikin kunneta.
“Kiyi gaggawar dakatar da Rafeeq yin abinda kika saka shi, in ba hakaba zaki haɗa rigimar da ke kanki baki san ƙarshenta ba”.
Kallonsa kawai ta ɗago tana yi dan kamar ba shine yay maganar ba. Dai-dai nan Ema... Da Zaharadeen suka shigo suna dariya. Cak suka tsaya tare da jan birki saboda cin karo da abinda basu yi tunanin gani ba. Boss da kansa a office ɗinsu. Tashin hankali. Cikin firgicewar bazatar ganinsa da sukai suka shiga gaisheshi. Sai lokacin ya ɗago ya zuba musu kaifafan idanunsa. Yayinda Maanal ke jin kamar ta fasa ihun da sai Abuja tayi girgiza gaba ɗayanta. Dai-dai nan suma wasu biyun suka sake kawo jiki, ai a sukwane suka taka birkin da yafi nasu Deeni. Shiko tuni ma ya ɗauke idonsa a kansu ya cigaba da dube-dubensa kamar bai san da kowa ba a wajen sai kansa. A haka har suka gama shigowa, babu kuma wanda zai shigo bai taka birkin firgici ba da ganin CEO ɗin. Shi kuma yaƙi kulasu sai jeruwa suke kamar ƴan