Showing 177001 words to 180000 words out of 221978 words
Chapter 60 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
ya ɗauka ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kawai ya zuba mata manyan fararen idanunsa dake cikin gilashi. Mus-mus take da baki alamar ƙunƙuni ga hawaye na zuba, shi sai abin ma ya so bashi dariya amma ya dake. Indai rashin kunya ce ai yasan ta iya fiye da kowa, kura ce kawai tayi lafiya. Harara ta zuba masa da suka haɗa ido. Sai ya ɗan waro idanunsa waje da faɗin, “Ni kike ma harara?”.
“Anyi ɗin, kuma ALLAH zai saka min karya nin da kai”.
“Tunda bakinki bai iya daina tsiwa yanzu ma na fara karyaki ai. Ni tsoro ma nake kada ki haifa min fitunannin yara irinki”.
“ALLAH ya kiyaye, ka nema mai haifa maka ƴaƴanka can. Kuma duk zaluncin da kaimin sai na haɗaka da Oum”.
“Maza kar ɗan ƙuda ya rigaki”.
Ya faɗa yana miƙewa a wajen. Can ya koma saman office chair ɗinsa. Hankalinsa kwance ya fara aikinsa. Sai kawai Maanal ta samu kanta da dakin hawayen da take faman riƙewa suka zubo. Hannu tasa ta share su, sannan ta miƙe tana ɗingishi ta nufo inda yake. Daga ɗan nesa da shi kaɗan ta tsaya, muryarta na ɗan rawa ta ce, “Dan ALLAH ka buɗe min ƙofa na tafi, kada mutane su fara min kallon wani abu a companyn nan. Bana son abinda zai zubar min da mutuncina.”
Tsohon sakanni bai kulata ba, bai kuma tanka mata ba. Sai da ya mula dan kansa batare da ya kalletan ba dai ya tura mata wasu takardu. Hankalinsa ya sake maidawa a computer ɗin saman desk ɗin cike da dakewa ya ce, “Ki zauna kiyi signing a cikinsu”.
“Na minene?”.
“Cinikin kanki”.
Baki ta tura, cikin ƙunƙuni ta ce, “Kaina yafi ƙarfin ciniki ai”.
Bai kulata ba, sai kan waya daya ɗauka ya kai kunnesa. Ana ɗagawa ya furta, “Turo min Kayende”. Daga haka ya ajiye kan wayar. Sai a lokacin Maanal takai zaune a ɗaya daga cikin visitor chairs ɗin gaban desk ɗin nashi. Dai-dai nan akai knocking, ya bada iznin shigowa. A kaikaice Maanal ta hararesa, sai kuma ta ɗauka ɗaya daga cikin tarin ƙyawawan pens ɗinsa dake cikin wani kyakkyawan abu. Tana jin wanda ya shigo ɗin yana gaishesa, a taƙaice ya amsa masa, sai kuma cikin bada umarni yace masa ya kwashe wannan kayan. Cike da girmamawa ya amsa masa, ya koma wajen kayan ya fara tattarewa. Ita dai takardun take dubawa, dan tafi son sanin na minene kafin ta sanya hannun. Amma sai bata fahimci wani abun kirki ba yanda take so. Ficewar kayende ya bata damar faɗin, “Ni ban fahimci komai anan ba”.
Ƙin tanka mata yay duk da sarai ya jita, harta fidda rai ma sai kuma a daƙile ya ce, “Zaki tsaya neman sanin na minene ɗin ne ko zakiyi abinda nace”.
Baki ta tura gaba, sai kuma ta shiga ƙunƙuni tana saka hannun. Haka ta dinga binsu ɗaya bayan ɗaya tana signing. Fin mintina goma sannan ta kammala. Gabansa ta turasu batare da tayi magana ba. Shima baice komai ba ya ɗauka ya dudduba. Ganin tayi duk yanda yake buƙata sannan shima yay nasa saka hannun a inda duk ya dace ya sake tura mata.
“Ki kaisu office ɗin CMO. Wannan yaron kuma idan na sake ganinki da shi sai ya bar companyn nan”.
Cike da takaici take kallonsa, har tana jin ma ta kasa cewa komai. Sai da ƙyar ta iya furta, “Kana nufin korarsa zakai? Ka rabashi da hanyar cin abincinsa? To ai saika koremu tare ni da shi”.
Ƙin tanka mata yay, hakan yasa wani irin haushi da takaici suka sake baibayeta. Ta jima tsaye tana ƙoƙarin haɗa abinda zatace masa akai knocking ɗin ƙofar. Tamkar ya manta da ita a office ɗin ya bada izinin shigowa. Director Mustapha ne. Sai da ya ƙare mata kallo sannan ya ƙarasa shigowa ciki. Batako gaida shi ba ta fice fuuuu. Sai ya samu kansa da binta da kallo. Dukan desk AA yay da ƙarfi, a ɗan rikice Director Mustapha ya ce, “I'm sorry Sir”. Yana nutsuwa. Sai kuma ya ƙaraso ya gaishesa. Bai amsa masa ba, sai ma wani banzan kallo da yake binsa da shi. Sosai Director Mustapha ya sake nutsuwa. A ƙasan ransa yana sake jin tabbacin lallai akwai wani abu tsakanin oga da yarinyar nan kam. A zahiri kuwa sai ya sake neman afuwa kansa a ƙasa. Siririn tsaki AA yay da bashi izinin zama. Haƙurin dai ya sake basa sannan ya kai zaunen.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣7️⃣
______________
........Maanal bata wani daɗe a office ɗin CMO ba ya sallameta. Dan nan ɗin ma cike-ciken wasu takardun tayi yay mata ƴan tambayoyi ya sallameta. Koda ta koma nasu Office ɗin bata kula kowa ba ta zauna. Tana lura da da kallon ƙurillar da su Deeni ke mata. A haka lokacin salla yayi. Saita samu kanta da saurin fita kafin ma Yaqub yace zasu fita tare. Ana idar da sallar ma wuff ta koma office, badan tsoron AA ba, sai don bata son zama silar yankewar hanyar cin abincin kowa. Sai dai bata daɗe da shigowa ba Yaqub ɗin ya shigo. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke da faɗin, “Oh ashe kin dawo, ina can ina nemanki. Kina lafiya kuwa yau?”.
“Lafiya Lau nake Yaqub, wannan aikin da Director Steven ya sakani tun last week nake son kammalawa.”
Cikin gamsuwa ya ce, “Okay haka nada ƙyau. Bari naje kitchen tunda ke nasan ba zuwa kike ba”.
Kanta kawai ta jinjina masa. Ya fice ita kuma ta cigaba da aikinta. Sai dai a ƙasan ranta tausayi Yaqub ke bata. Sam bai da damuwa. Ga nutsuwa da rashin son hayaniya. Gashi ya matuƙar sanin aikinsa dan ita kanta tana ƙaruwa sosai da mu'amularsu ta fanin aikin. Amma ga wannan ɗan balaja'un na neman sanya ma alaƙar tasu ido da ƙahon zuƙa.....
___________★
“Amma Baba sai kace ƴar nan bakune kuka haifeta ba. Kuna da damar amsheta fa a hannun Alhaji Usman Chalawa. Amma kun zauna yana muku gadara. Nasan mutumin nan tamkar yunwar cikina, ɗan zafin kai ne, dan na tabbatar shine ya sakasu yi muku wannan rashin mutuncin ma har mahaifiyar tasu”.
Cikin rawar baki Kawu Aƙilu ya shiga bama Sen... Bukar haƙuri. Tsabar zubar da mutunci harda duƙawa yana sake maimaita masa ya kwantar da hankalinsa, in dai Maanal ce fa kamar ya samu. Dan bata da miji sai shi. Hakama gwaggo hakuri take bashi. Babu ne dai baice komai ba, dan shi hankalinsa ma baya a kansu sam. Baima san mi suke tattaunawar ba. Cikin ƙara tsimewa Sen.. Bukar ya ce, “Shike nan zan ƙara muku lokaci, idan kuma kuɗin auren dana baku ne yay kaɗan zan ƙara ninkasu. Dan gaskiya ina buƙatar auren yarinyar nan kusa kaɗan. Saboda da ita nake son shiga gidan gwamnati dazan fito takarar gwamnan jihar mu ne”.
Wani irin washe baki Kawu Aƙilu yayi shida gwaggo. Cikin sake gurfana ya ce, “Kayyasa Masha ALLAH, muna murna, muna kuma fatan alkairi. Batun wagga ɗiya kuwa Manalu karma komai ya dameka. Ka bamu kwana kaɗan zamu gama da komai da komai”.
Gwaggo ma cike da zumuɗi ta shiga jera masa addu'a tana zungurin Babu dake gefenta. Amma ko gezau yayi matuƙar nisa a tunani. Miƙewa Sen.. Bukar yay yanama yaronsa Rabilu umarnin basu jakar gabansa. Sheƙeƙe ya kallesu yana faɗin, “Ga ƙarin kuɗi nan za'a kaiku airport yanzu domin komawa gida. Nan da sati uku zuwa huɗu naji daddaɗan labari. Dan zan yi tafiya ne ma zuwa kasar waje shiyyasa nace sati huɗun. Kafin dai na dawo kun kammala da komai da komai yazama matata kawai nake jira”.
Nan ma sake gurfana sukai suna jera godiya da tabbatar masa an gama. Abin nasu ma har ya so bama Rabilu mamaki da takaici, irin wannan zubar da mutunci haka, amma dai ya gimtse. Bayan fitar ogan nasa yace su tashi dan shine zai kaisu airport ɗin, tunda dama dai shine ya ɗakkosu daga gida, yanzu ma shine zai maida su...
Wannan kaɗan ne daga Sen... Bukar in har yana neman aure. Sam baya ƙyashin kashe kuɗi ga dangin yarinya da ita kanta yarinyar. Maƙalau gwaggo ta kama jaka ta matse a hijjabinta. Kawu Aƙilu naso ta bashi amma ta hana ta haɗe gabas da yamma. Shi ko Babu sai da ma suka taɓashi ya dawo hankalinsa. Haka kuma ya miƙe ya bisu kawai kamar wanda baya gane komai......
____________★
A makare yanzu kam ta fito sallar la'asar saboda meeting da sukayi da Director Mustapha gaba ɗayansu Junior Watch Designers na department ɗinsu akan wani ƙaramin project. Kasancewarta ita kaɗai mace sai da ta bari duk suka gama fitowa sannan ta fito daga conference room ɗin. Gudu-gudu sauri-sauri ta isa massallacin, da sauri ta nufi wajen alwala. Kafin ta kammala har an kai raka'a ta farko. Cikin hanzari ta shiga naɗa veil ɗin abayarta da iska ke neman kwashewa. Kamar zatai kuka ta samu da ƙyar dai ya zauna. Juyowar da zatai dan barin wajen ta hango AA dake ƙoƙarin fitowa a mota alamar daga wani waje yake. Yanda ya zuboma wajen ido ya bata tabbacin ya jima yana kallonta. Ɗauke idanunta tai kamar bata ganshi ba tai saurin faɗawa cikin massallacin.
Koda aka idar kasancewar bata samu sallar duka ba tana a cikin ƴan karshen fitowa. Kusan duk an wuce kitchen, dan haka ta nufi komawa ciki ita dai kam. Dan har yanzu zuciyarta bata ji zata taɓa cin abincin Companyn ba da ake dafawa.
“Sister Maanal”.
Muryar AS ta ratsa kunnenta daga bayanta kaɗan. Juyowa tayi, sai dai bata amsa masa ba har ya ƙaraso. Fuskarsa da murmushi ya furta, “Barka da rana, dama boss ne yace a kiraki”.
Idanu ta zuba masa sosai. Sai dai fuskarta harta canja. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ganin mutane a wajen, ta jinjina masa kai kawai. Shima bai sake cewa komai ba yay gaba a ransa yana sake jinjina miskilancin ta. Ganin sun nufi hanyar gate kamar zata tsaya sai kuma ta hango motar AA ɗin a can waje gefen titi. Mita take a zuciyarta kiran mi yake mata kuma a waje, itafa idan yace zai cigaba da takurama rayuwarta ALLAH zata fiddo masa kalarta, ya bar ganin tana wannan sauke kan bata son kowa a ma'aikatansa ya fahimci tana da wata alaƙa ta ɓoye ko zahiri ne da shi shiyyasa. Da wannan ƙunƙunin ta ƙaraso. Sai dai ta dogare a waje, yayinda shi kuma yaƙi sauke gilashin motar. Sai da AS ya ɗan masa knocking sannan, a hakan ma bai buɗe kai tsaye ba sai da yaja wasu sakanni. Saukar gilashin ya bata damar ganinsa zaune a mazaunin driver dan gilashin tinted ne. Hannu kawai ya ɗagama AS alamar yaje. Cike da girmamawa ya ce, “Okay sir a dawo lafiya.” daga haka yabar wajen ya koma cikin Company. Shiru ita da shi babu wanda ya tanka, amma shi kallonta yake ta cikin mirror ɗin gefensa. Yanda take ta faman ɓata fuska da motsa lips alamar ƙunƙuni take masa ya sashi lumshe oily ayes ɗinsa yana ɗan sakin miskilin murmushin da iya lips ɗin kawai ya motsa. Karaf kuwa sai a idon Maanal data matso inda yake a kufule. Gimtse fuskar yayi, itama ta sake gimtse tatan tana harararsa. Cike da takaicin murmushi data gani yanayi tabbacin da ita yake tunda kallonta ta kamashi yana yi, “Gani”.
“Na ganki ai”.
Ya faɗa cikin halin ko'in kula idonsa a kanta. Janye nata idanun tai daga kansa tana jin kamar ta balbalesa da masifa. Amma dai ta daure kodan securitys da zasu iya hangosu. Ita kuma bata buƙatar hakan. Kamar ya karanci abinda take tattaunawa da zuciyar tata ya miƙa hannu ya buɗe murfin side ɗin mai zaman banza tare da faɗin, “Get in”. Sosai yanzu kam ta zuba masa idanu babu ko ɗar, shima ya ko zuba mata nasa cikin tsakkiyar natan. Jitai tsigar jikinta na tashi amma tai jarumtar riƙe kanta da ƙyar. A dake ta ce, “Ni aiki nazo ba yawon banza ba”.
“Niko kinga yawon banzan na fito”. Ya bata amsa a daƙile. Kafin ta samu damar bashi amsa ya cigaba da faɗin, “Kina ɓatan lokaci, idan kuma kika bari na fito ALLAH da kaina zan ɗaukeki na sakaki”.
Tasan zai iya fiye ma da abinda ya faɗa. Wanda ya iya keta mata haddi a cikin gidansu me kuma ya rage. Garama ta shiga tunkan ya kunyata ta a bainar nasi. Sai dai bata shiga kai tsayen ba, sai da ta gama masa ƙunƙuni da hararar motar sannan ta zagaya ta shiga. Ƙin rufe murfin tayi, dan haka ya ranƙwafo tare da kai hannu zai rufo. Hakan ya basu matsanancin kusancin da har take jin kamar zai rungumota ne. Ga ƙamshin turarensa ya wani buɗeta tamkar yanzunne yake fesawa. Samun kanta tai da rawar jiki, sai kuma a zabure takai hannu ta jawo ƙofar ta rufe bam kafin shi yayi. Shiru yay yana kallon ƙofar batare daya janye jikinsa ba. Jin numfashinta kamar yana fisga da ƙarfi, ga sassanyan ƙamshin khumran data saka da wanda tai turaren kayanta na wani saukar masa da kasala. A hankali ya maida idanunsa kanta, ya zubama ƙyaƙyƙyawar cute fuskarta manyan idanunsa. Idanunta a rumtse suke, hakama lips ɗinta sai ɗan motsi yake, ga fuska ta takure kamar zata saki kuka. Idanunsa dake kallon lips ɗin ya janye cikin slow motion yana mai haɗiyar wani busashen yawu daya tokare masa maƙoshi. Kamar wanda aka kwaɗama guduma a ka ya janyo belt ɗin gefenta kawai yaja jikinsa baya ya maƙala ta gefen tsakkiyarsu. Da mugun ƙarfi tako saki numfashinta har sai da ya sake kallonta, sai kuma ya girgiza kansa a hankali yana mai janye idanun tare da lumshesu, sake buɗesu yay a saman titi yana kunna motar. A hankali taji sun fara tafiya, dan haka ta sake sakin sauran numfashin data riƙe tare da buɗe idanunta. Ƙin kallon sashen da yake tai, sai ma ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika mata idanu take yi. Dan haka kawai yanayin nasu ya tuna mata wani abu. Shiru motar ta ɗauka sai sanyin ac dake ratsasu, dan ko rediyo bai kunna ba. Sai wayarsa da aketa faman kira tana haske da ɗan motsi kawai, bai kuma kula ba kamar ma bai ji ana jera masa kiraye-kirayen ba. Tafiya ba wata mai nisa ba duk da a hankali yake tafiyar suka iso wani katafaren wajen Saloon mai shegen ƙyau. Kallon wajen kawai Maanal take yi, yayinda shi kuma ya samu waje yay parking. Sai da ya kashe motar gaba ɗaya sannan ya juyo yana kallonta. Muryar san nan ƙasa-ƙasa kamar abin dole ya furta, “Muje”.
Itama kallonsa tai a karo na farko ta ce, “Ina ɗin?”.
“Ina kikaga mun zo?”.
Ya faɗa cikin tsatstsareta da kaifafan idanunsa. Fuska ta ɓata sosai, bakinta a sama ta ce, “Ni mizanyi anan wajen? Haka kawai ka ɗakkoni daga wajen aiki ka kawoni nan......” sai kuma ta cigaba da magana cikin ƙunƙunin da baya ji.
“Kar dai ki zagen mara kunya kawai”.
“Toni ka maida ni inda ka ɗakkoni mana. Na gaya maka ina buƙatar zuwa nan wajen ne. Haka kawai dan neman mutum dai da faɗa.....”
“Ai ba sai kina buƙata ba, tunda ni ina buƙata ya wadatar. Ragguwan banza kita yawo da gashi a tsefe kina buɗema mutane suna gani. Oya fita kona ɗaukeki da kaina har ciki wlhy”.
Sosai idanunta suka kawo hawaye, dan har yanzu Maanal ba ƙaunar kitso take ba, ta gwammace a wanke a gyara mata kawai. Sai gashi ta marairaice fuska kamar ba ita ke shirin masa tsiwa ba. Idanunsa ya kauda daga kallonta yama buɗe motar ya fita alamar bazai ma saurareta ba. Sake tashi hankalinta yay, tana tunanin fita ta gudu taji an buɗe side ɗin da take. Da sauri ta dubesa, sai ga hawayen da take riƙewar na silmiyowa da gudu. Baki ya taɓe, tare da fara jan hannun jacket suit ɗinsa sama. Hakan na nufin shirin ɗaukar tata yake kenan da gaske. Ai da sauri ta fito tana harararsa da share hawayen dake cigaba da sakko mata. Murmushi yay abinsa cike da mugunta yay ma bayanta ƙaramin gwalo, sai kuma ya maida fuskarsa ya gimtse ya rufe murfin data bar masa a buɗe kamar baiyi komai ba. Haka ya tasata gaba cikin wajen tana shartar hawaye. Dai-dai nan Nurry da ƙawarta ke fitowa a kusa da wajen saloon ɗin daya kasance bakery. Cak tai wani irin tsayawa zuciyarta na bugawa da sauri, tuni ta