Showing 51001 words to 54000 words out of 75493 words

Chapter 18 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

ban taɓa ganinki ba a cikin wannan hali".

Sa'adda Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya sai ta yi shiru tana mai sunkui da kanta kas ta ki cewa komai. Kawai sai Sarki Nashmir ya zare wata wuka a jikinsa ya yanki kansa a damtsen hannun hagu, jini yai tsartuwa akan fuskar Ramlatul Siyam ya sake daga wukar zai daďa yi wa kansa rauni sai Ramlatul Siyam ta yi wuf ta rike hannunsa kuma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Saboda me za ka cutar da kanka?

Nashmir ya dube ta a lokacin da idanunsa suka cika da kwallah ya ce, "Ina amafanin rayuwata idan har ba zan iya yi miki maganin matsalar da ta same ki ba? Lallai akwai wani babban al'amari wanda kika daɗe kina ɓoye min shi, lallai sai kin sanar da ni shi a yau kuma a yanzu. Idan kuwa kika ki sai dai a fitar da gawata daga cikin wannan ďaki naki.

Koda jin wannan batu sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta rungume Sarki Nashmir ta fashe da wani sabon kuka sannan ta ce, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa na dade ina yin wani mugun mafarki amma ban taba sanar da kai ba.

Wannan Aljani da ka nuna mini a madubin tsafinka shi nake gani a cikin mafarkina kuma ana nuna mini cewa ya zo har cikin gidan sarautarmu ya yaki Dakarunka an yi kazamin yaki wanda ya zamo sanadin asarar miliyoyin rayuka da dumbin dukiya har sai da dukkan ginin gidan nan ya fadi kasa kuma gagarumar gobara ta kama ko ina. Ina ji ina gani wannan Aljani ya shiga tsakanina da kai ya raba mu ya dauke ni yai sama da ni a lokacin da kai kuma kake cikin wani mugun hali ka kasa koda mikewa tsaye".

Koda Gimbiya Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai Sarki Nashmir ya takarkare ya kwarara uban ihu. Al'amarin da ya firgita gabadayan jama'ar da ke cikin gidan sarautar ke nan. Dakaru suka rugo da gudu izuwa cikin turakar rike da makamai tsirara.

Da shigowar Dakarun suka ga rauni a hannun Sarki amma kuma babu kowa a cikin turakar sai su biyu jal shi da 'yarsa sai suka cika da dumbin mamaki.

Nan take Sarki Nashmir ya yi wa Dakarun inkiya suka juya da baya suka fice suka kullo kofar. Sarki Nashmir ya dubi Gimbiya Ramlatul Siyam cikin tsananin takaici ya ce, "Ya ke 'yata hakika kin yi babban kuskure da kika boye min wannan al'amari. Inda ace kin sanar da ni tun a ranar da kika fara yin mafarkin da tuni na dauki matakin gaggawa na kawar da waďannan abokan gaba nawa.

Yanzu dole ne na zuba ido na ga abin da zai faru tsakaninsu da Sarkin yakina Najwar. Idan har bai sami nasarar hallaka su ba dole ne na zauna na jira karasowarsu sannan ayi ta ta kare amma kafin sannan yanzu zan shiga cikin dakin halwar tsafina domin na binciko mafita. Duk abin da ake ciki kada ki kuskura ki fito daga cikin wannan daki face ni da kaina na zo na ce ki fito. Ina tabbatar miki da cewa in dai kina cikin wannan daki babu wata masifa ko wani tsautsayi da ya isa ya same ki."

Koda gama fadin haka sai Sarki Nashmir ya mike tsaye ya juya ya fice daga cikin dakin da sauri ya nufi inda dakin tsafinsa yake, ya bar Gimbiya Ramlatul Siyam a zaune cikin tsananin tashin hankali da rudewa.

Wannan shi ne abinda ya faru a Birmin HINDU bayan Sarki Nashmir ya tura Dakarunsa na farko izuwa dajin Hiuzurl Aswad domin su kashe su Aljani Maruful Dauwaz.

***
Al'amarin su Aljani Maruful Dauwaz kuwa, bayan sun shafe rabin sa'a a kwance suna hutawa sai Aljani Maruful Dauwaz ya karanta waďansu dalasiman tsafi. Nan take wata irin murtukekiyar sarkar tsafi ta fito daga cikin karkashin kasa ta nannaďe hannayensa, kafafunsa da fuka-fukansa sannan ta daure su tamau yadda ko motsa su ba zai iya ba. A sannan ne ya dubi Rahila da Sarki Laffaru ya ce, "Ku zo ku gyara mini karayar kasusuwan fuskata".

Koda jin haka sai Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce, "Je ka ka karyo mini dogayen itatuwa kamar guda bakwai masu dan kwari."

Nan take Laffaru ya tafi domin cika umarnin. Koda ya hau kan wata bishiya ya fara karyo itatuwan sai takaici ya kama shi saboda ya tuna cewa shi fa Sarki ne mai cikakken iko wanda duniya take tsoro amma yau ga shi mace tana sa shi aiki, tana ba shi umarni yana bin umarnin cikin rawar jiki.

Nan dai ya hanzarta ya je ya kai wa Rahila wadannan itatuwan. Tana karɓar itatuwan sai ta hau kan kirjin Aljani Maruful Dauwaz ta zauna kai ka ce akan wani katon tsauni take. Take ta umarci Maruful Dauwaz da ya bude bakinsa.

Ba tare da gardamar komai ba kuwa yawangame bakin nasa mai fadi tamkar rijiyar mutanen da. Rahila ta zura hannayenuta a cikin bakin.

Kodata kamo kasusuwan fuskar tasa wadanda suka kakkarye ta fara gyarawa tana daure su da itatuwa sai Maruful Dauwaz ya fara kwarara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogi. Ihun nasa ya haddasa wanzuwar iska mai karfi a cikin dajin wacce ta rinka zubar da bishiyoyi kasa.

Hakan bai sa ta tausayawa Maruful Dauwaz ba sai ta ci gaba da aikinta har ta kammala. Saboda tsananin azabar da Maruful Dauwaz yaji sai da hawayen wuya ya zubo masa.

Bayan Rahila ta gana gyara wa Maruful Dauwaz karayar kasusuwan fuskarsa ne suka bude jakar guzurinsu ita da Sarki Laffaru suka fiddo da abinci suka ci.

Shi kuwa Maruful Dauwaz sai ya gangara izuwa cikin wata katuwar korama ya kafa bakinsa ya kama shan ruwa, sai da ya sha ruwan mai yawan gaske wanda adadinsa ya kai duro ashirin da biyar sannan ya fito daga cikin koramar ya koma wajen su Rahila ya kishingida suka fara hira, inda Maruful Dauwaz ya dubi Rahila ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki me ya sa na ga kamar kina cikin damuwa ne kin kasa sakin jikinki ki ci abinci sosai?"

Koda jin zuciya wannan batu sai Rahila ta yi ajiyar sannan ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa ba komai ba ne ya sa ka ga ina cikin wannan hali ba face abubuwa biyu da suka dame ni.

Abu na farko shi ne, hankalina a tashe yake bisa ganin irin mummunan yakin da muka yi da Dakarun Sarki Nashmir wanda da kyar muka tsira da rayuwarmu. Tabbas na san cewa har a yanzu fa ba tsira muka yi ba kuma a ko yaushe za mu iya ganin waɗansu mugayen Dakarun nasa.

Saboda haka ni yanzu ina ganin cewa zamanmu ma a nan yana da hadarin gaske. Ko dai mu nemi wajen buya ko kuma mu tashi mu ci gaba da tafiyarmu in ya so mu yi jinyar jikin namu akan hanya.

Abu na biyu da yake damuna shi ne, yawan tunowa da sauran abokan tafiyarmu waɗanda muka baro a can kogon Darul Iksina.

Hakika ina matukar tausaya musu musamman idan na tuno da irin tsananin wuyar da muka sha tare da su da yadda wasunsu suka rasa masoyansu. Yanzu ga shi mun baro su a cikin kogon na Darul Iksina kuma babu yadda za su iya fitowa.

Yanzu shi ke nan duk burinsu ya yanke ke nan, sun hallaka bisa wannan tafarki?".Koda Rahila ta zo nan a zancenta sai ta fashe da matsanaicin kuka. Al'amarin da ya karya zuciyar Aljani Maruful Dauwaz da Sarki Laffaru ke nan su ma suka kama zubar da hawaye saboda tausayi! Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba. daga can sai Maruful Dauwaz ya dubi Rahila ya ce, 'Ya ke wannan 'yar Sarki, hakika kin zo da shawara mai kyau bai kamata mu ci gaba da zama anan ba domin masu iya magana sun ce, 'Zama waje daya tsautsayi ne in ji kifi'. Yana da kyau mu nemi maboya inda za mu yi jinyar jikinmu domin ina tabbatar muku da cewa ni kaina ba zan iya ci gaba da tafiya ba mai tsawon koda rabin sa'a a cikin wannan hali da nake.

Batun abokan tafiyarku kuwa da muka baro su a can kogon Darul Iksina ni kaina na yi matukar bakin ciki bisa halin da suka kasance kuma zan so ace sun kubuta sun fito daga kogon a raye amma maganar gaskiya abu ne mai matukar wuya. Na yı muku alkawari idan har mun sami nasarar shiga fadar Sarki Nashmir mun dauko Gimbiya Ramlatul Siyam lallai sai mun biya ta tsibirin Darul Iksina mu gani ko abokan tafiyar taku sun fito."

Koda Rahila da Laffaru suka ji wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe su suka ji kaunar Aljani Maruful dauwaz ta karu ainun a cikin zuciyarsu. Duk su biyun sai suka fada kansa suka rungume shi suna masu yi masa godiya.

Maruful Dauwaz ya ce, "Yanzu sai mu tashi mu tafi neman inda zamu buya a cikin dajin nan domin mu ya jinyar kanmu.

Za mu yi wasu tambayoyi kafin mu sako kashi na Hamsin da uku. Zan yi farin ciki idan na samu gamsassun bayanai daga gare ku wanda shi ne zai kara mini kwarin guiwa har mu samu mu shiga littafi na Huďu. Na gode!

Kafin daya daga cikin su Rahila ya ce wani abu sai Maruful Dauwaz ya sure su su biyun ya aza su a gadon bayansa sannan ya yunkura da kyar cikin matukar karfin hali ya tashi sama ya kama yawo a cikin dajin yana neman inda za su бuya.

Bai daďe da fara shawagi a sama ba kuwa sai ya hango wani katon tsauni mai yawan kofofin kogo. Kai tsaye Maruful Dauwaz ya durfafi wannan tsauni ya dira a cikin kofar kogon. Dirarsa ke da wuya sai ya yi tsafi wutar ice ta baiyana a kan hannayensa. A sannan ne Rahila da Laffaru suka sauko daga kansa suka tsaitsaya suna kallonsa kawai. Maruful Dauwaz ya dube su ya ce, "Ku zo mu duba ko ina a cikin dukkan kogon da ke kan wanna tsauni domin mu tabbatar da lafiyar tsaunin.

Ba tare da gardamar komai ba kuwa su Rahila suka amince da wannan shawara. Sai da ska shafe sa'a uku cur suna ta shige da fice a cikin ramukan da ke kan tsaunin amma ba su ga halitta guda daya ba a ciki, koda kuwa kwaro ko tsuntsu.

Abin da ya fi daure musu kai shi nc, duk ramin da suka shiga sai su ga ya bulle zuwa cikin wani, sannan sun ga wadansu irin manya-manyan tukwane irin na mutanen farko a cikin kogon gami da gidajen itatuwa da shimfidu na fatun dabbobi iri-iri, wata fatar ma ba su taɓa ganin irin ta ba kuma dukkan wadannan abubuwa sun yi kura matuka kuma yana ta lullube su alamar cewa an shafe shekaru masu yawa ba a yi amfani da su ba.

Koda ganin wannan al'amari sai Aljani Maruful Dauwaz yai ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas akwai maridan da suka yi rayuwa a cikin wannan kogo shekaru aru-aru da suka shude".

Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru yai sauri ya goge yanar da ke kan wani gadon ice sannan ya yaye shimfidar da ke kansa sai suka yi arba da wani katon kwarangwal na wani maridi. Hatta Aljani Maruful Dauwaz sai da ya firgita da ya ga wannan kwarangwal domin iya tsawon rayuwarsa a duniya bai taba ganin halitta mai girma kamarsa ba, don shi kansa ya fi shi tsawo a tsaye sau hudu.

Sarki Laffaru ya zare takobinsa ya kwankwashi kashin kwarangwal din, kawai sai ya jinjina kai ya ce, "Wannan kwarangwal din ya fi shekaru dubu uku da mutuwa a cikin wannakogo".

Cikin mamaki Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce, Kai kuwa yaya aka yi ka san wannan ilimi?".

Laffaru ya yi murmushi ya ce, "Ai lokacin da nake da karfin sihirin tsafina na yi bincike matuka akan wannan fanni na sanin dadewar abu a duniya, don haka na sami ilimi mai yawa akan hakan".

Gama fadin hakan ke da wuya sai Aljani Maruful Dauwaz ya dauki gawar wannan kwarangwal daga kan gadon icen yai jifa da ita izuwa jikin kogon dutse ta rugurguje sannan ya sake kade kurar da ke jikin fatar buzun da aka shimfida. Akan buzun ya kwanta akan gadon yana mai cewa, "Ni kam na sami wajen kwanciyata ku ma sai ku nemi naku. Lallai a cikin wannan kogo za mu yi jinyarmu tsawon mako biyu. Hankalina ya kwanta da wannan kogo domin ko wani mugun abun ne ya zo mana in dai muna cikin nan zai yi wuya ya iya hallaka mu cikin sauri".

Gama fadin hakan ke da wuya sai Maruful Dauwa ya rufe idanunsa, nan take barci ya dauke shi sakamakon tsananin wahalar da ya sha a bakin gumurzun da ya yi da Aljani Sharkamuza.

Kash! Rashin sani ya fi dare duhu! Inda Aljani Maruful Dauwaz ya san abin da zai faru da bai kwanta akan wannan gadon ice har bacci ya dauke shi ba.

Domin kuwa, yin barcinsa ke da wuya Aljani Barukul Masrur ya sauka a dajin dauke da sadauki Najwar suka duro a daida inda aka yi wannan bakin gumurzu tsakanin su Aljani Sharkamuza da su Aljani Maruful Dauwaz.

Ai kuwa suna dira suka yi arba da gawar Aljani Sharkamua. Koda suka ga irin kisan da aka yi masa, wato suka ga zururun rami ta cikin idonsa guda har bayan keyarsa sai suka cika da mamaki kuma zuciyarsu ta kama tafarfasa kamar za ta kone.

Nan take Aljani Barukul Masnur ya shaki numfashi sannan ya dubi sadauki Najwar ya ce, "Ya shugabana na ji kamshin bil'adama guda biyu a cikin wannan daji da kuma kanshin Aljani dan uwana guda daya".

Koda jin haka sai sadauki Najwar yai murmushin mugunta ya ce, "Abin da nake so da kai shi ka tashi sama ba can kololuwa ba ka dinga kaďa fuka-fukanka a hankali yadda ba za a ji motsinka ba har mu gano inda su Maruful Dauwaz suke. Sai dai kawai mu yi musu MAMAYAR BAZATO! Aljani Barukul Masnur ya yi dariya ya ce "Hakika ka zo da shawara mai kyau ya shugabana".

Gama fadin hakan ke da wuya Barukul Masnur ya bude fuka-fukansa ya yi sama yana mai daďa bude kofofin hancinsa domin ya jiyo kamshin su Maruful Dauwaz ya gano a inda suke.

A cikin kogon dutse kuwa, lokacin da Rahila da Sarki Laffaru suka ga Aljani Maruful Dauwaz ya kama barci har da yin munshari mai nauyi sai su ma su Rahila suka sami wuri suka kishingida domin su huta sosai kasancewar har a sannan raunikan jikinsu na damunsu da zogi.

Koda kishingiɗar ta su sai Rahila ta kurawa Sarki Laffaru idanu tana murmushi kawai, al'amarin da ya matukar ba shi mamaki ke nan ya dube ta ya ce, "Ya ke matata ta gobe ina dalilin wannan murmushi da kike yi a gare ni?"

Koda jin wannan tambaya sai Rahila ta sake yin murmushi ta ce, "Ba komai ne ya sa ka ga ina yi maka murmushi ba face ina aiyanawa a raina cewa ga shi mun yi aure har mun sami kwanciyar hankali".

Da jin haka sai Laffaru ya gyada kai cikin alamun karayar zuciya, ya budi baki don ya ce wani abu sai kawai suka ji wani abu mai tsananin nauyi ya fado kan tsaunin da suke ciki take saman tsaunin ya rugurguje ya rufto ciki.

Aljani Maruful Dauwaz ya farka cikin tsananin razana, amma kafin ya yi wani yunkuri sai ya ji an yi masa muguwar damka an bankare hannayensa da kafafunsa ta baya da karfin tsiya, ya ji kamar za a kakkarya shi. don haka sai ya kwarara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yake ji. Ya yi iya kokarinsa ya kufce amma sai ya kasa.

Ba wani bane ya yiwa Marutul Dauwas wannan muguwar damka ba face Aljani Barukul Masnur, hadimin jarumi Najwar.

Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suke cewa, 'Gaba da gabanta, Aljani ya taka wuta. Duk irin gagarumin karfin da Aljani Maruful Dauwaz ke da shi sai ya zamo na banza sakamakon Barukul Masnur ya ninka shi sau uku a karfin dantse.

Koda Rahila ta ga abin da ya faru da Maruful Dauwaz sai ta mike zumbur ta zare takobinta, shi kuwa Sarki Laffaru ko motsawa ya kasa saboda tsananin firgita da ya yi bare ya yi yunkurin zare makami.

Kawai sai suka ga sadauki Najwar ya fado gabansu ta cikin saman tsaunin inda Aljani Barukul Masnur ya faso.

Najwar ya dira a gaban Rahila yana murmushin mugunta a lokacin da ita kuma jikinta ya kama karkarwa.

Sadauki Najwar ya dube ta ya bushe da mahaukaciyar dariya, bayan ya kare mata kallo sama da kasa sai ya ce, "Yanzu ke a haka kike tunanin za ki iya yakata? Ki dubi jikinki fa ki gani kina da manyan raunika har guda uku kuma danyu. Ke ni abin kunya ne ma a ce na yi fada da ke domin sai dai na ci zalinki kawai. Duba fa ki ga halin da abokin tafiyar taku ke ciki. A haka kuke sa ran za ku iya shiga har fadar maigidanmu ku sace 'yarsa ku samo yawun barcinsa. Shi kansa Maruful Dauwaz din da kuka dogara da shi dubi yadda ya zamo tamkar dan tsako a hannun Shirwa, Ina tabbatar miki da cewa wannan Aljani da ya bankare Maruful dauwaz yanzu akwai irinsa sama da guda dubu dari a cikin fadar shugabana. Ya ya za ku yi da su?"

Koda jin wannan batu sai Rahila ta dubi sadauki Najwar cikin karfin hali da taurin zuciya ta ce, "Wannan kuma matsalarmu ce ba taka ba. Ka bai wa Aljaninka umarnin ya saki Maruful Dauwaz ko na afka muku na kawar da ku".

Da jin haka sai sadauki Najwar ya sake bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu ya ce, "Ai sai ki jarraba mu gani".Kafin ya gama rufe bakinsa tuni Rahila ta dako tsalle sama daga inda take tsaye ta kai masa wawan sara a wuya. Ko gocewa bai yi ba ya tsaya cak a inda yake. Koda takobin Rahila ta sari wuyan sadauki Najwar, sai nan take ta narke ta zama ruwa kuma ruwan ya dige a kasa ya zamana cewa kotar takobin ce kadai ta yi saura a hannunta. Kawai sai Rahila tayi jifa da kotar takobin sannan ta gyara tsayuwarta tana mai dunkule hannayenta biyu, alamar tana son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login