Showing 132001 words to 135000 words out of 221978 words

Chapter 45 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Tsaki Ammie taja da sake faɗin, “To uwar miye kika shigo kinama mutane kuka?”.
Fuska ta sake ƙwaɓewa da faɗin, “Ba Besty bane ba. Kawai dan Ya Abdull abokin Babban yaya ya bani chocolate na bashi yaƙi ya sha, shine kuma yake fushi da ni bayan ban masa laifin komai ba”.
Kasama magana Ammie tayi, ta zuba mata idanu kawai cikin wani yanayi. Bazata gaji da faɗa ba al'amarin yaran na bata tsoro, tun basu tafasa ba suna neman hanyar ƙonewa. Gefe ta ture tunanin batare da ta sake cewa komai akan batun ba ta juya zata fita. “Ki tashi kiyi wanka kizo ga abinci dan lokacin islamiyya ya kusa”.
Jitai kamar tace bazata je islamiyya ɗin ba. Amma tasan faɗar hakan na nufin Ammie yin tamaula da rayuwarta. Dan mace ce mai zafi sosai da sam bata ɗaukar wargi.......✍️




_To miya canja Ammie yanzu🤔?_



















✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖5️⃣7️⃣




______________




........Tamkar haɗin baki ta ɓangarorin biyu su duka sun tasa abinci gaba sun kasa ci. Yanda Ajwaad ke can a gaban Oum yana faman juya ɗan abincin daya zuba a plate anan ma haka ne ga Maanal. Oum dai ta ɗan lallashi Ajwaad, harta amshi spoon ɗin ta shiga bashi da kanta. Sai dai laumarsa batafi huɗu ba yace mata ya ƙoshi a shagwaɓe. Lallaɓashinsa ta shiga yi amma yace shi fa ya ƙoshi kamar ma zaiyi amai yake ji. Babu yanda ta iya dole ta barsa ya miƙe yana goge baki bayan ya saɓi bag ɗin islamiyyarsa. Dan su duka ukun sanye suke cikin uniform. Da kallo yayun nasa suka bisa da Mamy da itama take a falon, sai dai sam hankalinta bama a kansu yake ba. Sai dai babu wanda yayi magana har ya shiga store dake jikin kitchen ya fito, da alama akwai abinda ya ɗakko. Oum kawai ya kalla cikin sanyinsa ya furta, “Oum kimin addu'a sai na dawo”.
Fuskarta da murmushi ta ce, “ALLAH ya tsare Autana. ALLAH ya bada ilimi mai albarka. ALLAH ya daidaita tsakani kai da Besty”.
Idanunsa masu haske ya ɗan waro waje, sai kuma ya juya da sauri zai fice abinsa. Ai ko Fawzan ya kwashe da dariya. Yayinda Fadeel yay murmushi shi da Oum, Mamy dai kamar ma bata san sunayi ba. Harya saka ƙafarsa ɗaya waje Oum ta kira sunansa. Juyowa yay batare daya amsa ba.
“Mamy fa?”.
Oum ta faɗa babu wasa a fuskarta. Juyawa yay shima ya kalla Mamyn, sai kuma cikin sanyinsa da magana ƙasa-ƙasa ya furta, “Mamy sai na dawo”.
Karan farko ta ɗan juyo ta kallesu su duka, sai kuma ta ɗauke kai a taƙaice ta ce, “ALLAH ya bada sa'a”. Daga haka ta maida hankalinta a kallonta. Murmushi Oum tayi, zuciyarta na sake cika da so da ƙaunar kishiyar tata da takema kallon ƴar uwa. Yayinda Ajwaad ya fice abinsa yana amsawa...
Da ƙafa ya fito dan makarantar tasu babu nisa. Hakan yay dai-dai da fitowar su Shahidah Maanal biye da su. Bai tanka musu ba suma basu tanka masa ba. Sai da suka ɗan gota shi sannan ya lura da Maanal dake binsu a baya kamar bata so. Kallon juna sukayi kusan na sakan goma. Sai kuma kowanne ya ɗauke idonsa. Shi ya fara yin gaba like baima ganta ba. Itama sai tai nata gefen, sai dai duk da hakan a jere suke tafiya cikin tazara a tsakkiyarsu ta yanda ba lallai ka yarda tafiyar tasu ɗaya bace.
A aji ma koda suka zauna babu wanda ya kula wani. Sai da kusan minti uku sannan ya ciro kwalin drink da babban biscuit ya ajiye gabanta bayan ya buɗe kowanne. Batare da yayi magana ba ya ɗauka Al-qur'ani ya hau bitar karatu. Itama sharesa tayi taƙi ɗauka taci. Sai ma ta ɗakko littafin koyon larabci mai ɗauke da hotuna na zane-zane ta hau zana color. Cikin haushi ya ƙwace littafin ya sake tura mata biscuit ɗin da lemo.
“Bana ci”.
Ta faɗa a kumbure tana kalmashe ƴan hannayenta a ƙirji ta da juyar da kanta gefe. Cikin haushin shima ya ce, “K kin iyama mutane laifi ki fisu zuciya. ALLAH idan baki ɗauka kin ci ba sai na bar ajin nan.”
Tasan zai yi abinda yafi hakan. Dan haka bayan ta gama harare-harare ta ɗauka ta fara ci. Ajiyar zuciya ya saki a hankali yana sake maida hankalinsa ga Alkur'anin. Yanda taci da yawa ya sake tabbatar masa bata ci abinci ba. Yasan wannan halinta ne. In har tana fushi komi za'a bata in dai ba shine ya bataba bazata ci ba. Sauran wanda ta rage ɗin ta miƙa masa, babu musu ya amsa shima ya fara ci, wani ɗan guntu daya gutsira ya rage a hannunsa ta kamo hannun nasa ta saka a baki. Sai ya dungure mata kai. Dariya ta ƙyalkyale da shi. Hakan shima ya saka shi sakin dariyar. Kamar basu ba kuma sai suka warware. Bayan ya gama sukai bitar Alkur'anin tare kafin malami ya shigo musu.....


Koda aka tashi suka fito a jere Shahidah da Amaal kallonsu kawai suka tsaya yi, hakama Fawzan daya fito kallonsu yake yana dariyar shaƙiyanci. Maanal ce kawai ta tura baki gaba, shiko gogan bai kulashi ba yay gaba riƙe da bags ɗinsu. Koda suka iso gida su duka gidan su AA ɗin suka shiga. Tun a ƙofar falo Maanal ke ƙwala kiran Oum. Sai dai Oum na ɗaki bata amsa ba. Haka ta shigo ta nufi hanyar ɗakinta. Sai dai kafin ta shige sukaci karo da Mamy dake fitowa daga kitchen. Dakatawa Maanal ɗin tayi, tare da faɗin, “Mamy ina yini”.
Amsa mata Mamyn tayi da kulawa, tare da tambayarta makaranta. Maanal ta ce, “Alhamdullah” tana wucewa ɗakin Oum. Shima Ajwaad dake biye da Maanal ya gaishe da Mamyn, batare data kallesa ba ta amsa kawai tana wucewa abinta. Ɗan Binta yay da kallo, ganin kamar zata juyo sai ya ɗauke kai ya shige ɗakin Oum abinsa.
Oum na sallar magriba Maanal baje a gadonta. Ya ajiye bags ɗin nasu yana kallon Maanal ɗin. “Malama sallan fa?”.
Ya faɗa yana hararanta. Baki ta tura gaba da faɗin, “Zan huta ne na gaji. An jima ba sai nayi ba”.
Harara ya sake zuba mata, batare da yayi magana ba ya wuce toilet ɗin Oum, alwala ya ɗauro ya fito, gadon ya nufa, inda Maanal ta sake bajewa tana lumshe ido alamar barci ma take son yi. Duka hannayensa biyu yasa ya jawo ƙafafunta ƙiyyyy har ƙarshen gadon, ita kuma ta buga ihu tana kai masa duka da faɗin, “Ni ka barni ba nace zanyi ba anjima”.
Ko kulata baiyi ba ya direta a tsaye, cike da tsiwa ta dubesa zatai magana ya ce, “ALLAH kika sake magana sai na ɓata miki rai. Wuce alwala konaje na haɗaki da Babban Yaya ko Ammie”.
A duniya Maanal na tsoron Babban Yaya da Ammie, dan sune ke cimata ƙaniya a zauna kafiya. Cikin jin haushi ta cire ɗan hijjab ɗinta ta jefa a gadon Oum sannan ta wuce bayi fuuu. Shima ficewarsa yay batare daya sake kulata ba. Koda tayo alwalar kusa da Oum tazo tayi sallar itama...


Koda aka idar da sallar shi da Fawzan suka dawo, direct ɗakin Oum suka shigo, sun samu Maanal a saman jikinta kwance tana mata surutu. Fawzan ya gaida Oum, shima Ajwaad haka. Amsawa tai fuskarta da murmushi tana kallon Ajwaad, sai kuma ta kalla Fawzan suka saki murmushi. Ajwaad ɗin na kallonsu, amma bai tanka ba ya zauna kusa da Oum ɗin shima yana ɗakko bag ɗin Maanal na islamiyya. Sai da ya gama fiddo books ɗin duka sannan ya kalla Maanal dake ta surutu wa Oum.
“Parrot tashi kiyi aikin islamiyya idan anyi isha'i mayi na boko”.
Cikin ɓata fuska alamar fushi take da shi har yanzu, “Tace ni kayi min barci naje ji”.
“Ko mutuwa ko?”.
Ya faɗa cike da gatse. Tashi Maanal tai zaune idanunta cike da ƙwalla tana kallonsa. Sai kuma ta kalla Oum da faɗin, “Oum kin gansa ko, so yake ma na mutu ya huta ban girma naga ya zama kamar Daddy da Baabu ba”.
Da ƙyar Oum ta danne dariyarta, “A'a in sha ALLAHU Auta bazaki mutu ba sai kinga girman Auta ya zama kamar Daddy da Baabu. Yo ina dalili Auta gaskiya ka bari. Ƙuruciya tare tsufa tare in sha ALLAHU”.
Dariya Fawzan ya sanya da faɗin, “Wato Oum soyayyar nan fa na tafiya da ni.....”
Harararsa Ajwaad yayi, sai kuma ya rufe books ɗin zai tashi Oum tai saurin kama hannunsa ta maida shi ta zaunar tana gumtse dariya. Sai kuma taima Maanal nuni data matsa suyi karatun. Ƙarfin dariya Fawzan ya ƙara tare da miƙewa ya fice yana faɗin, “In dai nine ma nayi nan. Bara dai naje mu daidaita da Amaal nima kozan samu Besty na”.
Filo Oum ta ɗauka ta jefa masa. Ai ko ya ƙarasa fita a guje. Shi dai Ajwaad bai kulashi ba. Sai aikin da suka fara shi da Maanal na islamiyya. Basu tashi ba kuma sai da aka kira magrib. Ana idarwa ya dawo suka ƙarasa suka fara na boko kuma anan falo. Dan Oum sam bata barinsu su biyu a ɗaki, shiyyasa ma aka saka camara a ɗakinsu duk da ba'a taɓa kama ko ɗayansu da wani halin rashin tarbiyya ba gaskiya....
Da ƙyar Maanal ta bari suka kammala homework ɗin nan. Abinci ma tace ta ƙoshi sai da Oum ta lallaɓata ta bata tea. Ai ko tana gamawa ta ɓingire a jikinta ta hau barci. Sai da barcin yay nisa Ajwaad yazo ya ɗauketa ya kai ɗakin Oum ya kwantar, dan yasan ta gaji ɗin kam, kuma yanda tayi barcin nan duk bala'in dama za'ayi ayi bazata yarda tayi wanka ba.
Dama haka take, kusan rayuwarta raba dai-dai ce a tsakanin nan gidan su Ajwaad da can gidansu. Dan ko kayanta a rarrabe suke saboda ko'ina a gidajen biyu tana zama. Wani lokacin sai tai sati bata leƙa gidansu ba sai kewarta ta ishi Baabu ne ya aiko a kirata sannan. Idan kuma ƴan arziƙin na kanta kullum sai taje ta gaida Ammie da Baabu ɗin. Idan kuma aljanun nata suka koma can gidansu kullum zata zo ta gaida Oum ne......

_________★


A kwana a tashi asarar mai rai. Yau ga su Maanal da yin graduation na gama primary. Zokaga rawar kai wajan mutuniyar. Balle da taji Oum ta shirya musu party ita da Bestyn nata. Duk da dai shi ya nuna baya so, amma Oum tace babu fashi sai tayi tunda Maanal naso. Babu yanda ya iya dole shima ya sakko aka hau shirye-shirye. Ammie kanta ba son fatin take ba, dan tasan hanyar kashe kuɗi kawai Oum ta ƙirƙiro ma kanta. Dan koda ta sanarma Babu ma kai tsaye yace shifa gaskiya bai da kuɗi. Cikin sanyin murya ta ce, “Aunty ce fa dama ta shirya musu bawai kuɗi zaka bayar ba. Naga ya kamata ka sani ne shiyyasa”.
“Oh to ALLAH ya taimaka. Dan nima ina da nawa uzirin ne ma shiyyasa. Tunda hutun nan mai tsayine ina son muje gida gaskiya. Gwaggo nata magana akan hakan”.
Wani irin faɗuwa gaban Ammie yayi, a take zufa ta shiga tsatstsafoma goshinta. Ganin ya juyo yana kallonta saboda jin tayi shiru tai saurin gyara yanayinta tayi ɗan murmushin yaƙe. “Kai amma nasan yaran nan zasuyi murna sosai. Musamman ma Maanal da tunda aka baro garin ba'a koma da ita ba shekara kusan shida.......”
“Oh ke baki murna kenan?”.
“A'a haba yazance bana murna ni da garinmu. Baka fahimceni bane ba dai”.
Komai bai sake cewa ba sai shigewa toilet ma da yayi dan dama shirin wanka yake yi. Jagwab Ammie takai zaune zuciyarta na wani irin farfashewa a ƙirjinta. Gaba ɗaya jikinta rawa yake. Tabbas ta cancanci tai kewar tushenta, sai dai rasa wani giɓi da babban ƙalubalen data baro yasa mata jin tsoro da rashin son zuwa garin. Sai dai tasan ko giyar wake tasha bata isa bijirewa umarnin mijin nata ba kuma ɗan uwanta. Jin motsin zai fito yasa ta miƙe da sauri ta fita a ɗakin, tana mai ƙoƙarin danne komai..........✍️












✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖5️⃣8️⃣




______________




.........Babu bai sake bi takan bikin su Maanal ba, yama maida hankali a shirya musu tafiya gida. Yayinda Ammie taketa ƙarfin halin yin nata shirye-shiryen itama batare da su yaran sun san mi ake ba. A haka ranar juma'a akai partyn da Oum ta shiryama Maanal da Ajwaad. Abin kamar wasa sai gashi ya ƙayatar. Anci ansha yara sun sha bidirinsu musamman Maanal da ko zama ta huta batayi. Shi kansa AA duk ta takurama rayuwarsa. Haka dai aka tashi gab da magriba, tsabar gajiyar da Maanal tayi a inda tai sallar magrib anan ta ɓingire barci. Kallonta kawai Oum tai tana murmushi, dan a tare sukai sallar a ɗakinta. Ɗaukarta tai cak ta maida saman gadonta ta kwanar, ita kuma ta cigaba da lazimin ta.
Bayan idar da sallar isha'i su Ajwaad suka shigo harda Aban su. Kai tsaye ɗakin Oum Abah ya shigo. Yakai zaune bakin gado fuskarsa da murmushi yana kallon Maanal ya ce, “A'a anan surukar taki tai barci?”.
Dariya Oum tayi tare da faɗin, “Kaji Aban su da wata magana suruka kuma?”.
Murmushin sa ya sake faɗaɗawa shima da faɗin, “Eh mana. Ai abunne na Maanal da autanki akwai ban mamaki. Zan so wannan abotar tasu ƙarshenta ya kasance hakan”.
“To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Idan hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki Gandanga. Dan har cikin raina nake jin matuƙar ƙaunar yarinyar nan wlhy”.
“Nima haka yarinyar ta shiga raina sosai. Badan kar ace ma na cika zumuɗi ba nifa da a yanzu zan ɗaura musu aure kawai”.
Dariya sosai Oum keyi. Shima Aba na tayata. Sai da sukai mai isarsu Oum tace, “Ayi haƙuri dai a barsu sukai hankalin kansu. Kar a tauyesu musamman ita da take mace. Gara shi namiji ne yana da damar auren fiye da ita”.
“Hakane kuma kema kinyi magana. Kinga nama shafa'a ɗazun Baban nasu ke sanar min zasuje gida hutun nan ma, dan mahaifiyarsa tana kewarsa sosai.”
“Kai masha ALLAH, ai ni har ƙoƙarin su nake gani ma. Musamman Ammien Shahidah. Garama shi tace yaje kusan sau uku. Amma ita tunda suka dawo Kano bataje ba hakama yara”.
“Abin ne sai a hankali ai. Kin san idan iyali sukai nauyi tafiya ma wahala take yi. Balle wannan aikin nasu na ƴan sanda sai a hankali. Kwanaki ma kamar zasu masa transfer ALLAH dai ya taimakesa aka samu canji. Hankalinsa ya tashi sosai dan yace baya son yawon da yake da yaran musamman a yanzu da suka fara girma”.
“Yana da gaskiya. Ita kanta takance ALLAH yasa ko ya samu canjin wajen aiki ya barsu su anan Kano dan tana jin daɗin zaman garin......”
Sallamar Ajwaad ta katse Oum. A tare suka amsa masa da bashi izinin shigowa.
“Lafiya Autana?”.
Oum ta faɗa tana kallonsa. Fuska ya ɗan yamutse kamar zai saki kuka ya ce, “Oum kaina ke ciwo. Kuma ina jin yunwa”.
“Ya rabba. Autana badai duk kai kawon nan baka ci abinci ba?”.
Kansa ya ɗaga mata alamar “eh”.
Da sauri ta kama hannunsa suka fice tana jan salati. Aba ya mike yana musu dariya....


___________★


Sosai su Ammie suka shirya wannan tafiya. Yayinda su Shahidah keta zumuɗi banda Maanal da tace idan fa bada Ajwaad ba babu inda zataje ita kam. Babu wanda ya tanka mata dai akan batun. Su dai sun cigaba da shirinsu kawai.
A ɓangaren Ajwaad ɗin ma tunda yaji batun tafiya jikinsa yay sanyi. Da farko shima ya nuna son binsu. Har ya samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login