Showing 6001 words to 9000 words out of 75493 words
Chapter 3 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
sai ta daka wawan tsalle daga inda take ta dira a inda Imran ke kwance da nufin ta dauke shi, da yake zafin naman Maridin ya fi nata, sai ya sami nasarar kartar hannunta a lokacin da ta sami nasarar janye Imran har ya juyo da fuskarsa ya ga irin ceton da ta yi masa. Nan take hannun Shadira ya dare jini ya yi feshi, itama ta kwala ihu kuma ta fadi kasa a galabaice. Koda Imran ya ga yadda Shadira ta ceci rayuwarsa kuma ya ga abinda ya faru gare ta, sai ya fusata ainun ya daka tsalle sama tamkar an cilla shi daga cikin baka ya narkawa wannan maridi sanda aka. Take kan maridin ya tarwatse ya kife a kasa matacce.
Koda ganin haka sai Imran ya buďu baki ya buɗe muryarsa gaba daya ya yiwa sauran abokan tafiya bushara da su yi kokarin dukan kan maridan domin anan lagonsu yake. Kamar maridan sun fahimci abinda Imran ya fadawa 'yan uwansa sai suka daina sunkuyo da kawunansu. Nan fa bala'i ya kai bala'i, masifa ta yi masifa, turnuku ya kara tsanani. Zarina na cikin yin zilliya a karkashin maridan sai wani maridi ya tarfa ta ya naushe ta a kirji ta baje a kasa tana numfashi sama- sama, kuma tana gani dishi-dishi. Kawai sai maridin ya daga kafarsa zai tatsileta. Cikin bakin zafin nama Shaharan ya janyeta daga kasan amma kafin ya bar wajen kafar maridin ta take tasa kafar, fit sai babban dan yatsansa ya fice ya tsandara ihu, amma saboda juriya bai yarda ya fadi ba sai ya sungumi Zarina ya goya ta a bayansa ya ci gaba da gudu a tsakankanin maridan. Sai da aka shafe sa'a guda cur ana wannan bakin gumurzu ya zamana cewa babu wanda maridin ba su yi wa rauni biyu zuwa uku ba face Sarki Laffaru da kuma 'yan uwan jaruman wadanda dama tuntuni su tsoro ya sumar da su. Shi kuwa Laffaru don ya бuya ne a kasan boka Muzaffar wanda shi ma tunda ya suma bai farfado ba. A wannan lokaci ita kanta Rahila ta gaji ainun har ta fara sarewa ta sallama cewa lallai duk hallaka za su yi.
Sadauki Haiman ma ya karaya, domin ta kai cewa da kyar yake iya ci gaba da tarwatsa maridan kuma ga shi tunda maridan suka kewaye su a waje daya ake ta gumurzun sakamakon ihu da maridan suke ta yi ba su fasa ba. A wannan lokaci aljani Marhabul Zaurus ne kadai bai gaji ba, amma shi ma ya san cewa in dai aka kara 'yan dakiku a haka shi ma ba zai kai labari ba Lokacin da aljani Marhabul Zaurus ya ga mutuwa muraran na shirin afko masa sai ya tuna cewa shi aljani ne yana da fuka-fukai da zai iya tashi sama ya dunga dukan kan maridan, kawai sai yai kundunbala yai sama yana mai surar sadauki Haiman da gimbiya Rahila suka kama shawagi akan maridan suna saran kawunansu.
Ai kuwa sai ga shi maridan na zubewa kasa matattu kamar ana sassabe a gona. Damar da suka samu ke nan suka sauko kasa cikin zafin nama suka kwashe, dukkan abokan tafiyar tasu sannan suka ci gaba da ragargazar maridan.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin maridan kenan domin su kansu ba su taɓa shiga bala'i ba irin na wannan rana domin ba su taɓa haduwa da shaidanun da har suka sami damar iya hallaka koda daya daga cikinsu ba. Ya yin da maridan suka ga mummunar 6arnar da aka yi musu kuma ana daďa ci gaba da yi musu sai suka fara guduwa suna shigewa cikin ramukan da suka firfito. Kafin a jima wajen ya zama babu irinsu face matattunsu. Koda ganin hanya ta samu sai farin ciki ya kama su Rahila, nan take Rahila ta umarci aljani Marhabul Zauwas da ya yi sauri ya kai su karshen iyakar wannan daji inda za su iya tsayawa su yi jinyar raunikansu ba tare da fargabar kada maridan su sake kawo musu farmakin sumame ba.
Nan take kuwa aljani Marhabul Zauwas ya cika wannan umarni bai sauka a ko ina ba sai a gaban wata korama da ke karshen dajin Maridai!
A wannan lokaci ne Sarki Lafaru ya tsugunna a gaban boka Muzaffar ya kara kunnensa a dai-dai hancinsa sai ya ji yana numfashi, cikin tsananin farin ciki Sarki Laffaru ya ruga cikin wannan korama ya debo ruwa ya watsa wa Muzaffar nan take Muzaffar ya farfado daga dogon suman da ya yi yana mai ajiyar numfashi. Nan dai aka watsawa duk wadanda suka suma ruwa suka farfado.
Koda Zarina ta dawo haiyacinta sai ta je gun Shaharan ta durkusa a gabansa ta dube shi cikin tsananin mamaki ta ce, "Me ya sa ka sallama rayuwarka domin ceton tawa?". Da jin wannan tambaya sai Shaharan ya yi murmushi ya ce, "Zuciyar da ta kamu da soyayyar gaskiya ba ta shakkar mika rai da jikinta ga abin kaunarta?".
Koda jin wannan batu sai Zarina ta turbune fuska ta ce, "Kaiconka ya kai wannan jarumi...Ina mai shawartarka da ka yi kokari ka goge wannan kauna daga cikin zuciyarka har sai izuwa lokacin da bukatarmu ta biya muka sami abin da muka je nema akogon Darul Iksina, amma daga yanzu har izuwa wannan lokaci ba za ka sami amincewar abin da kake so ba. Na yi matukar bakin ciki da ka rasa babban dan yatsanka na kafa guda daya, amma idan har ba ka sami muradin zuciyarka ba ina yi maka fatan samun madadinta. Koda gama fadin haka sai Zarina ta mike tsaye ta koma inda take.
Shi kuwa sadauki Imran lokacin da ya dawo cikin haiyacinsa sai suka kama kallon-kallo tsakaninsa da Shadira. Ga shi dai ya san cewa ta ceci rayuwarsa kuma yana son ya yi ma ta godiya, amma sai ya kasa.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga yi wa masu rauni magani. Mahaifiyar Imran da kanta ta sawa Imran magani. Koda ta ga yadda ya samu manyan raunika sai ta fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar dungunzuma hankalin Imran ke nan ya rike kafadunta suka fuskanci juna sannan ya ce, "Ya ke Ummina ina dalilin wannan kuka naki?"
Koda jin wannan tambaya sai mahaifiyar tasa ta yi ajiyar zuciya gami da goge hawayenta sannan ta ce, "Ya kai ďana, ka yi sani cewa ba wani abu ba ne ya sa ni wnanan kuka ba face ganin yadda ka sami wadannan raunika saboda kawai ka cika mini burina. Hakika wannan tsautsayi da ya same ka ya sa na yi nadama bisa neman maganin nan. In da na san cewa wannan tsautsayi zai same ka da na hakura da wannan bukata tunda dai ni na tsufa, ba lallai ba ne na kara shekaru masu yawa a duniya".
Koda jin wannan batu sai kwalla ta ciko a idanunsa ya rungume mahaifiyar tasa yana mai cewa, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa raina da lafiyata ba a bakin komai suke ba muddin zan sami damar faranta miki rai. A duk sa'adda na tuno irin tsananin wahalar da kika sha a kokarin ganin na rayu sai na ga cewa har abada babu abin da zan yi miki na saka miki da shi. Ya za a yi na kasa yin wannan tafiya alhalin na san cewa ba ki da burin da ya fi ki ga kin mike da kanki kin taka kafafunki? Sa'adda Imran ya zo nan a zancensa sai mahaifiyarsa ta sake kankame shi a jikinta, a lokaci guda duk su biyun suka fashe da kuka.
Koda ganin wannan al'amari sai gaba dayan abokan tafiya suka kamu da tsananin tausayinsu. Wasu suka yi kwallah, wasu kuwa sai da suka zubar da hawaye.
A wnanan loakci Sarkin Farisa na sa wa gimbiya Zarina magani, lokacin da shi ma ya ga raunikan da ke jikin 'yar uwar tasa sai ya kasa ci gaba da sa ma ta maganin ya kama zubar da hawaye. Da ganin haka sai Zarina ta yi murmushi ta ce "Haba ya kai dan uwana akan wane dalili zuciyarka za ta karaya bisa abinda ya samevni? Ka sani cewa farin cikinka farin cikina ne, haka ma bakin cikinka nawa ne. Har abada ba zan taɓa samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba face na ga ka yi aure har ka haihu, sannan ne ni fa zan fara tunanin yin auren.
Ka tuna cewa tun muna yara da muka taso tare komai a lokaci guda muke yi, wani ba ya riga wani, don haka har abada ina kan wannan baka ba zan sauya ba.
Lokacin da gimbiya Zarina ta zo nan a zancenta sa sai Sarkin Farisa ya kara kamuwa da tsananin tausayinta ya ce, "Ya ke 'yar uwata rabin jikina ki ya sani cewa idan har kina son na yi aure to fa sai dai mu yi a rana daya Ina nufin a ranar da na sami lafiya. Idan kuwa ba ki amince da hakan ba to har abada ba zan yi aure ba. Koda jin haka sai hankalin Zarina ya dugunzuma ta yi shiru tana tunani, daga can sai ta lok daga kai ta dubi Sarkin Farisa ta ce, "Haba ya kai dan uwana saboda me za ka fadi haka? Sarkin Farisa ya ce, "Saboda na fuskanci cewa ko soyayyar ma ba kya so ki yi. Idan har za mu yi aure a rana guda dole ne ki nemi masoyi da wuri tun yanzu kafin lokaci ya yi domin hankalinki da shi ki tabbatar da soyayyarsa ta gaskiya yake yi miki ko saboda matsayinki yake yi miki ita ba. Tun a yanzu na fuskanci cewa kin sami wannan masoyi."
Cikin matukar mamaki Zarina ta dubi dan uwanta Sarkin Farisa ta ce, "Wa kake nufi?" Sarkin Farisa ya ce, "Wanda ya ceci rayuwarki dazu a can inda muka fafata da maridai, wato sadauki Shaharan. Tabbas sadauki Shaharan ya kamu da matukar kaunarki, kuma ta kauna ta gaskiya, domin inda da akwai algus a cikin son da yake yi miki da ba zai iya sallama rayuwarsa ba da ceton taki. Koda jin wannan batu sai jikin gimbiya Zarina ya yi sanyi, ta sunkui da kanta kas kuma ta yi shiru tana tunani. Daga can sai ta dago kai ta dubi Sarkin Farisa ta ce, "Ya kai dan uwana ka sani cewa na yi alkawari cewa ba zan taɓa yin soyayya ba face na ga ka sami lafiya Tabbas har yanzu ina nan akan wannan batu ba zan sauya ba, saboda haka zai fi kyau ka daina yi mini batun soyayya daga yanzu har izuwa lokacin da bukatarmu za ta biya.'
Da jin haka sai Sarkin Farisa ya ci gaba da sawa Zarina magani akan ciwonta, yai shiru bai kara cewa uffan ba.
A ɓangaren Lumaira da mijinta sadauki Haiman kuwa, lokacin da ta farfado daga dogon suman da tayi sai ta ji ta a jikin mijinta. Cikin dimauta ta rungume shi ta kama shafa jikinsa, ai kuwa sai taji ta tabo jini a wuri biyu.
Nan take hankalinta ya dugunzuma ta rasa abin da ke ma ta dadi. Kawai sai ta janye jikinta daga cikin nasa ta fashe da kuka. Cikin matukar tausayi Haiman ya ruko hannayenta ya danka mata garin magani ya ce, "Ya ke matata kukan me za ki yi kuma alhalin muna daf da samun biyan bukata? Kawai ki shafa mini wannan magani akan raunin da navji, domin ba komai ba ne face alamun masu tabbatar da cewa zamu sami nasarar samun abinda muka fito nema".
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Lumaira ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa zan iya zama da kai babu idanu har izuwa karshen rayuwata muddin zan rinka jin numfashinka a kusa da ni gami da koshin lafiyarka, duk da cewa ina matsayin makauniya. Ka yi sani cewa ba don komai na damu na warke daga cutar makanta ba sai dan kawai na ga irin fuskarka kafin ajálina ya riske ni, duk da cewa ina ayyana fuskarka a zuciyata. Da jin haka sai Haiman ya ji ya kara kamuwa da tsananin tausayinta. Kawai sai ya rungume ta ya kama zubar da hawaye.
Duk wannan abu da ke faruwa Shadira da Masnur sun nutsu suna kallon Lumaira da Haiman. Koda yaro Musnur ya ga abin da ya faru tsakanin Lumaira da mijinta sai shi ma ya dauki garin magani ya kama sa wa 'yar uwarsa Shadira a jikin raunikanta, yana yi yana zubar da hawaye. Ga shi dai akwai alamun cewa akwai maganganu a bakinsa amma saboda ba shi da bakin maganar sai yai shiru kawai. Lokacin da Shadira ta fuskanci halin da dan uwanta ke ciki sai ta fashe da kuka kuma ta rungume shi a kirjinta ta kamu da tsananin tausayinsa tana mai cewa, "Ya kai dan uwana kada ka damu da wannan matsayi da ka gan ni a ciki, domin ina ji a jikina cewar bukatarmu na daf da biya. Tabbas akwai alamun cewa zamu iya shan tsananin wuya a cikin wannan tafiya, wata kila ma wasunmu su rasa rayuwarsu, amma ni dai fatana shi ne ka sami lafiya, koda zan rasa rayuwa ta. Da jin haka sai yaro Masnur ya janye jikinsa daga cikin na Shadira suka fuskanci juna ya fara bayani a gare ta cikin yaren bebaye, wato amfani da hannu ya ce, "Ya ke 'yar uwata kin sani cewa tun da iyayenmu suka mutu kika ci gaba da kula da rayuwa ta ya zamana cewa ke ce uwata, kuma ke ce ubana. Babu wani mutum wanda na shaku da shi a duniya sama da ke. Yaya kike zaton zan kasance idan babu ke? Lallai idan kika rasa rayuwarki a cikin wnanan tafiya ni ma tawa ba ta da amfani, domin ba zan taɓa samun sukuni da kwanciyar hankali ba. Duk abincin da zan sa a bakina komai dadinsa ďaci zai yi mini. Yadda na ga rana haka zan ga dare, domin bazan iya rintsawa ba. A takaice dai komai na duniya zai dagule mini har bakin ciki ya haddasa mini cutar ajali. Da jin wannan bayani na hannu da Masnur ya yi mata, sai Shadira ta yi sauri ta janye jikinta daga cikin nasa suka fuskanci juna. Bisa mamaki sai ya ga ta yi masa murmushi sannan tasa hannu ta share masa hawaye ta ce, "Kwantar da hankalinka ya kai dan uwana, albarkacin kaunar da ke tsakanina da kai ba zan mutu ba a cikin wannan tafiya har bukatarmu ta biya mu koma gida lafiya. Sa'adda Masnur ya ji haka sai ya cika da farin ciki, fuskarsa ta cika da murmushi.
Ba shakka soyayya tana cikin litattafan yaki.
*********************
Al'amarin Shaharan kuwa, lokacin da ya ga Zarina ta ki yarda ma su yi wata magana duk da cewar ya ceci rayuwarta, sai hankalinsa dugunzuma ya rasa abin da ke masa dadi, domin shi hankalinsa dai ya san cewa ya kamu da tsananin kaunarta kuma ba zai iya sarrafa zuciyarsa ba ga barin abin da take so, amma da ya dubi dokinsa ya gan shi a raye sai zuciyarsa ta yi sanyi, ya ji, dadi a ransa, saboda ko ba komai dai har yanzu ya san cewa yana sa ran cewa ba tafiyar bazan yake ba yana kan tafarkin cika burinsa na duniya, wato zai ci gasar tseren doki ta duniya, zai mallaki dukiya irin wacce bai taɓa mallaka ba, kuma zai mallaki gimbiya Shalirat 'yar Sarkin birnin Hairil Salas. Koda ya zo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta ce da shi, "To wai shin me yasa yanzu kake son Zarina wacce a wannan tafiya ka hadu da ita, alhalin ga Shalirat can wacce ka shafe shekara da shekaru kana begenta da burin son aurenta?"
Koda Shaharan ya zo nan a zancen zucinsa sai ya kasa bai wa kansa amsa, kuma hankalinsa ya kara dugunzuma.
Sai da aka yi kwana hudu a bakin wannan korama ana jinya sannan kowa ya ji kwarin jikinsa aka yi shiri domin a shiga wannan daji na biyu.
A wannan lokaci ne jikin boka Muzaffar ya yi sanyi ainun ya kasa cewa a tashi da sauri a tafi. Shi da ya kasance jagoran tafiya sai ga shi ya kasa mikewa tsaye ma bare ya wuce kan gaba a ci gaba da tafiyar.
Koda ganin haka sai Sarki Laffaru ya je gaban boka Muzaffar ya tsugunna suka fuskanci juna ya ce, "Ya kai wannan boka, ka yi sani cewa gabadayanmu nan jikinmu ya yi sanyi bisa ganin yadda kai ma jikinka ya yi sanyi a cikin wannan tafiya. Shin ka fitar da tsammani ne bisa samun nasararmu?"
Sa'adda boka Muzaffar ya ji wannan tambaya sai ya sunkui da kansa kas yai ajiyar zuciya, kuma yai shiru kamar ba zai ce komai ba.
Daga can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki Laffaru cikin alamun tausayawa, kuma cikin sauke murya yadda babu wanda zai ji abin da yake fadi face Laffarun, ya ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa tun a baya sa'adda muka keta ta cikin wannan daji mai mugayen aljanu rukuni na uku zuciyata ta karaya ga samun nasararmu.
Ka tuna da irin tsananin wahalar da muka sha sa'adda muka riski rukuni na biyu da na ukun wanda in ba don jaruma Rahila ba da tuni gaba dayanmu mun hallaka. Yanzu kuma da muka shigo cikin daji na farko daga cikin guda biyar waɗanda daga su sai kogon Darul Iksina, na ga wannan masifa da muka shiga sai na tabbatar da cewa babu mai isa kogon Darul Iksina face mai tsananin NISAN KWANA.
Ka sani cewa bala'in da ke cikin ragowar dazuzzukan hudu yafi na wannan daji na farko. Ni kam na yi matukar nadama bisa yi muku jagora a cikin wannan tafiya, domin a yanzu na tabbatar da cewa kunya zan ji domin na dora ku akan hanyar da ba za ta bulle ba. Koda boka Muzaffar ya zo nan zancensa sai Sarki Laffaru ya bushe da dariya. Al'amarin da ya matukar bai wa boka Muzaffar mamaki ke nan.
Lokaci daya sai Sarki Laffaru ya murtuke fuska ya ce, "Ya kai wannan boka, ka yi sani cewa shi bala'i kafin ya zo ne ake tsoronsa ko kuma ake nadamar tunkararsa, amma idan ka riga ka shige shi sai a rungumi duk abin da ya zo da shi. Ina tabbatar maka da cewa har a yanzu ba na jin