Showing 9001 words to 12000 words out of 75493 words

Chapter 4 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

tsoro ko fargabar komai, duk da cewa ban yi kokarin komai ba a cikin wannan tafiya. In da ace karfin damtsena zai dawo jikina a yanzu ina tabbatar maka da cewa jarumtakar da zan yi ko jaruma Rahila ba za ta lya irinta ba. Ina mai shawartarka da ka daina nuna karayar zuciyarka ga abokan tafiya, domin kada suma su karaya su janye ci gaba da wannan tafiya. Ni kam gwara na rasa rayuwata da dai na koma gida babu biyan wannan bukata, tunda dai ni da gawar babu bambanci tunda zan rasa komai nawa, kuma dan cikina yavzo ya zama ajalina. Kai ma idan ka yi tunani rayuwarka a cikin mugun hadari take, idan har ba mu sami nasara ba bisa wannan bukata da ke gabanmu, domin ka kulla gaba da matata Sharlis, tunda kai ne ka kubutar da ni daga sharrinta. Ka fi ni sanin iyakar karfin Sharlis, don haka kai ne ka san abin da zai biyo baya fiye da ni".

Sa'adda Sarki Laffaru ya zo nan a zancensa sai kwalla ta cika idanun boka Muzaffar ya ce, "Ya kai abókina hakika duk abin da ka fadi gaskiya ne, kuma a yanzu ma inda ka san irin mummunar 6arnar da Sharlis ta yi mana ni da kai da ka dada tabbatar da cewa ba mu da wani kwanciyar hankali wanda ya fi mu sami nasarar abin da muka fito nema. Cikin firgici Sarki Laffaru ya dubi boka Muzaffar ya ce "Wane irin mugun abu Sharlis ta yi mini a yanzu bayan na baro kasata?".

Muzaffar ya girgiza kai sannan ya ce, A halin yanzu Sharlis ta yi yaki da mayakan Sarki Nurbas ita kadai ta tarwatsa su, kuma ta kashe Sarki Nurbas. Aljani Shalbasha ibini Rauhuba kuwa, wanda muka baro a matsayin halifanka ta gano ko wane ne shi, har ta tura shi izuwa birnin Zaruf yana wakilcin Shugabancin birnin. Akan karagarka kuwa ta mulki, ta dora danta Shaddad yana mulkin jama'arka cikin adalci da kyautatawa talakawa, saɓanin na ka mulkin. Ina tabbatar maka da cewa danka Shaddad ya sami farin jini ainun a wajen jama'ar Kasarka, basa fatan ka komo gare su. Dubi tafin hannuna domin ka ga zahiri".

Koda gama fadin haka sai boka Muzaffar ya bude tafin hannunsa. Nan take hoton fadar Sarki Laffaru ya baiyana, sai ga Shaddad yaro dan shekara uku akan karagar mulki, mahaifiyarsa Sharlis na zaune a gefensa, kuma ga fadawa sun kewaye Shaddad ana tafiyar da harkokin mulki, talakawa sai shigowa suke cikin fadar suna zubewa kasa suna kwasar gaisuwa, yaro Shaddad na sawa ana basu kyautar suturu, dukiya da kayayyakin abinci.

Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya sake turnuke Sarki Laffaru fiye da ko yaushe, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar za ta kone, bai sansa'adda idanunsa suka ciko da kwallah ba suka fara zubar da hawaye.
Lokacin da boka Muzaffar ya ga halin da Sarki Laffaru ya shiga sai ya yi sauri ya shafi tafin hannunsa, hoton komai ya ɓace, sannan ya dafa kafadar Sarki Laffaru ya ce "Kada ka damu ya kai abokina, ita rayuwa dama haka take, wata rana kai ne a sama, wata ran kuma ka zamo a kasa. Shin ka manta sa'adda kake kan sharafinka ne lokacin da ka buwayi gaba dayan kasashen da ke nahiyarka gaba daya?

Ina mai kara maka karfin guiwa akan wannan gagarumin aiki da ke gabanmu domin ba mu da wani zaɓi wanda ya fi mu tabbatar da cewa mun sami nasarar abin da muka fito nema. Koda gama faɗin haka sai boka Muzaffar ya yi shiru yana mai sunkui da kansa kas cikin halin tsananin damuwa. Sarki Laffaru ya dube shi ya ce, "Ya kai wannan jarumin boka, dazu ka gaya mini cewa kai ma Sharlis ta yi maka mummunar barna amma ba ka gaya mini irin ɓarnar da ta yi maka ba".

Boka Muzaffar ya dago kai ya dubi Sarki Laffaru ya ce, "A halin yanzu Sharlis ta kama matata da dana guda daya jal ta kai shi can wani gidanta da ke can dajin Bairul Aswan da ke karshen birnin Kisra, ta kulle su a cikin kurkuku, kuma ta yi alkawarin cewa ba za ta sake su ba face ta kama ni ta yi mini azaba mai radadi, sannan ta yi mini kisan gilla bisa taimakon da na yi maka.

Ka sani cewa a duniya babu abinda nake so sama da matata da dana, a dalilinsu ne ma nake son na mallaki rabin mulkin kasarka da rabin dukiyarka domin na cika musu babban burinsu a rayuwa. A takaice dai burin da nake son ya cika ba nawa ba ne na iyalina ne. Yanzu ga shi su kansu iyalan nawa suna cikin mugun hali kuma ba zan iya ceton rayuwarsu ba face da taimakon aljani Maruful Dauwaz, domin shi kadai ne zai iya zuwa wancan gida na Sharlis ya dauko mini iyalina saboda tsananin tsaro da karfin sihirin da ke gidan.
Duk duniya gidan Sarki Nashmir ne kadai ya fi gidan Sharlis tsaro" Da jin wannan batu sai Sarki Laffaru ya dubi Muzaffar cikin tsananin damuwa ya ce, "Amma hakika Sharlis ba karamar hatsabibiya ba ce. Ni kaina na yi mamakin yadda aka yi ta sami nasara a kaina har tsafinta ya ci ni ta raba ni da jarumtakata." Koda jin wannan batu sai boka Muzaffar ya bushe da dariya, al'amarin da ya bai wa gaba dayan abokan tafiya mamaki ke nan, duk da cewa basu san dalilin yin dariyar tasa ba, tunda basa jin abin da suke tattaunawa, saboda a can gefe daya suke zaune.
Bayan boka Muzaffar ya yi dariyar har ta ishe shi sai ya dubi Laffaru ya ce, "Ya kai abokina ai dole ne ka yi mamaki. Amma abinda nake so ka fahimta shi ne, ka kiyayi ramuwar mutumin da ka zalunta bisa ka fi karfinsa, babu yarda zai yi, domin zai iya shafe shekara dari yana yi maka TANADIN FANSA.

Ka yi sani cewa tun daga ranar da ka yi wa iyayen mahaifin Sharlis da sauran iyalansa kisan gilla, ka yi babban kuskure da ba ka kashe boka Narwas ba, domin sai da ya shekara bakwai yana neman karfin ilimin tsafi har ya gawurta ainun, amma duk sirrikan da ya samo sai ya dinga zuba su a jikin 'yarsa Sharlis, bayan ya samo ta a wajen wani masunci da ya tsince ta, ya dinga horar da ita akan yadda za ta dauki fansa a kanka har ta girma, kuma ya hane ta da kada ta kuskura ta ce za ta je ta tare ka har sai a ranar da aka zo har gida aka kama ta aka kai ta gabanka ka tara da ita, a sannan ne za ka rasa gaba dayan kuzarin jikinka ta sami damar yin ramuwar gayya akanka sannu a hankali har izuwa lokacin da danta zai girma ya yi maka kisan gilla". Sa'adda boka Muzaffar ya zo nan a jawabinsa sai jikin Sarki Laffaru ya yi sanyi, kuma yai shiru ya kasa cewa komai, Jim kadan sai Sarki Laffaru ya mike tsaye zumbur! Kamar an soke shi da takobi, kawai sa ya dubi abokan tafiyar ya ce, "Ku zo mu ci gàba da tafiya..

Ba tare da jiran komai ba Saki Lafaru ya zare takobinsa ya nausa cikin dajin kamar zai iya tsinana wani abu. Da ganin haka sai shi ma boka Muzaffar ya mike tsaye ya yafito aljani Marhabul Zaurus da hannu ya take masa baya suka bi bayan Laffaru.

Ba tare da ɓata wani lokaci ba sauran gabadayan jaruman suka goya masoyansu a bayansu suka bi bayan su Muzaffar aka ci gaba da tafiya. Lokacin da boka Muzaffar ya fahimci cewar an iso farkon wannan daji na biyu sai ya ďaga hannu sama yana mai nuni da a dakata. Nan take kuwa kowa ya tsaya cak. Boka Muzaffar ya dubi jaruma Shadira ya ce, Ya ke wannan jaruma mai jarumtakar ban al'ajabi, ki yi sani cewa yanzu ne za mu shiga dajin da ke kadai ce za ki iya yi mana jagora har mu sami damar fita lafiya, sai ki zo ki wuce kan gaba domin bai fi taku goma ba ya rage mana mu shiga wannan daji.

Koda jin haka sai Shadira ta ciro Bakanta daga bayanuta. Wohoho! Ita dai wannan baka ta isa abin kallo, domin Baka ce ta musamman wacce mutum bai taɓa ganin irinta ba. Bakar, ta kasance katuwa ga tsawo ga nauyi, idan mutum bai cika sadauki ba ko daukarta ma ba zai iya yi ba, taɓe bakar kuwa sai karti biyar sun hada karfi suke iyawa. Amma wani abin mamaki da hannu daya jaruma Shadira ta rike wannan Baka, da hannu ďaya kuma sai ta zaro kibiyoyi ashirin daga cikin kwanson kibiyoyin da ke daure a bayanta ta ďana su akan Bakan sannan ta wuce kan gaba ta nufi cikin dajin cikin sanda da kalle-kalle tana duban kowacce kusurwa.

A wannan lokaci ko kibiya ce ta zo gilmawa sai Shadira ta ɓaro ta kasa saboda zafin namanta da iya saitinta. Sa'adda boka Muzaffar ya ga Shadira ta wuce kan gaba sai ya dubi sauran abokan tafiya ya ce "Kowa ya zauna cikin shiri. Ku sani cewa kokarin Shadira kadai ba zai kwace mu ba sai mun haɗa da namu kokarin. Gama fadin hakan ke da wuya sai shi ma boka Muzaffar ya zare tasa takobin ya bi bayan Shadira. Lafaru ne ke biye da shi rike da takobinsa, kai kace shi ma zai taka wata muhimmiyar rawar gani a gumurzun da za a yi, musamman idan mutum ya yi la'akari da kwarjininsa da kuma kirar jikinsa irin ta manyan sadaukai.

Nan dai sauran jaruman suka bi bayan Sarki Laffaru gabadaya aka nausa cikin dajin.
Sai da aka yi tafiyar rabin sa'a a cikin dari-dari da tsoro-tsoro, amma ba su ga wadannan mugayen Birirrika ba.

Kwatsam! Sai suka fara jin sautin giftawar Biririkan a sama kan bishiyoyi. Yif! Shif!! Shif!!! Da kuma dirarsu, jif! Jif!! Jif!!! Amma ko daya daga cikinsu basu gani ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin jaruman ke nan, domin sun fahinici cewa a ko yaushe Birirrikan za su iya saukar mikiya a kansu.

A wannan lokaci ne jaruma Shadira ta fusata ainun bisa rashin ganin Birirrikan, sai jin sautin giftawar tasu da dirarsu kawai. Nan ake Shadira ta yi amfani da basirarta da lissafin kwakwalwarta kawai sai ta harba kibiyoyinta izuwa saman wadansu bishiyoyi masu duhuwar ganyaye da ke gabas da yamma, kudu da arewa. Wato a cikin dakika goma sha shida ta harba kibiyoyi tamanin.

Ba zato ba tsammani sai suka ga Birirrika tamanin sun fado kasa matattu, wadannan kibiyoyi sun cake a cikin kirajensu.
Kaico! Rashin sani yafi dare duhu. Inda Shadira ta san bala'in da zai biyo baya sakamakon wannan ɓarna da ta yi wa Birirrika da ba ta yi ba. Fadowar wadannan Birirrika guda tamanin kasa ke da wuya sai kawai sauran Birirrika kimanin su dubu dari uku da doriya suka taho a sama gabadayansu suka yi yo kan su Shadira.

Nan fa aka kasa mugun tsere. Duk da tsananin gudu irin na sadauki Shaharan sai da ya raina kansa a wannan rana, domin ya kasa tserewa Birirrikan, har shan gaban gabansa suke in ba don ma Shadira na kado su ba da kibiyoyi da tuni sun yagalgala shi.
Lokacin da jaruman suka fahimci gudu ba zai tserar da su ba sai su ma suka fara amfani da makamansu suna yakar Birirrikan, amma sai abin ya wuce saninsu, domin ko biri daya sun kasa kashewa, kuma Birirrikan suna kawo musu sara da suka cikin tsananin karfi da tsafin nama. Yawan Birirrikan ne ya fara rikita su, tun suna iya kai martani har suka kasa, sai dai kokarin kare kai. Gashi ana cikin gudu ne. Har sai da ya zamana cewa jaruman sun kasa ma kare martanin sun fara faduwa kasa, amma sai suka rinka mikewa zumbur suna daďa ci gaba da gudu suna kare harin saboda juriyarsu da nacinsu. In ba don jaruman sun kasance masu matukar juriya ba da tuni an gama hallaka su.

Shi kuwa Sarki Laffaru, boka Muzaffar ne ya rinka kare shi. Lokacin da masifa ta kai masifa sai boka Muzaffar ya goya Sarki Laffaru a bayansa domin idan ya bar shi yana gudu da kansa wadannan Birirrikan za su iya hallaka shi a ko yaushe. Haka boka Muzaffar ya ci gaba da yaki yana goye da Sarki Laffaru. Ga nauyin sarki Laffaru a bayansa, kuma ga shi yana gudu yana kare mugayen hare-hare na Birirrikan. Hakika shi bala'i ba shi da dadi komai kankantarsa.

Tunda wadannan jarumai suke gumurzu a yakuna da dama da suka halarta a rayuwarsu basu taɓa tsintar kansu a cikin yaki mai tsanani ba irin wannan, domin ga shi dai suna iya kokarinsu amma sun kasa kashe koda biri daya daga cikin Birirrikan. Ita kanta jaruma Shadira da ta fara samun nasarar kashe su da farko, yanzu kuma al'amura sun sauya, domin koda ta same su da kibiyoyin sai ka ga sun ki fadowa kasa daga saman, sai dai kawai su sa hannayensu su zare kibiyoyin su ci gaba da kai mata mugun hari, duk da cewa jini na бulɓula a jikinsu.

Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinta kenan ta gane cewa lallai shayi ba ruwa ba ne. Ana cikin haka ne Biririkan suka fusata ainun da irin ɓarnar da Shadira ke yi musu, don haka sai suka afka mata su da yawa kimanin su dubu saba'in a lokaci guda da nufin su yagalgala ta su yi filla-filla da sassan jikinta yadda wani ma daga cikinsu ba zai sami koda tsoka daya ba daga jikinta.

Koda Imran ya hango abin da ke shirin afkuwa sai ya kwarara uban ihu ya daka wawan tsalle sama, bisa sa'a sai ya dira akan wuyan daya daga cikin Birirrikan da suka lulluɓe ta, ya dankara masa duka da sanda aka. Take kwanyar kan birnin ta tarwatse ya sulale kasa matacce.

Cikin zafin nama Imran ya bar kansa ya dira akan wani ya ci gaba da yi musu rotse a ka. Nan da nan ya tarwatsa gaba dayan wadannan Birirrikan da suka yanyame Shadira, a lokaci guda wanda tuni sun kai Shadira kas har sun yi mata rauni biyar a jikinta da kaifin faratansu tamkar da kaifin takobi aka yanke ta, har jiri ya fara dibarta.

Yaro Masnur da ke goye a bayanta yaji ciwo a kansa jini na zuba har ma ya suma. Koda ganin wannan hali da Shadira ke ciki kuma ga shi yana goye da mahaifiyarsa a bayansa wacce ita ma ta ji raunika a jikinta sakamakon yawan faduwa kasa da suke yi ta fita daga haiyacinta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, zuciyarsa ta fusata, kawai sai ya sungumi Shadira ya goyata a kirjinsa ya daure ta tamau da wani rawani nasa sannan ya ci gaba da yakin a haka ya zamana cewa rai uku yake dauke da su shi kadai.

( WATO SADAUKI IMRAN YA CIKA GWARZON NAMIJI)

A haka yake yakin kuma yana gudu bai fasa ba yana ragargazar birirrikan ta sama da kasa. Wohoho! Idan maza sun kai maza dole ne ka ga suna jarumtaka ta ban mamaki. Shi kansa sadauki Imran ya yi mamakin ganin yadda ya iya yin wannan jarumtaka, domin bai taɓa yin kamarta ba a rayuwarsa. Sai ga shi yana samarwa da abokan tafiya hanya da karfin tsiya fiye da kokarin da Shadira ta yi da farko. A wannan lokaci Shadira ta fita daga haiyacinta matuka, amma tana iya ganin fuskar Imran dishi- dishi a gabanta kuma tana jin nauyin dan uwanta Masnur a gadon bayanta.

Haiman, Rahila, Zarina, Shaharan da boka
Muzaffar kuwa, a wannan lokaci duk sun shiga cikin wani irin mugun hali domin ta kai cewa an birirrikan sun fara samun nasarar yi musu rauni. Boka Muzaffar an soke shi da tsinin farce a gefen cikinsa, wajen ya bule jini na zuba, amma sai yai sauri ya sa tsumma ya toshe бular kuma ya daure wajen tamau ya ci gaba da gudu a haka yana kare harurruka duk da cewar jini bai fasa digaba daga cikin 6ular ba.

In ba don tsananin juriya da jarumtakarsa ba da tuni ya fadi kasa domin shi ma jiri ya fara dibarsa. Su kuwa su Haiman babu wanda Birirrikan ba su sare shi ba a kafa, hannu da kafada, har jan kafafunsu suke suna kasa gudu sosai, amma saboda naci sun ki yarda su fadi kasa domin sun san cewa suna faduwa za su zama gawa abincin Birirrikan.

Babu abinda zai baibwa mutum tausayi face ganin yadda gaba dayan jaruman suka jigata ainun ya zamana cewa babu sauran wani gwani a cikinsu, kuma babu wanda ke da tabbacin zai tsira da rayuwarsa. Lumaira da ke goye a bayan mijinta tana jin yadda yake ihu idan an sare shi ko an soke shi har jini na fantsamuwa a fuskarta, sai ta fashe da kuka, ta yi nadamar baro gida bisa cikar wannan buri da ke gabansu. Duk da cewa ba ta iya ganin zahirin abin da ke faruwa.

Shi kuwa Sarkin Farisa da ke goye a bayan 'yar uwarsa Zarina, lokacin da ya ga jikin 'yar uwarsa ya yi fata-fata da jini da raunika, sai shi ma ya kama kuka saboda tsananin tausayinta. Hakika dan uwa rabin jiki ne. A duk sa'adda wadannan Birirrikan suka kawo sara ko suka za su sami Sarkin Farisa da zarar Zarina ta ankara kuma ta ga ba za ta iya kare hare da makaminta ba sai ta juya baya a sami jikinta. Sai dai ka ji ta kwalla ihu ta durkushe kasa, amma kafin Birirrikan su sake lulluɓe ta sai ka ga ta sake mikewa ta ci gaba da gudu da artabu

Lokacin da aka kara shafe wani lokaci ya zamana cewa Zarina ba ta iya ci gaba da gudu sai tafiya tana tangadi kamar wacce ta sha giya ta bugu sakamakon yawan jinin da ke zuba a jikinta, jiri na dibarta. Ana cikin haka ne wani Biri ya make ta da tafin hannunsa a fuska. Saboda karfin dukan da ya yi ma ta sai da tayi katantanwa sau uku sannan ta kife kasa da rub da ciki a cikin mugun yanayi, tana gani dishi-dishi.

Wannan Biri sai ya dira a gabanta da nufin ya cisge wuyanta da wuyan dan uwanta Sarkin Farisa da ke goye a bayanta.

Ba zato ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login