Showing 42001 words to 45000 words out of 75493 words
Chapter 15 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
da tsananin mamaki bisa yadda Boka Muzaffar ya yaudari sauran abokan tafiyarsa ya jefa su cikin masifa haka.
Bugu da kari, sai hankalinsa ya dugunzuma ainun da ya ji cewar Boka Muzaffar ya mallaki Mashin Galilul Haras domin yana da cikakken tarihin mashin, ya san cewa duk wanda ya mallake shi zai iya mallakar duniya gaba dayanta. Sai da mahaifin Rahila ya shafe lokaci mai tsawo yana juya al'amarin a cikin zuciyarsa sannan ya yi ajiyar zuciya ya dubi Rahila ya ce, "Ya ke 'yata, ki yi sani cewa aikin da ke gabanku ba karami ba ne domain yaki da Sarki Nashmir na Birnin Hindu daidai yake da ninkin wahalar da kuka, sha a dazuzzuka biyar din da kuka ratsa kuka je kogon Darul Iksina. Kuma tabbas babu wani Aljani da zai iya kai ku fadar Sarki Nashmir har ku iya dauko 'yarsa kuma ku samo yawun barcin bakinsa face Maruful Dauwaz.
Ni babban abin da nake ganin cewa ma ba za ku iya samowa ba shi ne, yawun barcin Sarki Nashmir, domin ga yadda na sami labari a wajen masana, Sarki Nashmir bai taɓa yin barcin dare ba kuma a duk tsawon mako guda sau daya yake barcin sa'a shida da rana. Babu takamaiman ranar da ya ware domin yin barcin nasa. Ma'ana ranakun Litinin zuwa lahadi bai ware ranar yin barcin ba a kowacce rana zai iya yin barcin kuma a kowanne lokaci kin ga ke nan, ba karamin dace za ku yi ba ku riski lokacin barcin nasa.
To wai shin ma ta yaya za ku iya shiga Birnin nasa ma bare har ku shiga gidan sarautarsa alhalin duk duniya babu wani wuri da ya kai masarautarsa tsaro? In ba don ba a raba rai da buri ba, da sai na ce ku hakura da wannan bukata domin ban ga yiwuwar hakan ba."
Lokacin da mahaifin Rahila yazo nan a zancensa sai Rahila ta ji zuciyarta ta karaya kuma nan take hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke mata dadi a duniya, amma da ta tuna irin bakar wahalar da suka sha a cikin tafiyarsu ta zuwa kogon Darul Iksina da yadda suka tsira da rayuwarsu a lokacin da basu taɓa zaton samun kuɓuta ba sai ta sake samun kwarin guiwa ta dubi mahaifin na ta ta ce, "Ya kai Abbana kayi sani cewa babu wani abu da zai gagara a wannan duniya, don haka ba na fid da rai ga samun nasara bisa wannan gagarumin aiki da ke gabanmu face ba ma numfashi a doron kasa. Lallai za mu ba iwa Aljani Maruful Dauwaz dama ya shiga halwar tsafinsa ta kwana uku domin ya binciko mana ta yadda za mu fuskanci wannan gagarumar tafiya ta neman ceto rayuwar dukkan mutanen duniya da aljanun duniya daga sharrin azzalumi bakin mugu Boka Muzaffar. In da sauran Sarakunan duniya sun san halin da ake ciki da tabbas sun ba mu hadin kai an hada KARFI DA KARFE an tafi wannan gagarumin aiki".
Sa'adda Rahila ta zo nan a jawabinta sai mahaifinta ya kawo gwauron numfashi da ajiye sannan ya dube ta ya ce, "Ya ke 'yata ina tabbatar miki da cewa da yawan manyan Bokayen duniya sun san halin da ake ciki, kuma sun sanar da Sarakunansu tsananin tsoron Sarki Nashmir ne ya sa kowa ba zai iya hada kai da ku ba.
Duk fadin wannan duniya mutum daya ne wanda inda zai hada kai da ku da sai kun sami nasara farat daya akan Sarki Nashmir.
Ba wani bane wannan mutum face Sharlisa mahaifiyar yaro Shadadd, wanda a nan gaba zai yi shuhura ya zamo gagarumin jarumin da ba shi da sa'a.
Ko hauka ne ya sami Sharlisa ba za ta taбa hada kai da ku ba saboda idan ta yi hakan ba za ta taɓa cika burinta na son daukar fansa akan Sarki Laffaru ba.
A yanzu haka Sharlisa tana nan tana shiri da bincike akan yadda za ta tarwatsa dukkan shirinku, don haka, ku yanzu bala'i biyu ne a gabanku, akwai na Sarki Nashmir kuma akwai na Sharlisa. Shi kansa Sarki Nashmir a halin yanzu yana kan shirye-shiryen yadda zai kwace mashin Galilul Haras daga hannun Boka Muzaffar domin ya san cewa ya dauko mashin daga kogon Darul Iksina kuma in dai ya kammala aikin da yake yi a yanzu acikin dakin halwar tsafinsa na tsawon kwanaki arba'in tabbas sai burinsa ya cika.
Ita ma Sharlisa yanzu hankalinta ya rabu gida biyu, domin tana son ta tarwatsa shirinku kuma tana son ta mallaki wannan sihirtaccen mashi na Galilul Haras.
Saboda haka, BAKIN ARTABUN da za a yi akan wannan mashi yafi karfin masifar YAKIN DUNIYA gaba daya. Ya ke 'yata, ki yi sani cewa tun kafin ku iso nan na yi bincike a cikin tawa halwar tsafin na ga dukkan wannan al'amari."
Yayin da mahaifin Rahila ya zo nan a jawabinsa sai hankalin Rahila ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, ta ji kamar ta tashi a sannan ta tafi izuwa masaukin Sarki Laffaru domin ta sanar da shi halin da ake ciki su dunguma su je bayan gari wajen Aljani Maruful dauwaz shi ma su sanar da shi don su san irin sabon shirin da ya kamata su yi bisa wannan al'amari.
Daga can kuna sai ta taushi zuciyarta ta ce a cikin ranta, "Tunda dai Maruful Dauwaz ya ce zai shiga halwar tsafi ta kwana uku domin ya yi nasa binciken ya kamata na saurara na ji abin da binciken nasa zai samo".
Kamar yadda aka tsara haka al'amuran suka gudana; wato sai da Aljani Maruful Dauwaz ya kwana uku a cikin halwar tsafi bai sake ganawa da su Gimbiya Rahila ba.
A ranar kwana na uku da yammaci ya kammala bincikensa. Koda ya ga sakamakon binciken sai ya dimauce ya firgita ainun, bai san s'adda ya kwarara uban ihu ba ya kama gwara kansa da kasa.
Al'amarin da ya janyo karamar girgizar kasa ke nan a gaba daya Birnin na Shaufil. Gidaje suka rinka rugujewa suna danne mutanen da ke cikinsu, garin ya yamutse aka yi ta guje-guje da iface-iface kai ka ce duniyar ce za ta tashi. Har sai da Aljani Maruful Dauwaz ya daina ihu sannan komai ya lafa.
A wannan lokaci Maruful Dauwaz ya daddauje fuskarsa bai sani ba, har ta yi kaca-kaca da jini. Kawai sai ya fashe da kukan bakin ciki.
Yana cikin wannan hali ne Rahila, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila suka zo gare shi a sukwane bisa dawakai cikin halin firgici domin a zatonsu yakin bazata ne ya ɓarke tsakaninsa da wakilan Sarki Nashmir ko wakilan Sharlisa.
Koda isowar su Rahila sai suka iske Maruful Dauwaz shi kadai a zaune babu alamar ya yi yaki da wata runduna, amma ga fuskarsa a daddauje, jini yai masa kaca-kaca, kuma yana ta rusa kuka. Cikin dimauta duk su ukun suka yi sauri suka sauko daga kan dawakansu suka zube kasa gabansa. Rahila ta dube shi cikin tsananin damuwa ta ce, "Ya kai Sarkin Sadaukan duniya, mene ne ya faru gare ka muka riske ka a cikin wannan hali?"
Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful Dauwaz ya fusata ya daka musu tsawa. Nan take suka dimauce, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila basu san sa'adda suka saki fitsari ba a wando. Ita kanta Rahila gaba daya jikinta ne ya kama karkarwa tamkar an tsoma ta a cikin ruwan kankara.
Aljani Maruful Dauwaz ya dube ta a fusace ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki, ki yi sani cewa kun cuce ni da kuka je kuka fito da ni daga cikin kogon Darul Iksina. Inda na san abin da zai faru ke nan da na kashe kaina tun a can kogon na Darul Iksina sa'adda kuka zo mini da bukatarku.
Hakika a cikin bincikena na gano masifu da tashin hankali iri-iri. Tarzoma za ta yawaita a doron kasa, kuma za a yi asarar miliyoyin rayuka da dukiya. Kun riske ni a cikin bakin ciki kuma gashi kun sake jefa ni a cikin wani sabon baki cikin wanda ban san ranar karewarsa ba."
Koda Aljani Maruful Dauwaz yazo nanjawabinsa sai ya sake fashewa da matsanaicin kaka, Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin su Rahila ke nan suka rasa abin da ke musu dadi a duniya.
Tsawon dakiku masu yawa dayansu bai ce affan ba. Daga can sai Rahila ta dago kai ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Haba ya koai GWARZON MAYAKI mai DAKAKKIYAR ZUCIYA! Shin ka manta ne cewa in dai akwai rai, akwai buri, kuma akwai nasara da sa'a? Karfin dantse da karfin sihiri ba su ne kadai suke tabbatar da nasara ba, akwai tsananin rabo da tsananin sa'a. Ina son ka tattaro hankalinka a waje daya, ka sani cewa idan bala'i ya kunno kai babu wata hanya da za a iya kawar da shi face a rungume shi.'
Ka tuna cewa idan ma ba ka fito ba daga cikin kogon Darul Iksina sai wannan masifa ta faru, gwara ma da ka fito din wata kila ka iya taбlbuka wani abu wajen kokarin kawar da ita.
Ka tuna da alkawarin soyayyar da ke tsakaninka da masoyiyarka marigayiya Rashmin. Shin idan ka ki karanta wasiyyar da ta bar maka ka yi ma ta adalci ke nan? Ta mutu da bakin cikin rashin mallakarka kuma ta mutu da bakin cikin rashin cika burinta guda daya jal a duniya. Me zai sa ba za ka sallama rayuwarka ba wajen ganin ka cika wannan buri nata bayan ranta, domin ka bar abin tarihi wanda babu wani masoyi da ya taba yiwa masoyiyarsa a doron kasa".
Lokacin da Rahila ta zo nan a dogon jawabinta sai jikin Aljani Maruful Dauwaz ya yi sanyi gabadaya, yai shiru ga barin kuka kuma ya sake shiga sabon kogin tunani. Daga can sai ya dago kai ya dubi Rahila ya yi murmushi mai taushi a gare ta ya ce, "Madallah da jaruma mai dumbin hikima da hangen nesa.
Ki yi sani cewa wannan jawabi da kika yi mini na karshe ya zare mini dukkan tsoro daga cikin zuciyata domin kin tuno mini da wata kalma wacce mahaifina ya taɓa gaya mini tun ina yaro karami ban fi shekara bakwai ba.
Kalmar ita ce; "Ya kai dana, duk wuya, duk rintsi kada ka goyi bayan rashin gaskiya. Ka rike amana, ka zamo mai cika alkawari. Idan ka yi haka za ka yi tsawon rai a duniya, kuma makiyanka ba za su sami nasara akanka ba."
Har yau, har gobe ina amfani da wadannan kalmomi ba zan taɓa watsi da su ba. Tabbas yanzu na sami kwarin guiwa kuma ina ji a jikina kamar ni kadai zan iya tunkarar duk mayakan duniya muddin ban saɓawa wannan nasiha ta mahaifina ba
Abinda nake so da ku shi ne, daga yanzu ku je ku fara shiri, ni kam na gama nawa. Lallai gobe da sassafe za mu tashi mu durfafi Birnin Hindu domin aikata wannan gagarumin aiki da ke gabanmu!!"
Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a zancensa sai Rahila, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila suka sake cika da tsananin farin ciki.
Nan take suka yi wa Maruful Dauwaz godiya sannan suka yi masa sallama akan cewa za su koma cikin gari domin su fara shirye-shiryen wannan gagarumar tafiya.
Maruful Dauwaz ya yi murmushi ya ce,. "Ma za ku aikata hakan lallai zaku dawo da safe ku riske ni cikin jiranku kawai".
Nan take suka mike tsaye suka kama Dawakansu suka hau suka zabure su da gudu izuwa cikin gari.
A wannan rana sai da Rahila da Sarki Laffaru suka kwana suna tanadin kayan yaki iri-iri, kai ka ce miliyoyin Dakarun yaki za su diba su tafi da su. Har sai da gari ya fara wayewa ba su rintsa ba Bayan sun gama tara kayan yakin a waje guda, sai Sarki Laffaru ya kurawa kayan yakin idanu. Nan take idanunsa suka ciko da kwalla. Kafin ya ankara tuni hawaye ya fara sartu akan kumatunsa. Yayin da Rahila ta gan shi a cikin wannan hali sai ta cika da tsananin mamaki kuma hankalinta ya tashi don haka sai ta mike tsaye ta zo gabansa ta tsugunna tana mai rike hannunsa ta ce "Ya kai mijina na gobe, ina dalilin zubar wannan hawaye naka?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Laffaru ya yi ajiyar zuciya gami da share hawayensa sannan ya ce, "Ya ke matata ta gobe, ki yi sani cewa yau ne ranar farko a rayuwata da na ji na yi nadama bisa abubuwan da na aikata a baya.
Ki sani cewa da can ni gawurtaccen jarumi ne kuma SADAUKI, sannan GWARZON MAYAKI wanda gabadayan Sarakunan da ke nahiyata suke tsorona kuma suke yi min biyayyar dole, amma yau ga shi an wayi gari ko Kura ba zan iya kashewa ba a daji da hannuna.
Ba ni da sauran karfin dantse a jikina kuma ba ni da sauran karfin sihiri, Sharlis ta raba ni da duk wadannan abubuwa kuma mugun halina ne ya jefa ni a cikin wannan yanayi.
Lokacin neman gafara a wajen Sharlis ya wuce a gare ni, ba ni da sukuni ko sauran kwanciyar hankali face na auri Gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarki Nashmir na Birnin Hindu. A sannan ne karfin damtsena da na sihirina zai dawo amma duk da haka ba zan iya kare kaina ba daga sharrin dana SHADDADU face na haifi 'yar da za ta zamo mashahuriyar BASADAUKIYA.
Yaushe ne wannan rana za ta zo? Yanzu fa shekaruna sun haura arba'in. Yaushe ne zan sami kwanciyar hankali da nutsuwa a rayuwata? Tabbas yanzu ne na gane cewa zalunci da son zuciya ba sa haifar da komai a rayuwa face asara da nadama. Yau ga shi na rasa mulkina, dukiyata da kimata a duniya, kuma na yi hijirar dole na bar mahaifata ina garari a cikin duniya ba tare da na san makomata ba."
Koda Sarki Laffaru yazo nan a zancensa sai ya fashe da matsanaicin kuka. Nan take Rahila ta kamu da tsananin tausayinsa har itama hawaye ya zubo ma ta, kawai sai ta rungume shi a karon farko tun haduwarsu tana mai shafar gashin kansa kuma tana rarrashinsa. Al'amarin da yasa Sarki Laffaru jin wani gagarumin farin ciki ya baibaye shi domin bai taɓa zaton zai sake samun wani mutum da zai tausaya masa ba a rayuwarsa.
Bayan gari ya waye sosai sai Rahila da Sarki Laffaru suka yi gagarumar shigar yaki. Idan mutum ya dubi Sarki Laffaru a wannan lokaci ya ga irin shigar da ya yi da kuma irin kirar da Allah Ya yi masa ta sadaukantaka sai ya dauka cewa shi kadai zai iya yakar kasa guda. Amma ga wanda ya san sirrin al'amarin sai dai ya yi masa dariya, domin huhun-ma'ahun ne, da wanzuwarsa a filin yaki gwara ma a ajiye dutse wanda ba shi da rai, wata kila abokin gaba ya yi tuntuɓe da shi.
Lokacin da su Rahila suka gama kintsawa sai mahaifinta ya zo gare su domin su yi bankwana. Tun kafin mahaifin nata ya karaso daf da ita, ita da shi suka fara zubar da hawaye.
Rahila ta karasa gare shi a guje ta rungume shi kuma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Ya kai Abbana an zo an raba ni da kai a karo na farko bisa niyyar cewa zan tafi don cika burin rayuwata amma ga shi har yanzu burin bai cika ba. Yanzu ga shi zan sake rabuwa da kai a karo na biyu. Tabbas wannan ita ce rabuwarmu ta karshe domin idan na dawo na dwo ke nan ba za mu sake rabuwa ba. Ka kasance mai yi min fatan samun sa'a da nasara."
Koda jin wannan batu sai shi ma ya fashe da kuka ya ce, "Ya ke 'yata, tabbas zan kasance a cikin yi miki fatan samun nasara dare da rana har ki dawo daga wannan gagarumar tafiya. Ki tuna cewa ni ma dukkan burina ya dogara akan samun nasararki saboda ke ce kadai 'yata a duniya. Ba ni da burin da ya fi na ga aurenki kafin cikar ajalina domin na sami jikoki wadanda za su yada zuri'ata a doron kasa bayan rayuwata. Yanzu ga shi ba za ki yi aure ba face kun sami nasara a wannan gagarumin yaki da za ku tafi. Babu wanda yake da tabbacin za ku sami wannan nasara amma in dai da rai, akwai rabo."
Koda jin wannan batu sai Rahila ta sake kankame mahaifinta a jikinta tana mai daďa rushewa da kuka kuma ta ji kamar ta fasa wannan tafiya.
Da kyar Sarki Laffaru ya janye Rahila daga jikin mahaifinta ya dora ta a kan doki shi ma ya hau wani dokin sannan wasu Dakaru suka kwashi dukkan kayan yakinsu suka yi musu rakiya izuwa bayan gari inda Aljani Maruful Dauwaz ke jiransu. Da zuwansu kuwa suka iske Aljani Maruful Dauwa a tsaye cikin wata irin gagarumar shigar yaki irin wacce ba su taɓa gani ba a rayuwarsu.
Maruful Dauwaz na sanye cikin waɗansu bakaken kayan karfe na riga da wando. Hatta fuka- fukansa ya lulluɓe su da bakin karfen, sannan a kugunsa akwai wata zabgegiyar takobi mai tsananin tsawo, fadi da tsinin tsiya, gami da kaifin gayawa jini na wuce. Ita kadai takobin sai sheki da walwali take yi tana dallare idanun wanda duk yai arba da ita.
Sannan a wuyansa ya rataya wata garkuwa wacce aka yi ta da zallar karfe Lu'u-lu'u fari tas, ita ma sai sheki da walwali take yi.
Sa'adda Rahila da Sarki Laffaru suka ga Aljani Maruful Dauwaz a cikin wannan gagarumar shigar yaki sai suka cika da tsananin mamaki domin a duk tsawon tafiyar da suka yi tun daga kogon Darul Iksina ba su ganshi da wadannan kaya ba.
Abin tambaya anan shi ne, a ina Maruful Dauwaz ya samo wadannan kayan yaki? Amsar da suka kasa bai wa kansu ke nan, amma sai suka kudurce a ransu cewa lallai nan gaba idan an sami sukuni sai sun yi masa wannan tambaya.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka zuba gaba dayan wadannan kayan yakin akan Aljani Maruful Dauwaz, sannan Rahila da Sarki Laffaru suka hau kan Maruful Dauwaz din suma suka zauna.
Nan take Maruful Dauwaz ya bude fuka- fukansa ya tashi sama. Kafin kiftawar ido ya luluka a cikin iska ya fara tsala azababben gudu yana mai tunkarar hanyar da za ta kai shi Birnin Hindu.
Duk wannan abu da ya faru tsakanin su Rahila da Aljani Maruful Dauwaz, Sarki Nashmir