Showing 36001 words to 39000 words out of 75493 words
Chapter 13 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
da muka sha a baya ta zama a banza. Wasun mu sun rasa masoyansu, wasu sun rasa wani sashi na wani bangare na jikinsu, a karshe mun tashi a tutar babu, ba mu ga tsuntsu, ba mu ga tarko. Lallai Boka Muzzafar ya yi mana zaluncin da har abada ba zamu yafe masa ba face mun dauki fansa."
Koda Imran ya zo nan a zancensa sai duk su hudun kwallar bakin ciki ta cika musu idanu, su duka suka yi shiru har izuwa tsawon 'yan dakiku. Daga can sai Haiman ya dubi Imran ya ce, "Ya kai abokin tafiya ka yi sani cewa zama bai kama mu ba, ka duaki mahaifiyarka ka goya ta mu juya da baya mu koma inda muka baro su Boka Muzaffar wata kila mu riske su in ya so ayi duk wadda za a yi."
Imran ya ce, "Kwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau". Cikin hanzari ya mike tsaye ya dauki mahaifiyarsa ya goyata sannan suka juya da nufin su fice daga cikin fadar.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ga gaba dayan gumakan wadannan Dakaru sun motsa suna masu buga kafafuwansu da gyara makaman yakinsu.
A firgice su Imran suka juyo da sauri, ai kuwa sai suka ga ashe ruhi ne ya shiga cikin gangar jikin gumakan duk sun zama rayayyu.
Kafin su Imran su yi wani yunkuri tuni dakarun sun yi musu kawanya babu ta inda sa su iya gudu Kawai sai suka ji an kyalkyale ja dariya dagacan kan karagar mulki. Wannan karamin yaro mai rawani a kansa shi ne ya yi dariyar a lokacin da yake saukowa daga kan karagar mulkin.
Ta ke Dakarun suka buďewa yaron hanya ya tako a hankali cikin tafiyar kasaita ya iso har inda su Imran ke tsaye ya dube su a wulakance ya ce, "Yau shekara dubu daya ke nan rabon da wani mahaluki ya shigo cikin wannan kogo na Darul Iksina. Sunana RAUHUDUL MAUZUL, ni ne Sarkin MAYU na aljanun duniya. Lallai muna cikin tsananin kishirwar bil'adama, kuma mun daďe rabonmu da mu tauna nama da kashi. Yanzun nan za mu gididdiba ku gutsun-gutsun yadda za a sarrafaku izuwa nau'i-nau'in girki wanda zan kwana biyu ina walima."
Koda gama wannan jawabi sai wannan yaro ya juya ya nufi inda karagar mulkinsa take. Nan take Imran da Haiman suka fahimci cewa lallai yaron na isa kan karagarsa yana zama za a far musu a gama da su. Kawai sai Imran ya yunkura ya zare sandarsa a lokacin da mahaifiyarsa da ke goye a bayansa ta fara kuka. Itama Lumaira da ke goye a bayan Haiman sai zuciyarta ta karaya ta fara kuka.
Haiman ya dubi Imran cikin tsananin karayar zuciya ya ce, "Ya kai abokin tafiya mene ne amfani ka 6ata lokacinka kayi yaki yanzu? Shin ka manta ne da duk irin gwagwarmayar da muka yi a baya da irin tsananin wuyar da muka sha? Mece ce ribarmu idan ma mun sami hasarar hallaka wadannan aljanu? abin da muka rayu ma dominsa ba zamu samu ba. Ni kam yanzu na hakura da rayuwa na zaɓi mutuwa domin idan ma ban mutu ba takaici da bakin ciki ne za su kashe ni nan gaba".
Caraf! Sai Imran ya tari numfashinsa ya ce "Ya kai abokin tafiya ka yi sani cewa in dai da rai da numfashi akwai sa'a da rabo. Ina tabbatar maka da cewa ko a bakin Kura nake ban fid da rai da samun kuɓuta. Kawai ka tsaya mu ZAGE DANTSE mu yaki wadannan aljanu da iyakar dukkan karfinmu koda kuwa ba zamu yi nasara ba."
Koda jin haka sai Haiman ya yi yaken takaici sannan ya kwance matarsa Lumaira daga bayansa ya ajiye ta a kas ya dube ta sa'ad da hawaye ya zubo masa ya ce, "Ki yafe ni yake matata, yau ne ranar farlo da na gaza akan tafarkin kare ki da kulawa da ke domin ina ganin cewa mutuwa a gare mu ni da ke tafi komai sauki."
Kafin Haiman ya gama rufe bakinsa tuni Lumaira ta zabga masa mari sannan sai ta fashe da kuka tana mai cewa, "Ban taɓa sanin cewa kai rago ba ne sai yau. Tabbas zuciyarka mai rauni ce kuma ba ka cika jarumi ba, Imran shi ne JARUMIN KWARAI. Dukkan namijin kwarai baya mika wuya ga abokan gaba bare har yana ji yana ganin za a hallaka masoyiyarsa ya kasa komai. Ashe duk soyayyar da muka yi a baya ta zama ta banza in dai ka mika wuya ga wadannan aljanu suka hallaka mu ba tare da ka yi kokarin komai ba ka yanke duk kaunar da ke tsakaninmu."
Kafin Lumaira ta gama rufe bakinta tuni Haiman ya kwarara uban ihu cikin bakin zafin nama ya zare takobinsa da lafiyayyen hannunsa ya afkawa wadannan Dakaru da sara tun gabannin su Dakarun su karɓi izinin yin yakin.
Koda ganin haka sai farin ciki ya lulluɓe Imran shi ma ya afkawa Dakarun aka ruguntsume da azababben yaki. In ba don su Haiman suna da karfin sihirin tsafi daidai nasu ba da tuni Dakarun sun yi musu kisan farat daya. Babba abin da ya dugunzuma hankalinsu Imran shi ne, SARA DA SUKA ba ya tasiri a jikin wadannan Dakarun sai dai ka ga tartsatsin wuta na tashi kuma ko kwarzanar jikinsu ba ya yi, sannan kuma ko kadan babu alamar za su gaji.
Koda aka sami rabin sa'a ana wannan murzu sai Haiman da Imran suka raina dukkan jarumtakarsu da karfin sihirinsu domin ta kai da kyar suke kare harin da aljanun ke kawo musu bare ma su mai da martani. Kai da aljanun ma suka ga cewa wankin hula zai kai su dare sai suka rikide izuwa ainahin mummunar siffarsu ta aljanu suka ci gaba da gumurzu a haka.
Koda mahaifiyar Imran tayi arba da aljanun a cikin siffofinsu na zahiri sai ta sume. A daidai wannan lokacin ne karfin aljanun ya ninka na da suka fara kai su Imran kas har ma suka fara yi musu rauni ya zamana cewa an sari Imran sau uku, shi kuwa Haiman sau biyu aka sare shi ya zamana cewa jiri ya debe shi har ya kife kasa da rubda ciki
Koda Dakarun suka ga Haiman ya kife a kas shi da natarsa sai suka yi caa! A kansu da nufin su daddatsa su. Da dai Imran ya ga abin da ke shirin faruwa sai ya fusata ainun bai san sa'adda ya daka wawan tsalle sama ya dirga akan kafadar daya daga cikinsu ya dankara masa naushi a wuyansa a take wannan badakare ya sandare ya koma gunki haka su ma yan uwansa babu wanda ya kara yin motsi.
Duk abin da yake faruwa RAUHUDUL MAUZUL yana tsaye yana gani, cikin wata mummunar siffa abar tsoro. A daidai wannan lokacin ne sadaukin Haima ya farfado, cikin sauri ya dauko magani ya shafa a rauninsa sannan ya shafawa jarumi Imran shi ma. Wannan sarkin mayu ya ce, idan kun tsira daga sharrin dakarun masifa ai ba za ku iya tsira daga sharrin masifar ba, ga maza nan bisa kanku.
Haiman ya dubi Imran cikin tsananin fusata ya ce, maza mu afka masa kafin ya afko mana. Kafin Rauhudul Mauzul ya yi wani yunkuri tuni su Imran sun afka masa suka kacame da wani azababben yaki, duk da su Haiman suna yin yakin ne da dukkan karfi da iyawarsu sai da suka zama ababen tausayi a hannun wannan hatsabibin aljani.
Sai da wannan aljani ya sumar da kowanensu sau bakwai, yayin da ya sumar da wancan sai wannan ya farfaďo. Hakika shi kansa ya yi mamakin bakin naci na waďannan jarumai domin a tarihinsa bai taba haďuwa da masu taurin rai kamarsu ba. Suna cikin wannan gumurzu ne ya samu nasarar fesa musu wata shuďiyar iska daga bakinsa bakinsa a take suka zube kasa sumammu
***
Wannan shi ne abin da ya faru da su sadauki Haiman a cikin kogon Darul Iksina
Al'amarin su sarki lafaru kuwa bayan boka Muzaffar ya shige cikin ďaki na farko ya basr su a tsaye, sai Laffaru ya dubi Rahila ya ce, "Shin kina tare da ni?" Rahila ta yi murmushi ta ce "Ina tare da kai". Laffaru ya ce, "Tabbas na yi imani cewa Aljani Maruful Dauwaz yana cikin ɗaya daga cikin waďannan gidaje guda bakwai kuma ko shakka bana yi ba ya cikin gida na farko wanda Muzaffar ya shiga cikinsa, kuma ba ya cikin gida na uku wanda su Haiman suka shiga, haka kuma baya cikin gida na biyu wanda Muzaffar ya ce mu shiga mu debo dukiya. Tabbas yana cikin gida na hudu ko na biyar ko na shida zuwa na bakwai. Ya ke matata ta nan gaba, a cikin wadannan ragowar gidaje guda hudu wanne ne kike ganin zamu iya riskar Aljani Maruful Dauwaz a ciki?"
Koda jin wannan tambaya sai Rahila tayi murmushi ba ta ce komai ba, kawai sai ta zura hannu a cikin jakar guzurinta ta dauko wata 'yar gajeriyar SANDAR TSAFI ta tofa wadansu dalasiman tsafi a jikinta ta saki sandar. Maimakon sandar ta fadi kasa sai ta tsaya cak a sama cikin iska sannan ta nufi inda wadannan gidaje hudu suke ta fara dungurar kofar farko, sai ta matsa gaba ta dunguri kofa ta biyu nan ma ta wuce gaba har sai da taje kofar gida na bakwan. Koda ta dunguri kofar gidan sai ta tsaya cak a jikin kofar ta manne.
Koda ganin haka sai Rahila da Laffaru suka dubi juna suka yi murmushi. Nan take suka buɗe wannan kofar gida na bakwai salin-alin ba tare da sun fuskanci wata matsala ba, suka kunna kai ciki, suna shiga sai kofar gidan ta rufe kanta. Nan fa ya rage saura Zarina, Shadira da Shaharan a tsaye suna
kallon junansu aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Zarina ta dubi Shadira ta ce, "Ya ke abokiyar tafiya yanzu ke me kika yanke shawara akan rayuwarki?"
Sa'adda Shadira ta ji wannan tambaya sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ai ni yanzu bani da wani zaɓi wanda ya fi ni ma na shiga cikin gidan da su masoyina Imran suka shiga. Idan na iske su a raye shi ke nan, idan kuma sun mutu sai ni ma na mika wuya ga abin da ya kashe su ya hallaka ni tunda ban ga amfanin rayuwata ba a doron kasa domin rayuwa idan babu masoyi ba ta da dadi. Sa'adda Zarina da Shaharan suka ji wannan batu sai duk su biyun jikinsu ya yi sanyi suka ji sun kamu da tsananin tausayin Shadira, nan take suka tuno da irin wahalar da suka sha a cikin wannan tafiya wacce ta zame musu asara kuma abin takaici da bakin ciki, kawai sai suka kama kuka.
Itama Shadira sai zuciyarta ta karya ta taya su kukan. Sai da suka dan jima suna kukan sannan Shaharan ya goge hawayen idanunsa da lafiyayyen hannunsa sannan ya dubi Shadira ya ce, "Ya ke abokiyar tafiya ni da masoyiyata Zarina za mu yi miki rakiya izuva cikin wannan gida na uku domin mu kaiwa su Imran dauki idan har suna raye dukkan mugun halin da suke ciki. Idan kuma ba sa a raye lallai mun zaбi mu mutu a cikin gidan da dai mu fito a raye".
Koda gama fadin hakan sai Shaharan ya wuce kan gaba ya nufi kofar wannan gida na bakwai cikin hanzari Shadira da Zarina suka bi shi.
Nan take suka bude kofar gidan suka kunna kai ciki, kofar ta kulle kanta.
Al'amarin Sarki Laffaru da Gimbiya Rahila kuwa, lokacin da suka shiga cikin wannan gida na bakwai sai suka tsinci kansu tsamo-tsamo a cikin wani makeken kogi. A can karshen kogin wata matattakalar bene ce guda goma sha biyu wadda karshenta wani gini ne mai fadi da tudu.
Kwatsam! Sai suka ga wata shirgegiyar hakitta kwance akan wannan faffadan gini. Ba komai ba ne wannan halitta face Aljani MARUFUL DAUWAZ. Idanunsa na kallon rufin gidan, kuma suna ta dalalo da hawaye, ruwan hawayen na ta kwarara ta kan wannan matattakala guda goma sha biyu tamkar idaniyar ruwa ce ta ɓalle. Nan take Laffaru da Rahila suka gane cewa tabbas wannan Aljani da ke ta kuka hawayensa na kwarara shi ne Aljani Maruful Dauwaz kuma ruwan kogin da suka tsinci kansu a ciki shi ne ruwan albarka wanda Boka Muzaffar ya yi musu karyar cewa zai warkar da marasa lafiya!
(Na sha wahala a wannan posting ďin na yau sakamakon babu shafi guda biyu kuma shafukan da aka rasa suna da matukar muhimmanci. Na yi amfani da salon marubucin na shigar da fahimtata a madadin shafin da aka rasa. Na yi shisshigi)
Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya ji motsi a cikin wannan ruwan hawayen nasa sai ya cika da tsananin mamaki domin shi a saninsa tun da ya shigo cikin wannan kogo tsawon shekaru dubu biyu bai sake jin motsin wata halitta ba a cikin wannan gida da yake ba sai yau.
Cikin firgici ya mike zumbur! Ya dubi cikin hawayen nasa, kawai sai ya yi arba da su Sarki Laffaru da kuma Gimbiya Rahila. Nan take ya Kurawa Rahila idanu, idanunsa suka kafe akanta ko kiftawa ba sa yi. Amma da ya dube ta sama da kasa ya ga mutum ce ba aljana ba sai ya girgiza kai ya koma ya kwanta kamar yadda yake da farko ba tare da ya sake duban fuskokinsu ba ya ce, "Ya ku wadannan hatsabiban bil'adama yaya aka yi kuka zo har nan tsibirin kuma kuka shigo cikin wannan kogo na Darul Iksina? Mene ne dalilin zuwanku?"
Har Sarki Laffaru ya bude baki zai yi magana sai Rahila tayi wuf ta tari numfashinsa ta ce, "Ya kai NAMIJIN DUNIYA, BABBAN JARUMI na Sarauniyar Matan duniya GIMBIYA RASHMIN ka yi sani cewa mu bakinka ne na musamma kuma muna dauke da gagarumin sako wanda masoyiyarka marigayiya Gimbiya Rashmin ta bayar da shi a ba ka tun kafin rasuwarta."Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya mike zumbur ya fuskanci Rahila kuma ya dube ta cikin zakuwa ya ce, "Wane sako ne masoyiyata ta bari wanda har yanzu bai riske ni ba sai yau bayan gushewarta da shekaru dubu biyu da doriya?"
Rahila ta yi ajiyar numfashi sannan ta ce, "Ka kwantar da hankalinka ya kai DODON MAZA, ka yi sani cewa wannan sako da masoyiyarka ta ba ka ba komai ba ne face rubutacciyar wasiyya akan wani burinta guda daya da take son ka cika mata shi a duniya kafin cikar ajalinka.
Duk duniya babu wanda ya san inda wannan wasiyya take a ɓoye sai ni, kuma babu mai iya daukota sai ni din. Idan za ka iya tunawa lokacin da kake aikin bauta a gidan sarautar Sarkin aljanu mahaifin Gimbiya Rashmin akwai wani bawa wanda ya kasance abokinka wanda ake kira da suna TALMARA IBINI SAUMUR wanda shi ne mai kula da shimfidar Sarki, haka ne ko ba haka ba?"
Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful Dauwaz ya cika da tsananin mamaki bisa yadda ya ji Rahila ta san abokinsa Talmara alhalin rayuwarsa da shi tuni ta gushe sama da shekaru dubu biyu da suka shude.
Maruful Dauwaz ya gyara zama, nan take ya ji ya fara aminta da Rahila akan cewa ba ta zo masa da zancen karya ba, don haka sai ya dube ta ya ce, "Ya ke wannan bil'adama ma'abociyar kyawu da kamanni irin na masoyiyata wace ce ke, kuma ya aka yi kika san abokina Talmara ibini Saumur?"
Koda jin wannan tambaya sai Rahila ta nutsu sannan ta ce, "Da farko dai ni sunana Rahila, kuma mahaifina shi ne mai mulkin Birnin SHAUFIL wanda ke can yamma da kasar DAMASKA.
Yadda aka yi na san abokinka Talmara kuwa shi ne, na sami tarihin rayuwarsa ne a cikin KUNDIN TARIHI na masarautarmu. Ya taɓa yin bauta ga Kakana na dari bakwai da sittin da tara kimanin shekaru adadin zamanka anan cikin kogon Darul Iksina.
Tun a sannan ne Talmara ya kawo wasiyyar da masoyiyarka ta rubuta kafin ta mutu ta ba shi amana shi kuma sai ya damka ta amana ga wannan Kaka nawa ya ce, ya yi ta ajiyarta har sai a shekarar da aka gano inda kake a cikin duniya a damka maka ita.
Bisa wannan dalili ne wannan kaka nawa na dari bakwai da sittin da tara ya 6oye wannan wasiyyar a inda babu wanda ya sani sannan ya rubuta tasa wasiyyar cewa duk ranar da aka gano inda Aljani Maruful Dauwaz yake aje a dauko wannan wasiyya a ba shi.
A cikin wasiyyar ne ya bayar da labarin bawansa Talmara da kuma labarin soyayyarka da Gimbiya Rashmin da yadda aka yi aka raba ku da karfin tsiya har bakin ciki ya zamo sanadin ajalinta.
Ya kai Maruful Dauwaz ka yi sani cewa ko mahaifina yanzu bai san inda wannan wasiyya take ba domin na sauya ma ta maɓoya. Idan ka amince za ka biya mini tawa bukatar ni ma zan kai ka inda na бoye wasiyyar masoyiyarka na damka ta a gare ka, amma sai ka yi rantsuwa da darajar soyayyarka akan Rashmin cewar za ka zamo mai cika alkawari a gare ni, kuma sai bayan ka biya mini tawa bukatar sannan zan ba ka wasiyyar masoyiyarka".
Lokacin da Gimbiya Rahila ta zo nan a jawabinta sai Aljani Maruful Dauwaz yai shiru kuma ya fada kogin tunani mai zurfi yana juya al'amarin a cikin zuciyarsa. Daga can sai ya dago kai ya dubi Rahila ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki, ki yi sani cewa a iya rayuwata ta duniya babu abinda na tsana sama da yaudara da cin amana da kuma butulci. Bisa wannan dalili nake so ki rike amanata ni ma zan rike taki. Tun wuri idan kin san cewa wannan labari na wasiyyar masoyiyata da
kika zo mini da shi idan karya ne ki kau da shi, domin idan na gane karya ne sai na hallaka ki kuma na hallaka duk zuri'arki. Ke Birninku ma gaba dayansa sai na shafe shi daga doron kasa. Yanzu sai ki ci gaba da ba ni labarinki da yadda aka yi kika zo har nan kika riske ni sannan a karshe ki gaya mini bukatarki wacce kike son na biya miki. Ki sani cewa na yi alkawari ba zan sake shiga duniya ba har sai ajalina ya riske ni a nan cikin kogon