Showing 66001 words to 69000 words out of 221978 words

Chapter 23 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

wata hanya ce ta samun haɗin kan yaran nan ne da muketa fata tuntuni. Ni Huznah ta biyani ALLAH yay mata albarka”.
“Humm Asia! Shin baƙya tunanin akwai wani dalili?”.
“Haba Daddynsu wane dalili kuma? Dan ALLAH kada ka ɓatama yarinya ƙyaƙyawar niyyarta mana”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, acan ƙasan ransa yana sake jin matuƙar ƙaunarta da jin alfahari da ita. Ita ɗin ta dabance a duniyarsa. Shi yasan da sauran ne cikin ƴaƴan Asia wani yace zai je gidansu sai anyi bala'i kuma ace wani daliline zai kaisu. Amma ita gashi maimakon tai zaton sharri kai tsaye saboda komai a bayyane yake sai tayi na alkairi. Jawota kawai yay jikinsa ya rungume. Murya a raunane ya ce, “Asia ALLAH yay miki albarka kinji. Tabbas UBANGIJI yamin babbar ni'ima da samunki”.
“Nima haka Daddyn Hameed, kai ɗin babbar ni'ima ce a gareni daga cikin ni'imomin UBANGIJI na. Bani da abin faɗa sai cigaba da godiya a garesa”.
Sosai ya saki murmushi mai ƙayatarwa, sai kuma ya sake kai hannu ya rungumota tare da ƙoƙarin haɗe bakinsu. Da sauri ta kauce tana dariya, sai ma ta zare jikinta gaba ɗaya ta miƙe daga kusa da shi. Fuska ya ɓata da mata nunin ta dawo amma ta maƙe masa kafaɗa.
“Shike nan ni kike ma rowa ko?”.
Murmushi ta masa kawai.
Ya ɗan ƙara jinjina kansa da nufar ƙofa yana faɗin, “Zan rama”. Ya fice. Nan ma murmushin kawai tayi, sai da taji ficewarsa daga sashin gaba ɗaya ta koma jagwab a saman gadonta zuciyarta na wani irin harbawa. _(Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ƴar uwarta Shahidah tai sati ɗaya)_ kalamansa suka shiga dawo mata cikin kunne da amsa kuwwa. A bayyane cikin dafe kanta ta ce, “Ya ilahil'alamin Basariyya mi kike shirya min kuma? Ni nasan dole wannan zancen akwai wata a ƙasa”. Rashin mai bata amsa yaa sata yin shiru ta cigaba da zancen zuci. Ta jima a haka kafin hankalinta ya dawo jikinta ta miƙe ta shiga kitchen haɗama su Waleed abincin breakfast dana tafiya makaranta. Tana aikin tana tunani nan ma harta kammala. Tana cikin haɗa musu suka shigo sanye da uniform ɗinsu. Duk gaisheta sukayi suna mai rungumeta, tai musu murmushi tana amsawa. “Har an shirya ƴan makaranta?”.
Kawunansu duk suka shiga ɗaga mata. Sai kuma cike da shagwaɓa irin ta autoci Waleed ya ce, “Ammie mikika dafa min?”.
“Oh tama dafa maka bata dafa mana ba, kuji min ɗan iya”. Cewar Hameed yana hararsa da kai dankali bakinsa. Murmushi Ammie tai da faɗin, “Ni dai kunga kuyi ku wuce bana son surutu yau ɗin nan. Kowa ya duba abinda yake so shi aka dafa masa”.
Murna suka shiga yi, sai kuma suka ɗauki wanda zasu ci suka koma work table dake kitchen ɗin kowa yaja kujera sukai zaman ci. Ammie kuwa ta fara ɗan wawwanke kwanikan data ɓata dan bata son taga ambar kaya da datti, duk da tasan yanzu mai aikinta zata zo ta fara aikin ta gwammace ta tsaftace waɗan nan ɗin kafin ta iso. Tana kammalawa suma suka kammala. Sallama sukai mata kowa ya ɗauka lunch box ɗinsa suka fice. Sai kuma six dan makarantarsu tana tare da islamiyya ne...


Koda ta koma ɗaki saita gagara shiga wankan datai niyya, zama tai ta ɗauki waya ta shiga kiran Nene. Ba'a wani ɗauki tsawon lokaci ba Nenen ta amsa kuwa. Sai dai suka gaisa da tambayar juna gida kafin Ammie ta ce, “Nene yau zan sameki a gida?”.
Daga can Nene ta ce, “Eh bazanje ko'ina ba. Dama nina naso kiran naki ai sai kika kirani, zaki shigo ne?”.
“Eh Nene indai ya bari zuwa anjima kaɗan zan shigo”.
“To shike nan sai kinzo ɗin ina saurarenki”.
Daga haka sukai sallama kowa ta yanke.....


★ Sai kusan sha biyu Ammie ta samu damar barin gidan. Dan da ƙyar Daddy ya barta dan ma tace masa kitso zataje. Da yake yasan tana zuwa kitson kuma bai kawo komai a ransa ba. Shi irin mutanen nan ne da sam basa son yawan fitar iyalansu, sunfi buƙatar ko yaushe kina gida, shiyyasa a cikinsu babu mai fita aiki ko wani business. Ammien ce ma taga bazata iya wannan kashe kan ba komai sai abinda namiji ya baka tuni ta fara kasuwancinta a gidan Nene. Kuma Alhamdullah komai yana tafiya dai-dai.
Gidan Nene gida ne a matsayin family house. Dan kuwa ita da duka matan ƴaƴanta suna a cikinsa. ALLAH yayima mijinta rasuwa tuni, ita ta cigaba da gwagwarmaya da yaran har suka girma. Yanda ta horesu yasa duk suna da sana'o'in su, dan babu mai zaman banza. Badai kuɗi garesu ba amma ci da sha gwargwado da sutura irin ta gidan mai rufin asiri sun wuce da wannan kam. Sashen Babban ɗan Nenen ta fara shiga, matansa biyu, yaso auren Ammie a baya matarsa nata zuba rashin mutunci akan hakan sai ALLAH ma bai ƙaddara ba, to ashe kishiyar dai na bibiyarta, dan bayan Ammien tayi aure ya auro budurwa gal a leda yanzu haka haihuwarta uku a gidan itama. Wannan dalilin ne yasa sama-sama suke da Ammien. Koda ta shiga a kitchen ta samu Maman Salima kamar yanda suke kiranta, ta wani zubama Ammien ido zuciyarta na bugawa, tuni murmushin fuskarta kuma ta ɓace. A yanzu kam ba kishin Ammie ne ke damunta ba hassada ce. Ko'a jikin Ammie ta gaisheta da tambayarta yaranta. Daga kitchen ɗin ta amsa a daƙile, sai dai idonta na'akan suturar jikin Ammie.
“A'a Aunty Asiya ce a gidan namu?”.
Amarya dake leƙowa daga falonta ta faɗa. Murmushi Ammie tai mata da faɗin, “Aiko nice Amarya”.
“To sannu da zuwa Bismillah ki shigo”.
Babu musu Ammie ta shiga, falon ƙal an gyara shi sai ƙamshin turaren wuta yake kamar bamai ƙananun yara ba. Gashi da gani tana fama da laulayin wani cikin ne ma. Cike da girmamawa ta gaida Ammie kafin ta fita sai gata da ruwa.
Ammie ta ce, “Amarya ai da baki wahala ba ma. Ina yaran nawa ko duk an wuce makaranta?”.
“Duk sun wuce shiyyasa ai muka samu lafiya Aunty, sai Ameen kawai yana barci ne”.
“A'a ai shima ko ya kamata a sakashi makarantar tunda naji bakinsa akwai surutu”.
cikin dariya Amarya ta ce, “Sosai kuwa Aunty”.
Bayan Ammie ta sha ruwan ta fito, amarya biye da ita har ɗayan sashen. Nan kam mace ɗaya ce, itama ta amshi Ammie da girmamawa da mutuntawa, bayan sun gaisa ta fito ta shiga wajen sauran suma su biyu. Daga haka ta shiga wajen Nene. A falonta ta sameta zaune ta baje kaya tanata lissafi. Sai wata dake gefenta tana tayata. Da mamaki Ammie ta furta, “A'a Saratu yaushe a gari? Nene shine baki sanar min munada da baƙuwa ba?”.
Murmushi wadda aka kira Saratun tayi, yayinda Nene ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Zuwan nata ne dama ya sani nemanki, tunda ita dai fitinar gidanta bata ƙarewa”.
“Tofa wani abunne kuma ya faru Nene?”.
“Humm Asiya ke dai cire mayafi a kawo miki abinci, ga waina can nasa tun ɗazun aka sayo miki gidan Hajiyayye ALLAH yasa ma bata huce ba. Saratu ɗakko mata”.
Kasancewar Ammie na son wainar sosai ta zauna taci, sai da ta ƙoshi sannan suka fara maganar Saratun. Sosai ran Ammie ya ɓaci, tace bako zata bar gidan ba har sai sauran ƴan uwanta sun dawo ai zama akan al'amarin Saratun, wannan karon dole su ɗauki mataki akan mijin nan nata mara mutunci, dan bazasu yarda da auren duka ba. Bayan sun gama tattauna wannan suka koma batun nasu gidan, ita kanta Nene ta jinjina batun zuwan Huznah Abuja. Amma sai ta kwantarma Ammie da hankali akan ta barta taje ɗin, amma sun kira Shahidah sun gaya mata komai, sun kuma mata gargaɗin ta sanya ido sosai. Ammie dai bata bar gidan nene ba sai bayan magriba da sauran ƴaƴan Nene huɗu ringis suka dawo kasuwa suka tattauna batun Saratun. Da zata tafi sai ta wuce da Saratu can gidanta akan zata huta kwana biyu.


_________★


Washe gari ƴan Dubai suka wuce domin haɗo kayan lefe dana shagalin biki harma da kayan ɗakin amarya. Itama Huznah ta wuce Abuja, sai dai abinda ya sake tabbatar ma da Ammie akwai wata a ƙasa ko sallama Huznah batai mata ba. Sai bayan ta tafine uwar ta shigo tana cema Ammien tayi hakuri wai driver ne ya azalzali Huznah ɗin shiyyasa bata shigo ba. Murmushi kawai Ammie tai ta ce, “Babu komai ai ALLAH ya tsare hanya ya kaisu lafiya”. Daga haka bata sake tofa komai ba dole Hajiya Basariyya ɗin ta fito tana taɓe baki, dan taso ne Ammie ta biye mata su ɗan yi gulmar ƴan tafiya Dubai. Itama Ammien kuma ta ganota shiyyasa ta mata haka...


Maanal bata san wainar da ake toyawa ba. Da safe dai sanda Shahidah zata sauketa ne a office take gaya mata zuwan Huznah ɗin. Dan yanzu itace ke kaita, wani lokacin ta dawo a taxi. Tun randa AA Darma yay mata wannan gargaɗin ta so yima RK magana, sai kuma wani ikon ALLAH ma a daren ranar RK ɗin yay tafiyar gaggawa har yanzu bai dawo ba. Dan itama a waya ya kirata ya sanar mata. Busy kuma da yayi sosai yasa ba koyaushe suke waya ba sai ya samu lokaci. Amma ya tabbatar mata bazai wuce kwanaki biyar ba. Yau kuma kwanansa huɗu kenan gobe idan ALLAH ya kaimu take saka ran dawowarsa. Yazeed dai ne da yake yana garin yanzu kullum da dare sai yazo gidan Shahidah ɗin, dan da farko yaso ya mata fushi akan batun aiki wai bata sanar masa ba sai Daddy ya gaya masa, haƙuri kawai ta bashi da nuna masa ai Daddy ɗin dan ya isa da su ne su duka shiyyasa. Ya dai ƙyaleta kawai, amma a ransa ya gama ƙudirar wannan aikin sai ta barsa duk da yanada planing ɗin anan Abuja ɗin zata zauna ita ko anyi bikin su.
A gajiye ta fito daga office ɗinta zuwa office ɗin Designer Director ɗin dake kula da aikin nata, har yanzu dai suna akan project ɗin nan daya haye mata. Bayan tayi knocking aka bata izinin shiga. Ganin yana haɗa kaya alamar zai tashi ne a sanyaye tace, “Director badai zaka tashi bane ba?”.
Kallonta yay fuskarsa da murmushi, dan yanzu kam ta fara sabawa da su. Yanda kuma take girmamasu da bawa kowa hakkinsa da kame kanta yasa su jin ƙaunarta a rayukansu.
“Lallai baƙya kallon agogo, bakiji yanda company yay tsit ba kusan duk an wuce ai”.
Agogon ta kalla kafin ta sake dubansa, dan tabbas magrib tama kusa. “Ayya ALLAH ban lura ba. Dan ALLAH ka samun hannu a document ɗin nan, so nake yanzu na miƙasa office ɗin CEO idan ALLAH ya taimakeni da safe sai ya duba shi da wuri kafin zaman meeting”.
“Wayyo baƙya jin tausayina ALLAH, kinji bayana kuwa ga Madam nata kira na yau birthday ɗinta. Amma kawo nayi sauri”.
Godiya ta masa tare da matsawa ta ajiye masa file ɗin, tana daga tsaye ya shiga dubawa. Ɗagowa yay ya dubeta cike da tsokana ya ce, “Anya ba kwanan nan zan baki kujerar nan ba Manaal Giro? Ke ɗin ƙuruwace fa. Ɗan murmushi kawai tai masa kanta a ƙasa dan iyakarta da su kenan, shiyyasa duk da yanda take girmamasun wasu ke mata kallon mai girman kai da faɗin rai. Wasu a cikinsu duk sun ƙyasa, sai dai kamewarta na zame musu barazana, ga kuma RK da kowa ya tabbatar budurwarsa ce a companyn yanzu duk da kuwa yau ne take cika kwanta na takwas a Companyn. Bayan ya saka mata hannun ta karɓa tana masa godiya. Sallama ta masa ta fice, haka ya bita da kallo zuciyarsa na zallo. Tun ranar farko da sukama Maanal interview yarinyar tai masifar shiga masa rai. Abinda ya faru tsakaninta da Boss yaso taka masa birki, amma daga baya sai yaga kuma komai bai sake faruwa ba, sai sabon soyayyarta a zuciyarsa ya dawo fil, sai dai kuma Maanal babu sakin fuska........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖3️⃣1️⃣




.......Ita kam koda takai file office ɗin Boss ta ajema AS office ɗinsa ta koma ta cigaba da aiki, dan akwai abinda take son kammalawa kafin ta wuce gida. Kiran sallar magriba ya sata ƙarasawa sauri-sauri sannan ta tashi tayo alwala ta haɗa kayanta ta kashe komai ta fito dan su Yaqub tuni duk sun wuce sai ita kaɗai. Shiru babu motsin kowa duk an wuce. Sai offices ɗai-ɗaine ƴan over work irinta koma wanda suka fita ke'a buɗe. Ƙananun ma'aikata ma ta wuce kusan mutane huɗu basu wuce ba, koda ta fito harabar companyn ma motoci biyar kawai ta gani sai mashin biyu alamar na wanda suka ragene. Idanunta suka sauka akan motar boss. Janyewa tai tana taɓe baki, shi dama ai yafi kowa iya over work, dan kullum shine ƙarshen barin office. Masallaci ta nufa domin gabatar da magriba. Bayan an idar koda ta fito bata koma ciki ba, hanyar gate ta nufa abinta a ƙafa. Street ɗin shiru babu yawaitar mutane a ƙafa sai motoci, sai dai ko'ina akwai haske kamar kana wata ƙasa ba Nigeria ba. Taxi nada wahalar samu a wajen kasancewar duk manyan ma'aikatu ne ata wajen, sai gidajen cin abinci da suma ba laifi suke da yawa ta wajen da shopping malls guda biyu dake can farkon shigowa. Tsoron kar dare ya sake mata ya sata cigaba da tafiya a ƙafa tana jin nadamar kaiwa haka bata tafi gida ba, har Shahidah cewa tai zata aiko a ɗauketa idan ta gama tunda tace ita karta biyo ɗaukarta yau tana da aiki amma tace mata a'a zata hau taxi. Tayo tafiya babu laifi zuciyarta ta fara karaya, dan ƙafafunta sun fara gajiya. Mamakine ya kamata ganin ƴammata tsaitsaye kamar masu jira azo ɗaukarsu, amma abinda zai baka mamaki suna da yawa duk da kowanne yana tsaye ne shi kaɗai ko su biyu. Cigaba tai da tafiyarta dai tana ɗan kallonsu sai taji ana horn, da sauri duk hankalin ƴammatan ya koma wajen motar, wasu ma duk sun nufi motar ne, sai dai kuma mai motar bai tsaya ba ya cigaba da bin bayan Maanal ne ana kuma horn ɗin dai. Da sauri ta ɗan ja da baya sakamakon shan gabanta da akai da motar, cikin wani irin ɓacin rai ta ɗago dai-dai mai motar na sauke glass ɗinsa. Babban mutum ne da a shekaru ma zai iya haihuwar su Shahidah bama ita ba, yana daga baya kwance driver ɗinsa a gaba, cikin tsareta da ido ya sakar mata murmushi. Ɗauke kanta tai da sauri ta raɓa ta wuce wani irin ɓacin rai na mamayeta. Jin an ƙara biyo bayanta da mota ana mata horn again ta tsaya cak, cikin matuƙar fusata da harzuƙa ta ɗago dan ta gama shirya yima tsohon banzar nan zagin ƙare dangi, amma sai kawai taga motar boss ba wancan bane. Kafin ta iya haɗiye abinda ke bakinta AS ya fito daga gaba, kai tsaye inda take ya iso, furkarsa da murmushi ya furta, “Sister Maanal bismillah ki shiga”. Yay maganar yana miƙa mata hannu da nufin amsar kayan hannunta. Kai ta girgiza masa tare da janye hannun nata tana faɗin, “Karka damu na gode”.
“Idan shi bai dace ba, inaga ni kamar zan dace tunda dama ni na fara tayawa”. A bazata taji muryar tsohon nan cikin kunnenta daga bayanta. Jitai gaba ɗaya kamar ta daburce, ga zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri har numfashinta na neman fara yin sama-sama. Babu alamar wasa ko ragi a tare da ita ta juya ga tsohon nan, hannu ta ɗaga da nufin nunashi a hankali taji saukar wani tattausan hannu ya riƙe mata yatsu, batare da cewa komai ba yaja hannun nata. Ƙoƙarin fisgewa ta fara sai dai bai bata damar hakan ba har ya iso da ita jikin mota. Sai lokacin ta iya zuba masa manyan idanunta da suka kaɗa, shima kallon nata yake cikin ido. Kusan minti ɗaya suna kallon juna kafin ya zare kayan hannunta tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Get in”.
Rasama mi zata ce masa tayi, dan sam babu ko ɗigon wargi a fuskarsa. Yayi masifar yin kicin-kicin da ita kamar zatai aman wuta. Bai kuma sake cemata komai ba ya zagaya ɗaya side ɗin ya shiga mazauninsa ya ɗauke kai. Dattijon Alhajin nan dake tsaye ransa a matuƙar ɓace ya sake takowa inda Maanal take. Ai yana buɗe baki zaiyi magana kawai ta shige motar, shiko AS ya rufe mata murfin ruf tare da kallon Alhaji fuska da murmushi ya furta, “Bye bye grandpa”. Shima ya zagaya ya shige motar driver yaja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login