Showing 42001 words to 45000 words out of 221978 words

Chapter 15 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

kwana biyar bai leƙoku ba tunda yana Abujar shima.”
“Wlhy kuwa bai zoba Ammie, nama zata ko yana Kaduna ko yayi tafiya ne wani waje. Amma naga yana ƙoƙarin kiranta a waya yaji lafiyarta. Wai Ammie miya faru ko ɗaura musu aure kukai? Ko har yanzu Mamma ɗin ce ke tijarar bata son?”.
Ƴar dariya Ammien tayi da faɗin, “Kefa daɗina dake shirme Shahidah. Auren lafiya kuma yarinyata na a wannan halin na ciwo mai girma irin wannan hauka nake zan bari a mata aure bada amincewarta ba. Akan dai Hajiya Yaya ne da batun auren......”
Tsaf Ammie ta zayyanema Shahidah yanda komai ya faru da kuma matsayar da ake akai yanzu.
“Kai wannan mata ALLAH ya rabamu da masifarta Ammie. Ita dai ta sani mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi ma, dan wlhy garama ta auri Rafeeq ɗin amma haɗata kishi da wannan ƴar iskar yarinyar sangartacciya ai wani hatsarinne. Zasu iya haɗe kai su dinga cutar da ita watarana mu wayi gari zuciyar tata ta buga. Amma kinga Rafeeq ɗin nan wlhy Ammie yana da hankali da tarbiyya. Damma Maanal ɗin ce taƙi sakin jiki da shi kin dai san halinta”.
“Karki damu a hankali ne. Kudai ku cigaba da tayata da addu'a. Watarana ai sai labari. Amma in sha ALLAHU batun Yazeed kam nima bana mata fatansa kuma suje can su ƙarata. Yanzu ki bani zuwa gobe zan yi magana da Daddyn naku, idan ya tirje sai shi mijin naki ya masa magana ko naje Zaria na haɗashi da abokin nasa.”
“Shike nan ma Ammie wlhy dama haka kikayi”.
“A'a bari dai na fara masa magana dan bana son butsutsunsa. Yaya jikin autar?”.
“Alhamdullahi Ammie jikinta na ƙyau sosai. Dan naga har ta koma karance-karance novels ɗin nata na fama. Gata can ma tana shiri Abban Barru yace idan ya dawo zai kaita bookstore ta samo wasu”.
“To Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Nima zan shigo na sake ganinta in sha ALLAHU zuwa next week haka komai ya ƙara lafawa.”
“ALLAH ya kaimu Ammie muna nan muna jiranki. Itama Amal tace next week zata dawo”.
“To shike nan idan naga zai mana dai-dai sai kawai mu taho tare, amma ni ranar zan dawo gaskiya”.
“Kai Ammie miyasa bazaki kwana ba?”.
“Daga dubiya sai kawai na kama kwana. Tunda ina jinku kullum a waya ai Alhmdllh ya wadatar, ba kuma sai na zauna na kula da tsohon mijina ba da ƙananun ƴaƴana”.
Dariya sosai Shahidah ta sanya. Daga haka sukai sallama....


___________★


Kamar yanda Ammie taima Shahidah alƙawari ta tunkari Daddy da batun aikin Maanal. Sai dai kuma kamar fa yanda tai tunani ya nuna ɓacin ransa. Ya kuma tujareta da masifa dan dama yana riƙe da takaicinsu ita da Hajiya Basariyya a rai. Kasa magana Ammie tai sai duƙar da kanta kawai tai tana saurarensa. Sai da yay mai isarsa yay shiru dan kansa sannan ta tashi ta kwanta dan dama itace da shi a yau ɗin. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka dinga rige-rigen sakko mata. Sosai tausayin kanta dana iyalanta ke ƙara girma a zuciyarta. A rayuwarta tayi farin ciki ne da samun ƴancin kai na shekarun ƙuruciya kawai. Amma tun daga randa aka lulluɓa mata zanen aure zata iya cewa daga lokacin ƘADDARARTA ta fara. Daga lokacin ta fara tantance gatan iyaye da ɗacin rabuwa da su. Daga lokacin komai ya canja, sunanta na Asiya sarauniya ya canja zuwa Asiya baiwa. Eh dole tace bauta, duk da a zahiri baza'a kalli rayuwar tata ata mai bauta ba kasancewar wasu abubuwa sun mata ado a bayyane. Sai dai wanda yasan ainahinta ne kawai zai san minene mizanin bautar da take magana da ƴancin kai. Ansha gwagwarmaya na tsawon shekaru kafin ALLAH ya iyakance, iyakancewar bai zama sauƙi ba kai tsaye, wata sabuwar jarabawar aka sake shiga, ta yanda zaren ƙaddarar ne ya kawota a wannan matsayin da take a yanzu kuma. Bazatai butulci ma UBANGIJI ba, domin kuwa Alhamdullah, ta samu canje-canje masu yawan gaske a sabuwar rayuwarta, sai dai anan ɗin ma ta gamu da wata jarabawar rayuwa a cikin mugayen kishiyoyi da kansu kawai suka sani......
“Asia! Kuka kike yi?”.
Furucin Daddy ya katse mata tunaninta. Da sauri ta saka hannu cikin dabara ta share hawayenta, sannan ta juyo garesa fuskarta da murmushi. “A'a Daddyn Hameed wane irin kuka kuma. Kawai dai na kwanta ne”.
“Humm Asia kenan, nasan kuka kike, kina kuka saboda kina ganin kamar na tauye hakkin ki dana ƴaƴank.....”
“Ya arrahaman”. Ta faɗa da sauri tana mai gaggawar ɗaura tafin hannunta a saman bakinsa. Zuuuu hawayen da take riƙewa suka shiga zirarowa. Kanta ta fara girgiza masa da sakin kukan gaba ɗaya. “Dan ALLAH kada kace haka Daddyn Hameed, ban taɓa raba ɗayan biyu a tsakanin su Maanal da sauran yaranka ba. Ni kaina inama mantawa bakai ka haifesu ba, saboda kana musu dukkan abinda uba kema ƴaƴa. Kana musu abinda mahaifinsu ya gagara musu. Taya zan kasance butulu waje rarrabe gaskiya da akasinta. Dan ALLAH ka gafarceni idan nayi kuskure, wlhy ban nema amincewarka ga Maanal tayi aiki dan baƙanta maka rai ba ko ƙasƙantar da dokar ka b.....”
“Shiiiii!! Ya isa kukan haka to”.
Daddy ya faɗa yana mai jawota jikinsa ya rungume murmushi shimfiɗe a fuskarsa. A hankali yake shafa bayanta cike da lallashi. Tsahon minti ɗaya kafin ya furta, “Nasani Asia. Na kuma yarda dake ɗari bisa ɗari. Domin nasha gwadaki akan yaran nan batare da kin sani ba ke kanki kuma kina cinye jarabawar. Babu abinda zance dake sai godiya. Domin tabbas a cikin matana kina gaba a wadda nake alfahari da ita. Bance miki suma sauran sun gaza ba ko basu da martabar da nake kallonsu da ita ba. A'a ku dukanku kowa da inda yake tausasa min da kuma inda yake tsaurara min, amma kina da manyan lambar yabo kashi-kashi a gareni da bazasu lissafu ba Asia. Hakama su Shahidah, ni kaina biyayyarsu a gareni da girmamawa yakan sani manta ma bani na haifesu ba, ina jin alfahari da su, ina kuma godema ALLAH daya bani su matsayin ƴaƴana a yanzu. Ba aiki bane bana son Maanal tayi, domin nima na fahimci hakan zai taimaka mata ya ɗauke mata kewa musamman da nima nasan harkar zane-zane hubby nata ne. Kawai dai ina jin haushinki ne da tunanin baki son haɗa jini dani, shiyyasa yau ba fanshe haushin ta nan, sai nake ganin kamar baki son wannan haɗin da nake sonyi ne Asia. Alhalin ni kuma na ƙwaɗaitu ƙwarai da gaske da son ganin jinina ya sake gauraya da naki kozan cigaba da samun nagartattun zuria daga tsatsonki a cikin zuri'ata. Hakan zai sake dunƙulemu ya curemu waje guda. Tun akan Amal naso nayi wannan haɗin, sai na fahimci hankalin Yazeed akan Maanal yake shiyyasa na ƙwallafa raina a kanta.”
“Kayi haƙuri Daddyn Hameed sam ba haka bane kamar yanda kake tunani. Ka fahimceni dan ALLAH. Wlhy koda bana aurenka zan iya bama Yazeed auren Maanal. Domin ya taimakemu a gaɓar da muke matuƙar bukatar taimako. Zanma iya cewa ALLAH ya ƙaddara Manaal nada sauran kwana ne a duniya amma ya saka sanadin hakan a hannun Yazeed. Domin da ace kwannata ya ƙare tun a randa muka fara haɗuwa da sai dai wani zancen ake ba wannan ba. Dan haka ban taɓa jin bazan bama Yazeed Maanal ba. Kawai dai hankalina na matuƙar tashi kasancewar bakowane ɓangare bane ke buƙatar wannan haɗin, hakan kuma zai iya cutar da Yazeed ɗin kansa da ita kuma Maanal ɗin dake fama da rauni irin na ciwo mai haɗari. Amma yanzu masalahar da aka samu zai taimaka komai ya zama dai-dai itama ta samu sassauci haka shima Yazeed ɗin. Dan koba komai Hajiya Yaya mahaifiyace tana da tata darajar. Sannan Yazeed ya san komai daya shafi rayuwar Maanal, basai anyi sabon zama da zagaye-zagayen faɗa masa da fargabar zai amsheta ko zai canja ra'ayi”
“Hakane Asia. Na kuma fahimceki yanzu ɗari bisa ɗari. Zan kuma cigaba da addu'ar zaɓin ALLAH akan al'amarin insha ALLAHU. Sannan abinda ya shafeta ki daina wani damun a kansa kanki ai ƙaddara ce, bata wuce kan kowa ba kuma, ALLAH kuma shine shaida bataje takai kanta ba domin yin hakan jarabawace, wanda ma suke aikatawa kai tsaye ko suke zuwa bariki su kama ɗakin kansu suke auruwa cikin salama da kwanciyar hankali yanzu a ƙasar nan balle ita. Saboda haka na amince Maanal tayi aikinta. ALLAH ya sanya albarka ya kuma sa hakane yafi alkairi.”
Wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyar Ammie. Ta ƙanƙame Daddy da ƙyau tana amsawa da amin. Shima murmushi ya saki mai faɗin gaske da karɓarta sosai ya rungume. A ransa kuwa yana sake ganin fara aikin Maanal ɗin wata masalaha ce. Dan zai fake da shi bayan anyi auren suyi zamansu acan, ita kuma wannan zaɓin uwar Yazeed ɗin anan cikin gidan yake son ta zauna tare da su saboda wasu dalilansa......


Tofa, mi kuke tunanin wai ya faru da Maanal ne?🥺. Sannan zamuga yanda wannan cakwakiya zata ƙare😂🏃.


__________★


Wani irin farin ciki ne ya mamaye Maanal lokacin da saƙon Daddy ya risketa akan amincewarsa tayi aiki. Su kansu su Shahidah sai da suka tsaya suna kallonta ganin yanda taketa murmushi yau kamar ba Maanal ba. Sai suma hakan ya sakasu a farin ciki. A karo na farko na tarihi Maanal taima RK text massage da albishir ɗin amincewar Daddy. Ai ba'a haɗa awa guda ba sai ga bawan ALLAH a gidan. Yau ko lallaɓatan da Shahidah keyi na taje ta samu RK ɗin ba'ai ba. Yana kiranta yace gashi a gidan sai gata babu jimawa ta fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya jarabcesa da son wannan halittar ƙwarai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta in har hakan shine alkairi a garesu. Maanal ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon ƙurillar da yake matan. Baice komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta sharesa kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata da kulawa, kafin ya ɗora da tambayar yanda abubuwa suka kasance. A taƙaice ta faɗa masa, bai damu ba dan ya gama karantar ta zuwa yanzu. Bata da son yin doguwar magana sai idan itace taso hakan da kanta. Shine ya dinga zuba mata zance da yanda abubuwa zasu kasance. Ya kuma tabbatar mata nan da kwana biyu zaizo ya amshi takardunta. Ya kuma buƙaci ta ɗan zazzana wasu samples na agogunan zaizo ya amsa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai sake nunama mai Companyn. Duk da dai ya nuna masa wanda ta zana a asibiti. Ta tabbatar masa babu damuwa zatayi ɗin, daga haka sukai sallama ya fice ita kuma ta shiga gida.
Kamar ko yanda sukai alƙawari a wannan daren ta nutsu ta zana agoguna masu shegen ƙyau da ɗaukar hankali fin kala goma. Dan har gabannin asuba tana wannan aikin. Hakan ya saka mata makara. Tana yin sallar asubahi kuma ta sake kwanciya. Bata farka ba sai ɗaya saura. Ta samu RK yazo ya amshi zanen ma. Dan sun sanar masa tana barci yace kada a tasheta a barta tai barcinta, a bashi zanen kawai. Yana kuwa amsa bai jima ba ya wuce abinsa. Sai da ta tashi take jin yazo ɗin ya amsa. Har ta ɗauka waya kamar zata kirashi sai kuma dai ta fasa kawai. Tata tsumayen nasa kiran amma shima sai bai kira ɗin ba har dare. Sai da tana shirin kwanciya ne ma saƙonsa ya shigo.
_“Ina Kaduna yanzu haka. Mun gana da Daddy da Ammie, na kuma amso takardunki suna hannuna. Amma sai da safe zan dawo Abuja in sha ALLAHU. Kiyi barci cikin aminci tare da mafarki mai nutsuwa gimbiyar mata”_.
Baki kawai ta taɓe tare da jefa wayar saman gado ta cigaba da saka maɓallan rigar barcinta. Sai kuma ta tsaya cak kalamansa na dawo mata. Ya gana da Daddy da Ammie kamar yaya? Kai itafa shishshigin mutum nan ya fara bata tsoro. Kaji bala'i ko mi ya kaisa Kaduna?. Rashin mai bata amsa ya sakata jan ƙaramin tsaki ta haye gadon kawai ta kwanta. Addu'a tayi kamar yanda ta saba sannan ta kashe wutar ɗakin tana sauke ajiyar zuciya.........✍️




✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖2️⃣1️⃣




.......Maanal bata sake jin labarin RK ba tun ranar. Ya dai kirata washe gari yace ya dawo Abuja. Daga haka bata sake jinsa ba. Gashi ita kuma ta ƙagu taji yaya ake ciki. Dan haka kawai sai ta ƙwallafa ranta a aikin saboda zaman waje ɗayan kuma ya isheta. Da yaran Shahidah sun wuce makaranta itama da mijinta duk aiki suke fita, sai ita sai mai aiki kawai. Bata da aiki sai karatun novels da kwanciya. Amma kasancewarta sarkin kamewa da dakiya sai bazaka taɓa fahimtar hakan ba kai tsaye. Sati ɗaya dayin hakan sai ga Ammie da Amal sunzo. Matuƙar farin ciki Maanal ta kasance a wannan ranar, gashi weekend ne duk masu gidan suna nan. Yini sukai dan Ammie tace bazata kwana ba. Babu irin shagwaɓar da Maanal bataima Ammie akan ta kwana ɗin ba amma tace sam ita bata sanarma Daddy zata kwana ba. Haka babu yanda zasuyi bayan magrib suka rakasu train station kasancewar jirgin ƙasan zasu bi. Dama a cikinsa suka zo....


Kwanakin su Ammie biyar da zuwa da daddare tana shirin kwanciya sai ga kiran RK. Ido kawai ta sakama wayar tana kallo harta tsinke sannan ta kauda kanta. Sake kira akayi nan ma kamar bazata ɗauka ba sai kuma dai mita tuna oho mata tai yunƙurin ɗaukar, sai kuma taga bashi ɗin bane Ya Yazeed ne. Fuska ta ɓata shima kamar bazata ɗaga ba ta dai daure ta ɗauka. Gaisheshi ta farayi da girmamawa kamar yanda ta saba. Shi kuma ya amsa mata cikin nutsatstsiyar muryarsa dake nuna alamar a kwance yake. Sun ɗan yi shiru sai kuma ya katse shirun da faɗin, “Ina muka kwana akan batunmu Maanal?”.
Shiru tai kamar bazatace komai ba. Sai da ta mula dan kanta ta amsa masa da, “Yaya ni mikake son nace to. Ni duk abinda su Daddy suka yanke zanyi biyayya a kansa kawai”.
“Saboda dama baki sona?”.
“Ni dai Yaya bance ba. Amma ka tausaya mun mana. In dai kai namiji ka haƙura ka musu biyayya ni kuma sai naje nace ba haka ba.”
“Humm shike nan, amma ke yanzu baki jin kishin na fara auren wata kafin ke?”.
Karan farko ta saki murmushi mai faɗi, sai kuma ta zame ta kwanta. “Yaya ko naji kishi yaya zanyi. Ni dan ALLAH mubar ma maganar nan kawai ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”.
Murmushi taji ya saki da ga can, sai kuma ya ce, “Okay shike nan an barta. Tunda dai na gane ana kishina na gode”.
Shiru ta masa batace komai ba. Shima daga haka yay mata sallama akan maybe gobe ma ya shigo Abujan, zai kuma leƙo ya fara ganinta kafin ya fara sabgoginsa. Daga haka sukai sallama. Kamar jira RK yake dama, Yazeed yana yankewa kiransa na shigowa shi kuma. Sai yanzu ma ta lura ya mata kira yafi goma ashe sanda take wayar. Kanta kawai ta ɗan girgiza. Sai da tana gab da zata tsinke sannan ta ɗaga. Muryarsa a cinkushe ya mata sallama. Amsawa tai itama ciki-cikin tai shiru. Tsahon minti ɗaya babu wanda ya sake magana.
“Oh bama zaki gaisheni ba?”.
RK ɗin ya faɗa daga can. Yitai kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta ce, “Good evening”.
“Humm good evening to baturiya. Fatan kin yini lafiya?”.
“Lau”.
Itama ta amsa masa a daƙile jin yana mata magana cikin wani ji da kai.
“Humm! saboda kina waya da wannan tsohon tuzurun saurayin naki da baya dariya shine kika shareni.”
Ita dariya ma zancen nasa ya bata. Amma sai bata dara ɗin ba ta ce, “Hummm ashe kaima tsohon tuzurun ne tunda ba girmarka yay ba”.
“Oh zaki shigar masa faɗan ne kenan?”.
Shiru ta masa taƙi tankawa. Shima sai ya saki zancen kawai. Amma ransa fal kishin Yazeed ɗin. “Baki da kirki ALLAH, kwana kusan goma baki jini ba amma baki neman ba. Wannan wace irin soyayya ce?”.
“Kai dai ka sani. Rashin jinka kuma ai nasan lafiya ce ke ɓuya”.
“Humm borin kunya, ALLAH dai ya shirya min ke. Duk da baki tambaya ba bara na faɗa miki. Auntyna ce bata da lafiya a randa na dawo Kaduna da yamma jikin ya tsananta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login