Showing 3001 words to 6000 words out of 75493 words
Chapter 2 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
Shalbasha ya zaro idanu cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Haba yake matata! Yaya ni da nake mulkin babbar birni kamar wannan na Kufa za ki ce na koma birmin Zaruf na mulke su, ai na ci baya". Sa'adda Sharlis ta ji haka sai ta sake yin murmushi a karo na biyu sannan ta matso daf da aljani Shalbasha ta yi masa rada a kunne ta ce, tunda ba ka son maigidanka Lafaru ya wulakanta, idan za ka shiga cikin birnin Zaruf dauke da kan Sarkinsu sai ka juye izuwa wani kamannin daban kamar yadda yanzu ka juye izuwa na mijina.
Ya kai Shalbasha ka sani cewa umarni na ba ka a yanzu, idan kuma ka zo mini da tangarda yanzun nan takobina za ta sha jininka kamar yadda ta sha na Sarki Nurbas! Koda jin haka sai jikin aljani Shalbasha ya ci gaba da karkarwa fiye da farko, amma don kada jama'a su gane abinda ke faruwa sai shi ma ya yiwa Sharlis rada a kunne ya ce, "Tuba na ke ya shugabata na yarda zan bi umarninki, kuma ina rofonki da ki yi mini rai kada ki kashe ni. Ki sani cewa ni bawa ne kawai mai bin umarni, ba ni da laifin komai". Sharlis ta yi murmushi sannan ta ce, "Bana cutar da wanda bai cutar da ni ba, in da dai ban gano ko kai waye ba har aka cutar da ni da tabbas sai na cutar da kai.
Yanzu ka debi Dakarun nan birnin guda dubu dari ka tafi da su izuwa can birnin Zaruf, amma kafin sannan ina son ka juye izuwa kamannin wazirin Sarki Laffaru domin a halin yanzu wazirin na kwance agidansa yana jinyar rashin lafiya. Lallai idan mutanen birnin Zaruf suka ganka a cikin siffar wazirin Laffan kuma rike da kan Sarkinsu tare da Dakarun Sarki Laffaru dubu dari babu wanda zai yi ma ka tawaye, dole ne su yi biyayya a gare ka ka mulke su. Duk ranar da Sarki Laffaru ya dawo gida zan sa ya aika maka ka dawo a tura wani ya karɓi matsayinka.
Daga wannan lokaci sai ka san inda dare ya yı maka, idan kuwa na sake ganinka koda a kusa da birnin nan ne sai dai tsohuwarka ta haifi wani. Gama fadin hakan ke da wuya sai jaruma Sharlis ta tafi izuwa cikin birnin Kufa kai tsaye, ta bar Dakarun yaki a tsaitsaye suka bi ta da kallo kawai cikin tsananin mamakin yadda akavyi ita kadai ta tarwatsa dukkan abokan gaba har kuma ta sami nasarar kashe Sarki Nurbas
Daga wannan rana Sharlis ta rinka dora ɗanta yarima Shaddad akan karagar mulkin ubansa tana koya masa yadda ake tafiyar da mulki yana wakiltar mahaifinsa.
Al'amarin da ya jefa fadawan Sarki Laffaru cikin tsananin damuwa da bakin ciki ke nan, akan an bai wa kankanin yaro dan shekara uku shugabancinsu. Suna ji suna gani suka hakura dole da Shugabancin nasa, aka rasa wanda zai ce an yi ba dai-dai ba saboda tsananin tsoron kada fushin Sharlis ya tabbata a kansu. Su kuwa sauran mutanen gari na Kufa kuwa, sai wannan sabon mulki na ďan Sarki Laffaru ya zame musu abin alheri, domin gabadaya zaluncin da ake yi a kasar an daina. An daina kwacewa talakawa dukiya, yi wa mata fyade da zalunci na ba gaira ba dalili. Al'amarin da ya matukar kawo kwanciyar hankali da daukakar kasuwanci da arziki domin kowa ya saki jiki yana fito da hajarsa kasuwa ya kasa ta komai yawanta. Nan da nan fatake suka rinka yi wa birnin Kufa shigar burtu ya zamana cewa kasuwar garin na ci har sau uku a sati maimakon sau daya jal da take ciki. Nan fa birnin Kufa ya bunkasa ainun a karfin kasuwanci da arziki, mutane suka rinka yin hijira daga sauran kasashe makwabtaka suna dawowa birnin Kufa har garin ya cika ya batse, yawan al'umma ya wuce misali saboda haka sai Sarki Shaddad ya kafa doką aka hana baki shigowa su zauna sai dai su yi cinikinsu su fita.
Babu abinda yake bai wa jama'ar birnin Kufa mamaki face yadda wannan sabon Sarki nasu dan shekara uku jal! a duniya ke da basira da hangen nesa. Idan kuwa yana yi wa mutane jawabi sai ka rantse dan shekara dari ne yake zance. Nan da nan labari ya cika duniya cewar Sarki Laffaru ya ɓata ba a san inda yake ba, amma dansa Shaddad yaro dan shekara uku ya gaje shi har ma ya bambanta da ubansa domin shi adali ne saɓanin mahaifinsa da ya kasance azzalumi.
Bisa wannan dalili ne mutane suka rinka zuwa daga kasa-kasa, manyan Sarakai, attajirai da manyan bokaye domin kawai su ga Sarki Shaddad da idanunsu su tabbatar da abin al'ajabin da ake ta fada.
Babu abinda zai burge mutum face yadda ko yaushe Sarki Shaddad yake zama a fada tare da mahaifiyarsa Sharlis a kodayaushe tana damansa. Ga ta kyakkyawar gaske, kuma ga dan nata shi ma kyakkyawan gaske, duk sun yi shiga iri daya abin gwanin ban sha'awa.
Duk abinda Sarki Shaddad zai yi sai ya nemi shawarar mahaifiyarsa Sharlis, sai abinda ta ba shi umarni shi yake zartarwa, kawai dai sunan shi ne Sarki, amma Sharlis ce ke tafiyar da komai na mulki.
Sai da Sarki Shaddad ya sami kwana goma sha hudu akan karagar mulki sannan Sharlis ta sami nutsuwa ta shiga halwar tsafi domin ta binciko halin da Sarki Laffaru ke ciki. Ai kuwa nan take ta ga duk abinda ya faru tun daga lokacin da boka Muzaffar ya zo ya dauke Sarki Laffaru kawo izuwa sa'adda suka je suka dauko gimbiya Rahila sannan suka je suka dauko sauran abokan tafiya har suka iso wannan mugun daji inda suka fafata kazamin yaki da wadannan mugayen aljanu. Koda gama ganin wannan al'amari sai Sharlis ta kurma ihu cikin tsananin bakin ciki, hankalinta ya dugunzuma fiye da ko yaushe a rayuwarta, ta tabbatar da cewa an shammace ta
Sharlis ta yi shiru ta shiga tunani mai zurfi. Babban tashin hankalinat shi ne, ba za ta iya tafiya ta bar danta Shaddad shi kadai akan mulki ba, domin ta bi bayan su Sarki Laffaru ta wargatsa duk shirinsu. Nan fa ta fara tunanin wata dabarar da za ta yi ta wargatsa shirin nasu ba tare da ta bi bayansu ba.
Sharlis ta ce a ranta, "Yanzu dai kokarinsu shi ne su sami damar da za su isa kogon Darul Iksina su dauko aljani Maruful Dauwaz domin ya je ya sato musu gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarki Nashmir na birnin Hindu. To ai kuwa abu ne mawuyaci su iya tsallake wadannan masifu da ke cikin dazuzzukan nan biyar har su isa kogon Darul Iksina domin fiye da shekaru dubu biyu baya ba a sami wanda ya keta ta cikin su ba face shi kansa aljani Maruful Dauwaz aljanin da aka tabbatar da cewa babu kamarsa a zafin nama, karfin gudu a sama da kuma tsananin juriyar wuya kowacce iri ce.
Abu na biyu kuma shi ne, ai koda ma sun ami nasarar dauko aljani Maruful Dauwaz shiga fadar Sarki Nashmir har a dauko gimbiya Ramlatul Siyam daidai yake da tafiya neman jaki mai kaho. Domin hatta Sarki Bokayen aljanu na duniya almajirin Sarki Nashmir ne, a wajensa ya yi karatun tsafi. Tsaron da ke cikin gidan sarautar Sarki Nashmir da irin abubuwan masifun da ke cikinsa sun ninka wanda ke cikin wadannan mugayen dazuzzuka biyar na hanyar kogon Darul Iksina sau arba'in. Koda Sharlis ta zo nan a zancen zucinta sai ta bushe da dariyar murna, ta ce, "Ai babu wata hanya da burin su Sarki Laffaru zai cika, to amma duk da haka ba zan saki jiki ba na zuba ido kawai, dole ne na yi tunanin matakin da ya kamata na dauko, koda tsautsayi zai sa su sami nasarar daga yanzu zuwa lokacin da za su sami nasarar dauko aljani Daruful Dauwaz."
Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Kufa bayan ɓacewar Sarki Laffaru.
*****
AL'AMARIN su boka Muzaffar kuwa, kamar yadda boka Muzaffar ya bayar da shawara haka aka yi, wato sai da aka kwana biyu suna jinyar jikinsu ya zamana cewa dukkanninsu sun ji kwarin jikinsu sannan suka yi shiri domin su shiga daji na farko.
Bayan kowa ya gama kintsawa sai sukai cirko- cirko gaba dayansu aka rasa wanda zai fara wucewa kan gaba, har ita kanta kuwa gimbiya Rahila saboda tsananin fargaba da tunanin abinda ke cikin dajin.
Koda ganin haka sai boka Muzaffar ya dubi sadauki Haiman ya ce, Ya kai wannan jarumi mai jarumtakar ban al'ajabi ka yi sani cewa yanzu ne zamu shiga dajin Maridai, kai kadai ne za ka iya tarwatsa wadannan Maridai mu kutsa ta cikinsu mu wuce. Saboda haka kai ne za ka wuce gaba sanann gaba dayanmu mu bi ka a baya. Koda jin wannan batu sai sadauki Haiman ya zare takobinsa ya wuce gaba. Da ganin haka sai jaruma Shadira ma ta goya yaro Masnur a baya, jarumi Imran ya goya mahaifiyarsa, gimbiya Zarina ta goya dan uwanta sarkin Farisa.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sadauki
Shaharan ke nan, domin shi ba zai iya daukar
dokinsa ba.
Koda boka Muzaffar ya ga hankalin Shaharan ya tashi ainun, sai ya yi dariya, sannan ya dubi aljani Marhabul Zaurus ya ce, "Dauki dokin Shaharan ka taho da shi. Cikin matukar firgici aljani Marhabul Zaurus ya dubi boka Muzaffar ya ce, haba ya shugabana ya za ka ce na karawa kaina nauyi alhalin ka san irin bala'in da za mu shiga a cikin wannan daji.
Cikin fishi boka Muzaffar ya dakawa Marhabul Zaurus tsawa ya ce, "Ba wai rokonka nake ba umarni nake ba ka. Bisa dole Marhabul Zaurus ya dauki dokin sadauki Shaharan ya dora shi a gadon bayansa,sannan aka ci gaba da tafiya. Sadauki Haiman na kan gaba, jaruma Shadira na biye da shi, sai Zarina, Imran da Shaharan. Boka Muzaffar, Sarki Laffaru, gimbiya da Rahila ne a karshe sai kuma aljani Marhasul Zaurus wanda ke goye da dokin Shaharan.
Hakan dai suka ci gaba da tafiya har suka wuce iyakar dajin da suka baro suka shiga cikin farkon dajin gaba daya, wato dajin mugayen Maridai. Da shigarsu cikin wannan daji sai suka kamu da matukar fargaba. In ka dauke jaruman guda hudu da gimbiya Rahila da boka Muzaffar gaba daya sauran abokan tafiyar jikinsu karkarwa yake kamar wadanda aka tsoma a cikin ruwan kankara. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin yanayin wannan daji.
Wadansu irin gabza-gabzan bishiyoyi ne a dajin dogaye masu siffofin mutane kirar mutanen farko. Babu abinda zai bai wa mutum mamaki face yadda siffofin bishiyoyin suka zama haka tunda ba sassakasu aka yi ba, a haka suka tsiro suka girma. Da zarar mutum ya kalli bishiyoyin sai ya ji zuciyarsa na dukan uku-uku saboda munin siffofinsu kuma sai ya ga kamar za su kawo masa hari a ko yaushe. Dajin ya yi tsit tamkar wani abu mai rai bai taɓa wanzuwa ba a cikinsa, amma da zarar su sadauki Haiman sun taka busassun ganyayyakin wadannan bishiyoyi sai ka ji karar ruburбushewar ganyayen ta cika dodon kunne, kuma ta cika dajin gaba daya harda amsa kuwwa. Ga shi babu inda mutum zai taka inda babu ganyayen.
Abin da su Haiman basu sani ba shi ne, wannan kara ta ganyaye ita ce alamar da mugayen maridan suke ganewa cewa an shigo cikin mahallinsu.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai ga wadannan zabga-zabgan Maridai suna fitowa daga cikin wadansu ɓoyayyun ramuka a karkashin kasa tamkar an tashi matattu a makabartar da ta kunshi gawar da ba ta da dadi. Koda su Haiman suka yi arba da wadannan Maridai sai suka firgice ainun, nan take dukkaninsu suka ji sun yi nadamar baro kasashensu don cika burin kansu.
Shi kansa sadauki Haiman da aka ce shi ne zai iya tarwatsa maridan sai da ya tsorata ainun ya raina kansa, domin ya tabbatarwa kansa cewa boka Muzaffar karya ya yi da ya ce da shi shi ne zai iya tarwatsa su, domin ido ba mudu ba ne amma ya san kima, kuma ko ba a gwada ba linzami ya fi karfin bakin kaza.
Sadauki Haiman yaji kamar ya yar da takobinsa ya juya da baya a guje, amma da ya ga cewar tuni maridan sun yi musu kawanya babu hanyar gudu sai ya tsaya cak!
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, "Idan mutum ya ga mutuwa ta ritsa shi, to fa a sannan ne yake zama jaurmin dole, domin ya ceci rayuwarsa ta kowane hali." Lokacin da sauran jaruman tafiya suka ga sadauki Haiman ya tsaya cak bai yi yunkurin komai ba sai kallon maridan yake kawai sai suma suka gyara tsayuwa suna wasa da makamansu.
Su kuwa sauran abokan tafiyar tun sa'adda suka yi arba da halittun suka sume duk da cewa ana goye da su. Shaharan, Sarki Laffaru ne kawai ba su suma ba saboda su ma zuciyoyinsu na sadaukai ne
A iya tsawon rayuwar wadannan Maridai a dajin shekaru dubu biyu baya ba su taɓa ganin mutane ko aljanu masu dakakkiyar zuciya ba kamar su sadauki Haiman, domin duk wanda ya yi arba da su take yake sumewa ko ya haukace, amma su ga su daram a gabansu.
Sannu a hankali maridan da ke gabansu suka fara marmatsowa suna wangame manyan bakunansú masu kama da bakin rijiya da nufin su dasawa su Haiman wawaso su cinye su.
Koda Haiman ya ga mutuwa na durfafo shi gadan-gadan sai ya ďaga takobinsa sama ya kwarara uban ihu sannan ya ruga da gudu ya durfafi maridan. Cikin hanzari sauran abokan tafiyar suka yi koyi da shi.
Koda Haiman ya riski maridan sai ya hau su da sara da suka cikin tsananin zafin nama ya rinka tarwatsa su da karfin tsiya a guje yana samar musu. hanya suna wucewa, amma takobin tasa ba ta iya datsa jikinsu, sai dai mammake su suna zubewa kasa, amma da zarar sun fadi sai su mike zumbur a ci gaba da kasa tsere da su.
Jaruma Shadira, sadauki Imran, gimbiya Zarina, gimbiya Rahila da boka Muzaffar ne suka rinka taimakawa Haiman suna sara da dukan maridan ta gefe da gefe, da kuma bayansu. Babban abinda ya fi dugunzuma hankalin su Shadira shi ne, a duk sa'adda maridan suka kawo musu wafta ko sara da kaifafan faratan hannayensu idan suka goce suka sami kasa sai ka ga sun haifar da katon rami, idan kuwa bishiya suka samu sai ka ga sun datsata gida biyu, in kuwa dutse ne tarwatsewa yake ya farfashe. Haka kuma zafin naman maridan ya wuce misali, domin a cikin dakika biyu suna iya kawo hari goma.
Nan fa maridan suka ruda su suka rikirkita su. Idan ba don gimbiya Rahila na da matukar zafin nama ba da karfin dantse da tuni maridan sun gama hallaka dukkan abokan tafiyar da ke bayan sadauki Haiman, domin ita ce take wata irin gagarumar bajinta tana kare hare-harensu ta hanyar shawagi a sama, tayi gabas, tayi yamma, kudu da arewa tana saran maridan da takobinta tana karkadar da su.Duk wannan kokarin da Rahila ke yi sai ya
zamo a banza, domin ta kai cewa maridan sun far make jaruman suna faduwa kasa suna dada kai wawan taku da nufin mutsittsike su amma sai ka ga Rahila na janye su daga kasan cikin zafin nama tana kubutar da rayuwarsu. A haka aka ci gaba da gudu ana daďa ratsawa ta cikin maridan. Tunda sadauki Haiman yake gumura a yaki bai taɓa tsintar kansa a cikin bala'i irin wannan ba. Hatta bala'in da suka fuskanta a wadanna dazuzzukan da suka wuce bai kai na wannan ba. Lokacin da maridan suka ga an dauki dogon lokaci suna artabu da wadannan shu'uman mutane sai suka fara wani irin ihu mai tsananin karfi wanda ka iya sa mutum ya kurmance. Lokaci guda su Haiman suka kasa ci gaba da gudu suka toshe kunnuwan da hannayensu, damar da maridan suka samu ke nan suka ritsa su a waje daya suka ci gaba da kai musu sara da suka da faratansu.
Saboda karfin harin maridan da zafin namansu ya zamana cewa tun jaruman na iya kare kansu da makamansu har sun fara gajiya. Boka Muzaffar aka fara cakawa tsinin farce a saman kafadarsa. Farcen maridin ya faso ta bayansa, Muzaffar ya kwarara uban ihu sakamakon mugun zafin da yaji. Maridan na zare farcen nasa daga cikin kafadar Muzaffar sai jini yai tsartuwa, Muzaffar ya fadi kasa sumamme. A sannan ne hankalin sauran jaruman ya dugunzuma ainun domin sun zata ma boka Muzaffar ya mutu. Shi kuwa Sarki Laffaru da ya ga abin da ya faru ga boka Muzaffar abin dogaronsa sai yai sauri ya kwanta a kasa ya yi kamar ya mutu saboda sanin cewa ba zai iya tsinana komai ba a wannan gumurzu.
A dai-dai wannan lokaci sadauki Imran ba karamin kokari ya yi ba yana ta bubbuge kawunan maridan da sandarsa kuma yana samin damar tarwatsa su amma jaruma Shardira ta fi shi kokari domin a duk sa'adda ta dana kibiyoyinta ta harba sai dai ka ga kibiyoyin na cakewa akan maridan suna faduwa kasa amma saboda taurin ransu da nacinsu sai dai ka ga sun sa hannu sun zare kibiyar sun mike tsaye sun ci gaba da kai mugun hari duk da cewa jini na zuba a jikinsu.
Ita kuwa jaruma Zarina abin da ya taimake ta kawai shi ne, ta iya zulliya matuka. Duk ta inda maridan suka kawo ma ta farmaki sai ka ga ta goce ba sa samunta, amma tashin hankalinta shi ne ta fara gajiya, don haka a ko yaushe komai zai iya faruwa. Sadauki Shaharan ma karfin gudunsa ne ya cece shi domin a tsakiyar dodannin yake ta tsala gudu yana shiga karkashinsu, wani lokacin har jikinsu yake hawa yana gudu suna kawo masa mangari yana gocewa. Inda matsalar take shi ne, shi ma ya fara gajiya su kuwa maridan ko alamar gajiya ba sa yi, kamar ma kara kuzari suke. Ana cikin haka ne wani maridi mai shegen naci ya shammaci Imran ya yi masa dundu a take Imran ya baje a kasa da ruf da ciki a lokacin da ya ji kamar kasusuwan bayansa sun kakkarye, don haka sai ya kasa mikewa.
Maridin ya daga hannu zai caka faratansa a gadon bayan Imran. Koda Shadira ta hango abinda ke shirin faruwa