Showing 57001 words to 60000 words out of 221978 words
Chapter 20 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
ta bashi damar kamar yanda ƴan uwanta suka bata shawara a daren jiya. Sai dai ina ji take anya kuwa zata iya hakan? Amma sai wani sashe na zuciyarta ke sake ƙarfafata....
“Good morning my queen”.
RK ya faɗa yana ɗan duƙowa kaɗan saitin kunnenta. Wani irin numfashi taja tare da jan jikinta baya duk da bawani ya matseta bane akwai tazara a tsakaninsu. Murmushi yayi da ɗan ɗage mata gira sama ita kuma ta hararesa tana kauda kanta. Sai kawai ya fashe da dariya. “Oh ni ɗan Mamana irin wannan harar da akemin sai na sace amarya ai ko a sallar isha'i a ɗaura mana auren daga baya. ALLAH ki daina mun wannan hararar rikita min lissafi kike gimbiya. Balle irin yanda nai kewar nan taki kwana biyu dubeni har wata rama nayi marayan ALLAH abin tausayi”.
A yanda yake maganar batama san sanda taji murmushi na neman suɓuce mata ba. Amma sai ta dake abinta ta danne tare da ɗan girgiza kanta ta ce, “ALLAH dai ya shiryeka”.
“Amin matar Rafeeq Kasheem Kura”.
Manaal bata kulashi ba, dan wayarta dake neman agaji, ƙoƙarin cirota ta shigayi a bag shi kuma ya amshi ɗan lunch box ɗinta na abinci data haɗa. Yazeed ne ya bayyana ɓaro-ɓaro akan screen ɗin. Hakan ya saka RK taɓe baki cike da basarwa yabar wajen. Da kallo kawai ta bisa ƙasa-ƙasa tana mai kai wayar kunnenta a nutsenta tai masa sallama. Da kulawa ya amsa mata da ga can tare da tambayarta jikinta tace Alhamdullah ta samu sauƙi.
“Masha ALLAH nima zuwa anjima zan shigo duk kin bi kin tadamin hankali da rashin ganinki tunda nazo aikin ma yaƙi yuwumin yanda nake so. Amma yanzu na ɗan ji ƙarfi tunda na jiki Alhamdullah”.
Shiru tai ta kasa cemasa komai. Shima sai kawai ya saki murmushi daga can, tare da faɗin, “To sarkin kunya bari na barki nima zan fitane ma na kiraki”.
“ALLAH ya tsare ya bada sa'ar abinda za'aje nema”.
“Amin ya rabbi mar'atussaliha”.
Ya faɗa can ƙasan maƙoshi cike da shauƙin so da ƙara jin tarin ƙaunarta har ƙarƙashin zuciyarsa. Wayar tai ƙoƙarin maidawa cikin bag ɗin dai-dai da isowar RK wajen da mota. Fitowa yay ya buɗe mata mazaunin gefensa ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima yay ma motar key suka fice. Yanata dai ɗaɗɗaurewarsa bata kulashi ba. Dan ta fahimci yana masifar kishin Yazeed. Koyaya yaga wani abinda ya shafi Yazeed a tattare da ita zai fara fushi. Itako sai dai yay tayi, dan Yazeed dai tare ya gansu, yazeed kuma abin girmamawarta ne dan ya taka rawar gani a rayuwarsu a lokacin da kowa ya guje musu. Shiko fa daga sama ya tsinceta.
Sunyi nisa a tafiyar motar shiru dan kansa ya yanke shirun nasu ta hanyar ɗan juyowa ya kalleta fuskar dai babu walwala. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Har yanzu baki sanarma su Zulaiha kina Abuja ba ne?”.
Shiru kamar bazata tanka masa ba sai kuma a can ƙasan maƙoshi ta ce, “Sun sani wani abu ya faru ne?”.
“No babu komai, nagane basu zo dubaki ba har yanzu”.
“Ni nace su barshi basai sunzo ba.”
“Okay”.
Ya faɗa yana ƙara damƙe steering da ƙyau. Daga haka suka sake yin shiru har suka iso Mawaad Company. Yauma kamar wancan ranar komai a tsaftace a kuma nutse yake a companyn. Sai da ya daidaita parking da ƙyau tana ƙoƙarin ɓalle murfin motar ta fita ya dakatar da ita. “Na musu reporting akan baki da lafiya shiyyasa baki zo jiya ba kamar yanda suka buƙata. Dan haka ko sun tambayeki sai kisan amsar da zaki basu. Please dan ALLAH ki kula, wajen nan cike yake da ƙartin banza kar'a tsinceni a titi muna raba hali da al'umma”.
Ɗan kallonsa tai a karo na farko sai kuma ta janye lokaci guda tana mai girgiza kanta. Maimakon amsa masa batunsa ta buɗe kawai ta fice abinta. Ta ɗan fara tafiya taji alamar ana binta a baya, juyowa tai da taga shine riƙe da ƴar lunch box ɗinta. Tsayawa tai tare da miƙa masa hannu, amma sai ya girgiza mata kai yana nuna mata hanya alamar suje. Babu yanda ta iya haka suka jera har cikin Companyn...
Wani irin lumshe idanu AA Darma dake zaune cikin motarsa daga baya dan driver ne yau ya kawo shi Office ɗin tare da datse leɓensa ba ƙasa da ƙarfi. Sai dai sam bazaka taɓa fahimtar hakan ba kasancewar jarida a hannunsa yana dubawa. Shima isowarsu kenan, kuma tun a hanya a wajen fitilar bada hannu yaga motar RK ɗin, ya hango mace a motar amma baiga wacece ba. Sai dai haka kawai zuciyarsa ta bashi wacece ɗin, dan haka koda suka iso kasancewar sun riga su RK ɗin shigowa Companyn sai bai fita a motar ba. Komai daya faru a kan idanunsa ne dake sakaye a cikin glass mai matuƙar haske daya ƙawata ƙyawun nutsatstsiyar fuskarsa. A hankali yay wurgi da jaridar hannun nasa a sit ɗin gefensa.
Shi dai driver bai san mike faruwa ba, amma yana tunanin ko wani abin ogan nasa yake shiyyasa. Suna a haka RK ya fito fuskarsa cike da walwala kamar ba shine ya gama fushin kishin Yazeed ba. Motarsa ya shiga abinsa yabar harabar companyn, securitys ɗin gate suka ɗage masa karfe da aka gitta a ƙofar bayan gate ya fice. Wani siririn tsaki AA Darma ya saki a can ƙasan maƙoshinsa. Sai kuma ya ɓalle murfin motar aɗan fusace ya fito batare daya ɗauki komai nasa dake a motar ba. Sanye yake cikin ash color ɗin suit masu haske da sukai masa shegen ƙyau. Daga ciki black rigace mai wuyanta har saman wuya. Yanda yake taku cike da bada faɗi da cika waje ma kawai abin kallo ne. Securitys sai gaidashi suke amma hannu kawai yake iya ɗaga musu batare da ko kallonsu ba. Koda yazo ga ƙofar shiga da sauri aka buɗe masa ya shige drivern sa biye da shi da tarkacensa. Tsitt kake ji ma'aikatan dake wajen sakamakon shigowar tasa. Sai kuma kowa ya shiga faɗin, “Good morning Sir!”. Hannu kawai ya ɗaga musu sau ɗaya yay wucewarsa batare da ko kallon kowa ba anan ma. Hakan ya sakasu fahimtar yau fa gizagon boss ɗin yafi na kullum, sai kowa ya ƙara kama kansa.
Elevator ya shiga tare da danna floor ɗin ƙarshe 6th da office ɗinsa yake, shima drivern nasa ya shiga. Ƙofar zata fara rufewa Maanal da AS da yay mata rakkiya office tai singing da ake buƙatar tayi suka iso wajen. Shigowa sukai da sauri batare da hankalin AS ɗin yakai ga wanda ke cikin elevator ɗin ba kasancewar ya ɗan juyama ƙofar baya yana danna waya. Balle kuma Maanal da itama gaba ɗaya nata hankalin ke akan wayarta. Sai da suka gama shigowar AS ya shaƙi ƙamshin turaren boss. Sai kuma sukai ido huɗu da driver. Ya juya da sauri nan ma sukai ido huɗu da AA Darma.
Cikin ɗan rawar baki ya ce, “So...sorry sir good morning. ALLAH bamma lura kaine a ciki ba. Zan kai new staff ɗinmu office ɗinta ne bisa umarnin Director Mustapha”.
Kai kawai AA ɗin ya jinjina masa, yayinda Maanal da zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri-sauri ta sake dakewa abinta dan tunda AS ya fara magana ta ɗan ɗago ta gefen ido ta saci kallon wanda yakema wannan rawar bakin sai ta ɗauke kanta. Ɗan duƙowa yayi kaɗan ƙasa-ƙasa ya furta, “Boss ne kiyi gaisuwa”.
Shiru tai kamar bazata kulashi ba sai kuma a hankali a can ƙasan maƙoshi batare data kalla kowa ba ta furta, “Morning”. Daga haka taja bakinta tai shiru. Ita tai abin amma AS ta bari da ruɗani, sai wani irin haɗiyar yawu yake yana kallon AA ɗin ta gefen ido ko zaice wani abu akan gaisuwar rainin wayon sabuwar ma'aikaciyar tasu....
__________★
Fuska cike da murmushi Hajiya Basariyya ke kallon kayan da ƴar Tata Huznah ta baje a gabanta. Ba kayan ci bane ba kuma na sakawa ba kayan da malam ne na Zaria ya haɗoma Huznah ɗin bayan ta ɗauki tsawon kwanaki tana acan ana tsumata da wasu aikin. Ba kuma akan kowa akai hakan ba sai sabon saurayinta data samo a birnin tarayya Abuja lokacin bikin ƴar ƙawar Hajiya Basariyya ɗin. Sam kayan babu wani ƙyan gani ko birgewa a kallonsu. dan kuwa tarin guraye ne da ruwayen magani da layu sai garin magungunan da turarruka na shafawa harda su hoda da kwalli na idonka idona. Sai da ta gama mata bayanin komai dalla-dalla kafin ta ta fuska ɗauke da murmushi ta ce, “Kin daiga komai Ummi, bayan kuma wanda yay mun a jikina dan na aikata iya aikatuwa. Yanzu dai babu zama dole na shirya na wuce Abuja. Dan ya tabbatar min da in dai nayi komai yanda ya dace babu fashi auren mu zai kasance tare da na Yazeed ne a gidan nan”.
“Kai Alhamdullah Masha ALLAH. ALLAH dai ya sakama malam da alkairi wlhy. Shiyyasa bana baƙin cikin biyansa duk abinda ya buƙata dan shima ana samun biyan buƙatar daga nasa aikin. Tafiya Abuja kam dole ne. Sai dai Daddynku nake tsoro dan yana gari. Dama da yaya ya bari kika tafi Zaria ɗin nan. Yanzu ko akace Abuja nasan da rigima”.
Cikin matuƙar damuwa Huznah ta ce, “To Ummi yanzu yaya zamuyi kenan, dan ni dai ko ana ha maza ha mata sai naje Abujar nan wlhy??”......✍️
_Tofa, maji ma gani wai an bizne tsohuwa da ranta jama'a 😂🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣7️⃣
........Maimakon Hajiya Basariyya taji haushin furucin ƴar tata sai ta tuntsure da dariya tana faɗin, “Ja'ira wato ke ƴar daɗi soyayya ko? Kwantar ma da hankalinki komai zaizo da sauƙi bani lokaci dai nayi tunani.”
“To Ummi nidai dan ALLAH kar tunanin naki ya wuce yau da gobe dai. Dan a matse nake gashi nayi kewarsa ina son ganinsa.”
Anan ɗin ma dariya Hajiya Basariyya ta sanya abinta.
__________★
A can ɓangaren Aunty Sabuwa ma shiri takema ƴarta na mugayen mallaka, dan hatta da Hajiya Yaya aba'a ƙyaleba tuni sunanta na wajen boka. Kai shi kansa Daddyn ba tsira yay ba da sauran ƙannen Yazeed mata. Dan tace tako ina sai ta bama ƴarta garkuwa. Tako bayar ɗin gwagwargwadon abinda take ganin ya wadaceta. Ga maganin mata ana ɗirkama Nazeefa kamar babu gobe, gefe kuma fetsararrun ƙawayen uwarta su Hajiya Malika na koya mata kissa da kisisina harda salon kwanciya da miji.
A tacan ɓangaren Mahaifinta kuwa yana nasa shirin ne akan Daddy. Dan a wannan karon yaci alwashin samawa kansa nasara akan Daddyn. Sai kuma shirin biki na ƴar gata da sukeyi da ga shi har Aunty Sabuwa ɗin.
Ata nan ɓangaren Hajiya Yaya shirin suma suke na garari, dan a satin nan zata wuce Dubai ita da Baraka da Asalamiyya su haɗo lefe da nasu kayan cin bikin. Da farko Daddy ya hana tafiyar, saboda ya fahimci ana komai ne dan ƙuntatama Ammie. Amma sai Ammien ta dinga masa roko da magiya dan tasan hanawar wata sabuwar rigima ce, kuma dai laifin a kanta da baya so zai ƙare. Dan tuni Hajiya Basariyya tayi uwa tayi maɗaukiya a bikin shiyyasa ita ake kiranta ƴar baƙin ciki. Haka dai dole Daddy ya bari dan yana matuƙar jin kunyar Ammie ta roƙesa abu ya kasa mata saboda dattakonta itama, sai dai da sharaɗin karsu wuce sati ɗaya, idan kuma hakan ta faru zasu sha mamakinsa. To a hakan ma dai Ammie bata tsira ba dan sai da tasha zagi da habaice-habaice. Ita dai bata kulasu ba kamar yanda ta saba. Sai ma ta maida hankali akan shirin Daddy da shima yake yi dan wannan shine karo na biyu da zai aurar. Na farko ya aurar da su Shahidah da Asalamiyya a rana ɗaya, duk da dai an kwashi matuƙar rikici a wannan aure dan Hajiya Yaya cewa tai baza'a haɗa mata auren ƴa da agololi ba. Shiko yace tayi kaɗan tayi tsororo ma. Bayan dai an sha fama dole ta haƙura akayi yanda ya tsara ɗin. Sai dai ita Asalamiyya ma nata auren bamai jimawa bane. Dan a gida ma ta haifi ƴarta. To yanzu ko Yazeed kaɗai za'a aurar. Babban ɗansa kuma namiji, sannan ɗa mafi soyuwa a garesa da Hajiya Yaya. Damma ALLAH ya ragewa aya zaƙinta auren ba wanda yake so bane ba. Saboda har yanzu sam Daddy baya son wannan haɗin kawai dai babu yanda zai yi ne ya haƙura. Amma yaci alwashin sai ya bama kowa mamaki a auren Maanal da Yazeed in sha ALLAHU.
To daga can gidan Alhaji Mamman ma dai shirin suke. Dan jikokin duka biyu nasu ne, dan haka dole suma su taka tasu rawar da aljihunsu da kuma matsayinsu. Dan haka suka kasance cikin irin nasu shirin su da sauran ƴaƴansu da dangi. Dan ko tafiya Dubai ta zama kamar za'ayi ta a tare ne bisa ɓangarori biyu. Ba Hajiya Yaya da Asalamiyya da Baraka bane kawai a tafiyar harda mahaifiyar su Hajiya Yaya ɗin da kuma wasu ƙannensu Hajiya Yayan su biyu, da harda Aunty Sabuwa amma ta zamewa tafiyar dan akwai binne-binnen da suke son zuwa suyi a inda za'a saka amarya duk da ma Daddy ya ɓata musu tafiyar da buri wai anan gidan su Yazeed ɗin zasu fara zama a tare da su. A yanzu hakama ana kan gyara sashen samarin gidan da dama shine dai zaune a ciki kasancewarsa namiji tilo a baya sai yanzu da Ammie ta haifi Waleed da Hameed. Suma acan ɗin suke amma yanzu Daddy yasa ana musu nasu ginin ata can bayan na Yazeed ɗin kasancewar akwai fili sosai. Sai suka dawo sashen Ammie yanzu tunda ita kaɗaice. A wannan gini ma dai sai da akai ɗan rikici, ɗan daga Hajiya Yaya har Hajiya Basariyya nunawa sukai basu yarda ba. Sai da Daddyn yay musu kaca-kaca yace idan akwai wadda ta haifesa a cikinsu kota saya masa gidan ko suka haɗa kuɗi suka saya to tazo ta hanashi yima yaransa wajen zama sannan suka kama kansu. Amma hakan bai hanasu komawa gefe suna zagin Ammie ba da aibantata.
___________★
Shine ya fara fita a elevator ɗin, hakan yasa AS da driver rufa masa baya cikin hanzari. Cikin takaici da ƙunar zuciya Maanal ta raka bayansu da harara kafin itama ta fito tana jan tsaki. Maimakon tabi bayansu sai kawai ta samu waje ta zauna anan wajen elevator ɗin. Tsahon mintuna goma sai ga AS ya dawo wajen. Da mamaki yake faɗin, “Ina can inata tunanin inda kika maƙale ashe kina nan.”
Ɗan ɗagowa tai kawai ta kallesa batare da tace dashi komai ba. Shima sai ya kama kansa dan ya fahimci Maanal irin mutanen nan ne masu masifar miskilanci da kame kai. Har office ɗin Directors Mustapha ya kaita, sai dai sun samu baya ciki da alama ya ɗan fita. Wajen zama ya nuna mata yana faɗin, “Ki jirasa anan duk inda yake nasan baiyi nisa ba”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa. Shima sai ya juya ya fita abinsa. Bayan futarsa ajiyar zuciya ta ɗan sauke da numfashi mai ƙarfi. Dai-dai lokacin idanunta suka sauka akan hotuna huɗu da aka saka daga can saman saitin inda kujerar mai office ɗin take. Hoton farko shugaban ƙasa ne a jiki, sai Ministan Abuja. Hoto na biyu AA Darma ne da yay wani kalar masifar ƙyau, sanye yake cikin wasu shegun suit baƙaƙe da adon gold a jikinsu mai matuƙar ƙyalli, yaɗan zauna a saman kujera mai tsaho ɗin nan, sai ya kasance kamar ya zauna a karkace ƙafarsa ɗaya ya sakko ƙasa sosai ɗayar na daga jikin ƙarfen da akaima kujerar kwalliya. Takalminsa baƙi da kwalliyar gold shima. Bai saka rigar suit ɗin ba, yana riƙe da ita ne kawai da hannunsa na dama dake sanye da agogo kalar gold a saman kafaɗarsa, sai farar long sleeve shirt ɗin data sauna ɗaran a jikinsa ta fiddo da girman jikin dake a buɗe. Ya saki wani mayataccen murmushi daya sakata ƙurama cikakkiyar fuskarsa mai kwarjini da adon gashi ido. Idanunsa sanye da farin gilashi da tun ƙuruciya tasan yana sakawa. Sun wani haska oily idanun nasa da suke farare tas kamar an watsa musu madara tsabar yanda suke ƙyalli da ɗaukar idanu....
Kaɗan Director Mustapha ya ɗan bubbuga desk ɗin, dan sai sallama yake amma babu alamar tasan da shigowarsa. Numfashi ta ɗan ja ta fesar cike da kame kanta da vasarwa ta dawo hayyacinta. Murmushi ya ɗan yi a ƙasan ransa yace (Boss Sarkin sa'a. Akoda yaushe cikin kama zuciyar ƴammata yake).
Ita kam