Showing 99001 words to 102000 words out of 221978 words

Chapter 34 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

key, I want to drive myself”.
Babu musu driver ya rissina ya miƙa masa key ɗin. Sai kuma ya buɗe masa motar da sauri.
“Ka sama mata taxi”.
Ya sake faɗa yana ƙoƙarin shiga motar, kallon Huznah driver yayi, sai kuma ya amsa da sauri cike da girmamawa. Huznah kam dake tsaye kamar zata saki kuka kallonsu kawai takeyi, tana ji tana gani a gabanta ya birka motarsa ya fice cike da ƙwarewar iya tuƙi na nutsuwa da cikar kamala....
Lallai yau taga madarar wulaƙanci da babu ko gauraye a cikinta, wato mutumin nan cikin ruwan sanyi yake tsula maka tsiya babu hayaniya babu hargowa ko yawan magana. Dole ne ta koma Kaduna su sake shiri kam, amma zata fara bari ta haɗu da mahaifiyar tasa dan taga yaya nata takun itama, hakan zai sa susan irin shirin da zasu musu su duka.. da wannan tunanin ta ballama drivern harara ta fice da ƙafarta.....


★★★


Maanal ta jima a wajen tana kuka, sai da ta fara jin zuciyarta na mata nauyi a cikin ƙirjinta kafin ta ɗago kanta da ƙyar, office chair ɗinsa ta zubama ido sosai tamkar shine a wajen, har yanzu hawayen na cigaba da ziraro mata. Tunanin dake neman tasiri a ranta ta ture da ƙarfin tsiya tare da miƙewa ta nufi restroom ɗin kamar yanda ya faɗa, dan itama tasan ko giyar wake tasha bazata fita a haka ba ai. Sosai restroom ɗin ya haɗu, gashi ƙal-ƙal sai ƙamshi yake zubawa kamar ba toilet ba. Ta jima tsaye tana kallon kanta a mirror ɗin bayin tana hawaye kafin ta wanke fuskar tata ta fito bayan ta gogeta da ƙaramin towel fari tas dake a bayin. Harta nufi ƙofa ta koma da baya, shopping bag ɗin daya ajiye a gabanta ta ɗauka kasancewar ganin abinda ya rubuta a takardar daya ajiye a sama, sai kuma ta maida ta ajiye. Nan ma ta juya zata tafi idonta suka sake sauka a novel ɗin nan nasa. Baki ta tura gaba sannan ta ɗauka shi dai ta ficewarta..
Koda ta fito bata kula kowa ba a wajen ta shiga haɗa ƴan tarkacen kayanta, kallonta kawai su Zaharadeen suke cike da gulma. Sai Yaqub ne daya miƙe tsaye yana kallonta tun shigowarta ya furta, “Sister Maanal are you okay?”.
Kanta kawai ta jinjina masa batare da dace komai ba. Kafin ya samu damar sake magana ta kwashi kayanta zata wuce. Cikin sauri ya bita yana faɗin, “Ina zaki je?”.
“Gida”.
Ta bashi amsa a takaice. Cikin tashin hankali ya buɗe baki zai sake magana a fusace ta ce, “Please Yakub! Nace ba komai. Leave me alone”. Daga haka tai gaba abinta fuuuu. Shiru yay kawai yana kallonta, gaba ɗaya fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa da tashin hankali. Shin mike faruwa? Mi akai mata? A office na CEO fa aka kirata! Miya faru acan ɗin?”. Rashin mai bashi amsa ya sashi juyawa jiki a sanyaye ya koma ciki. Sai kuma ya sake tadda wani abun takaicin, su Zaharadeen ne suke buɗe babin gulmar Maanal ɗin. Wai maybe ta faɗama CEO tana sonshi ne shine ya koreta a aiki, sai ALLAH ya ƙara suke mata da kiranta mai girman kai da faɗin rai. Takaicinsu ya saka Yakub ko kulasu baiyi ba......

______________★


“Alhamdullahi ranka ya daɗe aiki ya kammala. Wannan shine cikakken bayani akan ainahin mahaifinta dama zuri'arta baki ɗaya”. Rabilu ne mai maganar fuskarsa washe da murmushi yana miƙama Sen.. Bukar bayani akan Maanaal daya binciko kamar yanda ya buƙata. Sosai fuskar sa ta washe da murmushi. Dan shi kaɗai yasan yanda yake azabtuwa da so da ƙaunar yarinyar nan data mamaye dukkan illahirin jinin jikinsa. Yanzu haka yau har gaban Mawaad company yasa drivern sa yaje ya faka mota har Maanal ta iso. Fitarta a motar Shahidah da dukkan abinda ya faru a wajen kan idonsa ne. Ji ya dingayi kamar ya sato ta saboda yanda tai matuƙar ƙyawu a cikin kwalliyar ta yau.
Rabilu ya cigaba da faɗin, “Su ɗin asalin su ƴan jihar Kebbi ne, ƙaramar hukumar suru a wani ƙauye da ake kira giro. Mahaifin nata ɗan sanda ne, dan har ya kai matakin DPO amma yanzu ya ajiye aiki sakamakon doguwar jiyyar da yayi. Ita kuma mahaifiyarta bata tare da shi a yanzu, dan sun rabu shekaru kusan takwas kenan, a yanzu haka tana auren wani Alhaji Usman Chalawa ne anan kaduna, yana riƙe da su kuma tamkar mahaifin nasu koma fiye da shi.”
Cike da zumuɗi ya furta, “Rabilu kaje wajen Oler ka amshi key ɗin motar ka sabuwa dal, zuwa dare zan nemeka idan na koma gida”.
Cikin matuƙar washe baki Rabilu ya shiga godiya harda ɗan zamowa daga visitors chair da yake zaune ta office ɗin Sen.. Aifa cike da zumuɗi ya bar office ɗin. Kai tsaye gidan Sen.. Bukar ya nufa domin amsar alƙawarinsa dan yasan baya magana biyu akan alkawari irin wannan daya shafi mata. Zai iya cewa dukan matan alhajin idan ka cire uwargidansa duk shine ya masa bincike akan sauran biyun. Ya kuma taka rawar gani akan samuwar auren fiye da zaton mai zato. Sai dai ya fahimci kamar Senator ɗin yafi sakin kuɗi da ɗoki akan wannan ƴar shilar. To ƴar shila mana. Akan matan Alhaji ai manaal ƴar shila ce. Dan ko jikansa na farko ya girmi Maanal sosai. Aiko ina sha ALLAHU zai yi iya ƙoƙarinsa dan ganin tako ina Alhaji bai samu matsala ba, ya kuma mallaki yarinyar da gaggawa. Dan yasan irin wannan kariɓujin arziƙin da ire-irensa sunta zuwa kenan. Zama kuwa ai ba nashi bane ba....


____________★


Cike da nutsuwa Daddy ke kallon Yazeed. Yayinda shi kuma kansa ke duƙe a ƙasa rauninsa na sake bayyana akan fuskarsa. Karo na farko Daddy ya ɗan saki murmushi, yayinda tausayin yaron nasa ke ratsa masa zuciya. Ya jima da fahimtar tsananin so da Yazeed kema Maanal, sai dai bai sake tabbatarwa ba sai a ɗan tsakanin nan. Musamman yau da yazo masa da roƙo da magiyar janye batun sai nan da wata biyar ayi aurensa da Manaal. So yake a haɗesa gaba ɗaya anan da sati biyun daya rage shi da Nazeefa. Gyaran murya yay da gyara zamansa. Hakan yasa Yazeed ɗagowa ya ɗan kallesa.
“Yazeed kasan dai ina bayanka nima ɗari bisa ɗari akan zancenka da Maanal. Sai dai ina son kamar yanda su Baba Kalla suka faɗa wannan karon naje da kaina da baba nema maka aurenta ga mahaifinta. Hakan shine zai bada salama game da tujarar mahaifiyarka akan al'amarin”.
“Daddy nima na yarda da hakan, amma dan ALLAH ina sake neman alfarmar haɗewar gaba ɗaya. Nasan ko'a cikin satin nan zaku iya zuwa ga mahaifin nata, idan kuma ka amince min ni saina fara zuwa na ganshi”.
Ɗan jimmm Daddy yayi, sai kuma ya shiga jinjina kansa. “Shike nan na yarda da zancen naka in sha ALLAHU za'a haɗe bikin nan da sati biyun, zan samu Baba da batun shima sai mu saka ranar zuwa muga mahaifin nata, kai ka tsahirta sai bayan mun dawo ɗin. Kadai je ka cigaba da shirinka na zama angon mata biyu a rana ɗaya”.
Ƙasa Yazeed yay da idanunsa wani murmushi na suɓuce masa. Yayinda zuciyarsa ke wani irin washewa da farin ciki mara misaltawa. Ji yake kamar an masa gafarar zunubansa. Yana fitowa ya shiga neman layin Maanal dan yay mata albishir, sai dai bata shiga ba. Duk da yasan yanzu tana office kasa haƙuri yayi ya shiga neman Shahidah. Bayan sun gaisa yake tambayarta Maanal fa. Cikin girmamawa ta sanar masa har yau ba'a dawo mata da wayarta data samu matsala ba ne, amma tana ƙyautata zaton yau za'a kawo mata, sai dai idan ta tashi zata haɗasu.....


___________★


Shiru kawai Ammie tai tana kallo Daddy dake mata bayanin sabon hukuncin daya sake yankewa akan dawo da zancen bikin Maanal da Yazeed anan da sati uku. Za'a haɗe ɗaurin auren kawai idan ma bikin Maanal ɗin ne za'a ɗaga nan da zuwa ko wata ɗaya ne idan ita bata shirya ba to. Sai kuma batun zuwa ga dangin mahaifinta kamar yanda sukai alƙawari tun farko. A yanzu haka ma yana shirin zuwa su tattauna da baba ne. Ya sanar mata ne koda sun gama yanke hukunci shi da baban basai sannan taji ba.
Zuciyar Ammie kaikawo kawai take a cikin ƙirjinta, sai dai kamar yanda ta saba dannewa yanzun ma saita danne ta amsa masa da girmamawa tare da jera addu'ar fatan alkairi. Wannan halayyar nata ke ƙara masa jin sonta da ƙaunarta. Bayan ya wuce hawaye cike da idanunta tayi kiran Nene, ko gaisawa basuyi ba ta sanya mata kuka. Sosai hankalin Nenen ya tashi, ta shiga tambayarta abinda ke faruwa a rikice. Sosai Ammie tayi kuka kafin ta zayyanema Nene komai. Itama hankalin nata tashi yay, harma taji ta gagara furta komai..


___________★


“Aunty Babba nifa ina son ku haɗu ke da Aunty Majdiya da Aunty Khaleesat kuyi magana da Baffah akan batun nan. ina so a cikin watan nan iyaye suyi magana, kuma wata biyu kawai nake so a saka, itama Maanal yau zanyi magana da ita”.
Baki Oum ta buɗe kamar a ɗan firgice zata bama RK amsa idanunta suka sauka akan AA dake kokarin shigowa, sai dai furucin RK ya sashi tsayawa cak shima..........✍️




_Wannan fa shine cakwakiya, tako ina kowa ya zaburo. Manaal akwai white blood kam🤣. Dangin AA wai mike damun Yayanku ne?🥱🏃_












✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖4️⃣4️⃣




______________




.......Kallonsa kawai Oum take yi zuciyarta na motsawa da bugawa da sauri-sauri, yayinda shima ya zuba mata gajiyayyun idanunsa da suka sake kaɗewa. A hankali ya ɗaga ƙafarsa zai juya ya fita ta kira sunansa a hankali.
“Ajwaad!”.
Cak ya tsaya batare daya juyo ba. Yayinda RK da bai lura da shigowar AA ɗin ba ya juya shima yana kallonsa. Cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa ya saki murmushi da faɗin, “Ni dai ban more ɗa ba. Malam dawo bafa wata magana bace daban kaima ayi dakai batun son zuwa a nema min auren ƙanwarka Maanal mukeyi kawai”.
Da wani irin ƙarfi AA ya rumtse idanunsa jikinsa na wata irin tsuma. Da sassarfa ya nufi ƙofa murya a shaƙe ya furta, “Oum na ɗakko su Mamy” daga haka yay ficewarsa.
Da mamaki RK ya dubi Oum shima, “Aunty mike damun ɗanki?”.
Murmushin yake Oum tayi kawai. Zuciyarta na ƙara raunana da mata nauyi. Cikin son danne komai ta ce, “Maybe aiki ne ko kuma an kunnosa daga waje. Kaga ka bari zamu tattauna anjima su Aban sun iso”....



___________★




Kamar yanda Sen Bukar ya faɗa zuwa dare ya sake sabon zama da Rabilu. Sun sake tattaunawa sosai tare da tsaida ranar zuwa Giro domin ganawa da mahaifin Maanal. Yayinda tun a ranar ya sanarma uwargidansa shifa zai ƙara aure. Dan yau a gidanta yake. Kamar yanda ta saba cikin nuna rashin damuwa tai masa addu'a da fatan alheri. Sai da ta fito daga ɗakin nasa ta koma nata taci kuka. Ita kaɗai tasan yanda take matuƙar takaicin aure-auren nan na mijinta. Dan ita macece mai tsananin kishi. Shiyyasa a dukansu daya auro kowacce jinta take a sabuwar kishiya. A gareta bata yarda da zancen hausawa da kance kishiya ta biyu ita kaɗai ce kishiyar uwargida ba. Ita duk kishiya sunanta kishiya a wajenta. Sai dai irin matan nan ne ita masu ƙullata da shanye abu a cikinsu bazaka taɓa jin sun furta da baki ba. Shiyyasa ake mata kallon mai haƙuri. Amma sam ba haka bane ba, domin kuwa tana nan tana tara abubuwan a rai suna mata nauyi...
Shiko Sen.. Bukar ko'a kwalar rigarsa, dan tun a daren yama gama tsara komai. A gefe kuma ya saka babban yaronsa Oler yo shopping na garari zuwa gobe domin yin tsaraba kaikace ganin danginsa zaije ƙauye ba neman iznin neman auren ba......


_________


Tunda ya baro sashen Oum kulle kansa yay a bedroom ɗinsa. Wani irin ciwo kansa ke masa, ga sanyi na ratsa masa ɓargon jiki da ƙashi, bai ko iya cire takalman ƙafarsa ba ya faɗa saman gado tare da jan duvet ya ƙudundune kansa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa zazzaɓi ya rufesa gaba ɗaya. _(Na tsaneka, wlhy na tsaneka Ajwaad. Bana son ganin ko fuskarka, da nasan ƙaddara zata sake haɗamu a duniyar nan dana roƙa ALLAH mutuwata kafin hakan. Na cigaba da yin aikin nan ne dan kawai baka isa hanani yin abinda raina keso ba a duniyata a duk inda naso hakan koda kuwa wajen ya kasance mallakinka ne.....”)_ wani irin sara masa kan nasa yayi sakamakon kalamanta da suke maimaita kansu a cikin kunnensa tamkar yanzu ne take ambatosu, ko a ɗazun ma dakewa kawai yake yi a gabanta. Ji yake tamkar yayta fasa ihu, ihu irin wanda sai ya janyo girgizar ƙasar da kaf gidajen duniya zasu narke cikin ƙasa. Sai dai ba zaiyi hakan ba, sai ma ambaton ALLAH da ya dingayi a zuciyarsa...
Dai-dai nan Oum da hankalinta ya kasa kwanciya ta iso sashen nasa. Dan har ta nufi sashen mahaifinsu ta fasa tayo nan. Ganin babu shi a main falo yasata haurawa sama da sassarfa. Nan ma babu kowa komai ma a kashe yake tamkar ƙasa. Bedroom ɗinsa ta nufa, tai nocking da kiran sunansa amma shiru. Handle ɗin ta kama zata buɗe dan zuciyarta na sake tabbatar mata babu lafiya amma sai taji gam. Sosai hankalinta ya sake tashi ta shiga kiran sunansa cikin damuwa da lallashi. Amma fin mintuna biyar baida alamar amsawa. Hawaye suka fara ziraro mata cikin rawar murya ta ce, “Haba sweetheart sokake na maka kuka. Ka buɗe naga halin da kake a ciki Please Autan Oum”.
Nan ɗin ma babu alamar motsinsa, hankalinta ne ya sake tashi, cikin sassarfa ta juya ta fita. Sashen Abah ta nufa, sallama kawai tayi batare da jiran amsa ba ta danna kai cikin bedroom ɗinsa. Dai-dai ya fito a wanka, batare da ya kalleta ba cikin barkwancinsa da Fawzan ya gada ya ce, “Ai ni da na cika fam saura kaɗan na fashe ganin matar gidan yau bata ɗokin dawowata kamar yanda shima ɗanta baiyi.....”
Jin tayi shiru sai ma kamar tana kuka ya sashi fasa nufar mirror da yay niyya ya juyo yana kallonta. Tsamm yayi sai kuma ya tako a hankali zuwa inda take cike da nutsuwarsa da cikar kamala. “Fateema miya faru?”. Ya tambaya hankali tashe. Idanunta dake zirar da hawaye ta zuba masa. Da ƙyar ta iya motsa lips ɗinta ta furta, “Ajwaad. Ya rufe kansa a ɗaki nayi kiran duniya bai amsa ba. Ina jin tsoro, tsoro nake ji Zaki na, kada yanayinsa na bayane ke son dawowa”.
Ɗan lumshe idanu Abah yay ya sake buɗewa a kanta (Sak ɗabi'ar AA da alama a wajensa ya gada rufe ido da buɗewa yayin magana😂👌🏃). Hannunsa yasa ya riƙo nata, cikin yanayin tashin hankalin shima ya ce, “Oh kenan akwai abinda ke damunsa? Dan a haka yaje ɗakkomu airport fuska kicin-kicin, daga gaisuwa ko bai sake kulamu ba har muka shigo gidan nan. Wani abu ya faru ne?”.
“Ni dai a sani na babu abinda ya faru a yau ɗin, duk da dai satittikan nan gaba ɗaya gashi nan dai tunda ya tashi daga zazzaɓin nan na gab da tafiyarku, yau kuma daga office ya wuce ɗaukanku dan da Fawzan ne zai je sai ya kirani akan akwai meeting na gaggawa da zai shiga dan ALLAH nama Auta magana yaje ɗaukanku ko Babban yaya. Shi kuma Fadeel ya tara aiki a office saboda zuwa Kanon nan da yay shiyyasa na turama Autan text akan shi yaje, ya kuma kirani a waya babu wani damuwa a tare da shi yace min zaije ɗin dan bashi da wani abu mai muhimmanci a lokacin, sai kuma gashi ya dawo yanzu a birkice.”
Cikin furzar da iska mai nauyi Dad ya ce, “It's okay ina zuwa.” closet ɗinsa ya nufa ya saka kaya tare da buɗe wata loka ya dudduba keys, ɗakko na sashen AA yayi yazo ya kama hannunta suka fito. Suna ƙoƙarin shiga sashen motar Fadeel da kowa ke kira babban Yaya a gidan ta shigo. Ganin yanda suka nufi sashen Auta kamar hankali a tashe ya sashi fitowa da sauri shima yabi bayansu ko rufe motar ma bai gama yi ba. Matarsa data fito daga flat ɗinsu domin tarbarsa ganin inda ya nufa ta ɓata fuska da binsa da harara, har zata juya a fusace sai kuma ta fasa itama ta nufi sashen AA ɗin dan son ganin mi mijin nata kema gudun zuwa yi sashen ƙanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login