Showing 18001 words to 21000 words out of 75493 words

Chapter 7 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

ba don samun rauni ba, sai saboda tsananin firgita bisa ganin wannan gagarumar masifa da suka tsinci kansu a ciki wacce tafi karfin jaruman da ke kokarin kare lafiyarsu.

Nan dai ya zamana cewa babu sauran jarumi guda daya da ke tsaye a cikinsu face sadauki Imran, shi ma albarkacin iya sarrafa wannan sanda da ke hannunsa ne yasa ya kai labari.

Koda Tsuntsayen suka ga saura jarumi Imran shi kadai a tsaye yana fafatawa da su, sai suka ja da baya gaba dayansu suka tsaitsaya a sama cak! Cikin iska kamar hadin baki, kai kace hutawa suke. A lokacin ne shi ma jarumi Imran ya tsaya cak! Ya gyara tsayuwa rike da sandarsa gamgam da hannu biyu, yayin da jini ke satatowa ta kan gefen hannunsa na hagu sakamakon wani lafcecen yanka da ke kan kafadarsa.

Imran ya dudi gabadayan jarumai abokan tafiyarsa ya gansu gabadaya a kwance a kas cikin mugu hali kamar ma wasunsu sun mutu, domin babu alamar rai a jikinsu.

A sannan ne ya tuno da mahaifiyarsa, wacce ke goye a bayansa, kawai sai ya kira sunanta, ai kuwasai ya ji shiru. Cikin firgici! Ya taɓo kanta da hannunsa guda, sai yaji kan ya langabe alamar babu rai a tare da ita.

Cikin gagarumin fushi Imran ya takarkare ya kwarara uban ihu ya falfala da matsanaicin gudu izuwa kan wadannan Tsuntsayen da dukkan fushinsa da karfinsa da nufin a yi ta, ta kare ko shi ko su!

Ai kuwa su ma Tsuntsayen sai suka taso masa gaba dayansu suna yin wannan ruri mai iya kurmantar da bil'Adama, amma shi bai ma san suna yi ba.

Kafin ya hade da Tsuntsayen tuni ya daka wawan tsalle sama tamkar an cilla shi daga cikin baka ya tari Tsuntsayen ya hau dukansu da sandarsa a cikin bakin zafin nama da dukkan iyakar karfin dantsensa.

Bisa tsautsayi kuwa sai ya sami daya daga cikinsu Tsuntsayen a ido. Nan take idon tsuntsun ya fashe, ya sulalo kasa. Ji ka ke tim! kamar giwa ta fadi, don har sai sa dakasa ta yi girgiza. Tsuntsun ya baje matacce a kas ko shurawa bai yi ba.

Koda Imran ya ga ya sami wannan nasa ta gano lagon Tsuntsayen sai ya ci gaba da dukan idanun Tsuntsayen da sandarsa. Ai kuwa sai ga shi yana karkaɗosu kasa suna mutuwa.

Babu abin da zai yi matukar burge mutum a wannan gumurzu face yadda Imran yake daka tsalle sama tamkar fuka-fukai ne a jikinsa, wato a sama yaci gaba da gumurzun da Tsuntsayen. Wani lokacin ma sai dai ka ga yana tattaka Tsuntsayen tamkar yana taka matattakalar bene. Abinka da Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi, a hakan ne wasu Tsuntsayen suka rinka kai masa sara da suka.

Wani loakcin ka ga sun same shi jini na tsartuwa da feshi a jikinsa yana kwarara uban ihu, amma saboda bakin naci da dakewar zuciya da juriya shi ma bai fasa ragargazar su ba.

Abin da ya ayyana a ransa shi ne, koda wadannan Tsuntsayen za su kashe shi sai ya tabbatar da cewa shi ma ya yi musu muguwar бarna da yawansu tun da dai ya gano lagonsu.

Haka dai aka ci gaba da wannan mummunan artabu tsakanin jarumi Imran da mugayen tsuntsayen har izuwa tsawon sa'a guda, ya zamana cewa ya kashe fiye da kaso biyu cikin ukunsu, amma fa a wannan lokaci ya gaji ainun, har ba ya iya yin tsalle sama a kasa yake yakin.

Wani lokacin ma idan suka make shi sai ya baje a kasa kamar ya mutu, amma da zarra sun yi caa! a kansa za su yagalgala shi sai su ga ya mike zumbur! Ya ci gaba da ragargazar su tamkar ma a sannan ya fara yakin. Kai wani lokacin ma har lambo yake yi wa tsuntsayen ya yi kamar ya mutu, sai dai kawai su ga ya sake mikewa ya ci gaba da kashe su.

Su kansu wadannan mugayen Tsuntsayen a iya wanzuwarsu a cikin wannan daji ba su taɓa haduwa da takadarin bil'Adama mai taurin rai ba kamar Imran.

Koda Tsuntsayen suka ga Imran ya yi musu gagarumár ɓarna, kuma ga shi sun kasa kashe shi sai suka karaya, suka dauka cewa ba za su iya kashe shi ba, don haka ba shiri su duka suka yi sama suka luluka izuwa can kololuwar sama, suka bar nahiyar dajin gaba daya.

A dai-dai wannan lokaci ne Imran ya kama layi da tangadi kamar wanda ya sha giya ya bugu, sakamakon jinin da ke zuba a cikin sassan jikinsa. Bai ma san sa'adda sandarsa ta suбuce daga hannunsa ba.

Tabbas a wannan lokaci inda Tsuntsayen na kusa da salin-alin za su sa masa wawa su cinye shi, ko ruburbushin jikinsa ma ba za su rage ba, domin ba zai iya kare kansa da komai ba, saboda dukkan karfinsa ya kare.

Inda Tsuntsayen sun san cewa haka za ta faru da tabbas basu gudu ba! Nan take Imran ya kife kasa sumamme. In da ace akwai mutum tsaye a filin da aka yi wannan bakin gumurzu da dole ya ce kowa ya mutu, domin babu wanda yake numfashi daga cikin su Imran.

Wajen gaba daya ya yi kaca-kaca da jini da kuma gawarwakin wadannan tauntsaye abin ba kyan gani. Sai bayan kusan sa'a biyu lokacin da wata irin iska mai tsananin sanyin gaske ta fara kadawa sannan jaruna Shadira ta farfado ita kadai.

Tana bude idanunta ta ji gaba daya jikinta yai ma ta nauyi tamkar an danne ta da katon dutse, don haka sai ta kasa mikewa tsaye. Koda ta dubi filin yakin ta ga gabadayan abokan tafiyarta a kwance babu mai numfashi, sai ta fashe da kuka, domin a zatonta kowa ya mutu babu sauran mai rai.

Nan fa ta fara jan jiki tana tafiya a hankali da kyar har ta isa inda jarumi Imran ke kwance. Shadira ta dago da kan Imran ta ga baya motsi, kuma babu alamar numfashi a jikinsa, sai kawai ta rungume kansa a kirjinta ta dada fashewa da matsanaicin kuka na bakin ciki.

Ruwan hawayenta da ke zuba akan fuskara ne ye zamo sanadin farfadowarsa daga dogon suman da yayi. Nan take Shadira ta ji Imran ya rike kafadarta da hannunsa guda.
Koda ta ji haka ta gane cewa bai mutu ba sal ta bushe da dariya ta sake rungume shi a kirjinta cikin tsananin farin ciki. Shi ma sai ya kama dariyar murna. Sai da suka daďe a kankame da juna suna ta dariya kamar ba za su saki juna ba. Bayan sun dawo cikin haiyacinsu ne duk su biyun suka dubi sauran abokan tafiyarsu, suka ga cewa har yanzu fa su biyu ne rak! Suka mike, sai hankalinsu ya dugunzuma ainun.

Imran ya dubi Shadira a lokacin da hawaye ya subuto masa, ya ce, "Yanzu mu biyu ne rak ke nan muka tsira da rayuwarmu a wannan daji?" Koda jin wannan tambaya sai ita ma hawaye ya zubo ma ta ta ce, "Haka dai yanayi ya nuna, amma zai fi kyau mu tashi mu duba kowa, babu mamaki akwai sauran mai rai, domin kaicma na fitar da rai da kai, amma kuma sai ga shi ka mike".

Koda jin wannan batu sai Imran yaji ya sami kwarin zuciya gami da farin ciki. Kawai sai ya yunkura ya mike tsaye da kyar yana tangadi kamar ba zai iya taku daya ba. A haka ya nufi inda sauran abokan tafiyar ke kwance yana harde kafafu kamar zai fadi, domin har a sannan bai daina jin jiri ba.

Ita kuwa Shadira sai ta sake yunkurawa domin ta mike tsaye amma sai ta kasa.
Imran ya je kan kowa daya bayan daya ya girgizavsu amma har ya gama duba su duka bai ga mai alamar rai ba.

Koda ganin haka sai ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa ya fashe da kukan bakin ciki. Koda Shadira ta hango halin da yake ciki sai ta ci gaba da jan ciki har ta riske shi sannan ta kwanta akan kirjinsa ta ci gaba da tayavshi kukan.

Da ma Imran mahaifiyarsa ce wadda ya duba daga karshe don haka, yana kankame da ita yana ta kuka, a lokacin da ya ji ya tsani kansa, kuma ya tsani duniyar gaba daya. Bayan sun yi kuka har sun gaji sai Shadira ta dago da kanta daga kan kirjinsa ta dube shi ta ce, "Ya kai masoyina, wai shin yanzu mene ne amfanin rayuwarmu a doron kasa? Na rasa dan uwana Masnur, kai skuma ka rasa mahaifiyarka. Dukkan burinmu na duniya ya yanke. Yanzu ga shi abokan tafiyarmu kaf ďinsu sun mutu. Mene ne amfanin zuwanmu kogon Darul Iksina tunda wadanda za mu je dominisu babu su?

Sa'adda Shadira ta zo nan a jawabinta sai Imran ya sake fashewa da matsanaicin kuka, ya ce, "Hakika rayuwarmu ba ta da wani amfani, gwara ma ace mu ma duk mun mutu" Koda jin wannan batu sai Shadira ta yi murmushi ta ce "Ai kuwa ni yanzu farin cikin da ya rage mini a nan duniya kawai shi ne, na mutu akan kirjinka, ko ba komai na mutu tare da masoyina na biyu wanda na so shi fiye da komai. Ka sani cewa in ban da dan uwana Masnur da na rasa babu wanda zuciyata ta aminta da shi kuma take kauna da gaskiya sama da kai! Koda jin haka sai hawayen farin ciki ya zubowa Imran daga can kuma sai ya ce, ba shakka kin zo da shawara to amma ta yaya za mu mutu a tare ba tare da ďaya ya riga ďaya mutuwa ba?

Shadira ta, mu nausa cikin daji watakila mu haďu da wata muguwar dabbar, sai mu sallama mata kanmu ta cinye mu ko kuma mu nemi katon tsauni mu hau karshensa sai mu rukunkume juna mu sallamo kasa bisa duwatsu mu hallaka. Koda jin haka sai Imran ya ce, "Tabbas kin zo da shawara mafi kyau".

Nan take Imran ya ajiye mahaifiyarsa a gefe daya ya kura mata idanu sa'adda hawaye ya ci gaba da shatata bisa kan kumatunsa har izuwa tsawon 'yan dakiku, sannan ya ce, "Ya ke Ummina ki gafarce ni, hakika zan mutu da tsananin bakin ciki bisa rashin samun nasarar cika burin zuciyata.

Na so a ce na mutu akan hannunki domin na nemi gafararki bisa abin da na kasa cikawa, amma idan har akwai wata rayuwar bayan wannan na yi miki alkawari sai na cika miki burinki.. Haka dai Imran ya ci gaba da surutai barkatai ba tsari.

Koda Shadira ta fuskaci alamun yana neman zautuwa sai ta yunkura da kyar ta kama hannayensa suka mike tsaye tare ta jan shi suka kama dingishi suna tafiya har suka yi dan nisa da wajen.

Ai kuwa nan take suka yi arba da wani rami mai zurfin gaske a gabansu. Kawai sai suka dubi juna suka yi murmushi. Ba tare da jiran komai ba suka durfafi wannan rami ko kallon gabansu ba sa yi, sai kallon fuskokinsu suna yi wa juna murmushin karshe.

Saura taku uku kacal tsakaninsu da ramin sai kawai Imran ya ji an kwala masa kiran. Cikin dimauta da razani ya juyo baya. Koda ya ga wanda ya kira sunan nasa sai ya cika da tsananin mamaki gami da farin ciki mara misaltuwa. Ba wani ya hango ba face mahaifiyarsa tana rarrafe ta tunkaro su kuma hawaye na zuba daga idanunta.

Nan take Imran ya ruga da gudu izuwa gare ta ya sure ta ya rungumeta a kirjinsa. Shi da ita suka bushe da dariyar murna, ya kama sumbatar ko ina a fuskarta yana mai cewa, Ashe ba ki mutu ba ya Ummana, ashe ba ki mutu ba" Mahaifiyar tasa ta rike fuskarsa da hannayenta biyu ta ce, "Ya za a yi na mutu alhalin kana raye a doron kasa, kuma akwai alkawari a tsakaninmu?

Ya kai dana, kayi sani cewa na dade ina mafarkin cewa burinmu ya cika, ina tabbatar maka da cewa ban taɓa yin mafarki bai tabbata ba. Lallai ina ji a jikina cewa, komai wuya, komai rintsi sai na sami lafiya na taka kafafuna ka gani da idanunka. Koda mahaifiyar Imran ta zo nan a zancenta sai Imran ya sake rungume ta a kirjinsa ya fashe da kukan farin ciki, tana mai tayavshi kukan.

Jaruma Shadira da ke tsaye a can bayansu tana kallonsu cikin tsananin murna sai ta taho gare su ita ma ta rungume su ta taya su kukan farin cikin.

Ba zato ba tsammani sai suka ji motsi yai yawa a bayansu. Koda suka waigo sai suka ga ashe sauran abokan tafiyar su ne suka farfado daga dogon suman da suka yi daya bayan daya. Cikin tsananin farin ciki suka karaso gare su suna tashinsu zaune.
Nan fa aka shiga taimakon juna. Masu manyan raunika a jikinsu aka rinka dinke musu raunin, raunin da za a sa masa magani aka sa masa maganin.

Zarina ce ta dinkewa Shaharan manyan raunika guda biyu da ke jikinsa da hannunta, ita kuma dan uwanta Sarkin Farisa ya dinke nata raunin da kansa.

Lokacin da Zarina ke dinkewa Shaharan rauninsa ne Sarkin Farisa ya lura da cewa Zarina da Shaharan suna satar kallon juna suna murmushi, don haka sai ya gane cewa lallai akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu.

A iya sanin da Sarkin Farisa ya yi wa Zarina ba ta taɓa koda taɓa wani da namiji ba face shi, kuma bai taɓa ganin ta yi wa wani murmushi ba sai shi, amma yau gavshi ta damu bisa ranin da ke jikin Shaharan har ta yi masa magani da hannunta, kuma tana yi masa murmushi.

Koda Zarina ta ga cewa dan uwanta ya fuskanci tana son Shaharan sai kunya ta kama ta kuma hankalinta ya dugunzuma, domin ta karya alkawarin da ta dauka cewa ba za ta yi aure ko soyayya ba face ta samowa dan uwanta maganin cutar da ke jikinsabCikin tsananin takaici da damuwa Zarina ta mike tsaye tsam! daga gaban jarumi Shaharan ta koma can gefe daya ta yi tagumi a yayin da idanunta suka ciko da kwalla tana mai bakin cikin saba alkawarin da ta yi.

A can gefe daya kuwa, gimbiya Rahila ce take sa wa Sarki Laffaru magani akan raunikan da ke jikinsa, ita kuma boka Muzaffar na sanya mata. Shi kuma aljani Marhabul Zaurus ne yake sa masa maganin. Abin da ya daurewa kowa kai a wajen shi ne aljani Marhabul Zaurus ya fi kowa samun yawan raunika a jikinsa a wannan bakin gumurzu da aka yi a daji na uku, amma kuma yafi kowa jure raunikan kuma da kansa ya yi wa kansa magani.

Dokin Shaharan kuwa, shi kadai ne bai sami rauni ko daya ba sakamakon kariyar da aljani Marhabul Zaurus ya ba shi, ya lulluɓe shi da dukkan fuka-fukansa, don haka duk harin da aka kawowa dokin akan Marhabul Zaurus yake karewa.

Lokacin da Sarkin Farisa ya ga 'yar uwarsa Zarina ta koma can gefe daya ta zauna sai ya dubi jarumi Shaharan ya ce, "Ya kai ma'abocin gudu, ka yi sani cewa kai ne saurayi na farko da 'yar uwata ta nunawa soyayya a duniya.

A dalilin son da samari ke yi mata, da yawansu sun hallaka bisa kamuwa da cutar begenta a zukatansu. A tunanina, har abada babu wani mahaluki da zai iya bai wa 'yar uwata farin ciki face ni kaina, amma yanzu na karyata kaina kuma na yi imani cewa kai za ka iya ba ta dukkan farin cikin rayuwa.

Na sani cewa ka dade kana begen 'yar Sarkin garinku a cikin zuciyarka, kuma ka baro kasarku ne domin ka yi gasar tseren doki ta neman auren 'yar Sakin naku.

Ina mai tabbatar maka da cewa 'yar uwata tafi 'yar Sarkinku kyau, ta fita karfin mulki da arziki. Ina ji a jikina cewa abu ne mawuyaci na rayu a cikin wannan tafiya tamu har burina ya cika, wato samo mini maganin cutar da ta addabe ni ta hana ni yin aure. Bisa wannan dalili daga yau na ba ka amanar 'yar uwata.

Idan har rai ya yi halinsa ina son ka aure ta domin ka debe mata kewa ta tunda kaivne za ka iya ba ta farin cikin da take samu daga gare ni. Ka sota, So na hakika, irin wanda dan uwa ke yi wa dan uwansa, ba wai So irin wanda saurayi ke yi wa budurwa ba.

Idan da hali ka So ta kamar yadda na ga mahaifiyar imran ke son danta Imran." Sa'adda sarkin Farisa ya zo nan a jawabinsa sai tausayinsa ya kama jarumi Shaharan har hawaye ya subuto masa nan take suka rungume juna. Shaharan ya ce, "Ni kuwa na yi maka alkawari lallai zan rike 'yar uwarka bisa amana da soyayya mara misaltuwa. Koda jin haka sai Sarkin Farisa ya kara Kankame Shaharan a kirjinsa yana mai yi masa godiya.

Bayan gimbiya Rahila ta gama sa wa Sarki Lafaru magani sai ya dube ta cikin mamaki ya ce, "Ya ke wannan ma'abociyar kyawu da jarumtaka, ke kuwa me ya sa kike nuna kauna da damuwa a gare ni?" Koda jin wannan tambaya sai Rahila ta bushe da dariya.

Al'amarin da ya bai wa Lafaru da boka Muzaffar mamaki ke nan. Rahila ta hade fuskarta sannan ta ce, "Shin ka manta ne cewa dukkan burina na duniya ya ta'allaka ne akanka? Kamar ydda naka ya ta'allaka akan auren gimbiya Ramlatul Siyam. Dole ne na fara nuna maka kauna tun a yanzu domin ta kowanne hali sai na aure ka sannan burina zai cika. Ni yanzu babbar matsalata shi ne, ba ni da tabbacin za mu isa can kogon Darul Iksina gabadayanmu nan a raye, domin na karaya bisa irin yanayin da muka tsinci kanmu a ciki.

Da farko dai na san cewa gaba dayanmu nan babu mai jarumtakata amma sai ga shi na kasa tsinana komai a cikin wannan daji na uku da muka shigo. Ko shakka ba na yi jarumi Imran ne ya kashe tsuntsayen nan kuma bai isa ya kashe su ba gaba daya ina kyautata zaton dai guduwa suka yi da suka ga barnar de yake musu ta yı yawa. Ku tuna cewa yanzu fa saura mugayen dazuzzuka guda biyu a gabanmu kuma masifar da ke cikinsu ta fi wacce muka wuce a baya."

Koda Lahira ta zo nan a zancenta sai jikin kowa yai sanyi kuma hankali ya dugunzuma aka yi tsit ana tunanin zuci. Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba.

Daga can sai sarki Laffaru ya dubi boka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login