Showing 195001 words to 198000 words out of 221978 words

Chapter 66 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

layin tuwon dare a boarding school (lolx🤣😂). Maanal kam ai ta kasa kallon kowa, tai ƙasa da kai kamar maƙaryaci a gaban sarki. Sai ta gefen ido ake ƴar kallan kallo tsakaninta da su Yaqub.
Fin mintuna biyar sai da ya mula dan kansa ya ajiye Drawing papers ɗin ya gyara tsaiwa sannan ya ɗago idanu ya sauke a kansu bayan ya zuba duka hannayensa a aljihun wandon suit ɗinsa. Babu alamar wasa a tare da shi ko sassauci ya ce, “Waye Abideen a cikinku?”.
Cikin tashin hankali Abideen ya ce, “Nine sir”.
Kallon sama zuwa ƙar AA ya masa. Sai kuma ya ja idanunsa ya maida a kan fuskar Abideen ɗin yana sauke masa wani zafafaffen kallo. Tsohon mintuna biyu kafin ya janye a matuƙar daƙile. Pen ya ɗauka a gaban Maanal da ƙaramar takarda ya fara rubutu, sai kuma can ƙasa ya furta, “Nawa suka biya ka?”.
A tare su Zaharadeen har ma da Maanal suka maida kallonsu ga Abideen da duk ya rikice. Rantse-rantse ya fara. AA da ko nuna yana ma jinsa baiyi ba ya ajiye pen ɗin da short note ɗin da yay a gaban Maanal ya miƙe sosai, batare da ya sake kallon kowa ba yay hanyar fita yana faɗin, “Ka tattara komanka ka saman a office”. Daga haka ya ratsa ta tsakkiyar hanyar da suka dare suka bashi ya fice abinsa.
Shi ko Abideen hankali tashe yake kirama kansa ya shiga uku ya lalace. Sai da AA yay nisa sannan su Yaqub suka sami damar baibayesa da tambaya. Maanal dai suman zaune tayi da mamakin mugun sabon halin da AA ya ɗauka yanzu. Koda yake tuni fa yana da mugun halinsa, kawai dai ƙuruciya yasa bata fahimta a wancan lokacin. To dan ALLAH in ba mugun hali ba taya zaka zo ka turke staff ɗinka a bainar nasi kana masa wannan kausasan tambayoyin na nuna isa da izza. Wai mi masu kuɗi suka ɗau kansu da rayuwarsu ne?......
“Sis.. Maanal dan ALLAH kizo muje ki bashi haƙuri, wlhy zan faɗa masa gaskiya....” furucin Abideen da ke binsu da wannan furucin su duka a birkice ya dawo da ita a hanyyacinta. Yayin da su Zaharadeen ke ƙoƙarin kamashi dan ya nutsu asan mafita. Amma ina duk ya ruɗe. Sai da ƙyar suka danna shi ya zauna a kujera. Ema ya bashi ruwa yasha.
“Ni dai shawarar dazan baka Abideen ka tashi kaje kasan dai boss baya son jira. Kuma tabbas tunda ya shigo office ɗin nan da kansa case ɗin nan naka babba ne. Amma ka rufama kanka a siri ka gaya masa gaskiya a tambaya ɗaya nasan zaka iya samun sassauci tunda ya tsani ƙarya ko kwalo-kwalo akan laifi kaima ka sani”.
Musa ne da wannan magana cikin damuwa. Dukansu sun gamsu da shawarar Musa ɗin. Dan haka duk suma suka shiga cema Abideen ɗin ya tashi yaje. Da ƙyar ya iya miƙewa ya fita. Duk suka bisa da kallo. Sai da ya fice gaba ɗaya Zaharadeen ya kalla Maanal cikin sauke ajiyar zuciya da ƙwarewa a gulma. “Sis... Manaal wai tun ɗazun boss yana nan ne dama? Sannan yayi wata magana ne?”.
Karan farko Maanal ta watsa masa harara. Cike da tsiwa ta ce, “Miyyasa baka tambayesa ba sanda yake nan? Ko sai ni marainiyar wayonka”.
Mutsut Zaharadeen ya haɗiye gulmarsa. Dan wani irin kwarjini ma yaga Maanal ɗin ta ƙara masa. Ga shi ta wani tsare sa da mayun idanunta masu haske. Harara ta rakashi da shi, sai kuma taja siririn tsaki ta maida kanta ga aikinta. Akan rubutun da yay ta sauke su. _“Ki saman ki bani amsata nan da awa ɗaya a office, in ba hakaba wlhy zan dawo da kaina na ɗaukeki na kaiki. Kar kiga ba canja topic yanzu tausayi kika bani”_. Muƙut ta haɗiye yawun daya maƙale mata a maƙoshi. Ita kam ga shiga uku da mutumin nan. Kafin ta samar ma kanta mafita Yaqub ya zauna dan su cigaba da aikinsu. Dole ta haɗiye komai da bashi hankalinta dan aikin mai muhimmanci ne. Sai dai kaso sittin na hankalinta ya tafi ga al'amarin AA ne da ƙarfin halinsa.....


_________★


Tunda taga awa ɗayan daya bata ya kusa cika hankalinta ya ƙara tashi, dan ta tabbatar AA baya faɗar magana bai cikata ba, tun ma kan yakai haka. Ta kasa samun nutsuwa, ta kasa tsaida zuciyarta waje guda. Ga Abideen har yanzu bai dawo ba tunda ya fita. Office ɗin nasu yanzu kam yay tsitt kowa damuwa shimfiɗe a fuskarsa. Sai dai fa kowa ya maida hankali akan aiki tuƙuru. Ganin fa saura mintuna biyar rashin nutsuwarta ya ƙaru. Kamar ance ta ɗago ta kalla ƙofa sai idonta akan AA ya wani kafe office ɗin nasu da kaifafan idanunsa. Ai bama tasan ta miƙe ba har Yaqub na ɗagowa shima ya kalleta. Key ɗin motar nan da wasu documents ta ɗauka tana faɗin, “Sorry Yaqub ina zuwa. Na manta CTO yace na kai masa documents ɗin nan tun ɗazun.” bata jira amsarsa ba ya fito. Dai-dai AA na gittawa da baƙonsa da alama ya nuna rakkiya ya masa, tsabar wulaƙanci yi yay kamar bai ganta ba, sai da ta ɗan kallesa taga ya mata wani salo da yatsu biyu ta baya yana saki wani ɗan iskan murmushi. Jitai wani ƙululu ya tokare mata maƙoshi. Amma babu yanda ta iya dole ta nufi elevator. Tana isowa AS ya bata umarnin ta shiga kawai. Harararsa tayi sannan ta wuce fuuuu ciki, tako bugo ƙofar har sai da AS ya ɗan zabura, dan harga ALLAH tsoro yaji saboda abin yazo masa a bazata..........✍️


🤣🤣 An dai ji kunya AS da tsoro.😂
















09032345899








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖8️⃣5️⃣




______________




.........A nutsensa ya turo ƙofar ya shigo. Ya kuma maidata ya rufe sannan ya shiga takowa cikin office ɗin. Duk da ƙamshinsa da motsinsa bai sa ta motsa daga tsayen da take ba. Sai ma sake kumbura take yi taf har ya ƙaraso bayanta daf ya tsaya. Tsabar yanda ya fita tsaho har tsakkiyar kanta yana gani tsaf, gently ya ranƙwafo a bayan nata batare da jikinsa ya taɓata ba ko kaɗan, fuskarsa a saitin kunnenta yana busa mata numfashinsa saman dokin wuya cikin raɗa ya furta, “Ko sai na ƙarasar dake ɗin ne dai saman kujerar?”.
A wani irin zabure Maanal tai gaba camak kamar wadda aka sarrafa da remote. Sai kawai hangota yay a saman kujerar. Murmushi ya saki da wani lumshe idanu sai kuma ya buɗe su yana miƙewa tsaye sosai ya shafo kwantaccen gashin sajensa zuwa wanda ya zagaye madaidaicin bakinsa. Maimakon yaje ya zauna a kujerarsa sai ya zauna visitor chair ɗin shima dake kallon wadda ta zauna. Basket ɗin saman desk ɗin nashi ya jawo, ya ciro ƙyawawan kulolin da aka shirya abinci. Tuni wani irin ƙamshi ya cika mata hanci, duk da shekaru sun shuɗa, ƙamshin girkin Oum bazai taɓa shuɗewa daga zuciyarta ba sam kamar yanda tasan shima kansa Ajwaad bazai taɓa manta na Ammienta ba. Dan haka ta fara satar kallon abincin. Sai da ya gama zubawa dai-dai cin mutum ɗaya sannan ya sake matsowa sosai da kujerar, sai dai duk da hakan sam jikinsu bai taɓa na juna ba akwai ɗan space. Abincin ya ɗebo a spoon ya kai bakinta. Ƙin buɗe bakin tayi, shiko ya wani zuba mata idanu. Hawaye ne suka fara taruwa a nata idanun, dan haka ta kauda kanta gefe a hankali tana mai haɗiye abinda ya tokare maƙoshinta.
Shima idanun nasa ne suka kaɗa sosai, amma da yake namijin duniya ne sai ya saki ɗan murmushi irin na danne damuwar nan. Muryarsa da wani kalar sanyi da kulawa ya furta, “Karfa na cinye ki dawo kina min rigima”.
Shuuuuu hawayen da take faman riƙewa suka ziraro daga idannunta tai murmushi, wasu abubuwa ne masu nauyi da suka shuɗe ke tsikarin zuciyarta, ƙirjinta ya mata nauyi matuƙa. Slowly ya kauda nasa kan shima daga kallonta, idanunsa sun sake masifar kaɗewa. Kusan minti ɗaya suna a haka kafin ya juyo, tissue dake saman desk ɗinsa ya zara biyu ya miƙa mata batare daya kalleta ba. Itama bata kallesan ba ta amsa tissue ɗin, hawayen ta share, tare da dunƙule tissue ɗin cikin hannunta taƙi zubarwa.
“Ka kori Abideen ne?”. Ta faɗa batare data kallesa ba har yanzu. Shi kam juyowa yay ya sauke nauyayyun idanun nasa a kanta, sai kuma batare da ya bata amsa ba ya furta, “Ci abincin first”.
“Ni bana jin yunwa.”
“Na sani”.
Ya bata amsa a taƙaice yana sake kai spoon ɗin bakinta. A hankali ta furta, “Bani zanci da kaina” tana kai hannu zata amsa spoon ɗin. Matsar da hannunsa yay kaɗan yana zuba idanunsa sosai cikin nata. Dole tai ƙasa da nata ta buɗe bakin kaɗan. Ƙaramar ajiyar zuciya sukayi a tare bayan ya zare spoon ɗin ita kuma ta fara tauna abincin a hankali...
Lips ɗinta kawai dake motsi yake kallo, sai kuma ya ɗan murmusa kaɗan da faɗin, “Kin tuna ranar da kika fara girki, da irin abincin nan kika fara har na samu wannan ciwon?”. Yay maganar yana kallon gefen babban yatsar hannunsa na dama gab da wajen tafi. Itama hannun ta kalla, dai-dai wajen akwai madaidaicin tabo da akallo ɗaya zaka fahimci sanda aka jisa ba ƙaramin ciwo bane.
“Oum!! Mamy!! Babban yaya ku kawo taimako hannun Besty ya gundile, ya gundile Abah kalla jini, wayyo Yaya F mun bani Besty ya zama mara hannu”. Ya faɗa yana kwaikwayon ƙaramar muryarta a wancan lokacin. Ai bama tasan ta sanya dariya ba. Taja mayafinta ta rufe fuskarta tana mai kifeta a desk ɗinsa komai na dawo mata kamar a yanzu yake faruwa. Shima dariyar yake sosai kamar ba shi ba. Ya ɗan girgiza kansa... “Kai yarinyar nan kinyi rashin ji wlhy. Kefa kika jimin ciwon, amma kika fini ihu da raki da cika kunnen mutane, ban isa kuma nace kece ba ki isheni da rigima da tsiwa. Ai naci girkinki na farko da wuya dai”.
Batare data ɗago ba ta ce, “Amma ai kaine kasa na ji maka ciwon ko, ba kaine kace na yanka albasan a hannunka ba”.
“Amma sai nace ki yanka ni? Anya bazan ramaba ma yanzu?”.
Da sauri ta ɗago tana waro dukkan idanunta a kansa, fuskarta tuni ta ƙwaɓe da shagwaɓa ta ce, “Kuma sai ka rama ɗin?”.
Shima kallon nata yake sosai cikin ido, sai kuma a hankali ya rissinar da nashi yana mai girgiza kai. “Zanyi tunani, idan da yiwuwar na yafe to”.
Baki ta tura tare da masa harara, shi kuma ya taɓe nasa yana sake kawo mata abincin daya ɗibo a spoon saitin baki.
Kafaɗa ta maƙe masa zatai magana ya ce, “Shiiii”.
“To ka bani zanci da kaina”.
“Kin tabbatar?”.
Da sauri ta jinjina masa kai. Plate ɗin ya miƙa mata babu musu. Dan shima dai ya fahimci idan bai batan ba za'a iya samun matsala. A hankali ta cigaba da cin abincin, sai kuma ta sake ɗakko masa batun Abideen kodan kauda wannan kallon da yake mata. Idanun nasa kuwa ya janye, sai kuma ya a harɗe hannayensa a ƙirji da kwantar da jikinsa a kujerar sosai. Tsohon minti ɗaya kafin ya amsa mata da.
“Miye damuwarki wai da zancensa? Ko shima saurayin naki ne? Dan naga ke samarin naki basu da adadin ƙirga”.
“Eh mana, farin jini ai kenan, ko kuma kana kishi ne?”.
“Mizai sa nayi kishi kuwa ina matsayin Yaya. Kidai sani sai na tantance wanda ya dace kozan bashi ke”.
Har ƙarƙashin rai zancen nashi ya soki zuciyar Maanal. Amma sai ta dake itama cike da basarwa ta ce, “Ba damuwa Yayana, ai duk yanda kayi dai-dai ne. Amma dai inada zaɓina gaskiya, nasan kuma bazaka min auren dole ba, kaima shine zai kasance zaɓinka ai ko?”. Ta ƙare maganar cikin salon waro idanunta a kansa. Wani hayaƙin takaici ne ya turniƙe sa, dan har launin idanunsa sun sauya. Janyesu yay daga cikin nata batare daya amsa mata ba. Itako saita wani ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki. Ta ce, “Koda yake ai kasan zaɓin nawa ma. Kai dai kawai ka fara shiri nan da wata biyu zaka aurar da ƙanwarka in sha ALLAHU. Dan Rafeeq ya tabbatar min baya son ya wuce hakan, nima kuma hakan nafi so. Dama ya kawo min ƙararka daren jiya”.
Da ace Maanal na kallon kalar mugun kallon da AA ke mata data tsuke bakinta, koda yake tana jinsa a jikinta. Amma ta daure ta danne abinta. Karo na farko yaja tsaki. Kallonsa tayi, amma shi kuma sai ba kallonta yake ba yanzu. Hasalima ya jawo laptop dake a saman desk ɗinne kamar a fusace. Gabanta ya tura, babu wasa a muryarsa ya furta, “Ki duba za'a tura miki saƙo a email ɗinki. Next week akwai tafiyar da kamfani zai yi har da ke ciki zuwa ƙasar Chaina. Tafiya ce ta kwana goma zuwa sati biyu. Wannan zanen nake son ki duba min shi kafin lokacin tafiyar, kije da laptop ɗin”.
Da mamaki ta ce, “Kamar ya? Amma dai kasan baza'a barni a gida ba, dan mi zaku saka sunana?”.
“Saboda dolene kiyi tafiyar”.
Dangwarar da plate ɗin abincin hannunta tayi, tare da faɗin, “Idan na ajiye aikin gaba ɗaya fa?”.
“Wannan ne baki isa ba ai”.
“A matsayinka na wa?”.
“Mi kike ci na baka na zuba”.
“Ajwaad kana shigar min hanci da yawa fa”.
“Ki fyatoni kawai ki huta mana”.
Rasama abin cewa tayi dan takaici. Shi ko da yasan ya kaita maƙura idanu kawai ya zuba mata cike da kallon ƙurullar daya saka illahirin jinin jikinta yamutsawa. Zuciyarta ta shiga kumburowa kamar ƙwaɓaɓɓiyar fulawar burodi bugun ƙato. Da ƙyar ta danne rawar da muryarta ke neman yi cike da masifa ta ce, “Wai wannan wane irin haramtaccen kallo ne dan ALLAH. Nifa wlhy ana takura rayuwata, ana shiga haƙƙinna, idan ba'a son aikin nawa a koran a kamfanin mana.....” daga ƙarshe ma harshen nata ya harɗe ta yanda ita kanta bata ma fahimtar abinda take faɗa. Shi dai ya zuba mata ido kawai yana hukuntata da su. Sai da tayi mai isarta ta gama sannan ya tura mata goran ruwa gabanta.
“Ai bance ina so ba”.
Ta faɗa cike da tsiwa.
“Hakane”.
Ya bata amsa shima baki a taɓe. Sai kuma ya tsuke fuska kamar bashi ba ya gyara zamansa ƙafafu a harɗe hakama hannuwansa harɗe a ƙirjinsa. Babu alamar wasa a tattare da shi ya furta, “Kinyi abinda na saki?”.
Harrarsa tayi, duk da yanayin nashi ya sa zuciyarta shiga tsoro, amma a dake ta ce, “Kai ka isa ne ka sakani abu nayi?”.
“Oh haka kika ce?”.
Baki ta murguɗa masa kawai.
“Hummm ki cigaba da min wannan gatsinan zanyi maganinki soon. Na kuma baki nan da gobe ki dakatar da Rafeeq daga yaudarar da kike son masa. Idan ba hakaba zan baki mamaki”..
Murmushi tayi mai ciwo da zuba masa idannunta da suka kaɗa. “Oh mamaki? Ai ka daɗe da bani mamaki tun shaiɗan na baƙauyensa. Ajwaad ka daina wahalar da kanka da tunanin wannan abubuwan da kakeyi zaisa na ji tsoronka. Kasa a ranka ni Maanal matar Rafeeq ce in sha ALLAHU. Ina raga maka ne saboda Oum da Abah da Mamy, amma wlhy idan ka cigaba da shiga sabgata zaka sha mamaki na”.
Daga haka ta miƙe tana ajiye masa key ɗinsa tai ƙoƙarin wucewarta. Amma sai ya saka mata ƙafa babu shiri ta koma cikin kujerar daɓar ta sake zama. Cike da isa ya ƙara jawo tashi kujerar gabanta ya wani tattare ko'ina ta yanda ko space ɗin fitar numfashi mai ƙarfi bai rage mata ba. Idanunsa da suka juye gaba ɗaya ya sauke a cikin nata, ya kuma hanata janyewa duk da ƙoƙarin hakan da take yi. Sai kawai taji kamar ta saki kuka ta huta.
Wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata, batare da ya sake cemata komai ba ya kamo hannunta ya ɗaura mata ƙaramar shopping bag mai tambarin apple a jiki, ya sake ɗakko key ɗin motar nan ya saka mata shima, ya ɗauka laptop ɗin itama ya ajiye a saman ƙafarta. Har lokacin idanun nasa a cikin nata yaja kujerar baya ya miƙe abinsa cike da takunsa na isa ya zagaya ya koma kujerar zamansa, desk ɗin ya dafe da duka hannayensa biyu ya ranƙwafo, duk da ba kusa suke da juna ba sai da taji wajen ya sake mata nauyi da matsatsi.
“Fatan nasara”.
Ya faɗa a hankali sannan ya kai zaune a kujerar ya hau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login