Showing 117001 words to 120000 words out of 221978 words
Chapter 40 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
nayi, masu hotuna nayi, masu guɗa nayi harda ƙawayen amarya. Dan babu kunya hatta amaryar ma tana a gidan abinta sai washare baki take da jin kanta sama ƙololuwa, dan tasan ita kam ta wuce tsara sai dai ta taya ƴan baya da addu'a kuma, amma 2025 kam tata ce...
Tukuyci na miliyan ashirin aka bama ƴan kawo lefe suma da tarin kayayyakin snacks da akai packaging, sai drinks da ruwa katon-katon, dambun kaji, danbun jan nama, soyayyu da gasassun raguna a ƙyafe guda biyar. Lallai wannan al'amari ya kai duniya tasan da shi. Dan kuwa ba garin Kaduna kawai ba duniya ce ta ɗauka sakamakon yanda komai ke yawo daki-daki a media tako ina. Dan hatta tarbar da suka samu da shagalin da akai a gidan Aunty Sabuwa shima anata ɗorawa. Hakama tukuyci da kayan alatun da aka maƙare musu motar da ta kawo kaya shima dai duk an ɗora. Hakan ya sakama jama'a kwaɗayi da shirin son ganin yanda wannan shagalin biki zai kasance na ƙwarya tabi ƙwarya. Wanda kuma suka san ainahin waye uban amaryar dan bai kai ko kwatar dukiyar uban ango Alhaji Usman Chalawa ba nata mamakin hidimar da su ma su Aunty sabuwar sukayi.
To kowa dai na son yaga yanda za'a kwashe kam, dan in dai har kawo lefe kawai duk akama waɗan nan hidimomin ai taron biki kam dole ko mu ƴan kallo mu kasance a cikin shirin shan kallon (😂 lolz)....
______________★
Sosai kasancewar su Oum a asibitin ya ɗan ragema Maanal nauyin da zuciyarta tayi. Dan ma hankalin Oum ɗin ya rabu biyu saboda AA. Dan shi ma bayan Doctor ya dubashi sosai sun ɗan kwantar da shi amma yace na yini ɗayan ne kawai. A wannan yanayin Shahidah ta iso asibitin ta samesu. Tayi farin cikin ganin Oum sosai. Kasancewar an hana kowa zama a ɗakin da AA yake dan suna son ya samu barci sosai duk sai suka tare anan ɗakin Maanal ɗin. Sai bayan sallar azhar da AA ya farka Oum ta nufi can. A lokacin ita kuma Maanal ta samu sallama. Koda suka gama tattare kaya zuwa mota Shahidah tasa Maanal gaba tai domin duba AA. Bata so hakan ba, sai dai bazata iya musu da Didinta ɗin ba. Musamman daya kasance RK na tare da su ne.
RK ne ya fara shiga bayan yayi knocking an bashi izinin shiga. Sai Maanal, Shahidah a ƙarshe. Oum na zaune a kujera, shi kuma AA na kan gadon ya jingina da filo Oum zata fara bashi abinci a baki, sai faman ɓata fuska yake alamar baya son cin abincin ko kuma duk ciwon ne oho masa. Plate ɗin abincin Oum ta ajiye tana kamo hannun Maanal da faɗin, “Masha ALLAHU ƴan matana anyi sallamar dai?”.
Kai Maanal ɗin ta jinjina mata a ɗan shagwaɓe. Ita kuma tayi murmushi da faɗin, “To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne.”
Amin RK da Shahidah suka amsa da shi, kafin Shahidah ta maida hankalinta ga AA daketa kallonta. Duk da yasan dama zai iya ganin nata, amma sosai mamakinsa ya bayyana amma ya gagara iya cewa komai. Wannan ba komai bane daga halayensa, dan haka Shahidah bata damu ba, sai dai zafinsa da suke ji tun na shekarun baya akan ƴar uwarsu taji yana taso mata. Komai dawo mata yake kamar yanzu ne yake faruwa. Da ƙyar ta iya dannewa ta tambayesa jikinsa. Karan farko yay ɗan murmusa, irin guntun murmushin nan mai tabbatar da ƙunar zuciya. Tabbas yaga tsanarsa a bayyane akan fuskar Shahidah, hakan na nufi har yanzu suma basu mance komai ba, basu mance abinda ya faru ba suna riƙe da shi a ransu fiye ma da Maanal. Baiga laifinsu ba, dan ko shine hakan zai yi, amma inama zasu fahimcesa kamar yanda Oum ta fahimcesa bayan ya zauna da it.....
Maganar RK ce ta katse masa tunaninsa, ya ɗan kallesa sai kuma ya janye idanunsa yana jinjina masa kai. Baya son sakama ransa tsanar ɗan uwansa kodan daraja da kimar Oum, amma tabbas zafinsa yake ji, kishinsa yake ji mai tsanani akan Maanal. Ta yanda ya gwammaci ya dinga masa shiru akan abubuwa da dama fiye da yin magana.
Sai yanzu Maanal da tunda tai masa kallo ɗaya bata ƙara ba ta furta, “Ya jiki?”. Daga haka tai shiru. Shima sai bai amsa ba, ya dai ɗago idanunsa ya kalleta kawai. Yana ƙoƙarin janyewa akai knocking ƙofar. Shahidah ce ta amsa sannan ta bada izinin shigowa. A hankali aka turo ƙofar, yana sanye cikin lallausan farin yadi da yay masa matuƙar ƙyawu, sosai kamanninsa da AA ke a bayyane, ta fuska da ɗabi'u. Sai a shekaru ne kawai suka banbanta da hasken fata. Ɗan ja yay ya tsaya turus yana kallon Shahidah da itama take kallonsa, sai kuma tai saurin kauda idonta. Shima janyewa yay ya maida ga Oum, sai kuma ya sake waresu akan Maanal da itama take kallonsa. Cikin kasa daurewa ya ce, “Oum kinga mi nake gani?”.
Murmushi sosai Oum ta saki mai ciwo, sai kuma ta jinjina kanta da faɗin, “Na sani Fadeel. Shahidah ce da Lillyn ka”.
“Wai da gaske ne kenan?”.
Yanzu kam har sai da hakwaran Oum suka bayyana a waje, sai kuma hawaye suka ciko mata idanunta. Da ƙyar dai ta iya dannewa ta sake bashi amsa........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣1️⃣
______________
.......Matuƙar mamaki Babban Yaya ya shiga da jin komai daga bakin Oum da RK. Sai satar kallon Shahidah yake da jinjina mamakinsa akan canjawar Maanal. Ta ƙara tsaho duk rashin jin nan da rawar kai babu yanzun. Hakan ba abun mamaki bane ba, musamman idan aka tara yanda abubuwa suka kasance zama a iya ganin fiye da hakan daga Maanal. Nan fa ya tasa Maanal da tambayoyi har ma da Shahidah duk da shi ɗin ba gwanin yawan magana bane ba.
Maanal ce mai amsa masan, dan itama Shahidah tana amsa ɗai-ɗai ne. Itafa Family ɗin nan idan ta cire Oum a ciki da Fawzan da Abah da Mamy bata jin sauran a ranta yanzu. Sai ma wani kalar zafinsu da take ji, amma darajar Oum yasa taketa ƙoƙarin dannewa dan Oum ta cancanta. Ana cikin hakan sai ga Fawzan shima ya iso, bayansa matarsa ce Nibras, sai Saheeba matar babban Yaya hannunta riƙe da ƴar budurwar yarinya mai tsananin kama da su Babban yayan. Sai budurwar yarinya ƙyaƙyƙyawa a ƙarshe biye da su hannunta ɗauke da irin box ɗin nan da ake saka kayan abinci. Ambatar sunan Lilly da Shahidah da Fawzan yayi ya saka Saheeba kallon sashen da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna da Shahidahn. A take fara'ar fuskar Saheeba ta ɓace ɓat. Itako Shahidah ta janye nata cike da basarwa tana bama Fawzan amsar maganarsa. Ita dai Nibras bata sansu ba a zahiri. Amma sunayen da aka ambacesu da shi ya sata tsatstsaresu da idanunta, dan ta ɗan san labarin dangantakar tasu da familyn Darma a wajen mahaifiyarta. Sai dai kuma bata da tabbacin waɗan can ɗin ne ko wasu daban.
Ita ko budurwar data shigo a ƙarshe gaba ɗaya hankalinta naga AA ne. Dan tuni ma ta kai gaban gadon babu ko kunya ta zauna a kusa da shi. Sai dai hararar daya jefa mata ta sata miƙewa tsaye zambar tana faɗin, “Sorry Yaya”.
Komai baice mata ba, ita kuma bata nuna damuwa ba ta ɗan rissina tana gaisheshi da tambayarsa jikin nasa. Sai kuma ta jawo kujera dake can jikin ɗayan gadon dake a ɗakin dan gado biyu ne Naufal na barci a wajen ta zauna kusa da shi sosai. Dai-dai nan Shahidah ta miƙe tana faɗin, “ALLAH ya ƙara lafiya bara mu wuce Maanal ta samu ta huta.”
Wani irin ɗagowa budurwar mai suna Nuratu tayi jin sunan Maanal a karo na farko. Sai a yanzu ta kalla Oum kasancewar Maanal ɗin na'a jikin Oum kamar ƴar mage. Tabbas bata san Maanal ba a zahiri itama a wancan lokacin na ƙuruciya dan ita ta rayune ba'a gidansu ba, yayar babansu ce ta riƙeta suna zaune a Lagos. Bayan rasuwar mijinta ne suka dawo Abuja, amma tasan komai na labari tsakanin yarinya mai suna Maanal da Yaya AA ɗinta. Burin ranta, da take fatan ya zama miji a gareta tun a randa ta fara tozali da shi a Lagos. Ƙoƙarin tuna inda tasan fuskar Maanal take yi, dan haka ta kafeta da idanu. Ƙirjinta ne yay masifar bugawa lokacin da suka haɗa ido da Maanal dake miƙewa Oum riƙe da ita. Sarai Maanal ta ganeta ita, hakan yasa ta janye idanunta cike da basarwa. Itako Nurry ta kasa janyewa dan ta gane Maanal itama, itace yarinyar da suka haɗu a wajen saloon ranar Sunday ɗin data gabata. Jitai jikinta kawai ya fara rawa, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri saboda tsoron abinda take hasashe, cikin rawar murya da suɓutar baki ta furta, “Wai itace Manaal ɗin da nake jin labari a gidan su Mamy na Kano Aunty Saheeba?”.
Ba Saheeba data ambata ba, hatta su Babban yaya sai da suka dubeta, shi kansa AA wani kalar mugun kallo ya zuba mata ita da yayar tata Saheeba duk da matar yayansa ce. Sai kawai jikin Saheeba da Nurry ya kama tsuma. Cikin daburcewa Saheeba da kallon rashin mutuncin da Babban yaya ke jifanta da shi gana AA a gefe ya gama rikitata ta ce, “Wlhy ni ba wani bad abu na sanar mata akanta ba. ALLAH ma ne shaida bani na gaya matan ba. Nuratu ko'a bakina kika ji?”. Ta juya tana kallon Nuratu da zuciyarta ke mazari. Dan ta fahimci itama katoɓarar data nema yi. Sai dai kuma wani irin jin tsanar Maanal ke sake haɗa wutar guguwa a can ƙasan ranta. Kai ta girgiza ma Yayar tan, sai kuma ta ce, “No nima fa ba ina nufin wani bad abu bane ba wlhy ko aka sanar min a kanta. Kawai na faɗa ne ta yanda zan tabbatar da ita ɗin ce bawai dan wani abu ba.”
Fawzan ne ya girgiza kansa kawai da katse yanayin ta hanyar faɗin, “ALLAH ya ƙyauta to. Amma wannan maganar ma baida wani amfani. Ƙanwata muje na saukeku gida ko”. Ya ƙare maganar idonsa akan Shahidah. (Da ada ne catake ita ba ƙanwarsa bace). Suyita musu da jayayya, dan da gaske Fawzan ya girma Shahidah ɗin da kusan shekara uku, kusan ma za'ace AA ne sa'anta. Amma ta girmesa itama da wasu watanni. Alaƙar Shahidahn da babban Yaya yasa suke ƴar jayayyar da Fawzan ɗin sarkin barkwanci da tsokana.
Murmushi Shahidah tai masa da faɗin, “A'a mun hutasheka Yaya Fawzan. Da mota ma nazo shiyyasa nace shima Rafeeq ya huta abinsa.”
Sai a lokacin RK da komai ke masa kaikawo yay magana. Maanal da tuni tai gaba ya kalla. Dan ita ko kallon Nurry batai ba balle wani dake ɗakin akan maganganun. Hasalima bata nuna tasan anayi ba, tunda tabar jikin Oum tai hanyar ƙofa abinta. Kai kawai ta jinjinama RK da sakar masa ɗan murmushin daya sake tokare maƙoshin AA tai ficewarta. Itama Shahidah sai kawai ta bita tana wani jin sake tsanar wannan family.
Biyosu RK yay da sauri, hakama Oum. Dakatar da RK Oum tayi, kafin ta ƙarasa inda Shahidah ke ƙoƙarin buɗe motarta ta riƙo hannunta. Da sauri Shahidah ta juyo, sai kuma ganin Oum ya sakata sakin murmushi. “Lah Oum ko munyi mantuwa ne?”.
Fuskar Oum cike da damuwa ta ce, “Ba mantuwa kukai ba Shahidah, haƙuri zan baku. Dan ALLAH kada abinda yarinyar can Nuratu tayi ya dameku. Nasan koda wani abu taji ba wanda kuke tunani bane ba. Dan dukkan abinda ya faru sirrine da iya mu da ku muka sanshi. Ni......”
Da sauri Shahidah ta shiga girgiza mata kai, “No Oum dan ALLAH kar kice komai. Mu tsakaninmu dake sai addu'a da fatan alkairi. Kamar yanda tun farko muke miki kallon uwa yayar Ammie haka har gobe wannan matsayin naki bai goge ba a zukatanmu. Bamu taɓa riƙeki a ranmu ba. Kosu wlhy albarkacinki dana Abah da Mamy suke ci har muke jin komai ya wuce kamar bai faru ba. Abinda ya faru ƙaddararmu ce mu duka da ku, babu kuma wanda ya isa ya iya canjata ba gashi komai ya wuce kamar ma bai faru ba”
“Na sani Shahidah, amma idan na tuna nakan ji na tsani dukkan kaina wlhy. Kuma ina sha ALLAHU addu'ar da nake tsahon shekaru bazata taɓa tafiya a banza ba. Da izinin UBANGIJI sai Ajwaad ya gyara ɓarnar da yay da kansa. Gaskiya kuma saita bayyana. Abinda duk ke a ɓoye zai fito fili”. Kuka ya sarƙe Oum...
Rungumota Shahidah tayi, yayinda Maanal tai saurin shigewa mota hawaye na gudu akan fuskarta. Jikinta sai rawa yake yi. La'ilaha'illa antas-subahanaka inni kuntu minazzalumin ta dinga ambata. Tsohon lokaci har bata san mi Shahidah da Oum suka cigaba da tattaunawa ba Shahidah ta shigo mota. Komai basu cema juna ba sai murmushin da Maanal ta ɗan sakar ma Oum dake mata magana ta ɗaga mata hannu....
Komai dake faruwa a idanun RK ne dake tsaye daga can nesa da su. Shifa gaba ɗaya an ƙarasa kulle masa kai. Yau ya fahimci lallai akwai wani babban al'amari daya shiga tsakanin wannan zumuncin. Sai dai miyyasa kowa ke son ɓoyewa ne? Anya bai kamata ya sani ba? To idan ya sani amfanin mi sanin zai masa. Kawai yana son Maanal hakan ya wadatar da shi. Idan lokacin ya san komai a tarayyarta da Darma Family yayi yasan zata sanar masa duk da ƴan uwansa ne jininsa na kusa kuwa. Koda Oum ta iso inda yake bai tambayeta komai ba. Sai ma murmushi da yay mata yana mai nuna mata hanya alamar suje. Zuba masa idanu Oum tayi sosai, sai kuma a hankali ta furta, “Rafeeq! Da gaske kana son Maanal?”.
Idanunsa sosai ya waro a kanta, sai kuma ya narke fuska cike da nuna damuwa ya ce, “Haba Aunty, wane irin tambaya ce wannan mai tarwatsa zuciya. Kema shaida ce ban taɓa kawo wata yarinya gareku da sunan soyayya ba. Miyyasa kuke ganin komai na kamar ba serious ba?”.
“Sam ba haka bane ba Rafeeq. Nasan kai mutum mai son wasa ne. Amma ban taɓa kallon al'amuranka a matakin rashin serious ba. Itama tambayar na maka itane kawai.”
Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “In sha ALLAHU Aunty zan tabbatar muku da babu wasa akan batuna da Maanal. Dan yanzu haka ma ta bani damar zuwa Kaduna na gana da Daddynta a next week”.
Cak Ammie ta tsaya gabanta na faɗuwa. Dan lips ɗinta har ɗan rawa yaso farawa amma tai ƙoƙarin dai-daita kanta da ƙyar. Sai kuma ta sakar masa murmushi kawai da faɗin, “Masha ALLAH, idan mukaje gida zamuyi magana”....
Koda suka dawo ɗakin sun sami babban yaya nata zuba faɗa ma Nuratu. Ta inda yake shiga tata nan yake fita ba. Sai shigowar Oum datai masa magana ya tsagaita. Amma duk da haka a fusace yace su wuce su koma gida ba'a buƙatar sake ganinsu a asibitin ma. Haka Saheeba da Nibras da ita Nuratun suka fita ransu a ɓace suma. Sai dai babu damar magana dan tabbas babban yaya da AA basu san wargi ba. Koshi Fawzan dake da yawan barkwanci bawai ya saki kansa bane raini ya shiga tsakaninsa da Matarsa ma balle ita Nuratun. Hatta da ita Saheeba dake matsayin matar babban yayansu da suke matuƙar girmamawa babu raini a tsakaninsu dan matsayin ƙanwa take a wajensa.. Anan suka bar yaran, dan tuni Anum maƙalƙale take da jikin Fawzan dama tun fara faɗan Daddynta. Shi ko Naufal har yanzu yana barci ne.......
____________★
Koda suka iso gida daga Shahidah har Maanal basu sake tada maganar nan ba. Shahidah tayi hakan ne kawai dan gudun tadama Maanal hankali, sai da ta shiga ɗakinta tai kiran Amaal suka tattauna. Sun jima akan wayar suna magana har Maanal ta shigo sannan Shahidah ta yanke kiran dan bata son tasan da Amaal ɗin take waya. Itama Maanal bata damu da sanin dawa Shahidahn ke wayar ba. Sai ma zama da tai a bakin gadon nata.
“Har kinyi wankan?”.
Kai Maanal ta jinjina mata cike da ƙarfin hali. Sai kuma tai ɗan murmushin san kore damuwar nan ta ƙarfin tsiya sannan ta furta, “Naga mutiniyarki na haɗa kaya fa ko Kaduna zataje ne itama?”.
Da mamaki Shahidah ta ce, “Wai Huznah?”.
Kai Maanal ta jinjina mata. Ita kuma tace, “Humm to ita dai ta sani, ai garama ta koma ɗin dan nikam