Showing 81001 words to 84000 words out of 221978 words

Chapter 28 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

biyu ALLAH ya sake baka, duk da nasan damar tazo da ƙalubale masu yawan gaske. Ka manta da abinda ya faru a baya domin ƙaddararku ce kai da ita, babu wanda ya isa hana faruwarta. Tun kafin Uncle Rafeeq yay wuff da ita kasan mai yiwuwa, dan yanzu 2025 muke ba shekarun baya da suka shuɗe ba, wannan Maanal ɗin ba wadda ka sani bace a baya, dan tabbas Uncle Rafeeq shima yana sonta sosai.....”
Da ƙarfi AA ya rumtse idanunsa da suka sake kaɗawa, tare taune lip ɗinsa. Kalmar _Sonta..._ ɗin nan na sukarsa.
Fawzan ya cigaba da faɗin, “Sai dai hakan ba yana nufin kai bazaka nuna taka bajintar ba, sai dai ka sani wannan shiru-shirun naka fa da miskilanci dole ka ajiyesa gefe ka koma mata Bestien ta nada da kukai wasan ƙuruciya tare, mai tare mata faɗa, mai damuwa da damuwarta sama da kowa. Dan bana raba ɗayan biyu har yanzu kana nan daram a zuciyarta itama. Nasan Oum zata baka goyon baya ɗari bisa ɗari. Sai kuma ƙalubale na biyu batun Nuratu, kasan dai su Abbah sun fara magana, akoda yaushe kuma zasu iya kai kuɗi idan har baka kawo zaɓinka ba kamar yanda sukace. Dan haka sai kaje kayi tunani kafin lokaci ya ƙure maka. Ina maka fatan nasara”. Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga kafaɗar AA ɗin batare da ya jira cewarsa ba yabar balcony ɗin.
Kasa ko motsi AA yay har Fawzan ya fita a sashen gaba ɗaya, daga ta harabar gidan ya kallosa yana nuna masa kansa sai kuma ya ɗaga hannunsa yay masa nuni da agogo alamar lokaci daga haka yay wucewarsa. Da kallo ya cigaba da binsa har ya shige sashensa. Dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Iska ya ɗan furzar mai ƙarfi daga bakinsa kafin ya zarota daga aljihu yana kallon mai kiran. Oum ce da kanta, dan haka ya ɗaga a kasalance ya kai wayar kunnensa yana mai zubama flat ɗinta idanu kamar zai iya hangota daga nan.
“Auta na kana ina ne wai?”.
Idanunsa ya lumshe sai kuma ya saki ɗan murmushin gefen baki daya kasance ɗabi'arsa. Muryarsa can ƙasa ya bata amsa. “Ina sashena Oum”.
“To maza zo ina nemanka”.
Daga haka ta yanke kiran. Wayar ya sauke daga kunnesa yana furzar da iska, sai kuma ya maidata a aljihun batare da yace komai ba yabar balcony ɗin.....


____________


Gaba ɗayansu suna a kan d/table kamar yanda Oum ta sakasu yi. RK da Oum ne kawai ke hira, sai dai kuma idanunsa nakan Maanal dake ta faman juya spoon a abincin da RK ɗin ya zuba mata da kansa. Tunda ya zuba matan bata kai ko lauma ɗaya bakinta ba, da farko ma hankalinta na'a kan Novel ne. Sai da Oum tai mata magana sannan ta rufe book ɗin ta ɗauki spoon ɗin. Shine kuma taketa faman juya abincin, ta kuma zuba masa idanu kamar mai irgashi ko tantance abinda aka dafashi da shi. Ita Oum ta fahimci abinda ya saka Maanal ɗin komawa hakan game da abincin, shiko RK sai ya ɗauka ko bata sonshi ne ko kuma dai hankalinta na gida... Kaɗan yay gyaran murya tare da kiran sunanta. A hankali ta ɗago manyan idanunta da kalarsu ta sauya kaɗan, a mamakinsa sai ta sakar masa murmushinta mai sanyi dake narkar da shi. Hakan kuma yayi dai-dai da isowar AA dining area ɗin, kuma a kanta idanunsa suka fara sauka dan haka yaga murmushin data sakar ma RK ɗin. Cak ya tsaya kamar wanda akama tsawa. Shiko RK sam baima gansa ba, dan haka ya maidama Maanal ɗin murmushinta cikin ɗan ranƙwafowa gareta ta yanda ita kaɗai zata ji abinda zai faɗa ya furta, “Gimbiya irin wannan murmushi haka ai sai kisa na ɓace ɓat. Dan ALLAH kici abinci nan fa gidanku ne. Kin san kowa na cikinsa kafin ki sanni ma. Idan kuma baƙya sonshi a canja miki da wani?”.
“Oum gani!”.
AA ya faɗa cikin kaushin muryar data fargar da kowa kasancewarsa a wajen. Sai kuma yanda yay maganar da zafi-zafi ya bama RK mamaki dan abune da bai saba gani ba. AA bashi da yawan hayaniya, amma kuma baida faɗa. Barshi dai da fushi da baƙar maganar tsiya kamar jikan banbaɗawa. Oum ko data fahimci inda fushin ya dosa sai tayi murmushi kawai da faɗin, “Yauwa Autana maza zo ga abinci kada yay sanyi, dan favorite ɗinka akayi”. Tai maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Maanal kam ko ɗagowa batai ba balle ma ta kalla inda AA ɗin yake, kai bama ta nuna tasan da zuwansa wajen ba sam. Hakan kuma sai ya ƙara baƙanta masa rai, koda Oum ta zuba masa abincin ma ya ɗau kusan mintuna biyu kafin ya fara ci, sai da ma ta sake masa magana da taɓashi.
Maanal ma dai ta fara tsakurar abincin. Duk da kuma yanda ta share kamar bata san da zuwan AA ɗin ba tana satar kallonsa ne ta gefen ido. Yayinda RK ke mata magana lokaci-lokaci, sai dai maimakon amsa ɗan murmushi kawai take masa da jinjina kanta ko girgizawa. Sai yanzu ne maganar Barrah ta sakata ɗagowa, sai idanunta caraf cikin na AA. Wani shegen kallo ya zuba mata data fassara dana tsananin tsana da ƙyama. Babu wani yanayi data nuna ko a fuska ta janye nata idanun zuwa kan Barrah ɗin. Daga haka bata sake yarda ta kalla inda yake ba ma har suka kammala. Itace ta fara barin dining area ɗin, hakan yasa RK tashi ya bita shima.
Da wani kalar yanayi AA ya lumshe oily ayes ɗinsa, batare da ya lura ba ya hankaɗe glass cup ɗin ruwan da aka ajiye masa. Tarwatsewar kofin da ruwan cikin saman ƙyaƙyƙyawan farin tils ɗin ya saka hankalin kowa dawowa wajen. Oum ta miƙe tana mai kamo hannun nasa da sauri ta ce, “Subahanallahi Auta bakaji ciwoba dai ko?”.
Idanunsa dake lumshe har yanzu ya buɗe, sai kuma ya girgiza mata kansa batare da yayi magana ba. RK da tuni ya ƙaraso wajen shima ne yay kiran masu aiki ta landline, kafin ya juyo ga AA ɗin yana masa sannu. Ko kallonsa AA ɗin bai yi ba, shima kuma sai bai damu ba. Dan halinsa babu wanda bai sani ba a gidan dama dangi baki ɗaya. Maanal dai na zaune daga inda take tana kallonsu kawai, amma bata da niyyar tasowa ma. Haka masu aiki suka gyara wajen kamar komai bai faru ba, shima sai ya miƙe.
Oum ce dake binsa da kallo ta ce, “Abincin fa?”.
“Oum na ƙoshi, zanje na kwanta sai da safe”.
“Kwanciya da wuri-wuri haka? Gobe fa babu office”.
RK ne yay maganar yana binsa da kallo. Kansa ya jinjina masa kawai, sai da yaje ƙofa batare da ya juyo ba ya furta, “Anan zaka kwana ne?”.
Kallon agogo RK yay, “No zan wuce dan inada aiki a asibiti ma zuwa nine. Dan har ma sun fara kirana. Zanyi sallama da Maanal kawai”.
A taƙaice ya ce, “Okay” yay ficewarsa. Shima RK wajen Maanal ya koma, yayinda Oum tai shiru kawai zuciyarta na mata kaikawo a ƙirji. Batare data sani ba ta zubama RK da Maanal idanu. Abubuwa ne da yawa ke cuɗa kansu a zuciyarta fiye da yanda take nazarinsu tun ɗazun. Sai dai bata da wani abincewa a wanan gaɓar gaba ɗaya....


★ ★ ★


Wanka yake son shiga yayi, sai dai haka kawai ya samu kansa da tsayawa jikin window ɗin falonsa ya zubama harabar gidan ido ko nace flat ɗin Oum. Shi kansa bai san ma'anar tsaiwar tashi ba, amma ya cigaba da tsayawar. Hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma yana faman ɗagosa ya kalla agogo alamar duba mintuna. Mintuna ashirin ya ɗauka cif a wajen kafin abinda zuciyarsa ke jiran gani duk da yana faman ƙaryata hakan su fito. RK ne gaba Maanal a bayansa, sai dai suna gama fitowa RK ɗin ya dai-daita tafiyar tasu kafaɗa da kafaɗa, tare da ɗan ranƙwafowa gefen Maanal yana magana fuskarsa da wadataccen murmushi hannayensa duk biyu goye a bayansa. Gani yay Maanal ɗin ta tsaya cak, tare da hararar RK ɗin, amma shi sai hararar ta juye masa zuwa kallon soyayya ne, musamman daya ga yanda RK ɗin yay wata irin dariya cike da nishaɗi yana kuma maganar da shi sam baya iya jiyowa daga nan. Da ƙarfi ya rumtse idanunsa tare da datse laɓɓansa da haƙori tamkar zai hudashi. Haka yake idan har abu zai ɓata masa rai ko zaiyi magana yanada ɗabi'ar rufe idanu.
Kamar wanda aka zabura ya wani irin buɗe idanun tare da fara takawa cike da nitsuwa da ƙasaitarsa yayo waje. Kai tsaye sashen gaban Oum ya nufa tamkar wanda ake ingizawa, dai-dai nan motar RK ta gama ficewa a gidan, yayinda Maanal dake tsaye har yanzu ta yunƙura zata koma sashen Oum ɗin tana sauke ajiyar zuciya. Haka kawai yau kuma sai abubuwan RK ɗin ke mata tasiri a zuciya. Duk da dai tasan a tsakanin nan tabbas bata jin zafinsa kamar sanda suna a Jos.
Da sauri taja da baya tare da tsayawa cak ganin mutum a gabanta gingirin. Sai a lokacin ni'imtaccen ƙamshin turarensa ya wani bulala mata cikin hanci saboda yanda iska ta kaɗo mata shi sosai. Ɗan lumshe idanunta dake a cikin gilashi tayi sai kuma ta buɗe a lokaci guda tana ƙoƙarin daidaita kanta. A dakenta, a kuma nutsenta ta ɗago manyan idanuntan ta sauke akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa dake a tsuke, sai dai tsukewar tata bai hana kwarjininsa da mutumtaka da gizagonsa bayyana ba. Shima idanun nasa dake cikin fari tas ɗin eyeglasses ɗinsa dake matuƙar sake ƙawata fuskarsa da gwarzantashi akanta suke. Hakan yasa suka zubama juna ido, kallo irin na tsakkiyar idanun nan. Sai dai sam Maanal bazata iya jurewa ba, dan haka ta janye nata a hankali tare da rissinar da kanta. Cikin sabon yanayinta dake baƙanta masa zuciya da ƙona masa ita ta furta, “Kayi haƙuri sir, ban san kataho bane”. Tai maganar ƙasa-ƙasa da ƴar muryarta mai zurfi tana sake jan jikinta baya, tare da raɓawa ta gefensa zata zagayesa ta wuce.........✍️








✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣7️⃣




______________




https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥💃💃 Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....🔥⭐⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑royal jelly na fidda shape din mace...💃💃⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥⭐👑💃🏼💃🏼 Haseer supplements ta kawo muku supplement kaloli sai wanda ranki keso hajiya a cikin farashi mai sauqi Phone: 08038796871


__________




........Babu shiri taja ta tsaya cak, sakamakon jin an cafke tsintsiyar hannunta. Idanunta ta lumshe da ƙarfi sosai, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito. Sai dai me wannan Maanal ɗin ba Little Maanal bace ta shekarun baya. Wannan Maanal ce, Maanal cikakkiya ɗiyar Ammien ta. Wadda taga jiya taga yau take kuma fata da ganin gobe. Maanal ɗin data iya ɗauka da shanye abubuwa masu nauyin gaske da ko namiji sai jarumine zai iya zama irinta. Tuni ta saita kanta cikin dakiya da jarumta. Batare da ta juyo ko yin magana ba tai ƙoƙarin fisgar hannun nata. Sai dai me wannan rikon bana rago bane, ba kuma na sakaran namiji bane. Dan riƙone akai mata irin na manyan sadaukai. Ta fahimci hakan ta yanda koda ta fisgi hannun nata duk da da ƙarfi tayi shima bai ko motsa daga yanda yake ba, bai kuma juyo ya kalleta ba balle yin magana.
Sosai zuciyarta ta fara hasala, hasala irin wadda har take jin ɗacinta a maƙoshi. Cikin bayyanar ɗacin a harshenta ta furta, “Minene ma'anar hakan da kake yi?”.
Idan ginin gidan ya tanka shima zai tanka kenan, maimakon yin maganar ma sai fisgarta yay da ƙarfi yay sashensa da ita. Tana ƙoƙarin tirjewa amma hakan bamai yiwuwa bane gareta. A haka ya bugi ƙofar sashen nasa da ƙafa tare da tura kai ciki. Da wani kalar salo ya jefa Maanal saman lallausar kujerar falon, kafin tai wani yunƙuri ya rufu a kanta ta hanyar ɗaura ƙafarsa ɗaya a kujerar ya dogare, ɗayar na a ƙasa.
Wani irin matsewa da matuƙar takura Maanal taji da tsaiwar tasa a haka, tuni jarumtar tata ke neman suɓucewa, dan yanayin neman tuno mata da babban al'amarin daya shuɗe yake a rayuwarsu ta baya amma tana fisgo dakiyarta da tsiya-tsiya. Komai ta haɗiye daga fuskarta da harshenta idanunta a rissine dan bazata iya kallonsa ba ta furta, “Sir minene kake yi haka ne?......”
“Oh you're still pretending?”.
Ya faɗa cikin wani irin kaushi da ɗacin murya mai razanarwa. Dan ita kanta Maanal ɗin sai da taji kayan cikinta sun kaɗa. Amma da yake itama yanzu gwanarce. Ta karantu daga kowanne irin salo da taku sai ta zuba masa idanunta, wani shegen murmushi mai saka yin kamar zaka lumshe idanu ta sakar masa. A nutsenta tana mai sake tsatstsaresa da idanu ta ce, “Pretending?! Dan mi zanyi pretending? Akan me kuma? Yallaɓai”.
Wani kalar taune laɓɓansa yay da rufe idanu yana dunƙule hannunsa. Kamar zai kai mata duka sai kuma miya tuna ya fasa. A maimakon hakan sai ya nunata da yatsansa manuniya.
“Na fiki zafin kai”.
Yanda yay furucin yana wani wara mata manyan oily fararen ayes ɗinsa masu girma da cikar gashi dake cikin gilashi sai ta sake jin tsoro na mamayeta. Amma dai tai ƙoƙarin sake dakewa yanzu ma ta taɓe bakinta ta dauke kanta kawai. Cikin ƙunƙuni ta ce, “Ina ruwana to da zafin kan naka”. Hannu ya kai zai cafko fuskar tata, a zabure ta matsar da jikinta tayi ta gefen daya ajiye ƙafarsa, dan gaba ɗaya ji take kamar an sakata a wani kurkuku dama. Hatta da iska bata shaƙa yanda ya kamata saboda kusancin nasu. Haka ta miƙe ta nufi hanyar fita cikin sassarfa. Wani irin juyowa yay tare da sanya mata ƙafa sai gata a saman kujerar ta sake zubewa.
Hannayensa duka ya zuba a cikin aljihun wandonsa yay wani irin tsaya mata bisa kai ya zuba mata idanun sa tamkar zai haɗiyeta da su. “Ni kike ma ƙunƙuni?”.
Baki ta ɗan tura gaba, sai kuma ta kauda kai gefe, “Ni yaushe na maka ƙunƙuni?”.
Ƙwafa yayi cike da sake ƙuluwa, cikin kakkausan lafazin da bata san ya iya ba ya furta, “Na baki nan da kwanaki uku kacal ki fito ki faɗama Rafeeq gaskiya. Idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki”.
A karo na farko ta zuba masa wani irin kallo tana miƙewa akan ƙafafunta, a gabansa ta tsaya sunama juna kallon ido cikin ido, cikin kausasa masa harshen itama ta ce, “Oh mamaki? Ai ba yau na fara shan mamaki daga gareka ba daman. Gaskiya kuma bismillah ai ban hanaka sanar masaba kai, maza sanar masa kafin iska ta rigaka. Ina dai iyaka yace ya janye daga aurena ko, sai me? Nace sai me idan yayi hakan? Ko hakan sabon abu ne daga cikin rayuwata balle ya daman. Ba shi kaɗai ne namiji ba, dubu bayansa biye suke dani kuma in har na basu dama tamkar ƙyaftawar ido zasu amsa da rawar jiki har suna shelantama duniya samuna cike da murna da farin ciki. Balle nayi imanin ko ƴaƴa goma na haifa a duniya Rafeeq zai amsheni ni da su da hannu biyu ya godema ALLAH saboda soyayyar da yake min ta dabance, SO na yake, tsananin SO da wani mahaluki baitaɓa min kwatankwancinsa ba a wannan duniyar.....”
“Ƙarya kike yi!!! I said you are lying!!!!!”.
Ya faɗa cikin wani irin ƙaraji idanunsa da suka kaɗa jazur na firfitowa tamkar zai mareta. Matuƙar tsorata tayi, dan ta gama yarda marin nata zai yi kawai, sai da taji shiru sannan ta buɗe idanunta data rumtse. Suma sun kaɗa sunyi jazur kamar nashi. Cikin dakiya da sake tsatstsaresa da idanun ta ce, “Kai ka ɗauka ƙaryar ne, amma ni da yake nunama soyayyar zan bada labari. Zan kuma tabbatar maka da hakan nan da ƙanƙanin lokaci. Wata ɗaya kacal zuwa biyu zan zama MATARSA, MALLAKINSA ta har ABADA in sha ALLAHU”.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login