Showing 189001 words to 192000 words out of 221978 words
Chapter 64 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
ALLAH sarki Fawzan sarkin haƙuri, sai ya sakar mata murmushi, muryarsa a sanyaye ya ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya wuce.....”
Bai ƙarasa ba AA ya miƙe fuuu ya fice a falon. Da kallo duk suka bi shi, musamman Nibras dake jin zuciyarta na kumfa a cikin ƙirjinta. Ji take kamar ta bishi da gudu ta rungumesa. RK ne ya katse yanayin da faɗin, “Aunty dafa autanki ne babban Yaya a gidan nan da kowa yaga takansa. Dan discipline Master za'ayi na gaske”.
Dariya Abah da Fawzan da Oum suka sanya, Babban Yaya yayi murmushi. Mamy kam wani shegen kallo ta watsama RK a kaikaice. Yayinda Nibras kanta ke a ƙasa kwai. Cikin nutsuwa da dattko Abah ya shiga musu nasiha Oum na taya shi, yayinda Mamy ta miƙe batare data tofa komai ba tunda ta shigo. Kallonta Oum tai fuska cike da murmushi. “Madam ya baki mana addu'a ba zaki tafi”.
Murmushi Mamyn ta saki kaɗan, “Oh baku gode bama dana taro muku ƴar taku dake shirin fita a gidan. ALLAH ya kiyaye gaba ni nayi nan mu kwana lafiya”.
Murmushi Abah da Oum suke yi, wata ƙaunarta na sake ratsasu. Hakama RK da su Fawzan, duk murmushin suke yi. Nan dai suka ƙara musu nasiha har RK da Babban Yaya musamman Nibras. Ta nuna nadamarta sosai, duk da ita hankalinta sam ba'a kansu yake ba yana ga AA daya fita a fusace. Ta san yau ko barci da wahala ta iya yi mai daɗi, sam bata son ganinsa a damuwa, balle kuma ace itace ta ɓata masa ran ai al'amarin yayi girma da yawa gaskiya......
Humm wannan Nibras ALLAH ya taroki dai to🏃😥. Wai da irinsu a gaske🤔 ko sai a novels 🥱🥺😌.
__________★
“Kai malam wai fushin ne har yanzu dai?”.
RK ya faɗa idonsa akan AA dake zaune a bakin gadonsa da waya a hannu yana sarrafawa. Daga wanka RK ɗin ya fito daga cikin bayinsa, dan yau anan ɗin zai kwana. Tunda suka baro sashen Oum shi da babban yaya yayo nan. A inda AA ɗin yake har yanzu anan ya samesa, yayi wanka ya canja kaya zuwa kayan barci. Tun daga amsa sallama bai sake kula RK ɗin ba shima kuma bai bi takansa ba ya ajiye dai basket ɗin da Oum ta haɗo musu abinci ya wuce toilet. Shine yayo wanka ya fito. A inda yabar AA ɗin ya sake samunsa, shine ya jefa masa wannan tambaya ta “Kai malam wai fushin ne har yanzu dai?”. Dai-dai yana zama a bakin gadon yana goge fuskarsa da ƙaramin towel. Karan farko AA ya ɗago ya kallesa, sai kuma yay guntun tsaki yana ajiye wayar. Shiru na wasu mintuna kafin ya ce, “Bazaka gane ba wlhy na tsani yarinyar nan. Ni banga mi Ya Fawzan ya gani a jikinta ba har yake zaune da ita. Gaba ɗayanta a zubinta ma shashasha ce”
“To miji da matar sa ai ba'ace miya gani a jikinta ba. Kawai dai ita na kula tanada matsala ne. Ince ko cikakken 5 months ba'ai da yin irin wannan case ɗin tsakaninsu ba. Boko da ƙarancin ilimin addini ya mata yawa ne kawai, ga gata data samu a gidansu mara amfani. Yo mara amfani mana tinda babu cikakken tarbiyyar ɗiyan malam bahaushe a tare da ita dam, gefe kuma nake gani akwai sharrin ƙawaye kamar dake zugota”.
“Oh, shine kuma duk zata tattaro haukarta tana saukewa a kansa. Ni ban san mike damun ya Fawzan ba sam, bana son wannan sanyin halin nasa. In dai zai ware rana ɗaya yaci mata uwa ai da ta dawo hankalinta. Kawai ka zauna yarinya ƙarama ƴar cikinka na raina maka wayo, da auren wuri yay daya haifeta ai”.
Dariya RK yay da ɗan dukan kafaɗar AA ɗin, “Common Oum's boy hakan fa normal ne ga ma'aurata. Bari dai kayi auren malam zama ka ɗauki fiye da hakan. Mace kuma ko jika kayi da ita a ɗakin aure ai dai-dai kuke tunda ta gama ƙure maka girma”.
Harrarsa AA ɗin yay. “Oh irinsa zaka zama kaima kenan?”.
Cikin dariya RK ya ce, “Idan ta kama mizai hana. Balle ma nasan ni tawa mai hankali ce zata dinga lallaɓani bazata bari ta ganni cikin fushi ba. Kai ni yanzu ma fa zuwa nai muyi magana da Aunty da Yaya akan batun nawa wannan kuma rikicin ya shiga tsakkiya. Magana ta ALLAH aure nake so, idan har anyi azumin nan dani a tuzuru bana son nayi babbar salla a gwauro”.
Sosai AA ya taɓe baki, sai kuma ya koma ya kwanta yana ɗaukar wayarsa, cikin halin ko in kula ya ce, “Ka samu matar kenan?”........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣2️⃣
______________
.......Harara shima RK ya maka masa yana miƙewa, sai da ya ɗauki hanyar closet ɗin AA ɗin sannan ya amsa masa da, “Bazaka bani auren ƙanwar taka Maanal ba kenan da kake min wannan tambayar rainin wayon?”.
Sai da AA ya wani cije lips saboda yanda furucin na RK ya dakar masa zuciya. Amma sai ya zaɓi masa shiru bai tanka ba. Shima RK ɗin bai sake magana ba sai da ya kimtsa ya fito daga closet ɗin cikin pyjamas. Zama yay ya jawo basket ɗin kayan abincin ya shiga zubawa. Batare daya kalla AA ba ya cigaba da faɗin, “Da gaske nake Ajwaad ina son ka muje Kano wajen Abbu da a weekend ɗin nan, amma sai mun fara zuwa wajen Baba Sardauna first, dan Maanal ta bani dama bai kamata kuma nayi wasa da ita ba.”
Shiru AA bai tanka masa ba. Dan haka RK ya ɗago yana kallonsa. Wayarsa kawai yake faman latsawa babu alamar ma yana da niyyar tanka masan. “Ikon rabbu, kaifa wani lokacin ɗan wulaƙanci ne baka jini bane wai?”.
A ɗan tunzure AA ya ce, “Malam mind your own business kaji, ka tafi kaje ka nema aurenka ina da abunyi. Dan zan mayi tafiya ne zuwa Chaina wannan weekend ɗin”.
“Chaina kuma? Yin uwar mi to?”.
Nan ma banza AA ɗin ya masa. Sai kawai RK ya taɓe baki da jan abincinsa ya fara ci. “Kai dai ka sani, idan ka tashi ka ƙarasa har katangar bangon duniya ba Chaina ba ma. Kai wlhy ina matuƙar tausayin matar da zata aureka a duniyar nan Ajwaad. Shiyyasa ma kayi kwantai har yanzu babu mashinshiniya. Ya kamata Oum ɗin taka ta saka a fara maka ruƙiyya ko aljanun kanka zasu ragu mu huta muma.”
“SHURI ne a kaina”.
AA ya faɗa yana miƙewa, bathroom ya shiga ya bar RK da dariya. “Ai da alama har shurin ma da kukoki za'a iya samu ALLAH. Murɗaɗɗen banza”.
AA na jiyowa amma bai sake tanka masa ba. Ya jima a bayin sannan ya fito, bai kula RK ba ya haye gadon yay kwanciyarsa. Shima RK ɗin sai bai sake kulashi ba. Sai ma ƙoƙarin neman number ɗinsa dake a hannun Maanal yake. Sai da tana gab da tsinkewa ta ɗauka, cikin yanayin mai barci tai masa sallama.
“Oh oh har kinyi barci yau haka da wuri?”.
Daga can Maanal ta ce, “ALLAH na gaji ne Ya Rafeeq.”
“A niba yayanki bane. Ga dai ƴaƴan ki nan ɗan balaja'u. Dan nima yanzu Yaya zan koma kiransa ma”.
Cikin rashin fahimta ta ce, “Ni kuma dai, a ina na samu Yaya?”.
“AA mana, gashi nan ya tasani gaba sai masifa yake min”.
Wani irin zuuuuu zuciyar Maanal tayi, amma sai ta dake tai ɗan murmushi mai sauti da faɗin, “Ai gara dai ka lallaɓashi dan kasan shine mai baka auren nawa.”
“Shiyyasa ai nake haƙuri da mugun halinsa. Naji ni na ajiye kawun a gefe zan girmamashi, idan ya bani ke sai mu dawo dai-dai my queen.”
Nan ma murmushi kawai tayi batace komai ba. Shima sai ya saki batun AA ɗin ya miƙe ya fita daga ɗakin ya koma falo suka cigaba da hirarsu. Duk da ma dai shine ke maganar ita kam sama-sama ne. Bai cika damuwa da hakan ba saboda zuwa yanzu ya gama fahimtar ta akan miskilancin ta da rashin yawan magana. Jin tanata hamma yay mata sallama. Koda ya dawo ɗakin samun AA yay har yayi barci, sai shima kawai yay shirin kwanciyar. Sai dai abinda bai sani ba duk AA na jinsa, dan idanunsa biyu kawai yayi shiru ne. Sai da ya tabbatar RK yay barci sannan ya tashi zaune. Wayar RK ɗin ya ɗauka ya fita falo, yasan password ɗonsa, dan haka ya buɗe ya shiga masa bincike dalla-dalla. Sannan yay tsiyatakun da zaiyi a ciki ya dawo ya ajiye masa wayar sannan ya kwanta. Yana hararar RK dake barcinsa hankali kwance.....
😆😆An dai ji k...
(Na daiyi shiru😂🤪)
__________★
“Wai shi wannan tagumin na miye Baby? Ba komai ya wuce ba”. Fawzan ya faɗa yana kallon Nibras. A hankali ta janye tagumin da tayi, tare da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ta matsa ta kwanta a jikinsa kanta a saman ƙirjinsa. Ji take inama a jikin AA take haka.
“Jaan”.
Ta kira Fawzan ɗin da sunan da take kiransa. Amsa mata yay idanunsa a lumshe yana shafa bayanta.
“Dan ALLAH ka kira Yaya AA a waya mana na ƙara bashi haƙuri. Kar yay barci da fushina”.
Ɗan jimm Fawzan yayi kafin ya buɗe idanunsa a kanta. Duk da maganar tata tayi masa wani banbarakwai sai ya daure ya ce, “Nibras na faɗa miki zai huce. Kema kin san halin Auta ai. Yana da zafi amma baida riƙo. Zuwa safe normal zaki ganshi kamar komai bai faru ba. Amma duk kinbi kin damu kanki. Please ajiye batun wani Auta a gefe zo kiga na nuna miki wani abu”. Bai bata damar magana ba ya haɗe lips ɗinsu waje guda. Kicin-kicin turesa ta shiga yi, sai dai bai mata da wasa ba. Dan in dai wannan wahalar ce ya saba sha a wajen Nibras a duk lokacin da yake buƙatar hakkinsa. Kuma a farkon aurensu ba haka take masa ba. Daga baya ne dai matsalar tasu ta fara. Sai sun sha uban daru wani lokacin ma ya nuna mata ƙarfi sannan. Amma bai taɓa faɗama kowa hakan ba saboda Fawzan akwai haƙuri. Ta ɓangaren zurfin ciki kuwa shi da AA suna kamancece niya..
Koda suka gama dai-daita tashi tai ta bar masa ɗakin. Da kallo kawai ya bita, zuciyarsa dai sai son kawo masa wani tunani take yana turewa. Daga ƙarshe ya miƙe ya shiga bathroom domin tsarkake kansa.....
________★
Washe gari suna breakfast a sashin Oum kowanne cikin shirin tafiya office RK ya sanar ma Oum batun zuwa Kano da yake son yi da kuma abinda zai kaisan. Har ga ALLAH sai da gaban Oum ya faɗi ta ɗan dubi sashen da AA yake har tana neman ƙwarewa da shayi. AA ɗin ne cike da dakewa ya miƙa mata ruwa yana mai tsatstsareta da idanunsa da suka ɗan juye..
(Magana ta ALLAH Uncle RK kana saka Oum da ɗanta a cakwakiya fa🥱 ka kiyaye mu😂🤣🏃🏃.)
Murmushi Oum ta ɗan sakarma AA na yaƙe, tare da sanya masa albarka bayan tasha ruwan. Sai kuma ta maida dubanta ga RK da shima ke mata sannu. Amsa masa tayi tana jinjina kanta. Sai kuma ta maida hankalinta ga abincin tana juya abinda ta ke son faɗa a cikin ranta. Fin mintuna biyu sannan ta ce, “Ita Maanal ɗin ce ta baka dama Rafeeq?”.
“Eh Aunty, tun kwana biyar ma daya wuce. Jiya kuma muka sake maganar da ita dan nace miki yaje kd. Sai kawai naga nima ya kamata naje su Abbu su san da zancen shi da Baba Sardauna ayi a wuce wajen ko ya kika gani”.
“Hakan yayi, ALLAH ya zaɓa abinda tafi alkairi.”
“Amin ya rabbi”.
RK ya faɗa fuska washe da murmushi. Miƙewa AA yay tsam, tare da ɗaukar wayoyinsa. Ɗagowa Oum da RK sukai suna kallonsa. Batare da shi ya yarda ya kallesu ba ya ce, “Oum na wuce office bye”. Sai kuma ya ɗan duƙo ya kama hannunta ya sumbata. Kafin ta samu damar yin magana har ya fice. Murmushi RK yayi da faɗin, “Uhmm Aunty wannan ɗan naki dai sai ke. Ko har yanzu fushin jiyan ne oho masa. Nace ya shirya muje Kanon wai shi Chaina zaije, haka ya balbaleni da bala'i daren jiya laifin matar Fawzan ya koma kaina”.
Murmushi kawai Oum tayi, “Ya dai faɗa ne kawai. Duka yaushe ya dawo ƙasar ma, balle a yanzu da suke kan project babba a Company.”
“Nima abinda na gani kenan, amma nasan sa kamar ɗan sama jannati yake ba wahala gantalin ke masa ba. Bara nima naje anata kirana daga asibiti. Komi kenan zan dawo mu sake tattaunawa dai”.
Kai ta jinjina masa tare da addu'ar fatan alkairi. Ya amsa da jin daɗi yana mai ficewa. Dan bayan uwa da uba a duniya ƴar uwar tasa da mijinta sune na biyu da yake matuƙar so da girmamawa. Yana musu kallon iyaye na biyu a rayuwarsa ne duk da suna amsa sunan yayu ne......
Wani irin gajiyayyen numfashi Oum ta sauke bayan fitar RK, sai kuma ta ajiye cokalin hannunta ta dafe kanta da taji yana mata nauyi. A hankali Abah dake kallonta ya kai hannu ya taɓata, firgigit ta dawo hanyyacinta, sai kuma ta zuba masa ido kamar yau ne ta fara ganinsa. Zaune ya kai a kusa da ita, tare da jimƙe hannunta cikin nashi sosai, cike da kulawa ya ce, “Fatima na mike damunki haka da irin wannan zurfin tunani? Ko akan Fawzan ɗin ne dai? Dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, jiya fa ina lura dake bakiyi wani barcin kirki ba sam, shin haihuwa bata ALLAH bace ba. Kuma lokaci ne”.
A hankali hawayen da suka cika mata ido suka shiga silalowa. Sai ta kauda kanta da sauri tana ƙoƙarin sharewa. Fuskar tata ya kamo cikin duka hannayensa, idanunsa cikin nata ya ce, “Zarah na kin san fa damuwar ki na tayar min da hankali, hakama yaranki da zarar sun ganki a damuwa hankalinsu tashi yake yi. Ki duba har na fita na sake dawowa saboda ban gamsu da yanayin dana fita na barki ba”.
“Kayi haƙuri Zaki na, in sha ALLAHU zan kiyaye. Zan kuma cigaba da musu addu'a su dukansu”.
“Yauwa haka shine dai-dai, ALLAH yay miki albarka kinji.”.
“Amin tare da kai kaima da yarana duka”.
Murmushi ya saki tare da jan hancinta kaɗan ya kashe mata ido ɗaya, ta saki dariya tana mai saka kanta a ƙirjinsa. Shima dariyar yayi yana rungumota. Sun jima a haka kafin ya ɗagota ya fara bata abincin a baki cike da kulawa.
“Gadanga!”.
“Uhmyim Fateeman Gadanga minene?”.
“Ajwaad da Rafeeq”.
“Miya samu Ajwaad da Rafeeq ɗin?”.
Sai da taja numfashi mai nauyi sannan ta ce, “Rafeeq ne yake cigaba da damuna akan aurensa da Maanal.”
Ɗan tsai Abah yay yana kallonta, sai kuma ya sauke numfashi shima yana mai furzar da iska. “To ni Fateema mi kike so nayi? Yaron kin nan ya cika murɗi. Tunda shi taurin kai ne aikinsa basai a bar Rafeeq ɗin ya aureta ba. Ni zanyi farin ciki da hakan, dan har cikin raina ina ƙaunar Yarinyar nan, har gobe tana a raina wlhy, zan so ta kasance a cikin zuri'ar nan tamu”.........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣3️⃣
______________
........“Humm amma Gadanga kasan Auta na matuƙar son Maanal. Ka duba al'amarin nan, kada mu biye ta nashi zurfin ciki ne kawai ke damunsa. Ka duba yanda bayan samun lafiyarsa ya shiryo yazo ƙasar nan yayta wahalar nemanta, duk da bai fito ya faɗa mana ba ai munji a majiya mai ƙarfi akan ƙoƙarin sa.”
“Amma yanzu daya gantan wane mataki ya ɗauka?. Tunda kika bani labarin komai ai na sanya ido a kansa, amma ban taɓa ganin wani yunƙurinsa ba, ko gidan Shahidah bai taɓa zuwa ba sai dai su haɗu a wajen aiki. Ni kuma ba zanje nema a bashi auren yarinyata dole ba. Itama sai ta zaɓa ta darje. Idan kuma har Rafeeq ya mata zan tsaya tsayin daga na