Showing 138001 words to 141000 words out of 215774 words

Chapter 47 - AJIYA A DUHU 3 End Hausa Novels By Billyn Abdull .doc

zaunar da Maanal dake lulluSe. Da ?yar ta iya daurewa tace ALLAH ya sanya albarka kawai. Wai ai tasan duk wanda ya isa ya mata nasiha ita basai tace komai ba.
? ? Shahidah da a yanzu Maanal ta gama nuna mata wani abu kaWan daga Mamyn sai tai murmushi kawai, tare da fassara zancen nata da ?yau a zuciya. Ita kanta Nene yau dai kam tasha jinin jikinta akan Mamyn, amma batace komai ba suka fito da Maaanal. Sashenta suka maidata, aka ?ara mata nasiha sukai sallar la'asar suka firfito dan tafiya. Kuka sosai Maanal keyi abin tausayi, dan ma Amaal na nan tare da ita sai Aunty Sakina. Sai zuwa magrib su zasu koma gidan Shahidah su sake kwana gobe su wuce kd.
? ? ?? Sashen Oum suka koma yimata sallama. Sosai Oum tai mamaki ganin wannan tafiya tasu ta yamma haka. Ta shiga lallashinsu akan su bari sai gobe da safe Nene tace ina ai in sha ALLAHU yau a Kaduna zasu kwana, abin ai sai ya koma rashin kangado kuma. Anyi komai an gama ai suma sai a barsu su huta haka nan abi yara da addu'ar zama lafiya.. Badan Oum taso ba ta ha?ura, nan fa aka shiga shirya musu kayan biki da aka tanada domin su, dan hatta Ammie sai da Oum ta haWa mata nata. Sashen Maanal Win suka sake dawowa tare da ita, acewarta ya kamata suyi sallama da AA dan ta kaisu sunyi da Abah yanata musu godiya, a can kuma suka sami Mamy itama. Kiran wayar AA datai a kashe kuma Fawzan ya tabbatar mata yana gidan sanda suke buWar kai ya shigo ya sata biyosu.
? ? ? Rungume Maanal dake zaune a bakin gado ta takure waje guda tana sharar hawaye har yanzu tayi, cike da tausasawa ta shiga lallashinta. Kafin ta bata umarnin hawa sama ta kira musu AA Win. Mayafin lafayarta ta gyara da ?yau, tayi ?yau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ?amshinta daban ne, ga ?unshinta raWam yanata Waukar ido daga ba?in har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autan ta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai Worewa kuma.?Tare da Oum suka baro bedroom Win nata suka haura sama. Zuciyar Maanal bata ?arasa fashewa ba sai da ta hawo upstairs Win, ya subahannallah komai yaji, ga wani mayataccen ?amshi mai ratsa zuciya. Zama Oum tayi a Waya daga kujerun, Maanal Win zata zauna itama ta katseta tana nuna mata kofar bedroom Win AA. Jikinta cike da sanyi ta nufa ?ofar, tana gab da isa sai gashi an buWe. Cak ta tsaya tana kallonsa. Kamar yanda shima yake kallonta irin na mamakin nan dan ko motsinsu bai jiba. Yama fito ne zai fita dan dama wanka ya shigo yayi rabonsa da wanka tunna safe manyan kayan jikinsa sun takurasa shiyyasa yazo yay wankan ya canja da ?ananu. Juyawa kawai Maanal tai tabar wajen, shima sai bai ce komai ba ya biyota saboda hango Oum zane a falon.
? ? ? Bata zauna ba, sai tai kamar ana kiranta a waya ta gudu ta barsu dan ta basu damarsu. Murmushi kawai Oum tayi danta fahimci wayo Maanal tayi ya gudu babu wani kiranta da akayi. Bedroom Winta ta wuce inda su Nene suke. Bata wani jima ba Oum ta shigo da sallama itama. Ta sanarma Nene ga AA zai shigo suyi sallama. Gyagygyarawa suka shiga yi kafin ya shigo bakinsa da sallama. Duk suka amsa banda Maanal datake kallon hotunansu a wayar Aunty Sakina. Cike da girmamawa ya rissina ya gaida Nene, hakama Aunty Sakina duk da ba girmarsa tayi ba, amma tunda akace matsayin ?anwa take a wajen Ammie yake girmamata. Shahidah ta ce,  Oh mu baza'a gaishemu ba Ajwaad .
? ? Hararrata yay ya Wauke kai. Su Nene suka sanya dariya. Oum da itama ke dariya tace,  Gaskiya fa Shahidah ta faWa Auta, dan yanzu babu batun ?ar gaddamar cewa bata girmeka ba matsayin yaya take dai .
? ? ??  Ni banzanyi Auntys da su ba Oum, Aunty Sakina ta isheni . Yay maganar ?asa-?asa yana hararar Amaal itama. Dariya kowa keyi, Amal ta ce,  Ni dai na ha?ura ma Yaya Ajwaad basai kace min Aunty ba, dan nasan bama cewar zakai ba. Kuma nima bazan so kace ba dan kai Yayana ne .
? ?? Oum ta ce,  Amaal yada saurin sallamawa haka .
? ? ??  Oum gara na sallama wlhy, dan kozan mutu na dawo Yaya Ajwaad bazai ce min Aunty ba kema kin sani .
? ?? Nan ma sosai suke dariya. Shi ko ya fuske abinsa. Sai ma satar kallon Maanal yake ta ?asan ido. Itako tayi kamar bata san ma da shigowar tashi ba, rabin fiskarta ma gyalen ya Wan rufe. Godiya sosai AA yayma Nene, tare da al?awarin zuwa gaisheta nan kusa in sha ALLAHU ita da su Ammie. Sosai Nene taji daWin hakan ta kuma sake yaba AA Win dan tarbiyyar sa ta birgeta sosai. Leda dake a hannunsa ya mi?ama Oum, yace ta basu, bai jira cewar kowa ba ya mi?e bayan Oum ta amsa ledan ta mi?ama Nene tana murmushi. Amasar ledar Nene tayi tana faWin,  Tofa mi muka samu kai Wan nan.....
? ?? Ta kasa ?arasa maganar sakamakon tozali da tai da kuWaWe ?an dubu bugun Abuja sabbi fil. Da wani irin sauri ta kalla Oum, sai kuma ta girgiza kai tana mi?a mata ledar.  Bazamu amsa ba Wiyata. Ai abun ma sai ya zama rashin hankali .
? ? Ro?onta Oum ta shiga yi itama, amma Nene ta dage akan bazasufa amsa ba. Sai ma ta mi?e tana ficewa tunda su Amaal da Aunty Sakina anan za'a barsu su ?arasa gyara mata gidan sai zuwa anjima kafin anguna su shigo dan ba'a barta ita kaWai ba.? Shahidah dai zata bisu saboda sai sun koma ta gidanta. Suma su Maanal Win fitowa sukai yi musu rakkiya, tuni AA ya haWa motocin da zasu kaisu can gidan Shahidah su Wauka sauran kayansu sai su kaisu train station. HaWa ido yay da Maanal dake sharar hawaye Aunty Sakina ri?e da hannunta. Su su Aneesa nata tsokanarta wai sai sun dawo Abuja suna bata kulasu ba. Suna ma haWa ido da AA Win ta risinar da idannunta ?asa. Haka suka shishshiga mota Oum ta dan?a ledar a hannun Shahidah, zatai magana ta harareta da mata alamar tai shiru. Dole tai shirun kuwa suka wuce. Ciki su Amaal suka koma da Maanal dake kuka sosai, AA ya girgiza kai kawai ya shiga mota ya fice a gidan dan zaije wajen abokansa dake shirye-shirye tafiya suma. Wasu dama tun safe duk sun wuce sai wanda suka rage da zasubi flight Win yamma....

? ? ? ?? _________&

? ? Mamy dai ciwon kai ya hanata sukuni, gashi tasha magani babu wani canji, dole Hajiya Turai ta ?ara turo musu Nurse Win nan ta dubata. Cikin damuwa ta ce,  Hajiya akwai matsala fa gaskiya, in dai bazaki rage wannan damuwar ba bp Winki fa bazai taSa ya sauka ba. Gashi zuwa yanzu hatta bugun zuciyarki ya canja. Jininki kuwa ba'a magana wlhy, shiyyasa ma kike ganin dishi-dishi ciwon kan kuma ya?i sauka. Dole zan sake miki allurar barci mai ?arfi sosai dan ki samu barci, amma ki sani allurarnan barci kawai zata sanya ki, kwanciyar hankalinki shine maganin matsalar  .
? ? ? Ita dai Mamy komai tama kasa cewa, dan abun duniya ne ya taru yama zuciyarta rubdugu. Haka Nurse ta mata allurar barci. Tun tana kallonsu da saurarensu har barci yay awon gaba da ita.....

? ? Oum bata san wainar ba ake toyawa ba, tana a tsakkiyar ?an uwanta dan duk dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce su kuma. Itama Oum Win bata kawo komai a ranta ba tunda taga Mamyn na zagaye da nata ?an uwan ne. Duk da dai duk yau bazatace tama ga giccin Mamy ba, koda yake ko Abah ba bi take takansa ba tanata hidimarta.

& Bayan sallar isha'i su RK da ire-irensa dake sa'oin su AA a family Win na Darma suka iso gidan domin masa rakkiya. A dai-dai lokacin ne su Amaal ke fitowa cikin shirin tafiya ita da aunty Sakina. Sun sake gyara ko'ina na sashen sun baza uban ?amshin da har a compound ana jinsa masha ALLAH. Sai da suka shirya Maanal Win itama da taimakon Hajiya Shuwa. An mata wanka da turare iya wanka fiye da yanda ake mata shi tun fara gyaran jikin nan. Kafin Hajiya Shuwa ta naWeta a cikin sabuwar wata lafayar ?ar ubansu mai shegen ?yau kalar peach da Wan fari-fari, sai uban stones saketa wal?iya a jiki, an mata kwalliya ?ar dai-dai a fuska aka sake mata turaren turare. Sai Wauri daya zauna mata akai sannan aka rufeta da lafaya Win. Suka saka mata ac dai-dai misali aka zaunar da ita a tsakkiyar kadon Wakin nan ?asa Win, Hajiya Shuwa tace su barta anan idan AA Win yazo da kansa sai ya mata jagora Upstairs Win idan ?ar rakiyar tasa sun tafi. Suna jin shigowar motocin su AA suka fito dan dama su suke jira. Suka ma Maanal wayon cewa bara suje wajen Oum kafin su AA Win su gama. Dan tun Wazun take ro?onsu su kwana anan, ganin zata botsare musu da kuka sukace sunji zasu kwana. Shine suka mata wannan wayon suka gudu. Dan ko sashen su Oum Win basu koma ba ganin can su AA suka shiga....

&Su AA sun shiga falon Oum a dai-dai lokacin da dukkan mayan matan family Win ke zaune zaman jiran su, dan dama ?a'ida kenan ga duk wani angon family Win a lokacin masa rakkiya Wakin amarya. Kuma abinda zai birgeka isu-isu sukema juna rakkiya ba abokai ba. Su duka su a ?asan carpet suka zauna dan duk iyayene. Yayinda AA yaje gaban Oum ya zauna, cike da sanyi ya Waura kansa a saman gwiwoyinta ya wani lumshe idanu. Abin mamaki sai ga hawaye. Murmushi sosai Oum tai saboda jin saukar hawayen nasa a saman ?afarta, cike da kulawa da tsantsar so irin na uwa ga Wa ta du?o ta le?a fuskar tasa. Kukan kuwa yake yi da gaske, itama sai taji hawaye sun cika mata ido. Ta dai daure tasa bakin mayafinta ta share masa su. Kafin a hankali cike da kulawa ta ce,  Haba Auta na yau ai ba ranar kuka bace, ranar farin ciki ce mun mallaki Maanal na har abada in sha ALLAHU. Dan haka bana son ganin hawayen nan kaji Babyna, addu'a zamuyi mu godema UBANGIJI daya nuna mana wannan rana bayan jarabawoyin da muka tsallake Abaya. Harma mu haWa da sadaka domin nuna farin cikin mu ga ALLAH okay .
? ? Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya buWe idonsa yana kallonta, tare da kamo hannunta ya sumbata...........
'?





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________


........Cike da tsokana RK ya ce,  Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa .
? ?? Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya Wauka fillo ya jefa masa. Cafewa RK Win yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta kakkanni, nan fa su Oum suka shiga karesa suma. Anyi wasa anyi raha kafin a koma nasiha da gaba Waya ta ta'alla?a ne ga AA Win, ta yanda zai zama mai ha?uri akan mace, ta yanda zai ?yautata mata, ta yanda zai shagwaSata ya riritata, ya sauke ha??okinta da ?yautatata mata. Ya tattala soyayyarsu kullum taita ?ara dan?o a maimakon rauni da maza da yawa ke saka soyayyarsu yi saboda sakacin sauke ha??o?in da suka dace akan iyalansu. Sun nuna masa muhimmancin sau?a?ama mace saboda kasancewarmu masu rauni. Suka kuma tunasar da shi zaman aure zaman ibada ne ba zama irin na saurayi da budurwa ba, yanzu maganar ?akin soyayya da farautarta ya ?are. Lokacine na tabbatar da ita ta jaddadata domin ta ?ara nauyi a sikeli da dan?o fiye da sufagilu. Ha?uri da kura-kuran mata dan mu a karkace muke, wanda ya dage ko fariyyyar son ganin ya lan?wasamu mun mi?e to ya tabbata sai dai mu karye Sas. Dan haka ya kula yasan miya dace ga zaman auren, ya zama mai tausasawa sai yaci ribar zaman har yay nisan zangon kaiwa wasu shekarun da za'a ringa lissafi shekarun aurensu suma. Daga ?arshe aka rufe da addu'a mai tsaho da ratsa jiki, sannan aka sallame su dan zasuje sashen Abah su masa sallama da su Babban Yaya. Kasa tashi AA yayi, har sai da Oum ta mi?e tana murmushi ta kamasa ta mi?ar. Sai kawai ya rungumeta. Harga ALLAH zuciyarsa tai rauni, wai shima yau yayi aure za'a dan?ashi ga matarsa ya bar Oum Winsa da yake manne da ita akoda yaushe, shike nan zai tashi daga saurayi ya koma magidanci. Da ?yar su RK da jikinsu yay sanyi suma suka janyesa. Dan soyayyar Oum da yaran nan uku musamman Ajwaad na taSa zukatan wannan Family Win matu?a. ?agosa Oum tayi ta share masa guntun hawayen sannan ta kamo hannun Modibbo ta dam?a na AA a ciki, sai ta koma ta zauna tana ri?e hawayenta itama. Yau finally ta aurar da autanta yaranta sun gama auren fari sai kuma ga masu burin ?arawa kamar yanda Fawzan yayi.
? ?? Da ?yar su RK suka ja AA dake ta kallon Oum suka fita da shi. Sun wuce sashen Mamy, sai suka samu tana barci, anan ko maimakon AA ya samu faWa da nasiha kamar a sashen Mamy sai su Maman Saheeba suka Sige da habaice-habaice. RK ne kawai ya fahimci inda suka dosa, sauran ko basu kawo komai a ransu ba sai shi AA Win kansa. Dan haka baici komai ba ya mi?e yay musu sai da safe ya barsu da ba?in cikin sharesun da yay. Haka sukaita zage-zage da aibanta Oum da Maanal dama Darma Family gaba Waya har Maanal da danginta basu tsira ba. Sashen Abah shine na uku, daga shi sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain da Hassan Winsa, anan ma nasiha mai ratsa jiki iyayen sukai masa. Tare da jadadada masa ha??o?insa na miji akan matarsa. Sai dabaru na kula da mace ta yanda aure ke ?arko da ikon ALLAH. Daga ?arshe akai addu'a sannan suka taso, sai sashen Babban Yaya. Sun sameshi shi kaWai a falo zaune yana shan shayi yana kallon labarai. Kama AA yay ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Kafin ya Wagosa yana murmushi ya ri?e masa fuska da hannaye biyu. Cike da raWa Babban Yaya ya ce,  Finally yau Autan Oum ya mallaki Lilly na, zata maidashi babban mutum, nan da wata tara su haifa min ?yawawan yara masu kama da su .
? ?? Kunya sosai ta kama AA. Sai kawai ya sake rungume Babban Yaya hawaye na cika masa ido. Dariya babban yaya ya sake yi sauran na tayashi sannan ya zaunar da shi kusa da shi. Shima dai yayma AA nasiha da jadadda masa zama miji na gari a wajen Lilly. Ya rufe da addu'a mai ?arfi. Daga nan sashen Fawzan suka nufa, shi kam sai Nibras kawai suka samu a falo. Duk tayi wani wujiga-wujiga da alama kuma le?ensu take ta window kafin su shigo. Bayan ta gaishesu cikin son danne kanta da ?yar RK yace ta kira musu Fawzan. Tana mi?ewa ma sai gashi yana sakkowa daga sama. Yana zuwa ya rungume AA, cike da raWa yanda kowa baya ji ya ce,  Oh oh yau fa Autan Oum zai shiga daga ciki. Babu dokar Aba a kansa Lilly zata dinga masa TAWAI .
? ? ? ?? Mintsininsa AA yayi, Yaya Fawzan ya ce,  Ouch wane muguntane wanan haka Auta? .? ?
? ?? Cike da sha?iyanci AA yace,  ?anwarka ta koya min .
Yanda yay maganar a fili ya sanya kowa dariya. Dan saika rantse bama shi yay zancen ba, babu wani fara'a a tare da shi. Yaya Fawzan yakai zaune yana faWin,  Shike nan na yafe maka kaci albarkacin Lilly, zauna na maka nasiha dan bazan yarda da rashin mutuncin mijin ?anwa ba lallasaka zanyi idan kai mata ko kallon banza eh . Babu wanda bai dara ba yanzu ma. Kafin Fawzan yaci serious kamar ba shi ba ya fara ma AA nasiha shima, daga ?arshe suka rufe da addu'a sannan ya sallamesu. Koda AA yace shi bazai masa rakkiyar ba? Sai Fawzan yay shiru, sai da yaga kamar AA ya ?waSe fuska sannan ya mi?e yace  Muje taSararre kawai. Yanzu dai zamu huta muma Lilly ta kwasa .
? ?? Lokacin da suke ficewa idon Fawzan ya sauka akan Nibras dake Soye ?ar?ashin bene tana kuka sosai. Kansa kawai ya girgiza yay gaba hannunsa ri?e dana AA. Shima AA Win sarai yaga Nibras Win, amma ya basar kamar bai ganta ba. Sauran ko babu wanda ya lura sam..

? ? ? Wani irin daddaWan ?amshi mai sanyaya zuciya da sauke gajiya ne ya fara musu sallama a falon, musamman ga AA daya fara shiga. Gaba Waya falon ya Wauki wani irin ?yau mai ?ayatarwa daka kallesa ka san a lallai gidan amarya kazo. Duk zama su RK sukai kowa na sauke numfashi, dan ba ?aramin daWi ?amshin gidan yay musu ba. AA zai

02, January 2026
Hafsat

Masha allah yayi albarka ya raya xuri a muna ilmantuwa

11, November 2025
Aisha

👍✨

11, November 2025
Aisha

😂

11, November 2025
Aisha

👍

11, November 2025
Aisha

Wow Allah ya Karo basira littafi yayi👍

06, November 2025
Oumshukura

I want download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login