Showing 24001 words to 27000 words out of 75493 words

Chapter 9 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

wani sakon inda Zakin ba zai iya shiga ba.

Gama aiyana hakan ke da wuya sai ta juya da sauri cikin zafin nama ta falfala da azababben gudun tsiya. Ai kuwa sai suka kasa tsere ita da Zakin. Kafin ta yi taku uku sai ta ga Zakin ya daka tsalle ya dira a gabanta, amma kafin shi ma ya juyo ya fuskance ta tuni ta juya ta sauya hanya tana mai ratsawa ta cikin bishiyoyi, shi ma ya tuso ta a baya. Sai dai ka ga Zakin yana banke bishiyoyin suna ratattakewa tamkar daka su aka yi a cikin Turmi. Kai ba ma bishiyoyi kadai ba, duk dutsen da Zakin ya bangaza da kirjinsa take yake tarwatsewa.

Nan fa aka ci gaba da tsere tsakanin Zakin da Zarina ta dage iya karfinta tana gudun ceton ranta dana dan uwanta wanda ke goye a bayanta. In ba don Zarina ta kasance tana da zafin nama ba gami da juriya da kuma sanin daji ba da tuni Zakin ya gama da ita.

Wani lokacin idan ta hango kwazazzaɓo sai ka ga ta bi ta cikinsu da gaiya saboda shi ma Zakin yana shiga cikinsu sai ka ga karfin gudunsa na raguwa. Babu abin da ke daga mata hankali face ganin duk sa'adda ta waiga bayanta sai ta ga ashe Zakin yana daf da ita kamar ma a ko yaushe zai iya wangame bakinsa ya hadiye ta.

Haka dai Zarina ta ci gaba da masifaffen gudu irin wanda ba ta taɓa yi ba a rayuwarta. Shi kuwa Zakin ya a ci gaba da binta babu alamar zai gaji.

Sakamakon shiga ko ina da take yi ne jikinta ya rinka buguwa da duwatsu da bishiyoyi ta rinka samun raunika a jikinta wani lokacin ma sai dai ta ji ice ya soke ta ta kwala uban ihu. Wani icen ma idan ya soke ta karyewa yake yi a jikinta sai dai tana cikin gudun ta zare shi, kana ganin jini na fita a jikinta amma ba ta fasa gudun ba. Sai da aka shafe sa'a daya da rabi ana wannan yseren gudu tsakanin Zakin da gimbiya Zarina, shi bai cim mata ba ita kuma ba ta tsere masa ba. A sannan ne jiri ya fara dibarta ta kama tangadi, amma saboda naci da tsaurin rai ba ta daina gudun ba.

Tana cikin wannan hali ta je ta gwaru da wata bishiya ta fadi kasa ta dinga mirginawa a kasa. Ai kuwa sai Zakin ya dako wawan tsalle da nufin ya diura akanta.

Abin da zakin bai sani ba shi ne, ashe sun iso daf da wani katon rami mai tsananin fadi da zurfin tsiya.

Zakin na dira akan Zarina sai santsi ya kwashesu duk su biyun suka gangara cikin wannan rami. Zarina ta kurma uban ihu a lokacin da ta ga ta fada cikin wannan rami. Shi ma Zakin sai ya wangame bakinsa ya kwarara uban gurnani domin ya tabbatar da cewa shi ma halakarsa ce ta zo, domin komai zai iya faruwa idan suka isa karshen wannan rami da nisan kasansa ya wuce a misalta shi.

Sai da suka shafe. lokaci mai dan tsawo suna fadawa can kasan ramin. Tun kafin su isa iskar da ke kadawa mai karfi ta sa duk suka sume ita da Zakin.

Bisa rashin sa'a sai Zakin ya fado akan wani dogon kahon dabba wacce ta dade da mutuwa a cikin ramin. Take kahon ya fasa gadon bayan Zakin ya bullutso ta cikinsa. Zakin ya kwarara uban ihu na karshe a rayuwarsa sannan ya ama gawa.

Ita kuwa Zarina akan wata ruɓaɓɓiyar gawar dabbar daji ta fado da rub da ciki.
Sai bayan sama da sa'a biyu sannan Zarina ta farfado daga dogon suman da ta yi tun sa'adda take fadawa kasan ramin. Idanunta ne suka fara budewa a hankali, ta yi arba da gawar wannan Zaki a gabanta. Nan take farin ciki ya lullube ta.

Jin nauyi a bayanta ne ya sa ta tuna cewa duk wannan gumurzu fa da tayi tana dauke da dan uwanta sarkin Farisa ne a bayanta.

Cikin hanzari ta kwanto sarkin Farisa daga bayan nata, ta shimfideshi a kas a lokacin da kansa ya langabe idanunsa suka kafe kuma gaba daya jikinsa ya sandare.

A zaton Zarina dogon suma ya yi, don haka sai ta mike zumbur ta rufa izuwa cikin wani kwazazzaɓo dake cikin ramin inda ruwan sama ya dan taru. Zarina ta kwarfo ruwa a cikin tafin hannunta ta zo ta watsa ruwan a fuskar sarkin Farisa amma sai ta ga ko motsi bai yi ba. Al'amarin da ya firgita ta kenan. Ta shiga girgiza shi tana yi masa fifita har izuwa tsawon lokaci amma shiru babu labari.

Cikin dimaucewa ta sa bakinta cikin nasa ta hura masa iska, duk dai a banza. A wannan lokaci ne ta tabbatar da cewa rai ya yi halinsa. Kawai sai Zarina ta takarkare ta kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba daya da amsa kuwa sannan ta kama gawar ta rungume a kirjinta ta sake fashewa da matsanaicin kuka. Allah Sarki, rayuwa ba ta da tabbas!

Duk wanda ya ga Zarina a wannan hali da ta shiga dole ne ya tausaya mata matuka musamman idan ya yi la'akari da tsananin wuyar da ta sha ta tserar da rayuwar abokan tafitarta daga sharrin wannan Zaki, amma sai duk abin ya zamo ma ta a banza tun da ga shi ita ta rasa dan uwanuta wanda a dalilinsa ne kadai take son ta je kogon Darul Iksina.

Wannan shi ne abin da ya faru ga gimbiya Zarina bayan Zakin da ya far musu ya hallaka tare dan uwanta Sarkin Farisa a cikin wannan rami ma matukar zurfi.

*********************

A can inda Zarina ta baro sauran abokan tafiya kuwa, al'amarin ba kyan gani, domin su duka sun yi fata-fata a cikin jini, kuma dayansu bai farfado ba sai bayan shudewar sa'a daya da rabi.

Jarumi Imran ne ya fara farfadowa. Koda ya ga naman ciyarsa ya fafe yana lage-lage sai yai sauri ya kamoshi ya hade sannan ya dauko jakar guzurinsa da ke zagaye a kugunsa ya fiddo zare da allura ya shiga dinke raunin. Yana dinkin yana ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yake ji.

Ko kadan hankalinsa bai kai kan sauran abokan tafiya ba saboda ta kansa yake. Sai da ya gama dinke raunin tsaf ya shafa magani akai sannan jini ya daina zuba.

A wannan lokaci ne ya dawo cikin haiyacinsa. Koda ya dago da kansa ya dubi sauran abokan tafiya ya ga halin da suka shiga sai ya kamu da tsananin bakin ciki kuma ya fashe da matsanaicin kuka. Babu abin da ya fi dugunzuma hankalinsa face ganin yadda Haiman da Shaharan suka rasa hannayensu dai-dai.

Har izuwa wannan lokaci babu wanda ya sake farfadowa daga dogon suman da suka yi. Imran ya sake daga kansa ya dubi can inda Shadira take ya hango ta baje a kas jini a hancinta da bakinta ko motsi ba ta yi, sai ya zata ta mutu. Cikin firgici ya yunkura don ya mike tsaye yaje wajenta amma sai ya kasa domin cinyarsa tai masa nauyi ko motsa ta bai son yi. Kawai sai ya kama jan jikinsa a kas, a haka ya je har inda Shadira ke kwance ya dago ta ya rungume ta a kirjinsa ya sake fashewa da matsanaicin kuka.

Yana cikin wannan hali ne ya ji Shadira ta numfasa. Cikin tsananin farin ciki ya janye ta daga cikin kirjinsa ya dubi fuskarta sai ya ga ta bude idanunta har tana yi masa murmushi.

Imran ya sake rungume ta, duk su biyun suka fashe da kukan farin ciki. A dai-dai wannan lokacin ne mahaifiyar Imran da Lumaira matar Sarki Haiman suka farfado. Koda mahaifiyar Imran ta ga danta a raye kuma rungume da masoyiyarsa Shadira, sai ta cika da dumbin farin ciki ta kama kyalkyala dariya.

Ita kuwa Lumaira matar Haiman ya yin da ta ga mijinta da dungulmin hannu kwance a cikin jini face-face sai ta dafe kai ta runtuma uban ihu sannan ta cicciɓe shi ta rungume tana mai tsala kuka domin zatonta ya dade da mutuwa. Ba zato ba tsammani sai ta ji ya kawo numfashi. Cikin murna ta kwantar da shi a kas tayi sauri ta cire mayafin jikinta ta naɗe dungulmin hannun nasa domin har a sannan bai daina zubar da jini ba. Sai duk suka kurawa junansu idanu suna masu zubar da hawaye. Duk da yake ba ganinsa take ba.

Daga can sai ta dube shi ta ce, "Ya kai mijina hakika in da na san za ka rasa hannunka a wannan tafarki da na kashe kaina domin kada ma ka yi wannan tafiya domin lafiyarka ta fiye mini rayuwata."

Koda jin wannan batu sai Haiman ya sake fashewa da kuka kamar ba zai daina ba, daga bisani ya dube ta ya ce, "Ya ke masoyiyata ki tuna cewa kin yi mini komai a rayuwa kuma ba dan ke ba, da ban rayu ba na kawo i yanzu.
Sai da muka shafe shekara da shekaru muna jinya sakamakon kaunarki da kulawar da kike ba ni. Ashe kuwa raina da lafiyata ba su da wani amfani muddin ban faranta miki rai ba.

Na rantse da darajar kaunar da ke tsakanina da ke, lafiyarki tafi rayuwar dukkanin mutanen duniya a wajena kuma ina tabbatar miki da cewa, koda zan rasa daya hannun nawa sannan na rasa duka kafafuna biyu muddin ina numfashi a doron kasa zan iya tafiya da jan ciki, to fa ba zan janye ba bisa wannan tafarki na nema miki lafiya har sai idan babu ruhi a jikina. Koda jin wannan batu sai Lumaira ta sake rungume shi suka kankame juna suna masu ci gaba da kuka.

A dai-dai wannan lokaci ne Shaharan da abokan tafiya kowa ya farfado. Koda Shaharan ya ga ya rasa hannunsa guda kuma ya ga bai ga Zarina da dan uwanta Sarkin Farisa ba sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya rushe da kuka.

Cikin hanzari ya yage rigar jikinsa ya nannade dungulmin hannunsa don tsaida jini sannan ya ruga izuwa cikin dajin yana kwallawa Zarina kira.

Da kyar da siɗin goshi sauran abokan tafiya suka mimmike zaune sannan masu kwarin cikinsu suka shiga yiwa sauran magani.
Shi kansa Boka Muzaffar sai da aka yi masa dinki a cikinsa. Shi kuwa Sarki Laffaru a gadon bayansa aka yi masa dinki.

Gaba dayansu dai ba su dawo cikin hayyacinsu ba sai bayan shudewar sa'a uku. A wannan lokaci ne kowa ya ji nadama bisa baro kasarsa don zuwa kogon Darul Iksina domin zukatansu duk sun karaya sun san cewa abu ne mawuyaci dayansu ya isa kogon Darul Iksina a raye duk da cewa saura daji daya kacal a gabansu.

Al'amarin jarumi Shaharan kuwa, lokacin da ya nausa cikin daji yana kwala wa Zarina kira, sai ya ji shiru kamar maye ya ci shirwa.

Bisa sa'a kuwa sai ya bi wannan hanya wacce Zarina da wannan Zaki suka bi suna masu kasa tsere kuma sai ya yi ta bin sawunsu.

Duk da haka sai da ya shafe sa'a biyu da rabi yana ta bilinbituwa a cikin daji yana dada ci gaba da kwala wa Zarina kira amma bai ganta ba kuma bai ji ta amsa kiran ba.

Kwatsam! Sai ya iso gaban wannan raini mai zurfi wanda Zarina ta fada. Yana lekawa cikin ramin kuwa ya hango ta zaune dirshan rungume da gawar dan uwanta Sarkin Farisa tana kuka. Shaharan ya sake kwala ma ta kira har sau uku amma ko dago kai ba ta yi ba bare ta kalle shi.

Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan ya rasa abin da zai yi.

Bayan Zarina ta sha kuka ta gaji har hawayenta ya kafe sai ta dago kai ta dubi Shaharan wanda ke can saman ramin ta yi masa wani irin kallo mai nuna alamun bankwana har tana daga masa hannu. Kawai sai ta zare wata zabgegiyar wuka a kugunta ta daga sama za ta cakawa kanta a ciki. Tsawar da Shaharan ya daka mata ne ya sa ta kasa lumawa kanta wukar ta dago kai ta dube shi a lokacin da hawaye ya zubo ya masa.

Shaharan ya bude muryarsa da karfi ya ce, "Ya ke masoyiyata kiyi sani cewa, kina kashe kanki nima zan fado cikin wannan ramin na kashe kaina, domin ban ga amfanin rayuwata ba muddin babu ke. Haka dai Shaharan ya ci gaba da gayawa Zarina kalmomi masu taushi irin wadanda ke kwantar da zuciya amma da kyar da sidin goshi ya shawo kanta ta fasa kashe kanta.

A sannan ne fa ya fara tunanin hanyar da zai bi ya iya fito da ita daga cikin wannan mugun rami mai zurfi, amma sai dabara ta kwace masa.

Koda ya ga ya rasa yadda zai yi sai ya ce da ita ta zauna ta jira zai koma inda ya baro sauran abokan tafiya domi su taru su hada tunani da basirarsu waje daya a sami yadda za a iya fito da ita a cikin ramin".

Zarina ta ce, "Shi ke nan za ta jira ya je ya dawo". Shaharan ya ce shi ba zai tafi ba har sai ta yi masa alkawarin cewar ba za ta kashe kanta ba bayan tafiyarsa ba. Nan take Zarina ta yi rantsuwa da darajar kaunar da take yiwa dan uwanta marigayi cewar ba za ta kashe kanta ba. Sannan Shaharan ya juya ya falfala da gudu izuwa inda ya baro su Muzaffar.

Da isarsa gare su kuwa ya tarar kowa ya dawo cikin baiyacinsa amma duk sun yi zugum-zugun kamar suna zaman makoki. Nan take ya shaida musu duk abin da ya faru ga jaruma Zarina cewar ita ce sanadin mutuwar wannan katon Zaki wanda yai musu wannan mugun lahani kuma dan uwanta Sarkin Farisa ya mutu.

Da jin haka sai dukkaninsu suka kamu da tsananin tausayin Zarina, wasu kuma suka kama kuka, wasu kuma suka kama zubar da kwalla. Jim kadan sai Boka Muzaffar ya dubi can gefe daya inda Aljani Marhabul Zaurus ke kwance dauke da dokin Shaharan kawai sai ya ga ashe shima ya rasa rabin fuka-fukinsa guda, shi kuma dayan fuka-fukin ya tsage a tsakiyarsa tamkar an sa Zabira an yanka tsakiyar takarda. Koda ganin wannan al'amari sai Boka Muzaffar ya yi ajiyar zuciya sannan ya dubi Shaharan ya ce, "Babu wanda zai iya fito da Zarina daga wannan rami face Aljani Marhabul Zaurus kuma ga shi shi ma yana da nakasa amma ban sani ba ko zai iya a hakan ba, mu je gare shi mu ji".

Nan take Boka Muzaffar ya yunkura ya mike tsaye da kyar, shi ma Shaharan ya kama kugunsa da hannun nasa daya jal da ya rage suka durfafi inda Aljani Marhabul Zaurus ke kwance. Da isarsu garshi sai Boka Muzaffar ya dube shi ya daka masa tsawa ya ce, "Ya kai Marhabul Zaurus ina son ka sauke wannan doki da ke bayanka ka tafi izuwa can inda Zarina ta fada rami ka dauko ta tare da gawar dan uwanta ka kawo su nan gare mu.

Sa'adda Aljani Marhabul Zaurus ya ji wannan umarni sai fuskarsa ta yamutse kamar zai fashe da kuka sannan ya dubi Muzaffar cikin tsananin damuwa ya ce, "Ya shugabana shin ka dubi halin da nake ciki kuwa yanzu? Na rasa rabin fuka- fukina guda, daya fuka-fukin kuma ya tsage. Ina tabbatar maka da cewa yanzu ba zan iya daukarku ba ku duka har ma na yi doguwar tafiya da ku a sararin samaniya."

Koda jin haka sai Boka Muzaffar ya sake dakawa Aljani Marhabul Zaurus tsawa a karo na biyu ya ce, "Ai ba cewa na yi ka dauke mu yanzu mu ci gaba da tafiya ba, cewa na yi ka je ka dauko Gimbiya Zarina da gawar dan uwanta kawai ka dawo da su nan."

Da jin haka sai Aljani Marhabul Zaurus y mika hannunsa guda ya dauke dokin Shaharan daga kansa ya sauke shi a kas sannan ya bude fuka. fukansa da kyar ya yunkura ya tashi sama yana tambal-tambal kamar zai fado kasa. Kai da gani ka san cewa ba karamin namijin kokari ya yi ba har da ma ya iya tashi sama.

A haka dai ya luluka izuwa can sama yana tsala matsanaicin gudu har ya ɓace da gani. Bayan kamar dakika dari da ashirin kacal sai ga Aljani Marhabul Zaurus ya dawo dauke da Zarina da kuma gawar dan uwanta rungume akan kirjinta ta kankame gawar tana ta kuka.

Al'amarin da ya kara karya zukatansu ke nan, su duka kowa ya kamu da tsananin tausayin Gimbiya Zarina aka kama kuka.

Sai a wannan lokaci ne Zarina ta lura cewa Shaharan da Haiman sun rasa hannayensu ďai ďai. Nan fa bakin ciki ya sake lulluɓe ta, ta fashe da sabon kuka, ya zamana cewa babu wanda ba ya zubar da hawaye a wajen.

Nan dai masu sauran kuzari a jikinsu suka haka rami aka binne Sarkin Farisa sannan aka yanke shawarar a zauna a wajen har tsawon mako uku sannan a ci gaba da tafiya.

Boka Muzaffar ne ya kawo wannan shawara Koda jin haka sai jaruma Rahila ta ce, "Wai shin mene ne ma amfanin ci gaba da wannan tafiya tamu?

Shin har yanzu kuna sa rai ne cewa za mu isa kogon DARUL IKSINA a raye ne? Ku dubi fa halin da muke ciki a yanzu, wasunmu sun nakasa, nakasar da har abada babu warkewa don haka fiye da rabin karfinmu babu shi. Dajin da ya rage a gabanmu shi ne dajin da ya fi kowanne daji haɗari, inda wannan katuwar Kunama take mai tsananin gudun tsiya wacce babu wanda muke sa ran zai iya tsere mata a cikinmu face jarumi Shaharan, kuma ga shi shi ma ya sami nakasa ya rasa hannunsa guda. Ta yaya kuke tsammanin zai iya gudun da zai iya tserewa wannan Kunama a haka har ya ja ta izuwa cikin wannan kogi inda za ta hallaka?"

Sa'adda Rahila ta zo nan a zancenta sai kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Boka Muzaffar ya dubi jarumi Shaharan ya ce, "Ya kai abin dogaronmu a cikin daji na biyar, ka ji abinda Rahila ta ce, shin gaskiya ne ba za ka iya yin gudu ba kamar yua ya kamata sakamakon wannan nakasa da ka samu?"

Koda jin wannan tambaya sai Shaharan yai ajiyar zuciya ya ce, "Ko shakka babu rashin Wannan hannu nawa sai ya rage mini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login