Showing 51001 words to 54000 words out of 221978 words

Chapter 18 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

office ɗin dukkan damuwarsa da AA ya dasa masa na guduwa daga cikin ƙirjinsa. Sai dai kuma hankalinsa nakan dalilin halin da Maanal ɗin ta shiga........✍️




_Tofa ƙaƙa raƙa ƙaƙa. Shin minene alaƙar Maanal da AA?, sannan minene alaƙar RK da AA kuma. Dan tabbas alamu sun nuna akwai sanayya mai ƙarfin gaske a tsakaninsu. Hhhh badaƙala kenan, mi kike son ji?😂 Ga wuri ga waina. To kawai mu haɗe a comments section 🤣🤣🤣🤣🏃._




✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖2️⃣4️⃣






.........Wata irin ajiyar zuciya director Mustapha ya saki. Sai kuma ya saki murmushi a ransa yana mamakin kansa da ɓoyema Doctor Rafeeq ɗin sauran gaskiyar abinda ya faru da yay... Kirane ya shigo daga landline ɗin office ɗin, ganin daga office ɗin CEO ne ya sashi saurin ɗagawa. AS ne ya sanar masa CEO na buƙatar ganinsa yanzun nan, kuma ya taho da file ɗin sabuwar staff ɗinsu. Bai wani tsaya wasa ba ya miƙe yana dariya. A fili ya furta, “Anya babu wata a ƙasa akan yarinyar nan kuwa? To madai ji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta”.
Sai da AS ya shiga yay masa iso sannan ya shiga. A yanzu kam AA ɗin na zaune ne a kujerarsa ta aiki saɓanin a yanda RK ya samesa ya kuma barshi. Gaisuwa Director Mustapha ya miƙa daga tsayen batare daya zauna ba. Shima AA ɗin da hankalinsa ke kan computern desk ɗin batare daya amsa ba yay masa nuni da vesitors chair ɗin gaban desk ɗin kawai. Zama yay, kafin cikin girmamawa ya ce, “Gani Sir. Dama ina ƙoƙarin ƙarasa haɗa komai ne na kawo sai kuma ga kiran AS akan kana son ganina”.
Shiru bai amsa masa ba, yanata aikin gabansa kawai har lokacin hankalinsa nakan screen ɗin computer ɗin, sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya ajiye tare da maido hankalinsa kan Director Mustapha ɗin. “Am sorry ina wani abune”. Ya faɗa cikin muryarsa mai zurfi. Da sauri Director Mustapha ya ce, “Babu komai Sir”.
Kansa kawai ya jinjina masa. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar ya basa file ɗin. Miƙa masa yay da sauri cikin girmamawa. Yayinda shi kuma ya shiga buɗesa yana duba komai daki-daki. Sai zuwa can ya ɗan ɗago. “Baku ƙarasa bane?”.
“Eh sir! Saboda kana fita itama ta miƙe ta fice muna ƙoƙarin tsaidata amma bata sauraremu ba. Mun cigaba da abinda ya dace ne kawai saboda ka bada umarnin hakan. Dan mu harma mun fara tunanin ko tanada wani c......”
Muƙutt ya haɗiye zancen saboda wani shegen kallo da AA ɗin ya jefa masa. Sai kuma ya duƙar da kansa yana shashshafa ƙeya. Shiru office ɗin ya ɗauka na kusan minti biyu kafin yay masa nuni da hannu alamar yaje. Miƙewa yay tare da ɗan rissinawa na girmamawa sannan ya fice a office ɗin.....


Duk yanda yaso cigaba da aikin zuwa lokacin break hakan ya hagaresa. Dan wani irin zazzaɓi ne ma ke neman rufesa. Ga ciwon kai. Dan hatta fararen idanunsa launinsu ya canja zuwa jaa sosai alamar akwai wani abu dake damunsa. Sai dai sam fuskarsa bata nuna komai.
Kwanciya yay a office ɗin bayan dawowa sallar azhar, kamar wasa zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa, ga wani irin sanyi da yake ji. Ya kulle kofar tare da ma AS gargaɗin baya buƙatar kowa. Hakan yasa ko lokacin Asr AS bai masa knocking ba dan yasan ogansa baya wasa da salla. Ganin har biyar na yamma lokacin ma'aikata sun fara tashi babu alamar zai fito hankalin AS ɗin ya fara tashi, ya dai daure dan yasansa da iya yin over work. Kamar wasa har magrib companyn yayi shiru sai securitys. Dole fa yaje ya fara masa knocking amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Hankali tashe AS yay kiran wata number, bayan an ɗaga yayi gaisuwa cikin girmamawa ya sanar da halin da boss ɗin nasa ke ciki. Banji mi aka sanar masa ba, sai dai ya amsa da girmamawa yana sauke wayar. Yana nan yana faman kai-kawo a bakin ƙofar sai ga wani nutsetstsen mutum da zai iya kaiwa shekara arba'in haka. Sosai yake kamanni da AA ɗin, hatta da rashin yawan fara'ar fuska kamar AA ɗin dai. Gaisheshi AS yay da girmamawa. Ya jinjina masa kai yana amsawa, sai kuma ya fiddo wani ɗan card a aljihun jallabiyarsa fara ƙal ya goga a jikin handle ɗin ƙofar. A take kuwa ta rabe gida biyu ta buɗe. Gaba ɗaya an kashe wutan office ɗin, hakan ya saka gabansa faɗuwa, dan sun san minene ganin AA a duhu yake nufi, wayarsa ya zaro ya kunna fitilar, hakan ya bashi damar ƙarasawa ga makunan fitulun office ɗin ya kunna. A take haske ya gauraye ko'ina. Idanunsa suka sauka akan AA dake kwance a kan sofa. Cike da sassarfa ya ƙarasa garesa yana kiran sunansa, amma shiru babu allamar zai amsa, har ya zauna a saman table ɗin gaban sofa ɗin tare da kai hannunsa saman na AA daya dafe kai da shi, hannun ya janye a hankali ya maye gurbinsa da nashi, sai da gabansa ya faɗin jin wani irin hucin zafi, sanyin hannunsa yasa AA buɗe manyan oily idanunsa gently, sunyi wani irin mugun kaɗawa jazur, sam babu hasken nan mai kama da madara a cikinsu yanzu, sai ƙyallinsu daya sake saka jan yin bauuu. Ga kuma jijiyoyin kansa da suka sake fitowa ruɗu-ruɗu....
“Ya arrahaman Auta! Baka da lafiya amma kazo nan ka kwanta? Are you mad da baka san muhimmancin lafiyarka bane?”.
Maimakon amsa masa sai AA ɗin ya maida idanun nasa kawai ya sake lumshewa. Tsaki mutumin yaja tare da miƙewa ya tada AA ɗin shima. “Oya get up and go home?”.
Bai masa musu ba ya miƙe ɗin, haka ya kamashi suka fito yana bama AS da hankalinsa ya tashi da ganin halin da boss ɗinsa yake ciki umarnin tattaro abubuwan AA ɗin. Cikin sauri ya amsa shi kuma ya wuce da shi......


_____________★


A hankali yake juya steering kamar baya so. Yayinda gaba ɗayan hankalinsa ke akan al'amarin Maanal. Yama rasa yaya zai fassara lamarin, musamman a yanzu daya koma Maawad yaji komai daya faru. Shin murnar samun aikin ce ta sakata kukan? Ko kuwa mike faruwa?. Rashin mai bashi amsa ya sashi ɗaukar hanyar gidan Shahidah, dan gaskiya yana buƙatar ganin Maanal ɗin. Ya ɗan yi nisa da tafiya kira ya shigo masa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma dai ya ɗauka saboda ganin abokin aikinsa ne na asibiti. Neman gaggawa ake masa zuwa asibiti yanzun nan, dole yay reverse zuwa asibitin dan yanda yaji Doctor ɗin a rikice yasan akwai babbar matsala. Kafin ya isa kiran wasu doctors biyu ƴan uwansa ya sake shigo masa. Dole ya ƙara gudu cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso.....


_________★


A ɓangaren Maanal kuka taci sosai na tashin hankali. Dan har yamma ta kulle kanta a ɗaki taƙi ta fito. Yara da suka dawo makaranta sunata buga mata bata kulasu ba. A haka shima baban nasu ya dawo ya tarar da al'amarin. Linda ce ta sanar masa iya abinda ta sani na shigowar Maanal ɗin da gudu tana kuka ta wuce ɗaki ta kulle kanta...
Hankalinsa ne ya tashi shima. Ya shiga knocking ƙofar yana kiran sunanta amma shiru. Sai ya fara tunanin kodai batama rayene? Gata tare da ciwo mai haɗari. Wayar Shahidah ya kira yace ta dawo gida yanzun nan. Hankali tashe ta shiga tambayarsa lafiya? Dan ita bata tashi a nata aikin ba. Amma sai yace ba komai tazo dai kawai. Daga haka ya yanke kiran ya fita neman maigadi dan yazo su gwada ɓalla ƙofar. Babu jimawa suka dawo, zuwa lokacin yaran nata kuka suna sake buga ƙofar. Sunta ƙoƙarin buge ƙofar amma bata ɓallun ba, dole maigadi ya ce, “Yallaɓai sai dai fa a nemo wanda yasan aikin karma ayi ɓarna. Bara muga na kira wani yaro dana sani”.
Kai kawai Uncle Sadeeq ɗin ya iya ɗaga masa. Dai-dai nan Shahidah ke shigowa a ruɗe. Cikin tashin hankali take tambayarsa abinda ya faru. Bayani ya mata kamar yanda Linda ta masa. A take jikin Shahidah ya kama rawa. Itama ƙofar ta fara bugawa muryarta na rawa tana kiran sunan Maanal ɗin amma shiru. Wani tunani ne yazo mata, ta fita cikin sassarfa zuwa can baya inda windows ɗin ɗakin suke. Binta shima mijin nata yay. Kwance suka hango Maanal sharɓan a gado babu alamar rai a tare da ita. Ai Shahidah bama tasan tayi wani irin yin baya ba tana neman faɗuwa sai da mijinta ya tarota. Cikin rawar baki data murya ta ce, “Honey ta rasu ko? Da alama Maanal bata numfashi”.
“In sha ALLAHU bata rasu ba Honey cool down. Zata iya yiwuwa suma tayi ko barci take”.
“Barci! Ina badai barci ba Honey.....”
Isowar su maigadi ya hanashi bata amsa. Kamata yay suka koma cikin gidan. Cikin abinda bai wuce mintuna goma ba aka ɓalle ƙofar ɗakin. Daga Shahidah har mijinta da yaran a guje suka afka ciki. Lokaci ɗaya ita da yaran suka zagaye Maanal ɗin. Koda ta cacumota sai tai mata wani jagab alamar babu rai tare da ita. “ Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un”. Ta shiga ambata jikinta na rawa. Yayinda yaran suka fara ihun kuka suna kiran Maanal ɗin. Shi kam mijinta ƙoƙarin neman number RK yake yi, sai dai sam taƙi shiga. Dole ya koma neman Dr Ranjet. Cikin Sa'a kuwa sai ita ta shiga. Bayani ya masa a taƙaice, hankali tashe Dr Ranjet yace gashi nan zuwa gidan RK ya shiga theater ɗin gaggawa ne tun ɗazun shiyyasa bazai samesa ba.
Alhamdullah Dr Ranjet ya iso akan lokaci tare da wata abokiyar aikinsa. Dandanan ya saka kowa ya fito suka kasance su biyu kawai a ɗakin. Taimakon gaggawa suka shiga bama Maanal ɗin, sunfi awa ɗaya kafin cikin amincin UBANGIJI ta farfaɗo. Dama ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu bugun zuciyarta ne yay ƙasa sosai shiyyasa numfashinta ya dakata ma amma tana da rai. Basu bari kowa ya shigo ba sai da suka gama dai-daita komai suka saka mata ruwa da allurai sannan.
Bayanin da Dr Ranjet yamusu ya saka su dinga sauke ajiyar zuciya a tare. Shahidah ta dinga share hawaye. Su duka suka shiga tare da yaran da mijin nata, ganin Maanal ɗin na barcinta hankali kwance ya sake saka musu nutsuwa. Bayan fitowarsu ne Dr Ranjet ke sanar musu dolene su kula sosai da shan maganin Maanal ɗin, dan yanzu ma yana tunanin sakacin hakanne ya kawo wannan matsalar, duk da ya fahimci akwai damuwa tattare da ita bai faɗa musu ba dai. Hakan kuwa ɗin ne kamar yanda yay hasashe, dan yasa an kawo masa magungunan ya duba ashe kona safe bata sha ba ta fita. Ya sake tabbatar musu da kula da shan maganin nata da shigarta kowacce matsalar damuwa komai ƙanƙantarta sannan suka wuce.
Dole yau Shahidah tare ta kwana da Maanal. Alhamdullah ta tashi cikin aminci kuma. Dukkan wata kulawa Shahidah ce ta bata a wannan safiyar, harda yara kowa tattalinta yake yi, hatta da abinci tara suka bata a baki, hakan ya sakasu makarar fita dan sai da ta sake komawa barci sannan. Bayan ta farka Linda tai ƙoƙarin taimaka mata tai wanka taci abinci tare da sanar mata zuwan RK gidan har sau biyu, amma sai Maanal ɗin taƙi cewa komai tana zaune kawai tana hawaye. Ana haka RK ya sake dawowa. Babu lallashin da Linda batai mata ba akan taje su gaisa ko shi ya shigo amma taƙi, tanata kukanta kawai. Hankalinta sai ya sake tashi tai kiran Shahidah dake a wajen aiki ta sanar mata. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata ta dawo gidan...


★ “Haba Maanal wai mike faruwa ne duk kinbi kin ɗaga mana hankali. Jibafa office na baro saboda kiran da Linda taimin duk da tarin ayyukan dake a gabana. Amma inata magana kinyi shiru sai kuka kikeyi. Idan jikin naki ne kuma muje asibiti. Ko na kira Ammie ne dai?”.
Da sauri Maanal ta shiga girgiza mata kanta tana sharce hawayen da suka gagara tsaya mata. “Didi kar ki kirata dan ALLAH. Ba wani abu baneba fa”.
“Haba Maanal ya zakice bawani abu bane gaki kinata faman kuka. Idan baki son na kira Ammien to ki faɗa min mike faruwa ne? Wani abun Rafeeq ɗin ya miki jiyan da kuka fita? Ko aikin ne basu ɗaukeki ba?”.
“A'a Didi babu ɗaya daga ciki, ina son yai zan koma KD”.
“Okay mune mukai miki wani abu kenan?”.
“Kai Didi ni mi zaku min. ALLAH ki kwantar da hankalinki babu komai”.
“Batun kwantar da hankali kam bazai kwantu ba Maanal, yanzu fa kike cewa zaki tafi KD. Amma dai bara na kira Ammien ni kam, ƙila ki sanar mata ko Nene. Ga Rafeeq can Linda tace yayi mayawa takai huɗu tunda safe amma kinƙi fita, kinƙi cin abinci, kinƙi wanka Maanal why? Gara nai kiratan dai zai fi”.
Caraf ta riƙe mata hannun tana girgiza kanta. Yayinda idanunta suka cika da ƙwalla tab. “Please Didi karki kirata zan gaya miki”. Kai Shahidah ta jinjina tare da sauke numfashi sai kuma ta sakar mata wayar da faɗin, “To ina saurarenki, mike faruwa?”. Sai da Maanal taja kusan mintuna biyu kafin da ƙyar ta iya furta, “Didi sun ɗaukeni aikin amma bazanyi ba”.
“Baza kiyi ba kamar ya? To saboda mi?. A wannan lokaci da aiki ke wahala Maanal. Kin samu cikin sauƙi haka amma kice baza kiyi ba. Ko auren Yazeed ɗin kike so to? Ko kuma dan kinji jiya ankai kuɗinsa gidan su Nazeefa ne har kika nema tadana kanki ciwo?”.
“Didi mizai sa na damu da auren Yaya Yazeed tunda ba'a kaina zata zauna ba.”
“To mike faruwa? Wajen aikin ne ya miki alamu na marasa ɗa'a ko me?”.
“A'a Didi kawai dai”.
“Miye kawai dai. Maanal ki fito kimin bayani mana yanda zan fahimta na kuma gamsu”.
Rasa yanda zataima Shahidah ɗin bayani tayi, ta fito fili ta sanar mata abinda idanunta suka gani a jiyan ko kuwa ta shanye al'amarin a cikinta kawai ta dage akan aikinne bazatayi ba. To amma tasan nacin RK, shima bazai barta ba ai. Sannan ita kanta Didi ba barinta zatai ta huta ba har sai ta san gaskiyar al'amarin. Sanin gaskiyar kuma na nufin abinda zata ɓoye a yanzu dan sai sun san komai. (Ya arrahaman) ita ina ya kamata ta kama ne?.....
“Maanal!!”
Shahidah ta kirata tana mai girgizata. Firgigit ta dawo hayyacinta kamar wadda aka tada daga barci, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da kai hannunta saman goshi tana murzawa a hankali.
“ALLAH Maanal tambaya ta ƙarshe zan miki daga nan zan kira Ammie ne kawai tunda ni baki son nasan damuwarki”.
Jin yanda Shahidah tai maganar a hasale tana ƙoƙarin miƙewa yasa Maanal saurin kamo hannunta ta dawo da ita. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Didi ba ɓoye miki nake ba wlhy, kema kin sani bana taɓa ɓoye muku komai a rayuwata. Kawai dai na fasa yin aikin ne saboda companyn na Bes...” sai kuma ta canja ta ce, *_“AA Darma_* ne?”.
Cikin matuƙar razani Shahidah ta miƙe zumbur hannunta dafe da ƙirji ta ce, “What!! Kina nufin *_Ajwaad!!_* Maanal!”.
“Shi Didi, shi! Shi! ɗin dai.” Maanal ta faɗa wasu hawaye masu zafi na sake gangaro mata.
Jagwab Shahidah ta koma ta zauna tana mai dafe kanta da duka hannaye biyu, ita kanta jikinta tsuma yake, sai kuma ta ɗago tare da jawo Maanal ɗin jikinta ta rungume dan kuka take mai ban tausayi da tsuma zuciya. Cikin sarƙewar murya ta ce, “Maanal kuma kin gansa ya ganki? Kin tabbatar shi ɗin ne dai?”.
Kai Maanal ɗin ta jinjina mata, “Ya ganni sosai, amma ya nuna kamar ma bai taɓa sanina ba tamkar a wancan ranar da yay......” nan dai ta labarta mata duk yanda komai ya faru. Gaba ɗaya mamaki ya gama kashe Shahidah, amma sai ta danne ta shiga Lallashinta har sai da tai shiru. Daga haka ma ta ciro maganinta ta bata kasancewar lokacin shan na rana yayi. Tana sha babu jimawa ta ɓingire wani barcin. Lallaɓawa Shahidah tai ta gyara mata kwanciya, sannan ta saka mata ac kaɗan ta kashe mata fitilar ɗakin ta fice..........✍️




_Tofa, wanene *AA Darma* a rayuwar Maanal Habeeb Giro?. Karku gajiya kumuje zuwa dan yanzune labarin AJIYA A DUHU ma zai fara. Labarin nan fa akwai cakwakiya ta musamman mutane na. Ni bamma san team ɗin wa zan kasance ba bana. Karna zaɓi AA ace min mayyar kuɗi🥲🥱🤪🏃_










✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login