Showing 204001 words to 207000 words out of 221978 words

Chapter 69 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Koda suka fito babu wanda bai yaba ba a falon. Wasu a dangin Daddy ɗin har suna faɗin, “Kai jama'a yarinyar nan ma ai tafi amaryar ƙyau da komai ga nutsuwa wlhy. Amma uwarsa na neman cuta masa. Ga yarinya mace har mace Masha ALLAH”.
Ita dai Maanal da su Ammie babu wanda yace komai. Haka suka fito compound. Kusan duk an wuce. Sai ɗai-ɗaikun mutane a gidan da suka rage. Dan ana kai wasu ne ana dawowa. Dole Maanal taja mota ɗaya, Amaal taja ɗaya Shahidah ma haka. Dan mota uku sukai, a hakan ma a ɗan matse suke dan Ammie tace bazatai driving ɗin dare bane dan Daddy ya hana.....


___________★

Gida ne katafaren gaske daya amsa suna gida. Komai a cikinsa tsari ne irin na gogaggun ƴan boko da sukaci suka yada kai aka kuma tashi a cikin rayuwa irin ta turawa. A nutse farar bafulatanar dattijuwar ke sakkowa daga staircase ɗin dake tsaye ƙam a tsakiyar katafaren falon tamkar an zana. Sosai ta manyanta, sai dai tsufane irin na masu jin daɗi da babu wahala. Ga ƙaramin jikin Fulani ALLAH ya bata. Cike da girmamawa masu aikin dake ta ƙoƙarin shirya abinci a ƙaton dining table suke mata sannu da fitowa. Amsa musu tai da kulawa. Kafin ta furta, “Babu wanda ya fito ne har yanzu?”.
“Eh Mah-mah, amma Alhaji ƙarami da Yaya Rafeeq yanzu suka dawo suna a sashen Yaya Rafeeq”.
Kanta ta jinjina kawai. Sai kuma ta sake juyawa upstairs ɗin tana faɗin, “Ku ƙarasa wani yay kiransu. Bara nama Doctor magana”. Daga haka ta sake hayewa saman.
Fin mintuna goma sai gasu sun fara firfitowa. Kamilallen tsoho da akaga jiya akaga yau Dr Kasheem Kura ne ya fara fitowa matarsa Hajiya Maryam Ishaq Darma biye da shi. Sai ga kuma wata matashiyar mata da bazata wuce shekaru talatin ba da ɗoriya itama. Sosai take kamanni da Mah-mah da su Oum. Hakan na nufin itama ta fito daga tsatson Baffa Ishaq Darma ne. Yara biyu biye da ita ƙyawawa da shekarunsu zasu iya kaiwa biyar da bakwai. Da gudu suka barta suka nufi tsoffin kakanninsu. (Rufaidah kenan, itace Autar su Abah, dan Baba Umar Ishaq Darma mahaifin Abah ne ya haifeta. Itace kuma ke auren Sulaiman ƙanin Oum dake bima Hajiya Majdiya, RK kuma ke bi masa. Yaransu uku duk maza, babban mai shekara tara bai kai ga fitowa ba. Suna zama a dining ɗin RK da Sulaiman da suke kira Alhaji Ƙarami suma suka sakko. Hira suke suna dariya kamar wasu abokai, duk da Alhaji Ƙarami ya girmi RK nesa ba kusa ba akwai shaƙuwa mai yawa a tsakaninsu. Rayuwar Turai sun tashi sune abokan juna, sune ƴan uwan juna. Suma duk kujera suka ja suka zauna, bayan RK ya gama ɗaga yaran sama suna dariya.
“Barka da dare Abbu, Mah-mah barkan ki”.
Murmushi Hajiya Maryam da Dr Kasheem sukayi a lokaci guda idanunsu akan RK da yay gaisuwar. Cike da kulawa Mah-mah ta ce, “Auta anya tuzurancin nan bai isa ba haka nan? Na fara gajiya da baka abinci fa a gidan nan”.
Kai RK ya shafa yana murmushi, sai kuma ya kalla Abbu. “Abbu ai kai baka gaji da kawowa naci ba ko?”.
“Nima kamar na kusa fara ƙorafi irin Mah-mahn ku”.
Dariya suka sanya gaba ɗaya. Alhaji ƙarami ya ce, “Abbu kaima bazaka bashi kariyaba yau?”.
“A'a ina zan bari aima Autana tawaye Alhaji ƙarami. Kawai dai nima ina son yayi auren ne na gaji da ganinsa haka nan.”
“Ai ni nama daina cewa komai Doctor. Amma gab nake da dubawa cikin ƴaƴan dangi na aurama Rafeeq da Ajwaad da Najeeb. Su ukun nan tuzurancin su ya ishi kowa a family ɗin nan. Garama su yanzu suna a ƙasar tasu, shiko Najeeb yaje ya tare a ƙasar turawa da anyi magana yace bussines”.
Fuska da murmushi Abbu ya ce, “Insha ALLAH zasuyi kwanan nan. Dan autanki dai gobe zamu tattauna akan nashi batun. To Inaga Ajwaad ɗin da Najeeb ɗin ma duk za'ayita ta ƙare, dan ta bakin Kamila sai an biyo musu ta bayan gida.”
“To ALLAH ya tabbatar da alkairi”.
A tare duk suka amsa da Amin, kafin kowa ya fara ƙoƙarin zuba abinda yake buƙata a plate ɗin da ya ɗauka. Dining ɗin RK ya ɗan kalla sai kuma ya duba Rufaidah.
“Ƙanwa! Wai ina spider man ne?”.
Baki ta ɗan taɓe da faɗin, “Yana ɗaki Yaya Rafeeq, fushi yake har yanzun. Daga ni har Mah-mah ya daina kulamu a gidan yau. Tunda kuka fita ma bana tunanin mun gansa, shi a dole sai yabi Mamy Abuja bayan kuma ga makaranta ba hutu akayi ba”.
Dariya Abbu yayi, cike da manyantaka ya ce, “Ai laifinku ne. Daga ke har Maman taki kun cika faɗa ne. Shi kuma ku lura yaro ne da bai son yawan hayaniya, komansa irin na iyayensa ne Ajwaad da Fadeel, shiyyasa ma yake ƙulafucinsu, dama kun barshi yabi Kamila ɗin sai a maidoshi ranar lahadi”.
“Tab Abbu murɗa-murɗa kenan. Garama Fadeel ɗin da ɗan sauƙi. Amma wannan Autan na Aunty Babba sai ita wlhy. Ai sai mu tattara idan yayi aure mu maida masa can su ƙarata. Dama ai duk duniya ba wanda Abdull ke ƙauna sama da Ajwaad”.
“To ai hali yazo ɗaya ne”.
Cewar Alhaji ƙarami. Dariya duk sukayi, sai kuma RK ya miƙe yana faɗin, “Ina zuwa bari na fito da shi.” abincin su sudai suka cigaba da ci. Kusan mintuna biyar kuwa sai gashi ya fito goye da matashin yaron a bayansa. Sosai yake kamanni da Alhaji ƙarami. Kai da ka gani kasan shi ya haifi abinsa. A kujerar kusa da shi ya saukesa, shiko yaron sai wani ciccin magani yake. Yaki ƙallon kowa. Dariya sosai Abbu yake gumtsewa, dan ganin Mah-mah da Rufaidah da yaran ke kira Ummy na hararrar yaron. Shi kuma sai wani ƙara tsare gida yake yi.
“Ni mutum ma idan ya sake shiga sabgata a gidan nan ba sai nayi kuli-kulin rakiya da shi ba”. Cewar Mah-mah. Aiko Abdull sai ya sake tura baki gaba yaƙi kallonta. Kasa haƙuri Abbu da RK da Baba Ƙarami sukai suka sanya dariya... Haka sukaci abincin nasu cike da raha. Dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin wannan zuri'a. Musamman daya kasance mahaifinsu mutum ne mai sauƙi da sanyin hali. Dan kaf halayen Rafeeq irin nashi ne. Mah-mah ce ma mai ɗan zafin yanayi............✍️















09032345899






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖8️⃣9️⃣




______________




........Shigowar su Maanal cikin hall ɗin ya matuƙar ɗaukar hankali. Dan a dai-dai lokacin da ake addu'a ne. Wajen ya kasance tsit. Suko yanda aka zubo musu idanun bai damesu ba. Sai ma wajen zama da suka samu aka ƙarasa addu'ar da su. Kafin a fara abinda ya shafi mutane. Duk motsin Maanal a idon Yazeed ne, ita ko taƙi yarda ma ta kalla inda suke shi da amaryar tasa da tasha ƙyau. Itama amaryar hankalinta duk yana akan Maanal ɗin, sosai take jin tsanarta, amma tsoron nunawa take a gaban Yazeed. Dan ranar data nuna ɗin ya tabbatar mata zai iya fasa aurenta akan Maanal. Dan haka ta kiyaye idan tana son kasancewa da shi. Dole ta kama kan nata take kuma yin taka tsantsan. Amma a ranta wata irin wutar ƙiyayyar Maanal ce mai ci da zafi da ƙarfi ke sukarta. Hakama mahaifiyarta Aunty Sabuwa. Dan ko yanzu taso yin abinda zai wulaƙanta su Ammie a wajen mai bima Hajiya Yaya ita kuma Sabuwar yayarta ce ta ƙwaɓeta. Dan ita tana da hankali da sanin yakamata matuƙa..


Taro ya tashi lafiya. Ammie ce kawai taje taima amarya da ango liƙi. Amma su Amal duk ƙi sukayi, balle Manaal da dama ko motsawa batai ba. Hasalima charting suke ita da RK hankali kwance. Ana tashi sune ƴan gaba-gaba a masu wucewa gida. Yanayin gajiyar tafiya da rashin samun isashen hutu suna shigowa gidan kowa makwanci ya nema. Washe gari safiyar asabar aka tashi da shirin ɗaurin aure. Sai yinin biki da Hajiya Yaya zatayi. Zuwa dare ayi dinner sannan a kawo amarya. Sai washe gari walima da buɗan kai baki ya tashi. Duk da nan gidan anguna ne bana su amarya ba cike yake...


Sosai abin duniya ya dami Yazeed. So yake yaga Maanal amma hakan ta gagara. Dan jiya daga wajen mothers event ɗin nan dole hotel ɗin da abokansa suka sauka yaje ya kwana. Ya kira wayarta kuma a kashe. Yanda ya kwana da ita a rai ya sashi zuwa gidan yau da wuri. Dama anan sashen Ammie aka haɗama abokansa breakfast, sai ya samu damar fakewa da hakan kuwa. Bayan ya gaishe da dangin Daddy dake nan sai ya zauna suka cigaba da hira. Dan yaga kowa tsakanin Shahidah da Amaal dake shirya abincin abokan nasa da Aunty Sakina amma babu Maanal. Cikin raɗa-raɗa yake tambayar Munaya da tazo gaisheshi.
“Uncle sun fita ita da Aunty Amrah.”
Sai da ya kalla agogon hannunsa da mamaki ya furta, “Fita kuma da safen nan? Ina suka je to?”.
“Nima ban sani ba”.
Shiru kawai yayi ransa na ƙara jagulewa da tunani. Sai kuma ya miƙe ya fita. Can waje ya koma ya tsaya a ƙofar gida. Duk ma inda suke ai dole in sun dawo tannan zasu shiga gidan. Yana a wajen kusan minti talatin yana dakon jiransu sai ko ga napep ta tsaya a ƙofar gate ɗin. Amrah ta fara fitowa tana dariya, sai Maanal fuskarta da murmushi, da alama dai wata maganar suke data basu dariyan. Su duka hannayensu da kaya. Amrah ce ta fara lura da yayan nasu, ganin yanda ya tsume fuska ya sata haɗiye dariyarta. Ita dama Maanal tuni ta daina murmushin duk da bata gansa ba, sai da ta juyo zasu nufi hanyar shiga idonta ya sauka a kansa. Ɗan turus tayi tana kallonsa, sai kuma tai ƙoƙarin janye dubanta a kansa a taƙaice ya ce, “Good morning ” ta raɓa zata wuce.
“Zonan”.
Ya kirata a dake.
Cak ta tsaya, jitake kamar tace bazata zo ba. Amma dai ta dake ta dawo da baya, yayinda Amrah ta amshi kayan hannun nata. Dan daga gidan Amaal suke, ɗinkunan su ne da tela bai samu gamawa ba sai jiya, shi kuma mijinta ya amso jiya da dare shine yau Maanal ɗin suka je ɗakkowa a gidan...
“Fushi ake dani ko?”.
Ya faɗa cikin kwantar da murya, kamar ba shike tsume fuska ba. Batare data kallesa ba ta ce, “Mi kamun da zanyi fushi da kai Yaya. Kawai dai yanayi ne”.
Murmushi ya saki mai armashi. Sai kuma ya sake matsowa kusa da ita sosai. Cike da lallashi ya ce, “To nidai ina roƙon afuwa dan ALLAH. Har yanzu kuma baki maida wayarki ba ne?”.
Kallon wayar tata dake hannunta tayi, batare data kallesa ba. “Kwana biyu da suka gabata na maida.”
“Shine kuma koma a taɓani. Naso sauka Abujan sai aka samu matsala. Dan bammayi zaton ganinki a kd ɗin ba”.
Yanzu kam murmushi ta saki, murmushin daba cika gani yay a fuskarta ba. Sai dai batace komai ba. Kafin shima yace wani abu wasu ƴan uwan Hajiya Yaya suka iso. Wani shegen kallon banza suke zuba mata, dan labarinta duk ya gama karaɗen danginsu daga jiya. Yayinda shi kuma Yazeed hankalinsa ke a kansu yana musu sannu da zuwa. Da wannan damar Maanal ta zame jikinta ta gudu. Sai waigawa yay yaga wayam bata a wajen. Yaso bin bayanta, sai baƙin suka sake janye hankalinsa dole ya haƙura......


_________★


Da mamaki Oum ke kallon AA dake shaƙar barci a gadonta. Da alama ma ya manta da yau zasuyi tafiya. Tunda suka kammala breakfast yau a ɓangarenta su duka gidan aka cigaba da hira shi kuma ya tashi ya shige bedroom ɗinta basu sake jin ɗuriyarsa ba. Umarnin zuwa kowa ya shirya da Abah ya basu ya saka kowa tashi ya nufi shiryawa. Ita dama cikin shirinta take dan haka ta shigo domin ganin mi AA ɗin keyi a ɗaki, kawai saita ci karo dashi a bargo ma ga ac ya ƙure.
Ac'n ta kashe, kafin ta ƙarasa gaban gadon tana kiran sunansa, dan tasan bashi da nauyin barci. Idanu kuwa ya buɗe a hankali ya sauke a kanta.
“Kowa nacan ya shirya kai kana nan kana barci Auta?”.
“Oum ALLAH ni barci nake ji, weekend ɗin nan nefa mutum ke ɗan samu ya huta. Wai inama za'aje ne?”.
“Koma inane idan munje zaku gani. Kuma ka tashi kafin Abah ya shigo ya samu baka shirya ba”.
Fuska sosai ya ɓata. Sai kuma ya yaye duvet ɗin ya tashi tare da sakkowa. Oum dai na tsaye tana kallonsa. Gadon ya fara ƙoƙarin gyarawa. Oum ɗin ta dakatar da shi.
“Kaga barshi jeka shirya zan gyara”.
Kafaɗa ya maƙe mata ya cigaba da gyarawa, sai da ya gama tsaf sannan. Wannan ba komai bane a garesu su duka. Dan Oum ta riga ta horesu da aiki har girki babu wanda bazai iya yi ba su duka ukun. Yana fita tayi murmushi, dan tasan a cike yake fam. Itama ɗan shishshirya abinda take buƙata ta shiga yi...


Kusan sha ɗaya duk sun fito cikin shiri, AA ne ƙarshen fitowa cikin ƙananun kaya. Aiko Abah ya korashi canjawa. Oum ya kalla a shagwaɓe, ta masa alamar ba ruwanta. Sai ya tura baki ya koma. Aiko Fawzan ya shiga dariya da tsokanarsa. Babban yaya yayi murmushi su Nibras na taya shi dan sun san su dai babu damar yi a zahiri. Abah ma murmushin yayi, yayinda Mamy tai kamar bata san anyi ba. Bai wani jima ba sai gashi ya fito cikin wani arnen yadi omo blue daya ji ajiyayyen ɗinki. Ya kawo hula ya murza. Kusan su duka sai da suka ambaci masha ALLAH a zukatansu. Dan manyan kaya nama AA masifar ƙyau shi kuma baya son sakawa. Nibras kam ji take kamar ta haɗiyesa ta huta. Fawzan da bakinsa baya iya shiru ya shiga yimasa hoto da faɗin, “Kai wankan nan gaskiya bai kamata ya tafi a banza ba tuzurun gidan mu. Dolene na poster ka a media ko zamu samu wata tace tana so mu haɗa mata da cin hanci.”
Dariya su Abah suka sanya. Oum ta ce, “Yarona yafi ƙarfin sai an haɗashi da cin hanci sannan ya auru. Fawzan ka kiyaye mu”.
“Oum kada fa ku cika baki, yanzu yayin yara ake masu jini a jika shi kuma ya zama tuzuru”.
AA dai bai kulashi ba. Sai ma kama hannun Anum yay suka shige mota. Aiko zaram Nibras ma taje jikin motar ta tsaya. Babu wanda ya damu da hakan, sai ma Abah da Oum da Mamy suka shiga tasu motar tare, Babban yaya ma ya shiga Saheeba ta shiga kusa da shi. Sai Naufal ya shiga baya. Can kuma AA a mazaunin driver Fawzan ya shiga kusa da shi Nibras da Anum suka shiga baya. Fawzan yasan AA ba ƙaunar tuƙi yake ba a rayuwarsa, dan haka ya kallesa da faɗin, “Zaka iya kaimu har Kaduna babu wata damuwa”.
Kallonsa shima AA ɗin yay da faɗin, “Wai dama Kaduna zamuje? To yin me?”.
“Nima ban sani ba, amma biki Abah yace ai kamar”.
“Yanzu saboda zuwa biki aka hanani barci na. Kuma dan ALLAH ba sai a tafi a train ba”.
“To ya muka iya, kasan Abah da Oum akan son dangi. Ni kaina yau inada wani ɗaurin aure a cikin Abujan nan, yanzu dai bani driving ɗin kawai”.
“No barshi muje, idan na gaji sai ka amsa”. Cewar AA yana yin horn. Shi ya fara fita, Babban Yaya biye da shi sai drivern Abah a ƙarshe. Haka suka ɗauki hanya a jere gwanin sha'awa. Babu damar yin gudu dan in ana tafiya tare da Abah dama babu zancen gudu yaci ƙaniyar mutum. Sai dai abinka da lafiyayyun motoci cikin amincin UBANGIJI sha biyu da kusan arba'in a Kaduna tayi musu. Babban Yaya da Abah suka koma motar AA. Nibras suka haɗe da Saheeba data amshi tuƙin Babban yaya, oum da Mamy suna tare da driver. Su gidan Ammie aka nufa da su. Su kuma su Abah suka wuce masallaci domin yin sallar juma'a da ɗaurin aure.
Invitation card ɗin Abah ta miƙama AA. Bayan ya gama dubawa ya juyo yana kallon Abah ɗin, dan suna baya shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login