Showing 75001 words to 75493 words out of 75493 words

Chapter 26 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

ya girma ya zama gawurtaccen jarumi kuma Sharlisa ta mallaka masa mashin Galilul Haras ya fito farautar Ziya'ul Hak domin ya kashe ta sannan ya zo har nan dajin Rauful Masnur ya kama Sarki Laffari".

Koda jin wannan labari sai hankalin Laffaru da na Ramlatul Siyam ya dugunzuma ainun.

Ramlatul Siyam ta fara zubar da hawaye ta ce, "Yanzu ya za a yi mu yi maganin faruwar wannanal'amari?"

Aljani Maruful Dauwaz ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Hanya daya ce za mu bi mu yi maganin wannan matsala.

Dole ne ita ma Ziya'ul Hak ta yi shiri ta tafi farautar jarumi Shaddadu domin ta hallaka shi, amma fa idan yana tare da Mashin Galilul Haras ba ta isa ta iya yi masa komai ba, amma tunda shi yaro ne ai mun fi shi wayo da dabara.

Ni zan yi wa Ziya'ul Hak rakiya a cikin wannan tafiya domin na zamo mai ba ta kariya da shawarwari akan yadda za mu sami nasara akan Shaddadu koda kuwa zan rasa rayuwa ta.

Ku sani cewa wanzuwar Ziya'ul Hak a doron kasa shi ne abin da ya hana ni kashe kaina, saboda ta dauke mini kewar masoyiyata.

Yanzu sai ku shirya mana wannan tafiya ku yi bankwana da ita."

Nan take Ramlatul Siyam ta kirawo Ziya'ul Hak ta sanar da ita duk abin da ake ciki.

Ba tare da ɓata lokaci ba Ziya'ul Hak ta yi bankwana da iyayenta tana kuka su ma suna kuka suka rabu suna masu yi mata fatan nasara.

Nan take Ziya'ul Hak ta hau kan bayan Aljani Maruful Dauwaz shi kuma ya bude fuka-fukansa ya tashi da ita sama suka luluka a cikin gajimare!

A nan muka kawo karshen littafin MAZAN JIYA na uku (3)
*****************

WANNE IRIN BAKIN GUMURZU ZA A YI IDAN JARUMI SHADDADU DA JARUMA ZIYAUL HAK HAR SUKA HADU?

SHIN SHARLISA ZA TA CIKA BURINTA AKAN SARKI LAFFARU?

YAYA KARSHEN RAYUWAR JARUMI SHADDAD ZA TA KASANCE?

SHIN ZAI YI SOYAYYA KUWA A RAYUWARSA?

YAUSHE NE ZA A JI LABARIN SADAUKI HULKAS NA BIRNIN ROMANIYA WANDA SHI NE CIKON JARUMI NA UKU DAGA CIKIN MAZAN JIYA?

Mu hadu a littafin MAZAN JIYA 4 (Kashi na hudu) don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari mai matukar kayatarwa.

Muna neman afuwa ga makaranta bisa tsayin labari, hakan ya faru ne sakamakon tsayin da hikayar take da shi.

Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.

ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI
(The King of Adventure Story)

Ni Maiboko, ina rokon makaranta wannan gawurtaccen littafin, da mu yi kokari mu tasirantu da kyawawan dabi'un da suka siffantu a cikin wannan hikayar.

Mu kalli dalilan da suka sa Maruful Dauwaz ya yi nisan kwana sannan kuma yake samun nasara a kan duk abin da ya sa a gabansa, sabanin gagarumar nadama da tashin hankalin da sarki Lafaru yake a ciki

Rayuwar aljani Maruful Dauwaz abar nazari ce da kwaikwayo duk da ta kasance a cikin hikaya ne.

Aljani Maruful Dauwaz, yana daga cikin dalilan da suka sa nake wannan posting ďin.

A karshe, yiwuwar cigaba da littafi na huďu na alakanta hakan da lissafin lokaci.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login