Showing 42001 words to 45000 words out of 215774 words

Chapter 15 - AJIYA A DUHU 3 End Hausa Novels By Billyn Abdull .doc

wadda sukai a baya ta ?uruciya musamman ga ita dake ?arama sosai, tunda ko acan bayan tasan nagaba yay gaba, kawai dai ita dashi haWuwar jini ce bawai abotar kai da kai ba. A hankali ta fara takawa zuwa inda yake tamkar mai koyan tafiya, maimakon zama a visitors chair kai tsaye inda yake zaune ta zagaya. Kusa da shi kaWan taja ta tsaya, hakan datai ya saka ziciyar AA ?ara gudu a ?irjinsa, dama can bawani aiki yake yi ba, dan ji yay bama ya fahimtar komai. A yasan shima yana da kishi mai karfi a kanta, dan haka yake so ta gane kuma ta kiyaye, duk da kuwa sanin hakan a gareta game da shi ba sabon abu bane ba ai, amma ya fahimci kamar ta manta ne....
? ? ??  AA! .
? Ta kirashi da sunan da abakinta ya fara jinsa, ga shi nan kuma ya bisa dan wasu da yawa a yanzu bama su iya tantance ainahin sunansa sai AA Darma kawai. Duk da harbawar da zuciyarsa ta shiga yi a ?irjinsa saboda tasirin kiran sunan nasa da tai bai kalleta ba, aikinsa kawai yake kamar gaske.?
? ? ? ??  Besty fushi fa ba ?yau! .
? ? Ta faWa tana le?a fuskarsa cike da shagwaSa. Nan ma tamkar dutse haka yay mata shiru. To itama fa zuciyar tata ta fara hawa, dan haka tai shiru kawai tana kallonsa. Tsahon mintuna uku taga ba kulatan zai yi ba kawai saita nufi barin wajen. Karan farko ya Wago ido ya bita da kallo, itako ta wuce fuuuu alamar dai itama ta hau sama. Shima ai yasan yanda ya tsani yay magana ai masa shiru haka itama ta tsani Wabi'ar. Har ita zai nunama zuciya da kishi, ita jiya ba Waukarta yay ya kaita wajen budurwarsa ba dan wula?anci, amma mitace masa, sai shi dan kawai ya ganta da abokin aikinta, to shike nan kuma bazata dinga mutunci da mutane ba'a Companyn?.
? ? ? Tana gama fita yay wani irin watsar da file Win hannunsa akan desk Win, sai kuma ya buga shi ya juya kujerar ya kalla bangon wajen daya kasance glass....

? ? Manaal na shiga office Winta kayanta ta tattara tsaf tai fitowar ta. Duk inda ta gitta gaisheta akeyi, ita sai suka ma ?ara bata haushi. ALLAH ya sota sanda ta fito harabar kamfanin duk ana ciki, sai securitys ne kawai ke Wan kai-kawo. Suma duk wanda ta gitta sai ya gaisheta, drivern AA dake cikinsu yana hira yana hangota ya taso da sauri, gaisheta yay, tare da faWin bara ya Wakko mota. Amma sai sai tace da fa shi karya damu su Abah na jiranta a waje. Jin tace Abah ya sashi dakatawa, haka ta fita a ?afa a kamfanin.
? ? ? ? Tun fitiwarta harabar kamfanin sosai idon AA ya sauka a kanta, har maganarta da drivern sa da gaisuwar da securitys suke mata duk ya gani, kawai dai baya jin mi suke faWa ne. Ji yay zuciyarsa ta ?ara hasala. Da ga zaunen da yake bazai iya ganinta ba yanzu saboda ta fita a kamfanin, dan haka ya mi?e tare da matsawa jikin gilashin. Sai ko ya hangota ta tsaida wata taxi ta shiga. Idan AA yace zuwa yanzu zuciyarsa batai kumburar da take neman fashewa ba yayi ?arya. Shi yarinyar nan zata wula?anta da mutuncinsa a garin nan tana matarsa ta shiga taxi, shi zatama laifi ta fishi zuciya kuma. (Amma ai ta zo lallashinka ka?i kulata) Wani sashe na zuciyarsa ta faWa. Ji yay kamar ya kaima zuciyar naushi, amma dai ya daure, wajen ya bari gaba Waya, sai ma ya koma rukunin kujeru ya zauna, dan yasan ko aikin yace zai cigaba shirme kawai zaita tafkawa.........
'?

-N3R(OFN' 'DDGO HNFP9REN 'DRHNCPJDO.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
_ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro._





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________



.........Maanal dai ta isa gida lafiya abinta, ALLAH ya sota a wallet Winta akwai kuWi, haka ta cire ta biya shi tai ciki. A ?asan ma?oshi AA dake bibiyarta ta hanyar GPS tracker ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya kife wayar a saman desk ya kwantar da kansa da bayansa jikin kujerar da yake ya lumshe idanunsa.
Maanal na shiga Nuratu da Hajiya Turai na fitowa a mota, da alama zuwansu kenan. Idon Maanal ne ya sauka akan ?aton akwatin da Bola ke fitarwa a booth. Tayi niyyar wucewarta, sai zuciyarta ta gargaWeta da hakan kodan Hajiya Turai dake babbar mace. Dan zata iya sa'a da Ammiensu koma ta girmeta. Duk da ta lura da kallon banzar da Nuratu ke mata saita watsar da ita, kaWan taWan matsa kusa da su ta gaida Hajiya Turai dake kallonta itama irin kallon ?asan idon nan na ?urulla. Bata kuma jira jin a yanda ta amsa mata ba tai gaba abinta. Daga Nuratun har Hajiya Turai binta sukai da kallo, tsakin da Nurry taja yasa Hajiya Turai faWin,  Ko itace Maanal Win? .
? ?? Baki Nurry ta taSe, a gadarance ta ce,  Waifa Momy itace, shegiya ba?ar banza, tana tafiya tana murguWama mutane Wuwawu dan asan tana da su ko .
? ? ?? Hajiya Turai dake bin Maanal Win da kallo har yanzu ta ce,  Yoni Baby yarinyar nan ma nada muhimmanci kuwa a gidan nan? Kamar fa daga wajen aiki take a ?afa alamar taxi ce ta ajiye ta, ace duk motocin gidan Darma ace surukar gidan na hawa taxi kuma matar AA duk dukiyarsa .
? ? ??  To Momy dama ba aikin asiri bane yasa ta shigo gidan, tunda ya riga ya gama da ita tun a titi wace soyayya zata gani kuma. Ba dai na shigo gidan ba, sauran asirin ma dan ubansa zan ?arasa karyashi ne. Ana gama bikinmu zata ware dan sai ta sha ?i ba?in cikin shagalin da za'a sha kafin na sa ya saketa.
? ?? Sosai Hajiya Turai ta sanya dariya. Tamkar wasu ?awaye ta bata hannu suka tafa. Daga hakan suma suka nufi sashen Mamy cike da nishaWi...

? Oho Maanal ma bata san sunai ba, tana shiga sashen Oum sama ta wuce abinta. Ta samu Oum da ba?uwa. Maanal ta gaishe da matar ?ya?y?yawa da ita. Itako cike da kulawa take tambayar Oum,  Hajiya Fateema ko Wiyar tamu ce? .
? ? Murmushi Oum tayi, ta ce,  Itace Hajiya Shuwa .
? ? ?  Kai Masha ALLAH, yarinya dirarriya ?ya?y?yawa haka ga nutsuwa. A ruwan idon autanki bai tafi a banza ba ashe, ashe yasan miya taka, Waya yake son tsamowa a cikin dubu, to ALLAH ya sanya albarka a cikin auren nasu .
? ?? Oum dake ta murmushi ta ce,  Amin ya rabbi . Sai kuma ta kalla Maanal dake nufar hanyar bedroom.  Baby wai har kun tashi ne? Ina Bestyn naki? .
? ? ? Cikin danne komai Maanal taima Oum bayanin su an basu damar zuwa suyi shiri ne saboda tafiyar jibi. Oum ta ce,  Tofa tafiyar ta tashi ke kenan? .
? ? Manaal ta ce,  Eh Oum. daga haka ta shige ta barsu. Hajiya Shuwa da gaba Waya Maanal Win ta ?ara birgeta ta ce,  Kai masha ALLAH, jiba yanda ta saki jiki dake kamar ba surukai ba, haka naso mu rayu da Amisha amma ?awayen banza sukai mata huWubar tsiya. Shiyasa yanzu nace masa aure zai ?ara, dan na gaji da Sacin rai wlhy Hajiya Fateema. Wani lokacin idan aka juya min kan yaron nan ko kallo ban isheshi ba, shiyyasa kikaga nai tafiyar nan marocco ko sallama ban miki ba. Shi ma kansa bai san na tafi ba sai bayan kwana uku .
? ? ?  Kiyi ha?uri Hajiya Shuwa jarabawa ce, kowa da irin tasa kuma. Amma Amisha ta bama kowa mamaki, dan nidai ina ganinta shiru-shirun nan banyi zaton haka a gareta ba. Ni kaina yanzu saboda tasan yanda muke dake bata shigowa gidan nan, har mukaci bikin nan muka tsare bata le?o ba, shima Ameer Win Fawzan yace baije mana Waurin aure ba, shine ma ya haWasu faWa shine yake cemasa ai dama Amisha tace ba sonsu muke ba, nice ke zugaki kina wula?anta masa mata. Nace ma Fawzan ya barsa baya cikin hayyacinsa ne kawai .
? ? ?? Kwafa Hajiya Shuwa tayi, ranta na sake mata zafi da halin da Wan nata yake Waya tilo namiji. Su Hajiya Shuwa sune makwaftan su Oum ta hannun damar su, asalinta ?ar marocco ce girman Libya, daga can mijinta Alhaji Mubarak KT ya aurota, yara biyu suka haifa kacal a duniya, Ameer shine babba, bayan haihwarsa ma ta jima bata sake ba harta ha?ura ma sai ga ciki. Sunyi farin ciki sosai ita da mijinta, ALLAH ya sauketa lafiya ta haifi mace ?ya?y?yawa itama suka saka mata Ameerah, bayan haihuwar Ameera bata sake ba kuma, yarinyar nada shekara goma a duniya ALLAH yayma Alhaji Mubarak rasuwa sakamakon bugawar zuciya na dare Waya daya samu. Shi Win babban Wan gwagwarmaya ne kuma Wan siyasa ta wani gefen, duk da dai bai saki jiki a siyasar ba gaba Waya. Yana kuma kasuwanci sosai. Ya tafi ya barta da yaran su biyu, ita ga cigaba da kulawa da rayuwarsu har girma, duk da dai sanda ma ya rasu Ameer har ya shiga University yana first year Winsa. Ameera ce ke primary 4. Tasha wahala da dangin mijinta dan dukiyar ?a?anta komawa tai tsole musu ido, acewarsu ai Wan uwansu ne ya tara, bazai yiwu ya aurota daga wata ?asa ba daga sama tazo ta mamaye komai, aiko suka ?ulla mata akan ta basu yara su cigaba da ri?ewa da dukiyar ita kuma ta koma ?asar ta. Hankalinta ya tashi, dan babu wanda take tausayi irin Ameera. Nanfa ta shiga faWi tashin ganin hakan bata kasance ba, tana neman taimakon abokan mijinta, amma mi, kowa sai ya nuna sai in ga amince zata auresa zai yi hakan, wasu ma da iskanci suke zuwa mata. A cikin wannan kai-kawon nata ne suka haWu da Ambassador Aliyu Darma, ta dalilin nashi abokin shima da ya kasance abokin mijin Hajiya Shuwa. Shima dai yayi mata maganar banza ne, ta fito ranta a Sace shine sukaci karo da Abah da yaji komai dan yay ?o?arin shiga office Win ne yaji kalaman abokin nasa sai ya tsaya, amsar da Hajiya Shuwa ta bashi yay matu?ar birgesa, data fito kuma ya ganta mace mai kamala da nutsuwa. Baice mata komai ba a lokacin ta wuce ya shige, bai kuma nunama abokin nashi yasan komai ba shima. Sai da ya dawo gida ya sanarma Oum komai, hankalinta ya tashi baiwar ALLAH harda kukanta. Itace ta ?arfafa Abah suka shirya taimakon Hajiya Shuwa, washe gari taje har gida ta sameta, zuwa ranar kuma Hajiya Shuwa ta sallama ma dan Oum ta sameta tana haWa kayanta, tana shirya nasu Ameera domin dan?ama dangin uban nasu kamar yanda suka bu?ata.  ALLAH sarki na ALLAH baya ?arewa duk rintsi ____wannan itace kalmar da Hajiya Shuwa ta faWa bayan Oum ta gama mata bayanin abinda ya kawota, daga haka ta rungume Oum tana kuka...
? ?? Wannan shine sanadin tarayyar su, Abah ya tsaya mata akan komai har sai da aka mata tsakani da dangin Alhaji Mubarak, aiko sai akaita gulma ai sonta Abahn keyi, dan har Mamy ma ba sonta take ba ta kuma tsargu da hakan, musamman data ro?a Abah ya sayi filinsu dake a kusa da su dan lokacin su suna a zone 4 ne. Da farko Aban ya?i, gudun kar ace ta basu ne shiyyasa suka taimaketa, sai da taita ro?onsa da tabbatar musu zamansu a kusa zai zamar mata garkuwane sannan ya amince. ?aton filine amma sai da Abah ya ?ara da wani a bayansu shine ya gina wannan babban gidan suka zama makwaftan juna. Anta jira aga Abah ya aure Hajiya Shuwa amma akaji tsit har ma shekaru suka ja. Ameera ita ta Wan ragema Oum kewar Maanal a lokacin, har ALLAH yasa ta wuce karatu waje ita, yanzu haka tana can, amma tana gab da dawowa ?asar haihuwarsa. Amisha ?ar ?anwar Hajiya Shuwa ce, auren zuminci ne ita da Ameer, duk da kuwa su sukaga juna suka gina soyayyar su ba iyayen suka haWasu ba. Farkon auren kowa nata yabon Amisha musamman data kasance da suffar mutane masu shiru-shiru da ha?uri, sai da tafiya tai tafiya sai komai ya canja, yanzu Amisha aya take gasama Hajiya Shuwa a hannu, har takai wataran idan ta juye kan Ameer Win sai ya manta da Hajiya Shuwa na a gidan ma tare da su gaba Waya. Sai ta dage da addu'a sai abin ya sassauta. Watanni kusan bakwai kenan abubuwa suka rikice a tsakaninsu shine kawai ta tattara ta wuce marocco sai jiya ne take dawowa, bata nan akai bikin su AA Win, sai bayan wucewarsu aiki ta shigo shine suketa hira da Oum Win dan ?awaye ne sosai...
? ? ? Ba?i da aka kira Hajiya Shuwa a waya cewar tayi ya sata tafiya gida, sai lokacin Maanal ta fito falon, tayi wanka abinta fes sai ?amshi take. Takardar da aka basu a wajen aiki ta bama Oum Win, tare da zama gefenta ta Waura kanta a kafaWarta. Shafa kan nata Oum tayi tana murmushi, cike da kulawa ta ce,  Ko azumin ya fara duka? .
? ? ? Shaf Maanal ta manta da ?aryar azuminta, ta kalla Oum tana dariya.  Lah Oum ?arya fa nayi dama babu wani azumi Wazun ban son karyawa ne kawai .
? ? ?? Idanu Oum ta zaro waje, sai kuma ta dungure kan Maanal Win tana dariya itama.  ALLAH ya shirya kin Baby na to da har yanzu bata canja hali ba . Dariya itama Maanal tayi, tare da Soye fiskarta a jikin Oum Win. Itama Oum na cigaba da dariyarta ta ce,  To aiko tare zamu shiga kitchen yanzun nan idan munyi sallar zuhur .
? ? ? ?? Haka Win kuwa akai, bayan Oum ta kammala duba takardun ta ri?e a hannunta akan zata nunama Abah, duk da dama ta masa bayani akan tafiyar amma bai ce mata komai ba. Salla suka je sukayi, koda suka fito kai tsaye kitchen suka nufa, sun fara aikin kenan Mamy da Hajiya Turai da Nurry suka shigo sashen. Oum ce kawai ta fita suka gaisa, basu wani jima ba Hajiya Turai tace bara ta wuce tunda taga Oum Win aiki suke itama zataje wani waje ne. Godiya Oum tai mata, sunzo zasu fita Maanal ta fito ta gaishesu. Tana kallon hararrata da Nurry take bata kula ba ta koma kitchen Win abunta. Sai da zasu fita Mamy ke faWin,  Lafiya ?arki ta dawo aiki da wuri haka yau? .
? ? ?  Lafiya Lau, daga office Win ne aka basu damar zuwa suyi shirin tafiya ne .
? ? ? Sai Mamy ta rasa ina zata kamo zancen tafiya kuma. Amma bata nema ba'asi ba dan tana son su fita su ?arasa zancensu da suke da Hajiya Turai. Ba kuma tason ma Hajiya Turai ta fahimci bata san da zancen da Oum Win keyi ba dan yanzu ta gama cika mata baki akan batun dawowar Maanal a taxi. Ta nuna itace ta kafa sharaWin sai dai Maanal ta hau taxi amma ba motocin gidan ba, shiyyasa sukaga hakan. (Mamy an iya ?ayya>?#?=?O?)
? ? Tsulum Nuratu taja ta tsaya tana faWin,  Momy bye nima zan zauna taya Oum girki, bara naje wajen sis.. Manaal Win . Daga haka ta juya ciki ta nufi kitchen tabar su Oum na murmushi. Duk da dai abinda Nuratun tayi ya bama Mamy takaici, amma sai ta danne... Maanal na cikin aikinta ita da su Inte dake musu ?an yanke-yanke a work table Nurry Win ta shigo. Ko kallon inda take Maanal batai ba, sai su Inte ne ke gaisheta a girmamame, itako tana amsa musu a yamutse. Sun riga sun san halinta shiyyasa basu wani damu ba. Dai-dai nan Oum ta dawo, dan haka Nuratu ta nufi wajen Maanal cike da makirci tana faWin,  Sis.. Maanal mizan tayaki da shi? .
? ? ? ? Wani shegen murmushi kawai Maanal ta saki tana kallon Nurry Win a tsakkiyar ido, a zuciyarta faWi take, (Yarinya ai indai makirci ne baki yar a ?asa ba, idan kuma kikace ni dake ta haka zamu buga wasan ?asa zaki sha kuwa a hannuna). A fili kam maimakon bata amsa fruits da za'a gyara ta nuna mata da hannu fiskarta da murmushin har yanzu. Oum data ?araso inda Maanal Win take ta ce,  Yauwa gyara su kam Nuratu, sai a gama da wuri dan yau nasan Auta a jigace zai dawo gidan nan ba'a aika abincin rana ba hira da Hajiya Shuwa ta Wauke min hankali .........
'?
? ? ??

_Hhhhh gaskiya Maanal baki ?yauta ba, ya zaki bama Nurry Winmu gyaran fruits >?#?>?#?_



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________

........Matu?ar ti?e Nuratu takaici yayi, amma bata da damar cewa bazatai ba tunda itace ta kawo kanta. Sannan duk iskancin nan nata mugun shakkar Oum

02, January 2026
Hafsat

Masha allah yayi albarka ya raya xuri a muna ilmantuwa

11, November 2025
Aisha

👍✨

11, November 2025
Aisha

😂

11, November 2025
Aisha

👍

11, November 2025
Aisha

Wow Allah ya Karo basira littafi yayi👍

06, November 2025
Oumshukura

I want download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login